Showing 21001 words to 21888 words out of 21888 words
Chapter 8 - MUGUN MIJI BOOK COMPLETE by Hamida Sunusi Ahmad.docx
mugun kwaɗayinsa da take fama da shi na shekara da shekaru. Nishin da suka ji a ƙasa ne ya yi mugun tsorata su,sai dai suna dubawa sai suka ga Hajiya na kokawa da numfashinta. A gigice Fauziyyah da Abbas suka yi kanta suna rige-rigen taimaka mata. Ganin yanda idanuwan Hajiya ke ƙafewa ne ya sanya Abbas fita waje da gudu dan nemo abun hawa,ganin shi ya fita a guje da kukan Fauziyyah ne ya jawo hankalin mutane zuwa ɗakin,Aunty Khairi da Barirah na shiga sai suka tarar da Hajiya a sume,cikin sauri Aunty Khairi ta ce.
"Ku kama min ita mu kai ta mota na kaita asibiti."
Babu gardama Barirah ta samo wasu matan suka kama Hajiya suka kai ta motar Khairi suka kwantar,Barirah ce ta shiga gaba bayan sun rufe motar Khairi ta ja suka wuce asibiti. Suna tafiya Abbas ya dawo da ɗan sahu ya na ta yanka zufa. Cike da bala'i da masifa ya kalli matan da sukai carko-carko a cikin gidan suna maida yanda akai ya ce.
"Kai dalla malamai kowa ya wuce ya bar gidan nan gulmar ta isa haka." Dogon tsaki ya ja ya shige ɗaki, yana shiga ya tarar da Fauziyyah idanu sun yi mata jawur,alamar ta ci kuka ta gode Allah. Ta na ganinsa ta miƙe ta nufe shi ta ce.
"Yanzu su Aunty suka wuce da Hajiya asibiti a....."
Marin da ya wanke fuskarta da shi ne ya sanya ta gimtse sauran kalamanta,nan take bakinta ya hau zubar da jini,matan da basu ƙarasa fita bane suka hau faɗin.
"A yi haƙuri Malam Abbas."
A zafafe ya yi kansu kamar zai dake su,suka kuwa kwasa a guje ana rige-rigen barin gidan,banda ashar da fatali da kwanikan da mata suka ci abinci babu abinda Abbas ke yi. Sai da ya tabbatar ya kore su ya koma ɗakin ya na masifa kamar zai haɗiye harshensa ya ce.
"Idan wani abu ya samu Hajiya sai na yi shari'a da kaf zuri'ar ku da ta yi saura. Wanne shegen ne ya ce a ɗaukar min uwa a kai ta asibiti? Ko baki ga na fita samo abun hawa bane?"
"My king gani muka yi kafin ka dawo ta wahala,domin kuwa har ta suma a bayan fitar ka."
"To yanzu wanne asibitin suka tafi?"
"Ban sani ba nima."
Kaiwa da komowa ya fara yi a ɗakin. Sun jima a zaune kowa da abinda yake saƙawa Shehu ya dawo. Abbas na jin shigarsa gidan ya fita waje,a harzuƙe ya ce wa Shehu.
"Maza ka kira matar ka ka tambaye ta ina suka kai min uwata?"
Cikin rashin fahimta Shehu ya kalli Fauziyyah da ta fito tana gyara mayafin kanta,a sanyaye ta yi masa bayanin abinda ya faru,kallon Abbas Shehu ya yi,ji ya yi kamar ya shaƙe matsiyaci ya huce takaicin faɗar masa da gaba da ya yi,ai shi a zaton sa kidnapping ɗin Hajiyar Barirah ta yi,ashe ma taimakon ta suka yi yake wannan iskancin,sai kawai Shehu ya wuce ɗakinsu ba tare da ya ce wa Abbas komai ba. Idan Hajiyar ta ji sauƙi ta dawo lafiya shikenan,idan kuma sa'inta ne ya yi Allah Ya jiƙanta,dama ta gaji da halin ɗan nata. Ganin Shehu zai shige ɗaki ba tare da ya bawa Abbas amsa ba ne ya sanya Abbas ya cewa.
"Ka san Allah Shehu Usmanu idan baka kirawo matarka ta faɗa min inda suka kai min uwata ba sai na yi ƙarar ku gaba ɗayan ku."
"Idan ka tashi ka kai ni barikin ladi a kulle,mahaukacin banza mahaukacin wofi kawai."
Ɗaki Shehu ya shige ya na jin zuciyarsa na tafasa. Ji yake yi da yana da iko da Fauziyyah da ya raba auren ta da Abbas. Domin Abbas bashi da maraba da dabba. Halayensa kaf babu na tsinta. Suna nan zaune Aunty Khairi da Barirah suka yi sallama suka shiga gidan,fuskar su gaba ɗaya ta sauya. Leƙen bayan su Fauziyyah ta hau yi ta na neman Hajiya,sai dai shiru babu ita babu bayanin ta. A kiɗime Fauziyyah da Abbas suka haɗa baki wajen faɗin.
"Ina Hajiyar take?"
Kallon juna Barirah da Khairi suka yi,sannan suka maida kallon su zuwa ga Fauziyyah da ƙafafuwanta ke rawa da Abbas da idanuwansa suka firfito waje. Shehu kuwa jin tambayar da su Abbas suka yi ne ya sanya shi fitowa ya na mayar da botiran rigarsa da ya fara cirewa. Kallon sa ya kai wajen Barirah,nan take ya gano tsananin kiɗima da tashin hankalin da take ciki, cikin sauri ya nufi inda take,tana ganinsa ta fashe da wani irin kuka mara sauti. Nan take Fauziyyah ta zube a ƙafafuwanta jikinta ya ɗauki wata iriyar rawa. Shin me ya samu Hajiya ne? Idan wani abu mummuna ya samu Hajiya ina za ta saka ranta ta ji sanyi?
*Wai shin makaranta wacece Fauziyyah ne?*
*A ina ta haɗu da Abbas har suka ƙulla soyayya suka zamo ma'aurata?*
*Menene ya jawo wannan zazzafar ƙiyayyar da Abbas ke nunawa Fauziyyah?*
*Wanene Abdullah a wajen Fauziyyah?*
*Ina iyayenta suke suka bar Abbas yake gasa ƴarsu kamar balangu?*
*Me zai faru da Barirah da Shehu saboda yawan taimakawa Fauziyyah da suke yi?*
*Shin wacce rayuwa Fauziyyah za ta yi anan gaba ita da king ɗinta da ƴar lelensa Muhseenah?*
*Kuna son ku san ya labarin mugun miji zai ƙare? Ku saka 500 ɗin ku a 0006366584 nan. Sai ku tura shaidar biya ta 09031416423.*