Showing 15001 words to 18000 words out of 21888 words
Chapter 6 - MUGUN MIJI BOOK COMPLETE by Hamida Sunusi Ahmad.docx
kafin ta ce.
"Ai Hajiya tinda cikin nan ya tsufa My king yake kwashe wanki na kaf ya kai wajen wankau,sai dai kawai na zo na ga an dawo da su a wanke,to yanzu ma tinda na ga babu kaya na na ce duk yanda akai ya kai su wajen wanki ne da muna asibiti."
"Au dama ba shine ya kai ki asibitin ba?"
Kame-kame Fauziyyah ta fara yi,cikin sauri ta ce.
"Eh ba shi ya kaini ba,sai daga baya ya je,da yake na fara naƙuda baya nan sai Aunty da mijinta suka kai ni a motar Malam Idris."
Ajiyar zuciya Hajiya ta sauke mai ƙarfi,cikin sanyin murya ta kalli Fauziyyah ta ce.
"Ai da har hankalina ya tashi,na zaci har yanzu Abbas na yi miki halayensa na baya,na ji daɗi matuƙa da ya sauya."
Jinjina kai kawai Fauziyyah ta yi ba tare da ta ce komai ba. Gyangyaɗin da Fauziyyah ke yi ne a zaune ya sanya Hajiya bata umarnin ta je ɗaki ta kwanta. Ta na shiga ɗakin babu jimawa ƴan barka suka dinga shiga gidan. Hajiya ce ta yi ta tarbon su ta na sanar da su Fauziyyah ta samu bacci.
Da misalin ƙarfe biyu na rana Barirah ta farka daga baccin gajiya. A gaggauce ta yi alwala ta yi sallah,ganin babu wadataccen lokaci sai ta ɗora taliyar da ta ji naman rago da kayan lambu,ta na gamawa ta zuba wa kowa ta fara kaiwa Hajiya da ke zaune a saman abun sallah ta na jan carbi. Na Fauziyyah kuma a wani sabon babban food flask ɗinta ta zuba,sai ta kai mata ɗaki da plate da duk abinda zata buƙata. Ko ta kan Abbas bata bi ba dan ta san a cikin na Fauziyyah zai ci tinda da yawa.
Babu jimawa kuwa Abbas ya yi sallama shi da abokansa,jaririyar ya shiga ya ɗauka ya na wasar baki tare da sanar da Hajiya tare yake da abokansa. Ko da ya koma sai ya ga har sun shimfiɗa tabarma sun zauna,miƙa musu yarinyar ya yi yana faɗin.
"Kun gani ko? Dama na faɗa muku da ni take kama ai."
Fatan alkhairi suka yi musu da taya shi murnar zamowa uba da yayi. Daga nan sai ya karɓe ta ya mayar da ita wajen Hajiya. Ɗaki ya shiga ya tarar da Fauziyyah zaune a bakin gado za ta zuba abinci ta ci,haɗe fuska ya yi ya ce mata.
"Dan iskanci kina jin na dawo shine kika yi zaman ki? Ko ki ma ɗan leƙo ki yi min sannu da zuwa ko? Da kyau,ba laifin ki bane. Ina abincina ba ni kaɗai bane ina da baƙi."
Kallon abincin ya yi a wulaƙance ya ce.
"Ɗan wannan abincin kawai aka dafa?"
Kasa cewa komai Fauziyyah ta yi,saboda rasa ta inda za ta fara yi masa bayani take yi idan yana faɗan rashin dalili. Kafin ta yi wani yunƙuri ya rufe flask ɗin ya ɗauka ya fita musu da shi waje shi da abokansa,ba tare da ya damu da tambayarta taci ko bata ci ba.
Tagumi Fauziyyah ta buga tana jin yanda cikinta ke kukan yunwa. Barirah na ɗaki ta ga gilmawar sabon food flask ɗinta a hannun Abbas,sai ta fito a fusace ta nufi ɗakin Fauziyyah. Ta na zuwa ta tarar da ita a bakin gado ta zabga tagumi,cike da masifa ta buɗe baki za ta yi magana,amma Fauziyyah ta yi saurin tashi tsaye ta kama hannunta ta jimƙe sosai,ganin yanda idanuwanta suka ciko da ƙwalla ne ya sanya Barirah sassauta muryarta ta ce.
"Wai kina nufin baki ci abincin ba wannan ɗan rainin wayon ya fitarwa garada wahalata waje?"
Cikin rawar murya Fauziyyah ta ce.
"Don Allah Aunty idan har kina son farincikina ki yi haƙuri ki barsu su ci su tafi. Kin ga Hajiya na nan bana so ta san me yake faruwa."
"Idan kuma bana son farincikin naki fa? Dalla ni sakar min hannu."
A hasale Barirah ta ƙwace hannunta ta fita daga ɗakin..........
[9/19, 7:50 AM] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: MUGUN MIJI.
RIBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✍️✨
PAGE 9.
*MUHIMMIYAR SANARWA.*
*1-Ƴar'uwa ki na fama da mummunar ramar da kike jin kunyar shiga cikin taro gudun kar a dinga tambayar lafiya kike kuwa ramar ta yi yawa? Matso kusa na zo maki da magani ingantacce wanda aka haɗa shi da kayayyaki masu inganci wanda ba sa cutarwa ko da bayan kin gama amfani da shi,za ki murje ki yi ɓulɓul kema ki juya mazaunan ki ki kaɗa ƙirjin ki gaban Oga da sauran mata yanda kike so ba tare da kin cutar da lafiyar jikinki ba. Ana shan wannan magani da Kunu ko fura,ko kuma Yghort.*
*2-Ke kuma matsalar zubewar nono da lalacewarsa tare da tamuƙewarsa kamar leda ke damun ki? Kar ki ce kin sha wancan da wannan kin gaji,taho ki gwada products ɗin mu mai abun mamaki domin samun confidence ɗin bayyana jikin ki a gaban oga.*
*3-Mummunar ƙiba mai haɗe da ƙaton tumbi da manyan kumatun da suka nitsar maki da hanci ciki ke damun ki? Ko kuwa irin ƙibar nan ce da ta maida ki kamar buhu babu gaba babu baya? Kar ki ji komai,domin kuwa na zo maki da ingantaccen maganin hausa wanda bashi da illa ga lafiyar jiki a farashi mai sauƙi cikin kwana uku zaki fara ganin sauyi,a kwana bakwai kuwa shape ɗin ki zai bayyana ki huta da nauyin jiki.*
*4-Kina son ki samu glass skin da an hango ki a ga yanda fatar ki ke haske da walƙiya tare da ɗaukan ido? Kema zo nan kar ki wuce na tanadar maki naki kayan da za su kyautata fatar ki.*
*5-Kina fama da matsalar ciwon sanyi mara jin magani? To ki zo na baki maganin da zai wanko maki shi,za ki gansa da idon ki yana fita kamar dusar awara,har ya wanke ruwan ni'imar jikin ki ya bayyana ki mori rayuwar auren ki.*
*Gaba ɗaya za ku iya samu na a wannan No 08038086083.*
Turus Barirah ta ja ta tsaya a tsakar gidan,ta na aikawa Abbas da abokansa da suke ta lashe hannu kamar tsofaffin mayu harara. Da ƙyar ta iya danne fushinta ta kalli Hajiya dake ta ƙoƙarin haɗa wuta a jiƙaƙen murhun Fauziyyah ta ce.
"Hajiya ai da kin bar kunna wannan murhun tinda an jiƙa shi,ga kuma yanayi na damina itacen ma kansa a jiƙe yake."
"Wai ai na ga a gas kike ɗora ruwan ne,kar ku yi ta asarar gas ɗin tinda shi dai iskar banza ce,babu wuya ya ƙare."
Murmushi Barirah ta yi kafin ta ce.
"Ai da yake ya fi sauri ne wajen aiki shi yasa nake jin daɗin aiki da shi,nan da nan sai ya biya miki buƙata ki tashi abunki."
"To da wannan dan wannan kuma. Maza ɗebo ruwa ki gani ga wutar nan ta kama ganga-ganga,idan na tafi kun yi a gas ɗin naku na ƴan zamani,yanzu fa sauƙi ya samu ba kamar da ba da mata suka sha wahalar rayuwar gidan miji,shi yasa nake mamaki idan na ga yarinyar nan ta nace ita ba ta son aiki a risho ko gawayin nan me saurin aiki wai ita ta fi son itace,ko meye abun daɗi a girki da itace oho? Ko ni da nake tsohuwa a kurfotina nake girki yanzu,ko na saka kalanzir a risho na ɓararraka abinda zan ɓararraka na tashi."
"Humm samu ne fa da bata yi ba Hajiya,domin babu wanda baya son hutu a rayuwarsa,ai na so itama Fauziyyahn na da gas ɗin musamman a lokacin da take da ciki. Tin kafin a kira sallah sai ki ga ta fito kunna wuta,watarana har gari ya yi haske wutar bata kama ba,yanzu kuwa ga yarinya,idan me ƙiwa ce haka fa za ta fito da ita cikin sanyin daminar nan,ta dalilin hakan sai ki ga sanyi ya kama ta."
"Wannan gaskiya ne,ya kamata itama a samar mata da gas ɗin nan,domin ta huta. Bari zan yi wa Abbas ɗin magana ai,zuwa ƙarshen wata ko da kuɗinta na wajensa ne sai a siya mata,kin san halinsa yanzu sai ya ce ba shi da kuɗi,to tinda yarinya da dukiyarta ai sai a yi mata abinda ya kamata ko ba haka ba?"
Cikin sauri da murmushin mugunta Barirah ta ce.
"Sosai ma kuwa. Kuma yanzu yanda abubuwan zamani suka shigo da suke sauƙaƙawa mace ayyuka,tsaf zai iya siya mata injin wankin nan,su blender iron da standing fan,gashi bana muna samun wuta sosai ba kamar da ba da sai a wuni babu wutar."
"Ƙwarai da gaske. Kai amma dai wannan yarinya Allah Ya yi miki albarka,ai ni duk ban yi wannan dogon nazarin ba,bari a gama hidimar suna sai mu yi maganar dashi,ba zan barsa ya huta ba har sai ya siya mata ƴan abubuwan da za ta dinga hutawa da ayyukan gida,yanzu zamani ya sauya,mata sun dena wannan wahalhalun ai. Yarinya da uwar kuɗinta ta zauna ta na izar jiƙaƙƙen itace?"
"Ah toh, dan a yanayin nan na damina fa sai ta kunna wutar sannan ta tara garwashin da za ta yi guga,lokacin guga da dutsen ƙarfe ai ya wuce. Da ace ma za ki sanar da shi yau ai da kin wa tufkar hanci da wuri,gudun kar ki manta."
"Wannan ma shawara ce mai kyau,bari baƙin nasa su tafi na same shi da maganar."
Ran Barirah ƙwal ta wuce ɗebo ruwa a babbar tukunya,dan ta san dole aljihun Abbas ya jijjiga. Tana dawowa da ruwan Hajiya ta karɓa ta ɗora a saman murhu,hira suka ci gaba da yi Barirah na ta zuga Hajiya,ita kuwa ta na ta adana maganganu a cikin kwanyarta,Abbas kawai take jira ya zo ta lissafa masa kaf abinda take so ya siyo wa Fauziyyah. Hajiya ce ta yi wa Fauziyyah wankan yamma da kanta,ta yi mata gashi sosai a inda ya dace,sannan ta sanya ta zama a ruwan ɗumi domin ta gasa jikinta da kyau. Hajiya na gamawa da Fauziyyah sai ta karɓi jaririyar ma ta wanke ta tas ta gasa ta sosai,anan ne Fauziyyah da Barirah suka ga yanda ake yi wa jarirai wanka me kyau,ba irin wanda ta jajjaɓa mata da safe ba. Suna zaune Hajiya na ta koya musu abubuwa irin na mutanen da Abbas ya shiga parlourn ya na washe baki,domin ba ƙaramin daɗin abincin suka ji ba shi da abokansa,har suna cewa gobe ma za su dawo su ƙara kwasar gara.
Cike da fara'a ya zauna a gefen Hajiyansa da ke sanya wa Yarinya kaya,cikin fara'a Hajiya ta kalle shi ta ce.
"Ah ah Ɗan lele Abashen Babansa irin wannan washe baki haka kamar wanda ya samu wata kyauta mai tsoka? To ba wannan ba,wai ni meye sunan yarinyar nan ne? Ko kai ma al'adar mutanen da za ka raya,ba za a faɗi sunan yaro ba sai bakwai ta zagayo?"
Kallon Fauziyyah ya yi ya tuna bala'i da masifar da suka kwasa a watannin baya akan cikin jikinta,nan da nan ya yi mursisi ya murje idanuwansa ya ce wa Hajiya.
"Ai Muhseena za a saka mata,amma za mu dinga ce mata Ummi."
Wata iriyar guɗa Hajiya ta saki,kafin ta koma yin hamdala,cikin tsananin farinciki ta kalli Fauziyyah wadda mamakin Abbas ya gama kashe ta a zaune ta ce.
"Ashe kun shirya yi min ba zata shine baki sanar da ni ba? Kaiii yaran nan Allah Ya yi muku albarka. Allah Ya raya mana takwarata Ya albarkaci rayuwarta. Sai dai ina roƙon alfarma a wajen ku,don Allah kar ku ɓoye sunan nan,ku faɗe shi kamar yanda kuke kiran ruwa. Mugunta wa yaro ne kawai bana so,a hau jibgar yaro be yi komai ba,idan kuka yi min haka kun gama min komai."
Murmushin yaƙe Fauziyyah ta saki kafin ta zaro kalmomin.
"Allah Ya raya mana ita Hajiya."
Da ƙyar ta furta. Ta na gama faɗin haka ta tashi ta shiga ɗaki ta damƙe bakinta ta na rusa kuka. Shin Abbas ya manta abinda ya faru ne? Ya manta alƙawarin da ya yi mata? Ko kuwa ya manta halacci da mutuncin da Mahaifiyarta ta yi masa a rayuwa? Lallai a yau ta tabbatar da cewa Abbas baya son ta,ba kuma ya ƙaunarta, yaudarar ta yake yi. A yau ta yarda da sunan da Barirah ke kiransa da shi,wato MUGUN MIJI. Duk wahalar da ta sha akan cikin nan tin daga ɗaukansa,da haihuwa,sai ya karya billensa ya haɗiye kalamansa ya yi wa tashi mahaifiyar takwara. Cikin kuka Fauziyyah ta ce.
"Na ɗauka ƴata ce ni kaɗai,na zaci sai abinda na ga damar yankewa akan ta shi zan yanke? Me ya sa ka zamo mai baki biyu?"
Muryar Abbas ta ji a saman kanta cike da ɓacin rai ya na faɗin.
"Saboda ni ne mijin ba ke ce mijin ba. Ni nake da iko da haƙƙin zaɓarwa ƴata suna,ko za ki hana ne? Sunan uwar tawa ne ya sanya ki zuwa ɗaki saboda baƙin ciki da iskanci ki dinga kuka kamar an yi miki mutuwa?"
Idanuwanta da suka rine suka yi jajawur ta zuba masa,har sai da tsigar jikinsa ta miƙe,a hasale ya kai wa kanta ranƙwashi murya ƙasa-ƙasa ya ce.
"Bar kallo na da shegun idanuwanki kamar na tsohuwar mujiya don uban ki. Kuma ki tashi yanzun nan ki ɗebarwa Hajiya wancan kayan miyan da na ga an lode a ƙofar kitchen ɗin ki,dan na san tinda aka ajiye a can to naki ne. Ta fara shirin tafiya zan mayar da ita gida yanzu."
Kasa cewa komai Fauziyyah ta yi,sai kawai ta hau share hawayenta ta nemi kwalli ta saka,sannan ta fito tsakar gidan. Kai tsaye wajen kayan miya ta nufa ta ɗiba sosai a leda ta koma ɗaki,Barirah na kallonta bata ce mata ci kanki ba,aikin girkin dare kawai take ta yi,zuciyarta fess dan ta san komai bala'in Abbas sai ya siyawa Fauziyyah abubuwan da ta kitsawa Hajiya a sai mata. Cike da jin kunyar Barirah ta gama cika leda da kayan miya ta nufi hanyar ɗakinta.
Turus Fauziyyah ta ja ta tsaya a ƙofar shiga ɗakinta saboda jin irin lissafin da Hajiya ke yi wa Abbas,jikinta na rawa ta hau cewa.
"Hajiya ai ni na fi son aiki da hannuwana na wanke kaya...ni..ni....ba...ban ma iya amfani da injin wanki ba,sannan blender tsoro take bani,ƙarar firgita ni take yi Hajiya kuma..."
Cikin hasala da ɗaga murya Barirah dake jiyo wautar da Fauziyyah ke yi ta ce.
"Tana firgita ki kike aron tawa? Ko kuma shi gas ɗin da nake baki ki yi girki idan wutar murhun ta ƙi kunnuwa tsorata ki yake yi? Ke wai wace iriyar yarinya ce Fauziyyah? Banda abinki ma uwa da ɗa suna magana ina ruwanki a ciki da za ki saka musu baki?"
Shiru Fauziyyah ta yi ta na rarraba ido,ganin irin azababben kallon da Abbas ke sauke mata,wanda ke ratsa gangar jikinta ya na shigewa har ya yi sanadiyyar da ta sanya ta ajiye ledar hannunta a gaban Hajiya cikin firgici da gigicewa ta ɗauki ƴarta ta shige ɗaki da sauri.
Murmushi kawai Hajiya ta saki,domin kuwa duk ɓoyewar da Fauziyyah ta dinga yi ta gano cewa halayyar Abbas ta mugunta na nan babu abinda ya sauya,ashe basaja kawai suke yi mata a ɗazun shi yasa bata gane komai ba. To kuwa ya yi shuka a idanun makwarwa,dole ne ya yi duk abinda ta lissafa masa,tinda ai akwai kuɗin ba babu ba.
Sassauta murya Hajiya ta yi,sannan ta dafa kafaɗar Abbas ta ce.
"Abashen Babansa ka dai ji abubuwan da na lissafa maka ka siyo mata ko? Na baka daga nan zuwa ƙarshen wata ka siyo ka ajiye mata su,domin ta samu hutu a ayyukanta na yau da kullum. Ba dan hidimar suna ba ma da ke gaban ka ai da na ce ka siyo mata su gobe,amma yanzu ka ji da ragon suna da sauran kunji-kunjin suna da za a buƙata. Allah Ya yi maka albarka,tashi ka mayar dani gida. Wannan kayan kuma a mayar dasu dan babu inda zani da su,ina can da kayan miya na jibgi,dan kuwa ko kafin na fito sai da na tsince wanda suka fara lalacewa na aika maƙota. Maza tashi mu tafi,garin ma kamar akwai hadari,shi yasa zafin ya yi yawa."
Abbas bai iya furta komai ba,tsabar yanda zuciyarsa ke tafasa,babban fata da burinsa bai wuce ya kai Hajiya gida ya dawo ya ji shegen da ya kitsawa Fauziyyah ta ce a siya mata abubuwan da Hajiya ta lissafa masa ba. Kamar wadda ke yin duba haka Abbas ya ji muryar Hajiya dake yafa mayafi ta na faɗin.
"Babu wanda ya sanar da ni abinda na yi maka lissafi Abbas,ni da kaina na duba na ga abubuwan da bata da su,take kuma da buƙata,wanda ya kamata ace ta jima da mallakar su amma bata da su,bayan ta na da kuɗinta ba wai babu ba. Kai idan ma bata da su ai kai ne ya kamata ka siya mata,tinda duk amfanin ku ne. Dan haka kar ka bari maganar nan ta kai mu ga ɓacin rai Abbas."
Sosa kai ya yi yana murmushi ya ce.
"Ai Hajiya na yi shiru ne ina tinanin kuɗaɗen da za a samu na wannan watan,ina lissafi ne na ga za su isa ko sai na yi ciko da albashi na? To Alhamdulillah na ga za su isa ma a yi mata komai,har a ci gaba da yin ajiyar da aka saba yi duk wata."
"To Alhamdulillah,Allah Ya baka ikon sauke nauyi Abbas."
"Amin Hajiyata."
Har suka fita Fauziyyah bata san ma sun fita ba tsabar yanda ta matsu su tafi ta tinkari Barirah ta ji ko ita ta kitsawa Hajiya maganganun da ta ji tana yi. To ta ina ma za ta fara tinkarar Barirar tinda bata da wata shaida akan hakan? Dafe kanta da ta ji yana sara mata ta yi,a hankali ta fashe da wani irin kuka mai azabtar da zuciya. Wannan wanne irin sabon bala'i ne ya tinkarota ko hutawa bata gama yi ba daga nishi da wahalar haihuwa da ta yi?...........
[9/20, 6:16 PM] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: MUGUN MIJI.
RUBUTAWA HAMIDAH SUNUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✍️✨
PAGE 10. LAST FREE PAGE.
*MUHIMMIYAR SANARWA.*
*1-Ƴar'uwa ki na fama da mummunar ramar da kike jin kunyar shiga cikin taro gudun kar a dinga tambayar lafiya kike