Showing 18001 words to 21000 words out of 21888 words
Chapter 7 - MUGUN MIJI BOOK COMPLETE by Hamida Sunusi Ahmad.docx
kuwa ramar ta yi yawa? Matso kusa na zo maki da magani ingantacce wanda aka haɗa shi da kayayyaki masu inganci wanda ba sa cutarwa ko da bayan kin gama amfani da shi,za ki murje ki yi ɓulɓul kema ki juya mazaunan ki ki kaɗa ƙirjin ki gaban Oga da sauran mata yanda kike so ba tare da kin cutar da lafiyar jikinki ba. Ana shan wannan magani da Kunu ko fura,ko kuma Yghort.*
*2-Ke kuma matsalar zubewar nono da lalacewarsa tare da tamuƙewarsa kamar leda ke damun ki? Kar ki ce kin sha wancan da wannan kin gaji,taho ki gwada products ɗin mu mai abun mamaki domin samun confidence ɗin bayyana jikin ki a gaban oga.*
*3-Mummunar ƙiba mai haɗe da ƙaton tumbi da manyan kumatun da suka nitsar maki da hanci ciki ke damun ki? Ko kuwa irin ƙibar nan ce da ta maida ki kamar buhu babu gaba babu baya? Kar ki ji komai,domin kuwa na zo maki da ingantaccen maganin hausa wanda bashi da illa ga lafiyar jiki a farashi mai sauƙi cikin kwana uku zaki fara ganin sauyi,a kwana bakwai kuwa shape ɗin ki zai bayyana ki huta da nauyin jiki.*
*4-Kina son ki samu glass skin da an hango ki a ga yanda fatar ki ke haske da walƙiya tare da ɗaukan ido? Kema zo nan kar ki wuce na tanadar maki naki kayan da za su kyautata fatar ki.*
*5-Kina fama da matsalar ciwon sanyi mara jin magani? To ki zo na baki maganin da zai wanko maki shi,za ki gansa da idon ki yana fita kamar dusar awara,har ya wanke ruwan ni'imar jikin ki ya bayyana ki mori rayuwar auren ki.*
*Gaba ɗaya za ku iya samu na a wannan No 08038086083.*
Kasa fita Fauziyyah ta yi,sai ta ƙunshe kanta a ɗaki ta hau kumbura kamar wata shagwaɓaɓɓiyar yarinyar dake fushi da iyayenta. Barirah na kula da take-taken ta,sai ta yi banza da ita,ta ci gaba da sabgar gabanta. Tana gama tuwon dare ta zuba mata ta kai parlour ta dire,ko neman ta bata yi ba,ballantana ta jira sannunta ko kuma godiyar ta. Kafin Shehu ya dawo ta salla wanka ta ɗauki gayu da ƙananan kaya,sai ƙyalli da ƙamshi take bazawa. Kitchen ta je ta kwashe abincin su ta kai ɗaki ta jera sannan ta zauna ta ɗauki ƙur'aninta ta hau karantawa. Hayaniyar Abbas da ta jiyo tin daga tsakar gida baisa ta daina karatunta ba sai ma ƙara ƙarfin muryar ta da ta yi,saboda bata son jin me yake faɗa. Ta riga ta sanyawa ranta ko Fauziyyah ba za ta kula ba ballantana wani Abbas,domin babu wanda ke binta bashin bayani a cikin su,kuɗi ne dai sai ya fitar ya kashewa baiwar Allah,tinda haƙƙinta ne ba na wani ba. Cike da ɓacin rai Abbas ya sake dakawa Fauziyyah tsawa ya ce.
"Ba da ke nake magana ba dan uwarki? Uban wa ya sa ki sakin baki ki gayawa Hajiya baki da washing machine da iron da blender? An faɗa maki kuɗin banza ne da ni da zan siya miki duk waɗannan abubuwan da kika lissafa mata?"
Barirah na nan zaune jikinta na tsuma domin duk yanda ta so toshe kunnenta hakan bai hana ta jiyo hayaniyarsu ba. Cikin rawar murya Fauziyyah tace.
"Haba My king,me yasa kake yi min irin haka ne wai? Anya na cancanci wulaƙanci da cin mutuncin ka kuwa? Ni fa ba ni na faɗa mata komai ba,ita da kanta ta yi wannan tunanin kuma ta sanar da kai abinda take son ka yi min,wanda ya dace a ce ka yi min tin kafin wani ya ce ka yi ɗin. Sannan da ka ke cewa baka da kuɗin banza ba fa da kuɗin ka za ka siya min ba,da kuɗi na za ka yi amfani ka siya. Ina ce hakan dika rufin asirin mu....."
A harzuƙe Abbas ya kai wa bakinta duka sai da jini ya fito,yatsansa manuni ya nuna mata ya ce.
"Wato gori ma kike yi min har kike sanar dani a kuɗin ki za a siya miki ko? To shikenan zan siya miki duk abinda Hajiya ta lissafa,amma na rantse miki sai na lahira ya fiki jin daɗi a cikin gidan nan,sai kin gwammace kiɗa da karatu,sannan sai kin yi da kin sanin sawa na saya maki kayayyakin nan,idan ma wata ƴar iskar ce ke zuga ki to ki sani na kusan korar shegu daga gidan nan,na gaji da iskancin da matar nan ke yi min da gadara a cikin gidana da na gida da kuɗi na ba da kuɗin uban kowa ba."
Wasu irin zafafan hawaye na masifa da bala'in dake cin Barirah ne suka hau zubar mata a kunci. Lallai ba dan kada Shehu ya dawo ya ji labarin ta dambace da mijin wata ba,da babu abinda zai hana ta fita su ci uban juna ita da Abbas,sai dai a yi kare jini-biri jini ita da shi amma ba za ta yarda ya dinga zaginta ba har yana kiranta da ƴar iska. Ƙwafa ta yi ta share hawayenta sannan ta rife ƙur'anin ta hau addu'o'i. Ta na kammalawa ta tashi ta haye gado ta kwanta ta yi shiru ta na saƙe-saƙe a zuciyarta.
Fauziyyah kuwa kallon hanyar da Abbas ya bi ya fita daga ɗakin ta yi ta na ci gaba da risgar kuka kamar ranta zai fita. Kanta har wani sarawa yake yi kamar ana buga mata guduma. Dafe ƙirjinta da ya yi mata nauyi ta yi ta na jin iska ta yi mata kaɗan. A hankali ta miƙe tsaye ta kunna fanka kaɗan ta kwanta kanta na kallon sama. Ƙarar buɗe kwano ne ya tabbatar mata da Abbas na parlour babu inda ya je. Hawayenta ta share ta ci gaba da sauke nishin wahala a hankali. Shi kuwa zama ya yi ya jawo plate da spoon ya kwashi naman miya son ransa,ya buɗe tuwo leda biyu ya ci ya ƙoshi. Ruwa ya huda na pure water ya sha ya ƙoshi sannan ya miƙe a doguwar kujera ya kunna TV. Tashar da ake raye-raye na kudancin Nigeria ya kai ya na kallon mata tsirara-tsirara ya na gyaɗa kai kamar ƙadangare. A haka bacci mai daɗi ya ɗaukesa.
Lokacin da Shehu ya dawo Barirah ta labarta masa kaf abinda ya faru faɗa ya yi mata,ya ce da ta sani da bata yi hakan ba,domin garin taimakon Fauziyyar gashi ta jawo mata duka da zagin iyaye a wajen miji mara daraja kamar Abbas. Sannan nan gaba ba a san me zai yi mata ba. Jikinta ne ya yi mugun sanyi,nan da nan ta hau nadamar biyewa zuciya har ta zuga Hajiya akan Abbas ɗin,gashi yanzu ya saka ƴar mutane a gaba da azabarsa. Da dare ruwan sama aka lema musu mai yawan gaske,sai garin ya ɗauki sanyi sosai,dan haka Abbas na parlour a kujera bai san cewa Fauziyyah na ɗaki ta na fama da mummunan zazzaɓi ba,haka yarinyar ta dinga tsala kuka ba tare da ya ji ba ballantana ya leƙa su. Kafin safiya Fauziyyah ta fita hayyacinta ta yi zuru-zuru. Sai da aka fara kiran sallar asuba ta samu wani irin bacci mai daɗin gaske ya sace ta.
Washegari da asuba Barirah ta tashi da wuri ta ɗora girkin safe. Ta na gamawa ta saka ruwan wanka. Sai da ta zubawa kowa abincin sannan ta ɗauki nasu ta fara kaiwa ɗaki. Ganin ƙofar su Fauziyyar a buɗe sai ta yi zaton Abbas ya samu zuwa masallaci,shi yasa ya bar ƙofar buɗe,murmushi ta yi ta ce.
"Ohh yau wacce rana,dama shi ibadar ma kamar fushi yake da ita,lokacin da ya huce ya je masallaci,idan kuma yana dokin fushi sai ya fi wata bai leƙa masallacin ba. Allah Ya kyauta."
Kanta tsaye ta nufi ɗakin Fauziyyah,sai dai kafin ta ɗaga labulen ta jiyo munsharin Abbas ɗin,cikin sauri ta koma baya,kyaɓe baki ta yi ta ce.
"Kai jama'a,Allah ka shirya wannan bawa naka."
Kitchen ta wuce ta ajiye musu abincinsu wanda ta rabawa mazubi,saboda sanin halin mugunta irin na Abbas da haɗama da son kai,shi be ƙi a dinga kwashe masa naman miyar ba kaf ya zamo abincinsa shi kaɗai.
Abbas bai fito daga ɗakin ba har sai da tara na safiya ta buga,a wannan lokacin Barirah ta gama yanke hukuncin zuwa ta doka musu kofa,dan kuwa ruwan wankan da ta sake ɗorawa a karo na biyu ya kusa hucewa. Miƙa ya fito yana yi ya wuce banɗaki, yana shiga ta shige ɗakin sai ta tarar da Fauziyyah kwance bakinta ya kumbura,ga jaririya kwance tana bacci,miƙa hannu ta yi dan ta ɗauke hannun Fauziyyah dake kan jinjirar,sai ta ji hannunta da zafi zau,tausayinta ne ya kama ta,sai ta ɗauki yarinyar ta tashe ta. A hankali ta furta.
"Ki shirya ki shiga wanka,dan ruwan ma ya kusan hucewa,bari na je na yi mata wanka,idan kin fito ki ci abinci ki sha maganin zazzaɓi,Allah Ya baki lafiya."
Murya a dashe Fauziyyah ta ce.
"To Aunty na gode."
Barirah waje ta yi, ta na jin kamar ita ce sanadiyyar shigar Fauziyyar cikin wannan ƙunci da zazzaɓin da take ciki. Jiki a sanyaye ta yi wa yarinyar wanka,ta na shiryata ta tina kalaman Shehu kafin ya fita kasuwa.
'Ki tabbata kin bata haƙuri ko ta ji sanyi a ranta.'
Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi ta ƙarasa sanyawa yarinyar kaya. Ta na jin Abbas ya shiga kitchen ɗinta ya juye mata ruwan zafi saboda tsabar neman magana da gadara. Gyaɗa kai ta yi cike da takaici ta saɓa yarinyar a kafaɗa ta fita tsakar gidan. Kallon ta ya yi ya watsar ko nauyin abinda ya aikata bai ji ba,wanka ya shiga ya yi,sannan ya fito ya dangwarar da bokitin a tsakar gida ya shiga ɗakinsu. Har ƙasa Fauziyyah ta durƙusa ta gaida shi,sannan ta sake bashi haƙuri akan abinda ya faru jiya,ko kallon inda take bai yi ba,ballantana ta saka ran zai amsa ta.
Gajiya ta yi da durƙuson ta miƙe ta wuce zuwa wanka. Sai da ta gasa jikinta sannan ta yi wankan sabulu ta fito,ko da ta koma ɗakin ta tarar da ya cinye abincinsa sannan ya ɗebi nata ya ƙara da shi. Girgiza kai ta yi ta hau shiri,kayan ta ta saka tsofaffi ta saka kwalli. Sabon pant da pad ɗin da su Shehu suka kawo mata da shi ta kintsa jikinta. Tana tsaka da cin abinci Barirah ta shiga ɗakin,kallon juna suka yi suka saki murmushi. Cikin sanyin murya Barirah ta ce.
"Don Allah ƙanwata ki yi haƙuri da abubuwan da suka faru jiya. Raina ne ya ɓaci har na yi wa Hajiya magana akan halin da kike ciki na rashin kayan aiki,ban zaci hakan zai jawo matsala har haka ba,na zaci faɗa kawai zai yi komai ya wuce."
"Uhumm babu komai Aunty,Allah dai ya sa ya gane ya dena abubuwan da yake yi."
"Amin Ya Allah,ɗazu yayanki ya kira Hubby,yana so ku gaisa,sannan ya sanar dake Auntyn ki za ta zo saboda a yi suna da ita."
Gaban Fauziyyah ne ya yanke ya faɗi,cikin sauri ta ce.
"Me kuka ce masa to?"
"Ah hukunci na wajen ki mana. Idan ya dawo sai a kira yayan naki ku yi magana. Amma dai kin san idan kika hana ta zuwa baki kyauta ba ko? Wai me yasa ke ba za ki iya tsayawa kan ki bane ki ƙwaci ƴancin ki?"
Murmushi kawai Fauziyyah ta yi, ta ci gaba da cin abincinta. Tana kammalawa ta sha magani ta kwanta ta na tunanin hanyar da za ta bi ta hana Auntyn nata zuwa gidan,dan kuwa ta san muddin Abbas ya ƙyalla ido ya ganta a gidansa sai ya yi mata ruwan rashin mutunci da rashin hankali. Ita kuwa ba za ta so hakan ta faru ba. Gwara ta yi yanda za ta yi ta hana ta zuwa kawai,maganin kar a yi to fa kar a soma.
Har dare ya yi Fauziyyah bata samawa kanta mafita ba,sai kawai ta fawwalawa Allah komai. Fatan ta shine kada Abbas ya yi abinda zai sake nesanta ta da danginta. Washegari Shehu ya bawa Barirah ɗinkakkun atampopi uku shadda ɗaya,sai leshi mai kyau da tsada,ya ce ta bawa Fauziyyah,Yayanta ne ya ce a bata su a ɗinke gudun kada Abbas ya hanata amfani da su ya siyar. Da yammar Barirah ta shiga ta kai mata kayan,sannan ta bata shawarar kar ta sanar da Abbas daga inda kayan suka fito,idan kuma tana ganin babu matsala sai ta sanar da shi. Godiya ta yi mata sosai,sannan ta leƙa ƙofar ɗakin Barirah ta yi wa Shehu godiya. Ta juya baya ta na ta zabga godiya Abbas ya shiga gidan kamar ko da yaushe babu sallama. Hannu ya naɗe a ƙirjinsa ya na kallon ta har ta gama ta miƙe tsaye za ta koma ɗaki. Kallon kallo suka tsaya yi wa junan su. Jiki na rawa Fauziyyah ta shige ɗakinta ta tsaya a tsaye ta na jiran ta ji tijarar da Abbas ɗin zai yi mata idan ya shigo,sai dai ganin da ta yi ya gegare ta ya wuce uwar ɗaka ya barta ba tare da ya ce komai ba ne ya sanya ta shiga damuwa. Da sauri ta bi bayansa,ta na shiga ta tarar da shi ya na ɗaga kayan da aka kawo mata ya na kyaɓe baki,yana gama gani ya wurga su saman gadon sannan ya ce.
"Daɗin abun dai ni ne mijin ki,kuma ni ne uban ƴar ki,dan haka duk wata rawar kai da shisshigi da wani zai yi ba zai sauya hakan ba."
Parlour ya je ya ja abinci ya hau ci ya na kallo,hankalinsa kwance ba tare da ya ji takaicin kansa ba na rashin siyawa matarsa koda adiko ne dan ta ci suna da shi. Ajiyar zuciya mai ƙarfi Fauziyyah ta sauke,godiya ta yi wa Allah da faɗan nasa ya tsaya a iya haka. Cike da farinciki da ɗoki ta hau ɗaga kayan ta na kallo,ƙarshe sai ta cire na jikinta ta na gwadawa. Yanda suka yi mata kyau,suka fito da farar fatarta ne ya burge ta,kallon kanta ta sake yi a madubi ta na tina rayuwarta ta baya,hawaye ne masu zafin gaske suka hau zubo mata. Da sauri ta share su ta cire kayan ta ninke,a zuciyarta ta gama sanin ba zai yanka ragon suna ba,shi yasa ma ko zancen bata taɓa tinkarar sa da shi ba.
Ranar suna mutanen unguwa sun shiga sun taya Barirah aiki. Masa da miyar gyaɗa suka yi,sai kuma shinkafa dafaduka da ta ji naman rago da kayan lambu,har rana ta take Abbas bai kawo ragon suna ba,sai da Hajiyansa ta gaji da jiransa da kuma surutan mutane da ke ta ƙusƙus akan ba a yanka ragon suna ba sannan ta shige uwar ɗakin Fauziyyah da ke zaune ta ci ado suna hira da Auntynta. Gaishe ta suka yi ta kalle su ta ce.
"Kuna nan kun ƙunshe a ɗaki mutane na tsakar gida. Haba ai ba a haka,ku je ku gaisa da mutanen da suka zo taya ku murnar samun ƙaruwa mana."
Aunty Khairi ce ta ɗauki Muhseenah ƴarta Nooratu na biye da ita, suna zuwa parlour mutane suka hau yaba kyawun da Fauziyyah ta yi,ita kuwa murmushi kawai take zubawa ta na jin kanta kamar wata sabuwar halitta,kunya ta dinga ji musamman idan ta ga mutane na kallon ta,ko ana satar ɗaukan ta a hotuna.
Hajiya kuwa Abbas ta kira a waya ta hau zazzaga masa masifa,cike da bada umarni ta ce.
"Ka tabbata ka shigo da ragon suna cikin gidan nan kafin nan kafin la'asar,idan kuma ba haka ba Abbas sai dai ka nemi wata uwar ka ƙarasa rayuwa da ita,amma ba ni ba,shashashan yaro wanda bai san halacci ba."
Zama ta yi a bakin gado ta na maida numfashi,cike da ɓacin rai ta zaro maganinta na hawan jini a jaka ta sha da ruwan da ke cikin gorar ta wanda ba ta rabuwa da shi. Babu jimawa bacci ya fara fisgarta,a ƙasa can gaban gadon ta yada pillow ta kwanta ta hau yin abunta.
A can ɓangaren Abbas kuwa ha'incin da ya so yi ne ya tashi. Domin kuwa so ya yi ya siyo kan rago da ƙafafuwa a gyare,sai ya siyo nama mai yawa ya kawo ya ce ai an gyara tin a can,sai dai wayar da ya yi da Hajiya da umarnin da ta basa ne ya sanya shi siyan wani ƙarmasasshen rago,rai a ɓace ya samu abun hawa ya dawo gidan. Ya na zuwa ya nemi waje ya ɗaure shi ya wuce matan dake zaune suna ta hira ko amsa gaisuwar su bai yi ba. Ganin Auntyn Fauziyyah a kusa da Fauziyyah da Barirah ne ya sanya shi ƙara tsamke fuska tamau. Ba tare da ya gaishe ta ba,ko ya tsaya amsa barkar da take yi masa ba ya wuce ɗakinsa ya na huci. Tsaye ya yi a tsakiyar ɗakin ya na jiran Fauziyyah ta shiga ya sauke mata tijarar da ya ƙunso. Idanuwansa sun rufe bai hango ƙafafuwan Hajiya da ta yada pillow ta gaban madubi ba tana bacci. Fauziyyah na shiga ɗakin ya watsa mata mugun kallo ya ce.
"Me waccan matar take yi min a gida? Dama kun shirya ta zo ta ɗauki hotunan ki ta tafi da su ta nuna wa wannan munafukin ko? To ki je ki sanar da ita ta gaggauta fita ta bar min gida na idan kuma ba haka ba,ni da kaina zan shiga cikin taron munafukan matan da kika tara min a gida na kore ta. In banda baƙin munafurci me ya tara su basu tafi ba har yanzu la'asar ta wuce? Ohh suna jiran a kawo ragon suna kowacce shegiya ta yagi rabonta kan ta tafi ko? To ba zan yanka shi yanzu ba sai bayan magariba. Sannan kar ki sake na fito na ga wannan munafukar a gidana na faɗa miki."
Tinda ya fara magana Fauziyyah ke zubar da ruwan hawaye,shin ta ya za ta je ta ce wa Aunty Khairi ta bar gidan? Sannan maganar ragon suna ita ai ta cire rai ma ba zai siyo ba kamar yanda ya ce a baya. Sannan yanda ta ci nama daga haihuwarta zuwa yanzu ta tabbata ta cire