Showing 12001 words to 15000 words out of 21888 words

Chapter 5 - MUGUN MIJI BOOK COMPLETE by Hamida Sunusi Ahmad.docx

24 Sep 2025

1183

ya shigo gidan hannunsa riƙe da siyayyar da ya yi,tare da ƙaton bread suger da kayan shayi. Kallon kallo suka yi wa juna shi da Shehu ,sai Shehu ya ɗauke kai ya wuce ɗakinsa shima Abbas ya buga tsaki ya yi nashi ɗakin................

[9/17, 7:18 AM] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: MUGUN MIJI.

RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✍️✨

*Wannan littafin na kuɗi ne. Idan kina son shiga paid group ki saka 500 a wannan account ɗin 0006366584 Ja'iz Bank Hamidatu Sanusi Ahmad. Ki tura shaidar biya ta 09031416423. Ba kullum zan dinga posting ba. Amma idan comments suka yi min daɗi ina iya posting sau biyu idan da lafiya da lokaci.*

PAGE 7.

Ɗaki ya shiga, kai tsaye ya wuce wajen da take ajiye masa plates ɗinsa da cups da sauran abubuwan buƙata. Zama ya yi ya ware ƙafafuwansa ya saka siyayyar da ya yi a gaba ya buɗe ledar indomie da soyayyan ƙwai,nan da nan ƙamshi ya buɗe parlourn. Yawu ya haɗiya kafin ya jawo cup ya juye shayinsa haɗin kauri. Ya na gamawa ya tsotse ledar ya yar a wajen. Madarar da ya siyo da millo ɗaya ya fasa ya zazzagi rabi a kowacce leda sannan ya ajiye a gefe. Ledar bread ya buɗe nan ma ya yanki fiye da rabin bread ɗin sannan ya ajiye a gabansa. Ba tare da ya yi bismillah ba ya hau turawa cikinsa abincin nan yana lumshe idanuwansa saboda daɗin na kai masa yanda yake so.

Motsin sa da ya yawaita a parlour ne ya fito da Fauziyyah riƙe da food flask a hannunta na dama,hannunta na hagu kuwa ta riƙo ƙaton kofin silver cike da shayin da ya ji madara da Ovaltine,sai tashin ƙamshin kayan yaji yake. Turus ta yi ta na kallon bajakolin da Abbas ya yi a parlour. Wani irin abu ne ya tsaya mata a ƙahon zuciya,cikin ranta ta ke ayyana.

'Ni ina nan na ajiye abincin da Aunty ta bani dan ya dawo mu ci tinda babu yawa,ashe shi ya na nan yana zuba wa cikinsa abincin da ni ya kamata ya kawowa a matsayi na na wadda ke buƙatar hakan a yanzu. Anya Abbas ya na tina lahirarsa kuwa?'

A tsawace ya sake kiran sunan ta ya na faɗin.

"Meye haka za ki zo ki saka ni a gaba da shegen idanuwan nan naki masu kama da na tsohuwar mujiya? Shi wannan kwanon na uban meye da kika min zaƙeƙe aka kamar zaki ɗor min a ka? Matsa dalla kar ki sa na ƙware. Uhum nan ga madara da millo ki haɗa ruwan zafi ki gasa hanjin ki."

Kallon fasassun ledar madara da millon hannunsa ta yi,cike da murmushin takaici ta kai dubanta zuwa ga cup ɗin da ya haɗa kakkauran shayinsa har da lafceciyar wainar ƙwai da indomie'n da ke ta ƙyallin mai. Juyawa ta yi ɗaki idanuwanta na tsiyayar da hawaye masu mugun zafi. A bakin gado ta zauna bayan ta ajiye abincin a saman mirror ta dinga rusa kukan baƙin ciki. Abbas kuwa da ya ɗauki abinda ta yi masa a matsayin raini da wulaƙanci tare da nuna masa iyakarsa sai ya miƙe cikin tsananin ɓacin rai ya nufi ɗakin. Zaune ya tarar da ita ta na wani irin kuka kamar za ta haɗiye numfashinta. Kallon banza ya yi mata sannan ya ce.

"Wato saboda waɗannan mutanen masu fuska biyu suna taimaka maki,shi ne ya baki damar ki wulaƙanta ƙoƙarina akan ki ko? Idan ba za ki ci abinda na kawo miki ba a matsayi na na malamin makaranta mai ƙaramin albashi,ai sai ki sanar da ni,ba wai ki bar ni riƙe da leda a hannu ba."

Cikin kuka mai ciccira Fauziyyah ta ce.

"Yanzu Abbas tukuicin da zan samu kenan a matsayina na matarka....da...da ta haifa maka ƴa? Ashe bani da...darajar da za...ka iya siya min...abinda zan ci mai kyau....ko da na rana ɗaya ne? Ni fa na haihu...na zubar da jini...amma kai ne ka ke cin kayan daɗi...madarar da za ka bani ma sai da ka raba ta biyu....haba My king me na yi maka da zafi haka a rayuwa? Me yasa ka zamo me manta alkhairi? Me yasa ka manta halaccin da na yi maka a rayuwa? Me yasa?"

A wulaƙance Abbas yake kallon ta har ta kai aya,kafin ya ce wani abu ta miƙe da ƙyar jiri na kwasarta ta isa gaban ƙaton kofin da Barirah ta haɗo mata shayi ta ɗakko shi,sannan ta buɗe masa kwanon hannunta ta nuna masa,cikin kuka ta cigaba da cewa.

"Ka duba fa ka...gani,abinci aka kawo min...na kasa ci saboda ina tunanin kai baka ci komai ba...na ajiye maka na san kana son farfesun kayan ciki...wanda kai ya kamata ka bani....amma shine za ka kawo min bread ɗin da ko rabi be kai ba...da......"

Cikin matsanancin fushi Abbas ya yi kanta,ita kuwa sai ta yi saurin ajiye kwanon da cup ɗin ta dunƙule waje ɗaya tana jiran saukar dukansa kamar yanda ya saba. Sai dai shirun da ta ji ne ya sanya ta buɗe idanuwanta da ta rintse a hankali ta na kallon sa. Yanda idanuwansa suka rine suka yi jawur ne ya sanya ta saurin kawar da nata idon gefe. Hannu ya hau nuna mata ya na kaɗawa,ya ma kasa furta komai saboda ɓacin rai. Tabbas Fauziyyah ta fishi gaskiya,sai dai jin sallamar Hajiyansa ne ya dakatar da shi daga mugun nufin da ya yi niyyar aikatawa. Ƙwafa ya yi ya juya ya koma zuwa parlour. Cikin sauri ya saisaita fuskarsa ya nufi wajen Hajiyansa ya na washe haure kamar jinjirin biri. Cike da farinciki Hajiya ta kalle shi ta ce.

"Abbas ɗina kuma an zama Baba. Ohh Allah na gode maka da ka nuna min wannan rana mai albarka. Ina mai jegon take?"

Sosa kai Abbas ya yi ya kama jakar Hajiya ya na biye da ita a baya za su shiga ɗakin nasu. Ganin Barirah ta fito riƙe da yarinya ta saka mata kaya masu kayu ne ya sa ta tsaya,baki a buɗe take kallon jaririyar fara sol kamar iyayenta. Barirah na miƙa wa Hajiya yarinyar sai ta durƙusa a gaban Hajiya ta na kwasar gaisuwa.

"Lafiya ƙalau Barirah,ashe mun samu ƙaruwa? To Allah Ya raya mana Ya yi mata albarka. Irin wannan fari haka kamar zabaya? To ni dai barka na Malam baya nan ballantana a min ƙwacen miji. Ina mai jegon take ƴar albarka?"

Tinda Hajiya ta fara magana Barirah ke amsa mata cike da fara'a da girmamawa,ta na ambatar Mai jego sai Barirah ta nuna mata hanyar ɗakin nasu ta ce.

"Ta na ciki,ku shiga bismillah,bari mu je mu ƙarasa gashin cibi zan kawo miki ƙawar taki ta taya ki hira."

Cike da munafurci Abbas ya ce.

"Sannu da ƙoƙari fa,Allah Ya saka da alkhairi."

Wani mugun kallo Barirah ta watsa masa,shi kuwa sai ya kashe mata ido ɗaya ya na dariyar iskanci ya bi bayan Mahaifiyarsa da ke tsokanar Fauziyyah. Tsaki Barirah ta ja ta ce.

"Munafukin banza da wofi kawai,in Allah ya yarda sai ka yi dakasanin duk wannan iskancin da kake yi."

Dariya ya sake bushewa da ita kafin ya ce mata.

"A daidai ina? Dalla wuce ki gasa mata cibi ki kawo min ƴata."

Baki a sake Barirah ta kalli Abbas,cikin ranta take ayyana.

'Anya wannan mutumin lafiyarsa ƙalau kuwa? Ko dai ya na watsa kwayoyi ne? Na ga alama ya ma mai da ni abokiyar wasansa.'

Shehu ne ya fito daga wanka ya kalli Barirah a tsaye ita ɗaya a tsakar gida ta shiga cikin dogon tunani,magana ya yi mata ta kalle shi a ɗan tsorace,cike da yaƙe ta ce masa.

"Ka fito? To mu je ka shirya ka tafi kasuwa,yau kam ka makara,Allah Ya sa su Khalil sun fita shagon da wuri."

"To Amin,dan yaran nan mashiririta ne,kullum faɗa muke yi da su akan rashin maida hankali a shago."

"Allah Ya shirya."

"Amin Ya Allah."

A tare suka shiga ɗakin su,Barirah na gasawa jaririya cibiya ta na tina iyashegen da Abbas ya yi mata,ƙwafa ta yi ta ci gaba da abinda take yi ta barsa da halinsa. Ta na gamawa ta ɗauki yarinyar ta wuce ɗakin Fauziyyah da ita. Ta na shiga ta sha mamaki,domin kuwa gani ta yi Abbas ya saka Fauziyyah a gaba ya ajiye mata soyayyar indomie da soyayyan ƙwai ga shayi mai kauri,sai lallaɓa ta yake wai ta cinye duka kar su yi sanyi. Fuska cike da damuwa da tashin hankali Fauziyyah ke kallonsa. Ta na so ta ci dan a daidai wannan lokacin yunwa take ji sosai,sai dai ta na tsoron abinda zai je ya dawo idan ta ci wannan abincin. Hajiya da ta karɓi jaririya ta na mata wasa kuwa sai ta ce.

"Ah toh gwanda ka sa ta a gaba ta ci ta ƙoshi,ai shi jego ba wai a yi ta lafka wa mace ruwan zafi bane jego. Jego mai kyau shi ne mace ta ci mai kyau,ta kuma sha mai kyau. Maza ɗauki ki ci ki ƙoshi kin ji?"

Cikin sauri Barirah da ta san cin wannan tarkacen na Abbas mai zai jawo wa Fauziyyar sai ta yi saurin miƙewa ta nufi ɗakin Fauziyyah ta ɗakko mata farfesun da ta ɗumama mata tin safe,da shayi ta ajiye a gaban Fauziyyah ta ce.

"Ai Hajiya wannan kayan maiƙon a ganina ba yanzu ya kamata ta fara ɗurawa cikinta su ba,ta dai sha me romo ta ɗora da zazzafan shayi."

"Haka ne kuma ƴannan,lokacin da na haifi wannan yaron haka surukata ta dinga yi min dabgen naman rago da naman ciki. Ga kuma kunun kanwa mai kyau da ya ji kayan yaji,kafin ki ce me na zamo wata narkekiya."

Dariya suka yi gaba ɗayan su,cike da dariyar shaƙiyanci Abbas ya ja abicinsa gabansa ya na faɗin.

"To tinda mai jego ba ta cin me maiƙo mu bari mu cinye mata,sauri ma nake yi na leƙa makaranta,duk da dai dama ba ni kaɗai ke da makullin office ba, senior master na da shi za a buɗe wa malamai su yi signing."

"Ni fa mantawa nake yi shaf wai kai ne hedimasta,ya kamata kam ka yi ka gama ka tafi."

Hajiya ta ce ta na miƙawa Fauziyyah yarinyar da ta fara kuka,alamar tana neman abinda za ta sa a bakinta. Fauziyyah da ta kusan cinye farfesun gabanta saboda yunwar da take ji sai ta karɓi yarinyar ta miƙe ta shige ɗaki da ita dan ta shayar da ita. Murmushi Hajiya ta yi,dan ta gane kunyarta Fauziyyah ke ji. Ta na nan zaune Abbas ya cinye abincinsa tasss ya kora da shayinsa. Ya na gamawa ya shiga ɗaki ya hau cire kayan sa. Kallon Fauziyyah dake shayar da yarinyarsu ya yi,manyan ƙirjinta da suka cika ne suka burge shi,yawu ya haɗiya kawai ya kau da kansa,ba dan Hajiya na nan ba,da duk yanda za ta yi da shi ita ta sani,amma dole ne ya huta da ita. Ya na wannan tunanin ya cire kayansa ya sanya jallabiyya ya wuce wanka.

Barirah na tsakar gida ita da Shehu suna sallama suna zuba soyayyarsu. Tsakin da Abbas ya ja ne ya sanya su juyawa suka kalle shi. Murtuke fuska ya yi ya wuce wajen da suke ajiye bokitai ya ɗauka ya zuba ruwa ya wuce banɗaki.

Girgiza kai Shehu ya yi sannan ya kalli Barirah ya ce.

"Kar ki damu,ana kammala suna da sati ɗaya ko biyu komai zai zo ƙarshe,na gama shirya komai,dama iznin ki nake jira,kuma na samu,to Alhamdu Lillah."

Murmushi kawai ta yi masa,zuciyarta cike take da tinani kala-kala,shin ta sanar da Hajiya irin halin ƙuncin da Fauziyyah ke fuskanta a wajen Abbas ne,ko kuma ta ƙyale su idan gumu tai gumu ta faɗawa Hajiyan da bakinta?.........

[9/18, 9:04 AM] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: MUGUN MIJI.

RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✍️✨

PAGE 8.

Kafaɗa Barirah ta ɗaga tare da kyaɓe baki sannan ta ce.

"Bari na kama bakina na tsuke,dan kuwa na san yarinyar nan tsaf za ta ƙaryata ni a gaban uwar mijinta dan kawai ta kare shegen mijin nan nata. Amma ai rana dubu ta ɓarawo ce,rana ɗaya tak kuma ta mai kaya,a juri zuwa rafi da tulu,dan watarana zai fashe."

Ɗakinta ta shige ta hau gyarawa,kafin daga baya ta koma kitchen ɗinta ta duba ruwan wankan da ta saka wa Fauziyyah. Ganin ya tafasa ne ya sanya ta zuwa ta ɗakko babban bokiti ta kwashe ruwan,sai ta tsaya ta na jiran Abbas ya fito ta saka roba a banɗakin ta juye sai ta ƙaro sauran. Ta jima sosai ta na jiransa a bakin ƙofar kitchen ɗinta kafin ya fito ya na goge kansa da ƙaramin towel,ko kallon inda yake Barirah bata yi ba,shi kuwa tsayawa ya yi ya na kallon yanda ruwan zafin gabanta ke turiri. Ji ya yi kamar ya je ya ɗauka ta ya tsoma a ciki tsabar yanda yake jin tsanarta a ransa.

Harara ya banka mata kafin ya ajiye bokitinsa da ƙarfi,ya shige ɗaki. Hira ya tarar da Fauziyyah na yi ita da Hajiyansa,hannunta riƙe da jaririyarsa da ke bacci,murmushi ya yi ya wuce ɗaki ya na faɗin.

"Gaskiya Hajiya yarinyar nan da ni take kama sosai."

Cikin ɗaga murya yanda Abbas ɗin zai iya jiyo ta ta ce.

"Eh to ba zan yi maka musu ba,dan kuwa ta ɗakko kamannin ku kai da Fauziyyah dika. Amma fa ku sani shi jariri ba a shaidar kamanninsa,yanzu zai yi kama da iyayensa da ya girma ya koma kama da kakanninsa ko da maƙotansu."

Dariya sosai Fauziyyah ta yi,jin sautin dariyarta a cikin kunnuwanta ne ya sanya ta tsagaitawa,a hankali take ƙoƙarin tina lokaci na ƙarshe a rayuwarta da ta yi dariyar farinciki ba yaƙe ba ko murmushin takaicin halin ƙuncin da take fuskanta a hannun Abbas. Ƙwalla ce ta taru a idanuwanta,cikin sauri ta hau ƙoƙarin mayar da su,sai dai kalaman Abbas ne suka dawo da ita daga duniyar da ta lula,cikin wani irin amon sautin da ya sanya Hajiya yin shiru ta na nazarin kalaman sa ya ce.

"Lallai kuwa idan yarinya ta yi kama da maƙota sai a tuntuɓi uwarta a ji garin yaya ƴarta ta je kalan dangi har ta yi kama da maƙota?"

Suna nan zaune kowa da abinda yake saƙawa a cikin ransa Abbas ya fito cikin shiri,cike da munafurci ya kalli Fauziyyah ya ce.

"My Queen na gode sosai da ɗawainiyar da kike yi dani,duk da cewa kin haihu kina cikin jego baki manta ba sai da kika fitar min da kayan da zan saka,sannan kika goge min takalmi na,Allah Ya yi miki albarka."

Fauziyyah ji ta yi kamar ya kwaɗa mata guduma a kanta,a razane ta ɗaga kai ta na kallon fuskarsa,tsoro ne ya kamata domin tinawa da rayuwarsu ta baya da ta yi,fatan ta Allah kar ya jarabce ta da maimaita rayuwarta ta baya a gidan Abbas,wannan ma da take ciki neman mafita da salama take yi,me zai kai shi dawo da hannun agogo baya yanzu? Abbas kuwa jakarsa ya rataya ya na kallon fuskar Hajiyansa da ke zabga murmushi,cikin farinciki Hajiya ta ce.

"Ai kana shiga bayi ta tashi ta shige ciki,ashe kayan ka ta ɗakko maka baiwar Allah. Da kuwa na ga tana goge maka takalmi sai da na hana ta,amma sai ta ce wai ladan take kwaɗayi,tinda ta haihu lafiya me zai hana ta goge takalmin ka? Allah dai ya dawwamar da ku cikin zaman lafiya,ina alfahari da sauyawar da ka yi Abbas. Allah Ya yi muku albarka ya sa haihuwar nan da kika yi ta zame muku sanadin samun dawwamammen zaman lafiya a tsakanin ku."

"Amin Ya Allah Hajiyata. To ni na wuce. My Queen ki kula da kan ki da baby,sai na dawo. Ga wannan ko za a siyi wani abun."

Nera dubu ya ajiye mata a gabanta, sannan ya bawa Hajiyansa dubu biyu ya bar gidan ransa ƙwal kamar an yafe masa zunubansa. Fauziyyah kuwa murmushi kawai ta yi,dan kuwa banda Allah babu wanda ya kaita sanin halayyen Abbas gaba ɗayansu. Kuɗin ta ɗauke daga ƙasa ta adana masa abunsa a parlourn. Sallama Barirah ta yi ta ce ta taso su je su yi wanka. Babu musu ta miƙe ta shiga ɗaki ta ɗauki abubuwan da take da buƙata ta wuce banɗaki.

Suna kammala wankan Barirah ta ce.

"To bari na ɗan kwanta na huta tinda ga Hajiya nan,idan anjima sai na tashi na ɗora abincin rana,idan kin ji yunwa kafin na farka ki shiga kitchen ɗina ki haɗa shayi mai kyau ba tsalala ba.kayan tea ɗin suna cikin loka,sai ki buɗe ƙaramin fridge akwai bread ki ci ki ƙoshi. Idan na tashi da wuri zan yi miki tuwo,mai jego sai da abinci mai gina jiki. Ko akwai abinda kike buƙata na yi miki yanzu?"

Kallon Barirah kawai Fauziyyah take yi,ji take yi kamar ta ɗauketa ta buɗe zuciyarta ta sanya ta a ciki tsabar son da take yi mata. Babu zato ko tsammani Barirah ta ji Fauziyyah a jikinta ta saki wani marayan kuka,nan da nan idanuwanta suka ciko da ƙwalla itama. Tsananin tausayin Fauziyyah da take dannewa ya taso ya mamaye zuciyarta. Da ƙyar Fauziyyah ta ɗaga ta ta durƙusa ta hau godiya,cikin sauri Barirah ta ɗaga ta ta na sassauta murya ta ce.

"Kar ki manta kayan shayin nan fa an saye su ne da kuɗin da yayan ki ya aiko a saya maki abun duk da kike buƙata ba da kuɗin mu ba,dan haka babu wata godiya da za ki yi min,sai dai ki godewa Allah,ki kuma godewa Yayan ki."

"Kuma ai dole ne na gode muku da ke da Yayah Shehu,Allah Ya saka muku da alkhairi ya baku abinda kuke nema duniya da lahira."

"To Amin,bari na wuce ɗaki sai anjima ɗin."

Ɗaki Barirah ta wuce ta bar Fauziyyah na wanke idanuwanta dan kar Hajiya ta gane ta yi kuka. Ta na gamawa ta shiga ɗaki ta shirya cikin wata tsohuwar atampar ta. Ta na fitowa Hajiya ta haɗe fuska ta ce.

"Me zan gani haka wai ɗuwaiwai ya mutu ya bar zani? Wannan atampar baki rabu da ita ba dama Fauziyyah? Don Allah wuce ki je ki sauya wasu kayan tin ƴan barka basu fara zuwa ba."

Murmushin yaƙe Fauziyyah ta yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login