Showing 6001 words to 9000 words out of 21888 words
Chapter 3 - MUGUN MIJI BOOK COMPLETE by Hamida Sunusi Ahmad.docx
fitowa daga idanuwanta suka hau kwaranya,cike da mutuwar jiki da saddaƙarwa Fauziyya ta hau warware ɗaurin ɗankwalinta. Ta riga ta sani tinda ya shiga wannan yanayin babu wanda ya isa ya ƙwace ta ko da kuwa mahaifiyarsa ce ta zo. Hannayenta na masifar rawa ta ɗaga rigarta tin daga ƙasa ta hau cirewa. Tsaye ta yi a gabansa kanta duƙe kamar wadda mijinta da surukanta suka kama a ɗakin kwarto. Kallon tsayayyu kuma cikakkun ƙirjinta ya yi ya haɗiyi wani mugun yawu,faffaɗan ƙugunta mai ɗauke da manyan cinyoyi ya koma bi da jajayen idanuwansa yana kallo. Muguntar da ya shirya mata ce ta sanya shi fashewa da dariya kamar wani zararre. Hannu ya sanya ya zaro wayarsa daga aljihunsa ya kunna ya koma ya jingina da allon gadon. Bai sake kallon inda take ba. Ita kuwa jikinta ne ya ɗauki rawa kamar mazari,ji take yi kamar ƙafafuwanta ba za su iya ci gaba da ɗaukar gangar jikinta ba. A gajiye ta hau motsa ƙafafunwanta tana ɗaga su daga wannan zuwa waccan. Sai da Abbas ya gama abinda ya mayar ibada sannan ya ɗaga idanuwansa da suka sake rinewa suka koma jajaye ya ce.
"Zo nan."
Da ƙyar Fauziyyah ta ɗaga ƙafafuwanta ta fara takawa zuwa gabansa,hannayenta sun yi sanyi ƙalau kamar wadda ta taɓa ƙanƙara,sai zufa suke tsiyayarwa,zama ta yi a wajen da ta riga ta saba da zarar ya yi mata irin wannan kiran,hannu na rawa ta hau zare masa safar ƙafarsa,tana gamawa ta cire masa dogon wandonsa da rigarsa ta ninke su ta mayar inda take ajiyewa kafin washegari kuma ta wankesu. Ta na kammalawa ta koma saman gadon ta zauna a gabansa tare da sadda kai ƙasa. A wulaƙance Abbas ke bin surar jikinta da wani malalacin kallo. Hannunsa ya sanya ya ɗaga haɓarta ya na kallo,cikin sauri ta buɗe nata idanuwan ta na bin cikin idanunsa da kallo gudun kar ta sake yin wani laifin. Cike da mugunta Abbas ya hau sarrafa gangar jikinta da ta ya ke kira da 'Marar amfani' a koda yaushe......
[9/13, 7:34 AM] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: MUGUN MIJI.
RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️ ✨
PAGE 4.
Kwance ta yi kawai ta na jin duk wani bidiri da Abbas ke yi a kanta cike da mugunta da zalunci da rashin tausayi. Domin jin daɗin sa duk wani abu da zai faranta masa rai ya bashi nishaɗi shi ya dinga yi ko da kuwa ita zai zame mata azaba.Tsananin tausayin kanta ne ya sanya wasu zafafan hawaye gangarowa daga idanuwanta suka sauka a saman pillown da ta ɗora kanta. Kiran sallar magrib ne ya sanya Abbas haƙura ya ƙyale ta,domin kuwa ya tina da bai yi sallar la'asar ba. Kallonta ya yi ya ce mata.
"Ki shirya sauran na dare kuma."
Kuka ne ya kusan ƙwace mata,dan ta san babu abinda zai hana shi yin abinda ya furta sai ikon Allah. Dan haka dole ta yi haƙuri ta danne kukanta kafin ya fara yi mata masifa akan haƙƙinsa,se ka ce ita bata da wani haƙƙi nata da ya rataya a wuyansa.Cike da nishaɗi ya tashi ya zira gajeran wandonsa ya fito tsakar gida ya na miƙa. Barirah ce ta ɗaga labule za ta fita domin yin alwalar sallar magrib, ta na yin arba da Abbas sanye da gajeran wando ta yi saurin sakin labulen ta koma ɗakinta. Zama ta yi a kan kujera tare da zabga tagumi ta na jin tsana da takaicin Abbas na mamaye ranta. Tsaki ta zabga kafin ta ce.
"Jahilin banza da wofi kawai,da ma na sani da na gama girkina nayi wanka alwalar na yi gaba ɗaya,yanzu zai je ya ɓata lokaci nima ya ɓata min."
Ta na nan zaune ta ji ya ɗebi ruwa a bokiti ya shige banɗaki,cikin sauri ta miƙe ta fita da nufin ɗaukar buta ta yi alwalarta a gaggauce kafin ya fito. Fauziyyah ta gani a bakin ƙofar ɗakinta kwance kamar gawa. A guje ta isa wajenta ta na faɗin.
"Ke lafiya? Me ya same ki haka? Ko dai naƙuda kike yi?"
Girgiza kai Fauziyyah ta yi,a wahalce ta ce.
"Ruwa...ruwa zan...shaa Aunty."
Cikin sauri Barirah ta matsa kusa da randar da Fauziyyah ke zuba ruwa,ta ɗebo mata ta kafa mata kofin a bakinta,wani irin sha take yi wa ruwan kamar shi kaɗai ne abu mafi mahimmanci a rayuwarta. Ta na gama sha ta lumshe ido ta koma ƙasan ɗakin ta kwanta ta yi lamo. Tunda Abbas ya tashi daga jikinta take jin ƙishirwa,sai dai ta riga ta san ko mutuwa za ta yi ba zai bata ruwan nan ba,sai dai idan ta isa ƙiyama ta sha. Sanin hakan ne ya sa ta yi shiru har ya saka gajeran wandonsa ya bar ɗakin. Ya na fita ta ja doguwar rigarta ta mayar a jikinta. A hankali ta sauka daga gadon,da rarrafe da jan jiki ta iso bakin ƙofar ɗakin,sai ta fara jin jiri ya na neman ya sanya ta kwantawa a saman cikinta,cikin azama ta yi dabarar kwantawa a gefen ta na dama,ta na nan ta na ambaton sunan mai kowa mai komai ta ji motsin Barirah,farinciki ne ya mamaye zuciyarta,domin ta san ita ba za ta taɓa barinta a wulaƙance ta wuce ta ba.
Alwala Barirah ta yi idanuwanta na zubar da hawaye,ta na idarwa yana fitowa,ko ɗaga kai bata yi ta kalle shi ba ta bar wajen ta shige ɗakinta,sallah ta tada tana ci gaba da sharce hawaye. A sujjadarta ta ƙarshe sai da ta yi wa iyayenta da mijinta addu'a sannan ta yiwa Fauziyyah addu'a da fatan Allah ya kawo ƙarshen wannan zaman nasu ita da Abbas,domin a ganinta babu wani alkhairi da ke cikinsa,ba zai taɓa sauyawa ba.
A yanda ya ganta a sheme a tsakar parlour bai yi wani yunƙurin taimaka mata ba,sai ma ware ƙafafunsa da ya yi ya tsallake ta ya shige ɗaki,kaya ya sanya ya fesa turarukansa sannan ya tada sallah,caccaken kurciya ya yi ya sallame,cike da masifa ya koma parlour ya tsaya a saman kanta ya ce.
"Raguwar banza da wofi kawai. Ke wai yanzu sau biyun ne ya gajiyar dake tsabar rashin amfani? To ki buɗe kunnen ki da kyau ki ji ni,zamu haɗu dake zuwa anjima,dan haka gwanda ma ki miƙe ki ƙwarara jikin ki dan ba wai na samu abinda nake so bane,manage kawai na yi. Ni zan fita,ga wannan ki leƙa ki aiki yaro a siyo kalanzir ki saka a risho tinda dare ya yi kuma na ga itacen har yanzu da jiƙa ba lallai ki gama girkin da wuri ba,ni kuma yunwa nake ji sosai. Maza ki tashi ki dafa mana abinci,kar na dawo baki dafa komai ba."
A rikice ta tattaro ragowar ƙarfin da ya yi mata saura ta kalle shi ta ce.
"My king babu fa ƙwayar hatsi da ta rage a gidan nan,kuma na faɗa maka tin wancan satin abubuwa sun ƙare,ɗazu ma ban ci komai ba ku na juyewa duka."
Ji ya yi kamar ta watsa masa tafasasshen ruwa a fuska,a hasale ya daki ƙafarta tare da wara hannayensa ya yi mata daƙuwa sannan ya ce.
"Dan iyayen ki a gidan uban wa kika sanar dani abubuwa sun ƙare? Ko ni soko ne irin ki da zan manta abu mai mahimmanci irin wannan? Bari na mayar da ɗari biyu na za ta min amfani,kin san yanda zaki yi ki ciyar da kan ki. Ba kuma gwaninta kika yi ba da kika hana kan ki abinci kika bamu ni da abokaina,wannan neman suna da wajen zaman ba zai sauya kallon da nake yi maki ba."
Tsallake ta ya yi ya zari takalminsa ya bar gidan ya na ci gaba da masifa har ta dena jiyo shi. Kasa zubar da ko da hawaye ta yi domin ta ji daɗi a ranta. Wannan shi ne sakamakon soyayyar da ta samu a wajen mutumin da ta ɗauka ya fi kowa sonta da ƙaunarta a duniya. Murmushi ta yi ta yunƙura da ƙyar ta tashi. Ruwa ta ɗiba ta je ta dasa kujera a banɗaki ta yi wanka sannan ta fito. Sallar la'asar da be barsu sun yi ba ta gabatar sannan ta ɗora da magariba. Ta na nan zaune aka yi Isha'i,sai da ta yi Isha'i ta yi shafa'i da wutiri sannan ta kwanta a wajen ta na sauke ajiyar zuciya. Sallamar Barirah ce ta tashe ta zaune. Murmushi ta sakar mata sai ta ga idanuwan Barirah sun kumbura sun yi jawur,kwanon hannunta ta karɓa ta ajiye a gefe ta riƙe hannayenta ta ce.
"Don Allah Aunty ki dena damun kan ki saboda ni,ai bahaushe ya ce duk tsuntsun da ya jawo ruwa shi ruwa zai doka. Ni ce na jawa kaina duk abubuwan da Abbas yake yi min,ba dan komai ba sai dan soyayyar da na nuna masa,wadda har yanzu taƙi barin raina,ina jin son sa a cikin jini na wanda yake zaune a zuciya ta,ta yanda duk wani bugu da za ta yi sai ta harba min dafin soyayyarsa a sassan jikina. Kin ga kuwa dole na jure duk wani tukuici da yake bani."
"Ki gudu wajen ɗan'uwanki Fauziyyah,Abbas kashe ki yake so ya yi,ta ya zai bar mace da tsohon ciki da yunwa? Ga munanan kalamai babu lallashi ko tausayawa? Na gaji da ganin halin da kike ciki,idan har baki ɗauki mataki akan Abbas ba,mu zamu ɗauki matakin raba zuciyoyinmu da damuwa da tashin hankalin da kike ƙunsa a ƙarƙashinsa. Ki tashi ki ci abincin nan a gabana na wuce da kwanona,domin ni ba zan zauna zaman dafawa mara mutunci abinci ba kullum. Idan kika ga na bashi abincina to sai dai bashin zai kare ki daga zaluncinsa."
Murmushi kawai Fauziyyah ta yi,tabbas ta san kalaman Barirah akan gaskiya suke,amma yanayin yanda take aibata mata miji yana sukar ranta. Babu yanda ta iya kan dole ta ci abinci ta sha ruwa,Barirah ta wuce da kwanonta,cikin sauri Fauziyyah ta goge bakinta da brush sannan ta wanke hannunta da guntun sabulun wanki gudun kar ya gane. Zama ta yi ta na karanto ayoyin ƙur'ani da ka har Abbas ya dawo. Zaune ya tarar da ita ta sauya kaya daga wanda ta saka da rana,duk da cewa rigar ta koɗe sosai ta yi mata kyau,saboda ita ɗin kyakkyawa ce. Leda ya ajiye mata a gabanta sannan ya koma gefe ya ɗakko plate da cup ya zauna a kujera. Shayi haɗin kauri ya juye a cup sannan ya juye dankalin turawa da gasasshen kifi tare da soyayyan ƙwai a plate,sai ya kunce ledar bread ya fara aikawa cikinsa,ƙamshi da kyawun abincin da ya sa a gaba yana ci shi kaɗai ne ya sanya Fauziyyah saurin ɗaukan ledar gabanta ta sake furta masa kalmar godiya wadda ya ƙi amsa mata tin ta fari da ta yi masa. Ta na buɗewa ta ci karo da ruwan bunu da yankakken bread irin na wajen masu shayi da burodin nan. Ƙwalla ce ta taru a idanuwanta,sai kawai ta fasa ledar ruwan bunun ta dinga korawa a haka,domin ta riga ta san ko mutuwa za ta yi a gabansa ba zai lasa mata romon abinda yake ci ba,ballantana ya bata ta ci ɗin. Idan ta kurɓi ruwan bunun sai ya jima bai wuce a maƙoshinta ba saboda yanda yake ƙulle mata wuya da takaici. Tinda ta kalli Abbas sau ɗaya bata sake kallonsa ba har sai da ta ji ya yi gyatsa ya baje ƙafafuwansa har suna taɓo ta. Kallonsa ta yi ta ga ya rage kan kifin da guntun dankali da ƙwai,a ranta ta ji farinciki ya lulluɓe ta har sai da ta saki murmushi,da alama yau ƴan mutuncin na kusa kenan tinda ya rage mata,dan idan ya tashi irin wannan mugun halin nasa ko ya ƙoshi zai ce ta ajiye masa saura ta ɗumama masa gobe ya ci. Hannu ta kai za ta ɗauki plate ɗin ya buɗe idonsa guda ɗaya da ya lumshe,a hankali ya ware dika idanuwasa akan ta ya na binta da wani mugun kallo,cike da masifa da bala'i ya ce.
"To mayya baki na yi da za ki ɗaukar min?"
Kame-kame ta fara yi,cikin sanyin muryarta ta ce masa.
"Na ji ka taɓa ni ne da ƙafar ka,na zaci ka na nufin na ɗauka ne. To ka yi haƙuri don Allah."
"To ba nufi na kenan ba kwaɗayayyiya,tashi ki bar nan kafin na ɓalla ki. Marar godiyar Allah kawai,idan ba za ki ci abinda na baki ba ki zubar."
Da ƙyar Fauziyyah ta dafe ƙasa ta miƙe ta na jin yanda cikinta ya yi ƙasa sosai,ɗaki ta shiga ta adana bread ɗinta dan ta san zai yi mata amfani. Shi kuwa duk da ya ƙoshi sai ya sake baje ƙafa ya ci gaba da ɗurawa cikinsa. Ya na gamawa ya tashi ya wanke hannunsa,ko brush bai yi ba ya shiga bedroom ɗin,kwance ya ganta a yanda yake so,sai ya saki murmushi ya haye gadon.
Ita kuwa tana shiga ta hau yin duk abinda yake so,gudun kar ya tsamama mata jikinta fiye da yanda yake a wannan lokacin,ta samu waje ta kwanta ta na jiran shigar sa ɗakin..........
[9/13, 5:57 PM] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: MUGUN MIJI.
RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 5.
Tsananin azaba da gajiyar da Abbas ya tarawa Fauziyyah ne suka yi sanadiyyar sanya ta nannauyan bacci. Shi kuwa gogan bai kwanta ba har sai da ya lalubo brodin da ta adana saboda amfanin kanta,ya koma ya haɗa shayi da kayan tea ɗin da ya ɓoye a aljihun rigarsa. Zaune yake a gefen gado ya na kurɓar shayi ya na latsa waya,fuskarsa ɗauke da murmushi ya jiyo muryar Fauziyyah a cikin bacci ta na faɗin.
"Don Allah ku tafi dani zai kashe ni,Ummah na yi kewar ki da yawa,zan bi ku.......Allah ka shiga lamurana,Allah ka kuɓutar da ni daga zaluncin Abbas...Allah na tuba ba zan sake....."
Wani irin mahaukacin duka Abbas ya buga wa cinyarta da ke buɗe,a gigice ta farka daga nannauyan baccinta ta na sosa wajen tare da kwaɓe baki za ta yi kuka,sai da ya ajiye cup ɗin da yake shan shayi a ciki,ya ƙarasa tauna burodin da ke bakinsa sannan ya sa yatsansa a saman laɓɓansa yana zare mata idanuwansa ya ce.
"Yi min shiru munafuka,wato ƙara ta kike kai wa Allah kina bacci dan tsabar mugunta da munafurci ko? Fauziyyah wai me na tsare miki a duniya ne kike son ganin baya na?"
Hawaye ke zuba daga idanun Fauziyyah kamar ruwan korama mai gudana. Ita bata san lokacin da ta kai shi ƙara wajen Allah ba da yake faɗa akai,ta san dai tana bacci mai daɗi cike da mafarkin iyayenta ya ɗasa mata mugun duka a cinya. Tsawar da ya daka mata ne ta sanya ta girgiza kai ta na bashi haƙuri,cikin kuka ta ce.
"My king akan me zan kai ƙarar ka wajen Allah bayan auren soyayya muka yi ba na ƙiyayya ba? Don Allah ka yi haƙuri ba zan sake ba to."
"Ohh ba za ki sake ba to,watom ma ƙarya na yi miki ko? Fauziyyah ki fita daga idona na rufe,kar ki bari kaina ya juye na yi maki shegen duka a zo ana cewa kuma bani da mutunci,tom."
Ya yi ƙwafa ya haye gado ya kwanta ya na kaɗa ƙafafu tsabar masifa na cin zuciyarsa. Fauziyyah kuwa tin da ta farka sai ta kasa komawa bacci. Da misalin biyu na dare yunwa ta addabe ta sai ta hau duba bread ɗinta,babu inda bata duba ba amma bata gansa ba,sai guntun da Abbas ya rage da shayi kaɗan a saman ƙaramin table. Kallonsa ta yi ta ga ya yi bacci, ga uban munshari da yake ta ja,a hankali ta ja jikinta ta ɗauki cup ɗin ta hau shan shayin da guntun burodin,ta sani da safe ko da ta bari ma lalacewa zai yi,ba kuma sha ze yi ba,iyaka ya yi mata masifarsa da baya gajiya. Ta na gamawa ta yi niyyar tashi dan ta tsarkake jikinta,sai dai taku ɗaya zuwa biyu da za ta yi ta ji ruwa na bin ƙafarta,tare da ciwon mara mai tsanani. Cike da tashin hankali ta kalli Abbas da ke sharar bacci,cikin matsananciyar damuwa ta ce.
"Ya zan yi ni Fauziyya? Idan na tada shi yanzu na shiga uku,musamman idan ba haihuwar bace ba. Allah ka kawo min agaji."
Jiki babu ƙwari ta dafa gini ta shiga banɗaki,wanka ta yi sannan ta dawo ɗakin ta hau safa da marwa. Leɓenta ta dinga cizawa tare da jan gashin kanta,idan azaba ta yi azaba sai ta duƙa ta zuba salati ta hau nishi,da ta lafa mata sai ta miƙe ta ci gaba da sintiri. Ganin abun ba zai lafa mata ba ne ya sanya ta shiga ɗakin gabanta na masifar faɗuwa ta daki ƙafar Abbas a hankali,juyi ya yi ya koma baccinsa ba tare da ya buɗe ido ba. Sake tashin sa ta yi a karo na biyu,a hasale ya farka ya wurga mata mugun kallon da ya sanya ta duƙewa a wajen ta na nishi da ƙyar,cikin jin azabar naƙuda ta ce.
"Don Allah My king ka taimaka min zan mutu."
Hawaye ne suka fara zuba a idanuwanta,cike da hargowa Abbas ya ce.
"Yanzu Fauziyyah saboda tsabar iskanci ina bacci za ki tada ni ki sanar dani zaki mutu? To wahayi aka yi miki ko me? Ina ce ƙarata kika gama kaiwa wajen Allah ɗazu? To ki tabbata yanzu ma kin nemi taimako daga wajen Allah,dan ni bacci nake ji,gobe akwai inda zamu je da abokaina."
Daskarewa Fauziyyah ta yi a wajen da take a duƙe tsabar mamakin furucinsa. Ƙafarta ce fa ɗaya a duniya ɗaya a lahira ita da irin da ya dasa mata a mahaifa har ya isa girbewa,amma shi bashi da sauran imani da tausayin da zai kalle su da idanun rahama ballantana har ya taimaka musu. Da jan jiki ta fita daga ɗakin ta na gunjin kuka kamar ranta zai fita ta zauna a tsakar gida,jin kukanta ne ya sanya Barirah da Shehu fitowa tsakar gidan. Ganin halin da take ciki ne ya sanya Barirah rikicewa ta isa gabanta a guje ta tallabo ta ta na faɗin.
"Me yake damun ki Fauziyyah? Wannan dai kamar naƙuda kika fara