Showing 9001 words to 12000 words out of 26773 words

Chapter 4 - Ido A Duhu Book Free Complete By billy S Fari.doc

ne". ta faWa cikin sigar lallashi tare da bayyanar da damuwa ?arara akan fuskarta, nan ma yafi minti biyar bai tanka mata ba gaba-daya duk tabi ta ruWe sai faman lallashinsa takeyi tamkar wani ?aramin yaro, iska ya furzar da iska ta baki kafin yace. "Mom wai kamar ni za'a tare wa hanya? Ni za'a ce a daka Mom saboda an gama renani". "Wait Umar Farouk duka kuma? kamar ya a dake ka? Ko ni dana haifeka tun kana ?arami ban taSa sa hannu na dake ka ba balle yanzu daka girma, waye yai wannan gangancin halama bai san kai ko Wan gidan waye ba? Bai san waye ubanka bane hala?" Momy ta faWa cikin Sacin rai tana kallonsa, ajiyar zuciya ya sauke kafin yace, "Zan sanar dashi in dai a makarantar yake, kuma ko yanzu nayi masa abinda gobe akace ya sake tsare mani hanya bazai yi ba, zan kuma cigaba da yi masa matukar yana a cikin makarantar nan sai nasa ya barta da ?afafuwansa, "No kar kayi haka Umar Farouk, kasan halin mahaifinka bazai taSa goya maka baya ba idan ka aikata hakan har wani abu ya taso daga baya, kayi hakuri ka ?yalesa ina ai ka ja masa kunne ko?" "Mom ki dubi abinda yayi mun fa?" Ya shafa gefen bakinsa inda ya fashe kaWan, Mom ta kallesa tace, "Na gani, amma garin ya hakan ta faru Umar Farouk? Ko faWa kukayi dashi ne?" "Kusan haka Mom ". "To kayi hakuri na tabbata kayi masa abinda yafi wanda yayi maka, don haka ka ?yalesa, ka tashi kaje ka watsa ruwa kafito ga abinci na shirya maka kaci, ta shi muje na haWa maka ruwan wankan amma don Allah wannan magana ta mutu anan na kashe ta kaji ko yarona?" Ta faWa tana shafa kansa cike da son lallashinsa, ba yadda Umar Faruk ya iya don duk zuciyarsa yana matu?ar son mahaifiyarsa, duk abinda zata hanasa ko yana sonsa ya hakura kenan, ya Wago kai ya yi ya kalli mom tare da ri?o hannunta yace, "Shikenan Mom na hakura wake amma, ba don haka ba da ya yabawa aya za?i". "Aikin kenan, Indai kaine nasan zaka iya fiye da haka tunda ba gudun abun magana kakeyi ba, yanzu kuma kai da waye Farouk?" Dady da fitowarsa kenan daga Sangaren Hajiya Hussaina uwar gidansa ya faWa yana ?arasowa cikin paloun ri?e da hannun Fauzah, Wago kai Umar Farouk ya yi ya gaishesa sannan ya mi?e zai fita, "Ina zaka je? Koma ka zauna". Dady ya faWa yana nuna masa wajen zaman daya tashi ba alamun wasa a fuskarsa, komawa ya yi ya zauna Dady ya ce, "Tambayarka nakeyi kai da waye kayi faWa?" "Ban san shi ba Dady". Umar Farouk ya faWa yana haWe rai, "Ai tun a office an kirani an faWa mani komai, yanzu kai abinda kayi dai-dai ne? Ka fasa masa glass Win mota sannan kayi faWa dashi saboda Wai ya tare maka hanyar fita sai kace gate Win na gidanku ne, to shi kuma fa daka tare masa hanya kaki bashi waje ya wuce sannan kuma ka fasa masa glass Win mota me zai ce Farouk? Baka fa san shi ba yanzu ta ina kake tunani zaka gyara wannan laifin daka aikata". "Dady shima fa yayi mani laifi, akan me zai tare mani hanya?" Umar Farouk ya faWa cikin Wan fushi tare da mi?ewa yabar paloun, Momy dake gefe tsaye tace, "Ka gani ko? Yanzu fisabilillahi daga faruwar abu har ansamu yan gulma an kiraka an faWa maka, kai kum kazo ka zauna akai ka yarda? Wlh ni narasa me yaron nan ya tare wa mutane, duka duka Farouk guda nawa ne da za'a tasa shi agaba haka, kazo ba bincike kuma ka rufesu da faWa". "Yau kika haifesa Maryam, nace yau kika haifesa! Wannan wace irin tarbiyya ce kike Wora yaronki akai? Shikenan yayi laifi baza'a yi masa faWa ba? A gabanki ina yimasa magana ya tashi ya tafiyarsa. gaba-daya kin Sata yaro da sunan soyayya sai abinda yaga dama yake? To baku isa ba daga ke har shi wallahi, bazai yiwu ya ri?a dauko mani magana ba a gari, kina kallo baya da abokanai sai mata amma kullum faWa kikeyi ai ?awayensa ne abokan karatunsa, to na gaji idan bazai yi karatun ba aure yake so ya fitar da mata nayi masa auren na huta.." Yadda Mom taga ran Dady ya Saci yana ta faman faWa ya sata yin shiru har ya gama sannan tace, "Kayi ha?uri, amma don Allah kana bincike idan aka faWa maka abu akansa, gabaWaya abun nan na tambayesa ya faWamun ba haka ya faru ba, shi wancan Win shiya fara shiga harkar sa..." Wani dogon tsaki Dady ya ja jin abinda take faWa haWe da mi?ewa yabar paloun, bai san har sai yaushe zata fara yarda da kuskuren Umar Farouk ba, ko sau dubu ya yi laifi itama sai ta karesa sau dubu, sashen sa ya nufa ita kuma Momy ta nufi na Umar Faruk da abincinsa data jere masa akan tray, ko data shiga yana wanka bai fito ba, ta sauke ajiyar zuciya tare da Wauke masa kayan daya cire daya watsar anan paloun ta gyara sannan ta fice daga Wakin, tasan tunda har ya shiga wanka to ya hakura, hakan ya sama mata natsuwa a zuciya tare da bata tabbacin ya sauko daga dokin fushin daya hau.
*****
A can Sangaren Ya Nu'aym kuma suna isa gida sashensa ya nufa ya shiga toilet ya yi wanka ya shirya cikin ?ananun kaya, yunwa yake ji sosai don haka yana gama feshe jikinsa da turare ya nufi palour, kana kallonsa kasan babu walwala a tattare dashi, a gefe Waya kuma bakinsa ya Wan kumbura inda ya fashe, fuskarsa ma da tayi ja har yanzu bata koma normal ba saboda hasken da yake dashi, Iyayensa ya tadda zaune a saman dining tare da Nu'aymah da itama har ta watsa ruwa ta fito shi kadai ake jira, wajen ya ?arasa ya jawo kujera ya zauna ba tare daya kalli Waya daga cikinsu ba yace. "Ummi barka da marece, Abba ina wuni?" Tare suka amsa masa da lafiya ?alau kafin Abban nasa da tunda ya doso wajensu yake kallonsa yace, "Nu'aym me ya jimaka a baki ne? Me ya samu fuskar ka haka?" Ba tare da Nu'aym ya Wago ba yace "Ba komai Abba". Ummi ce tasa hannu ta Wago fuskarsa idanuwanta suka sauka agefen da bakinsa ya Wan taso tace, "Karya kakeyi Nu'aym akwai abinda kake Soye mana, me ya fasa maka baki haka?" Ya Nu'aym da har ya zuba abincinsa ya samo ci yace, "Ummi ba komai nace". "Idan haka ne ya akayi naga fuskarta haka? Kafara Soye muna abu ko?" "Abba mun Wan yi faWa ne da wani yaro, shine har ya fasa glass Win motar Nu'aymah". "What!?" Daga Ummi har Abba suka faWa tare, Abba har yana mi?ewa tare da dukan dining table Win dake gabansa kafin yaci gaba da cewa, "Kaga matsalar ?asar nan ko? Shi yasa bana son zamanka anan kana mingling da yaran talakawa da basa martaba komai balle daraja sa, ya fasa mata glass Win mota sannan kai ma ya fasa maka fuska, to kai me kayi masa ne?" Nu'ayma yayi shiru bai ce komai ba yaci gaba da cin abincinsa, Nu'aymah ce ta da gaba-daya ta tattara hankalinta ga abincin da take ci tace.
"Abba shima ya fasa masa baki amma laifin ya Nu'aym ne, sai da nace ya ?yalesa kada ya biye masa amma ya?i.." "Ke dallah rufe mun baki shashashar yarinya". Ummi tayi saurin katse Nu'aymah tana ci gaba da cewa, "So kike yi ya zama sakarai kamar ke?". Abba da takaici ya gama rufewa yace. "Fadamun wane yaro ne shi? Na rantse idan na ganowa ko waye ubansa sai ya biya kudin wancan glass Win motar daya fasa, kai kuma ka haWa kayanka gobe ka koma wajen aikinka don banga ma amfanin zuwan nan naka ba". "Abba sai zuwa jibi zan wuce". Ya Nu'aym ya faWa yana ci gaba da cin abincinsa hankali kwance. Ummi ta Wago ta kallesa tace, "Ai da gobe da jibi Win duka Waya ne kawai ka koma hankalinmu zai fi kwanciya, upper month muna nan zuwa idan su Nu'aym sun kammala exam". "Amma Ummi ban gama abinda nake son yi ba, shikennan don Wan wannan abun ya faru duk sai kubi ku tayar da hankalinku? Gaskiyar Nu'aymah ne laifina ne, da ban biye masa ba da duk hakan bata faru ba, Please Ummi, Abba don Allah kubar wannan zancen, zuwa jibi zan koma kamar yadda na tsara". Yana gama maganar ya ture abincin gabansa ya mi?e ya bar wajen. Da kallo duka suka bisa cike da mamaki kafin Abba ya kalli Nu'aymah yace, "Ke Wan gidan waye suka yi fadan dashi?". "Ban sani ba Abba". Nu'aymah ta faWa don ita kam bazata iya faWar ko waye ba, Ummi ta maka mata harara haWe da cewa, "Baki sani ba halama ba Wan makarantar ku bane?" Nu'aymah ta langaSe kai tare da kallon Ummi sannan tace, "Yanzu Ummi Shikennan duk wanda ke cikin makarantar dole sai na sanshi? Please kubar maganar mana kamar yadda yace". "Anki abari shashasha da bata san ciwon kanta ba, wallahi kika kuskura na ga hannunki ga key Win motata sai na saSa maki". ta ?are zancen aWan hasale tare da mi?ewa yanar wajen itama ta koma palour, Abba ma bai iya cin abincin ba ya tashi ya fice daga gidan saboda dama cikin shiri yake zai fita...





ALLAH KA JIKAN IYAYENMU =?O?
[6/15, 3:18 PM] Qee's Queen=?x?: *IDO A DUHU*

? ? ? ?? *NA*

*BILLY S FARI* =؎?

Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9

? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 7.

Nu'aymah ma mi?ewa tayi ta nufi Wakinta, tana shiga ta tadda wayarta na ?ara da sauri ta ?arasa inda take ajiye agefen bedside ta Wauka ta Waga tana zaunawa bakin gado. "Hello Besty ykk?" Ta faWa bayan takai wayar a kunnenta, Janaam dake kwance saman katifar Wakinta irin ?atuwar nan da inches Winta zai kai girman gado ta sauke ajiyar zuciya tana cewa. "Alhamdulillah, ina kika shige Aymah inata kiranki baki Waga ba, wallahi na dauka wani abun ne ya faru da naji shiru baki Waga ba, ya jikin Ya Nu'aym?". "Yaji sauki ina sa ran ma ya fita don yanzu su Abbah suka gama faWa dashi wai ya koma gobe". "Injin ba saboda abinda ya faru bane?" "Kusan haka dai Besty, kin san shi Abbah yafi son zaman ya Nu'aym can ?asar UK, shine fa da ya ji abinda ya faru shi da Ummi suka ce lallai sai ya koma gobe, amma dai naji kamar yace bazai koma gobe ba sai jibi". "Allah ya kyauta Besty, ai abunne baiyi daWi ba, shiyasa kika ga bana shiga sha'anin Umar Farouk, infact ma ni na tsanesa wallahi". "Tofah! Da yai maki me? Ni fa mamaki kike bani Janaam, ban taSa ganin Umar Farouk ya shiga harkar wani ba tunda muke makarantar nan, kawai dai idan mutum ya shiga harkar sane bazai sha da daWi ba, kuma banga laifinsa ba saboda ko kece bazaki lumunci ari?a shiga gonar ki ba haka kurum dole ki dauki mataki". Na taSe baki don tuni na kwana da sanin ?awar tawa ta fada a soyayyarsa, cikin rashin gamsuwa da kalamanta nace, "Wannan duka bazai zamo hujjar wula?anta Wan adam ba, ai abun nasa ne idan kika lura Besty yai yawa wallahi, kai kenan ba?in rai da cin zarafin jama'a, ga ba?ar zuciya da muguwar Wabiar zama cikin yan mata sai kace Wa.." "Kinga ya isa haka, wannan rayuwarsa ce fa duka! Inaga kawai mubar zancen nan, bana son yi da mutum?" Nu'aymah ta ?are zancen kamar ta Wan ji haushi, na saki dariya haWe da cewa, "Ba wani yi da mutum kawai dai kice bakya son gaskiya". "Na ji Win, ya Mamah take?" "Tana lafiya ina Nihla mutuniyar?" Nu'aymah ta amsa mani da "Tunda muka dawo ban sakata a idanuwana ba, "Taya zaki sakata kina cin zalunta, gobe karfe nawa zamu fita?" "Karfe bakwai" Nu'aymah ta faWa, zaro idanuwa nayi haWe da cewa. "Lokacin ko bacci ban tashi ba, 8 fa zamuyi lecture?" "Idan bance maki haka ba bazaki fito da wuri ba har sai kinsa mun makara, yau ma ba don Allah ya taimaka malamin bai shigo kan lokaci ba da tsaf kin ja ya hana mu shiga". "A'a fa, yau ba laifi na kaWai bane hadda na Ya Nu'aym". Na faWa ina dariya don dama nasan zata yi wannan korafin, "Ehmm to shikenan zan faWa masa ko me kika ce".
Fira sosai mukayi da ita kafin muka yi sallama jin ankira sallah magrib. Tashi nayi na shiga toilet na Wauro arwala nayi sallah sannan na fita zuwa Wakin Mamah, samu nayi tana kitchen tana aiki na karSar mata ina cewa. "Sannu Mamah, tun Wazu nake son zuwa na ri?a maki aiki na tsaya yin waya da Nu'aymah". "In jin dai tana lafiya?" "Lafiya klw, gobe 8 muke da lecture Mamah in Sha Allahu tun bakwai da rabi zan fita". "Ba laifi, sai ki samu wani abunda zaki haWa sai ki tafi dashi tunda nasan ba tsayawa zakiyi nagama breakfast ba, akwai wrap Win samosa acikin fridge dana haWawa yayanki Wazu, ki Wauka ki haWa gobe idan kika tashi warming Winta kaWai zakiyi". Na amsa wa Mamah da to ina ?arasa kwashe tuwon dana isko tana tu?a wa, bayan na kammala na kwashi kayan abincin na kai akan dining na jere sannan na koma kitchen na soma haWin samosa Win don akwai komai a kasa, Mamah kuma ta shiga wanka, ina kammalawa na sakata cikin fridge na gyara kitchen Win tsaf sannan na dawo falo na zauna ina latsar wayata kafin Mamah tafito. Ya Jameel ne ya shigo bakinsa Wauke da sallama. Na amsa ina ajiye wayata gefe haWe da mi?ewa na karSi ledar daya shigo da ita a hannunsa ina yi masa sannu da zuwa, murmushi ya saki yana cewa. "Barka da hutawa auta". Don wata rana haka yake kirana kasancewar daga ni sai shi Allah yaba iyayenmu, mahaifin mu kuma ya rasu bayan na kammala secondary, lokacin kuma ya Jameel na wajen bautar ?asar sa, mutuwar mahaifin mu ta haifar da abubuwa da dama na kewa da kaWai ci atare damu, sai dai bata canza kyakkyawar kulawar da muke samu daga wajensa ba lokacin da yana raye kasancewar babu abinda muka nema muka rasa daga wajen Ya Jameel, tsaye yake sosai a kanmu ni da mahaifiyata, duk wani abu na jin daWi yanayi mana daidai ?arfinsa, baya taSa bari mu gani ga wani muyi sha'awa ba tare da muma mun mallaki abun ba, kama daga kan ci, abun sha da kuma suturar sawa don yana gama bautar ?asarsa a ma'aikatar da aka turasa Allah ya dubi maraicinmu suka Waukesa aiki, shi ya sama mani gurbin karatun gaba da secondary mai kyau kuma yake biya mani tare da Wauke duk wasu lalurorina na makaranta. Sau Waya bai taSa gajiya ba wajen bani kudin transport da sauransu har Allah ya hore masa abun hawa, lokacin ne kuma Besty tafara kaini da Wauko ni kasancewar ajin mu Waya kuma a anguwar mu Waya, ko kadan bai son alakar mu da ita kasancewarta yar gidan masu kuWi, a cewar sa baya so watarana tayi mani gori ko tayi mani wani abun da zai zubar mani da mutunci na don bazai lamunta ba, yaso hanani tafiya school tare da ita a motarta yace shi da kansa zai ri?a kai ni kuma ya Wauko ni, amma Mamah tace ya ?yaleni ai kamar rage masa aiki ne tunda shima aiki yayi masa yawa ba zaune yake ba, babu yadda ya iya dole ya ha?ura ya barni tare da ja mani kunne akan nadai rage shige masu, ni kuwa a nawa tunanin ba wani abu bane don tun muna ?anana tare muke da Besty iyayenta sun san gidanmu nima iyaye na sun san gidansu, sai dai ba kamar yanzu ba da sha?uwar mu tayi yawa.
Turo baki nayi jin abinda ya faWa ina buWa ledar dana karSa a hannunsa haWe da cewa, "Ni dai Ya Jameel kadena cemun auta, Allah da baba nada rai kasan na isa Mamah ta haifa mun ?ane ko ?anwa". "To ai dai ba'a haifa maki Win ba yanzu sai kiyi hakuri, ko baba nada rai tunda aka zo wannan lokacin ba lallai ne a haifi wani ba, don haka sai ki hakura tunda kece ?arama ki amshi auta". Mamah ce ta fito tana faWin. "Kara dai kam, saboda ni da ya'ya yanzu ai sai naka Jameel idan ka haifa ko kuma nata".
Nasan halin Mamah biye masa zatayi suyi ta tsokanata don haka sai kawai na wuce kitchen da ledar dana karSa hannunsa, fruit ne sai drinks masu sanyi, na cire drinks Win na Wauki fruit Win na wanke na gyara sannan na hado da drinks Win akan tray na kai saman dining, fira na isko sunayi da Mamah tana yi masa zancen aure yana cewa ta taya shi da addu'a Allah ya bashi ta gari wacce zata kula mashi damu ta kuma yi hakuri zama tare damu don bazai iya barin mu yaje yayi gini wani wurin ba muna nan, Mamah tace, ba komai indai ya dace da mata ta gari da zata kula mata dashi ita Alhamdulillah ta yi zaman ta anan Win, ni dama inda rayuwa aure zanyi natafi gidan mijina. Kaina na Wora a saman kafaWarta haWe da cewa, "Nifa Mamah bazanyi aure ba na fiso naci gaba da zama tare dake har ki binneni ko na binneki". Suka sa dariya ita da ya Jameel tana cewa, "Bana fatan hakan ai Janaam". Na turo baki cike da shagwaSa ina bubbuga ?afafuwa ?asa, Ya Jameel ya buWe baki yana kallona kafin yace. "Iyeee...idan aka ce maki auta kice ba haka ba, yanzu Mamah wannan abinda take yi maki kina wani shafa kanta idan ba auta ba wa zai yi hakan yaci duka? Ai in kika ga nadena ce maki auta to gaban 'ya'yanki ne, shima don kar su ri?a fadar hakan ne, sai dai su ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login