Showing 9001 words to 12000 words out of 21888 words
Chapter 4 - MUGUN MIJI BOOK COMPLETE by Hamida Sunusi Ahmad.docx
ko?"
Kai kawai Fauziyyah ta iya ɗaga wa Barirah,wani irin zafi zuciyarta ke yi mata,ga azabar zafin naƙuda na ratsa ta. Da gudu Barirah ta shiga ɗakinta ta ɗakko wata ƙatuwar leda mai kyau,hijabinta ta ƙarasa sakawa sannan ta kalli Shehu ta ce masa.
"Hubby ina ga fa dole ka je gidan Malam Idris ya taimaka mana da mota,tinda ka ga mu machine gare mu."
"To ina shi ɗan rainin wayon yake?"
Shehu ya faɗa ya na kallon Fauziyyah da hanyar ɗakin nata,murmushin takaici kawai ta yi ba tare da ta iya furta masa komai ba. Barirah ce ta ja tsaki sannan ta harari ƙofar ɗakin nasu ta ce.
"Don Allah Hubby ka je ka taso Malam Idris ni ba zan iya karɓar haihuwa a gida ba,saboda ban iya ba ban san ya ake yi ba."
Cikin sauri Shehu ya fita waje ya sa makulli ya buɗe gidan ya nufi hanyar gidan maƙocinsu dake da mota. Barirah kuwa igiya ta kalla ta ga zannuwa guda biyu da Fauziyyah ta ke wanka da su a wanke da hijabinta,sai kawai ta ɗauke su ta ninke ta saka a cikin ledar da ta fito da ita ta miƙawa Fauziyyah hijabin dan ta saka. Ta na nan tsaye ta na jiran Shehu,hankalinta a tashe ta ji motsin Abbas,shigowar Shehu ke da wuya Abbas ya fito hannunsa riƙe da rigarsa ya na ƙoƙarin sakawa ya ce.
"Gidan uban wa za ku kai min matata da tsohon daren nan?"
Shehu ji ya yi kamar ya ɗura masa ashar,sai ya danne ya bashi matsayinsa na mijin Fauziyyah ya ce.
"Baka ga naƙuda take yi ba? Asibiti za mu kai ta mana."
"Da yawun wa za ku kai ta asibitin to?"
"Da yawun..."
Hannu Shehu ya ɗaga wa Barirah ya ce.
"Za mu kai ta asibiti yanzu ko da matsiyacin yawunka ko babu,idan ya so ka biyo ta da takardar saki a can ka ga idan ta gama iddah ba za ta samu mijin da ya fi ka ba? Shashasha kawai. Ke barira kamo ta mu wuce kin ji."
Cikin sauri ta taimakawa Fauziyyah ta miƙe ta na bin kyakkyawar fuskar Abbas da kallo, wataƙila wannan kallon shine kallo na ƙarshe da za ta yi masa,murmushi ta sakar masa ta gyara zaman hijabinta da Barirah ta bata dan ta saka suka fara takawa zuwa waje. A hasale Abbas ya ɗaga murya ya na faɗin.
"Ai na faɗa mata tin cikin nan yana ƙarami ni ba zan je asibiti ba,a nemo ungozoma ta zo har gida ta karɓi haihuwarta,dan haka idan kuka kuskura kuka kai ta asibiti sai dai ku yi hidimar asibitin kuwa,sisi na ba zai yi ciwo ba."
Ya na magana ya na ɗaga hannaye kamar me shirin kai musu duka,babu wanda ya kula yinsa suka wuce suka barshi ya na banbamin faɗa. Ganin fa da gaske asibitin za su kai ta ne ya sanya shi saurin kulle ɗakin su,ya tada nashi machine ɗin ya bi su,ya na fita ya tarar da har sun shige mota Malam Idris ya tada za su tafi,cikin gaggawa ya kulle gidan ya bi bayan su,a hanya ya zaro wayarsa ya kalli lokaci,ƙarfe uku da kwata na dare. Gudu kawai suke zubawa saboda titin babu kowa. Kai tsaye asibitin Aminu Kano suka wuce saboda a can Barirah ke ganin likita. Suna zuwa suka yi duk abinda ya dace,kafin su kammala naƙudar ta taso gadan-gadan,ɗakin haihuwa aka kai Fauziyyah cikin gaggawa. Abbas na ƙarasa shigowa Fauziyyah ta silluɓo jaririyarta kyakkyawa mai kama da iyayenta. Nurse ce ta leƙo ta ce.
"Ina ƴan'uwan Fauziyyah Aliyu? Ku kawo kayan jariri. Ga kuma wannan za ku siyo abubuwan da aka rubuta a jiki ku kawo yanzu."
Wata takarda ta miƙa wa shehu, ya karɓa ko ta kan Abbas bai bi ba ya wuce ya na hamdala ta sauka lafiya. Barirah ce ta miƙa ƙatuwar ledar nan ta koma gefe ta na wasar baki,suna haɗa ido da Abbas ta zabga masa harara tare da sakin wani mugun tsaki,shi ɗin ma hararar ta ya yi tare da rama tsakin da ta yi masa sannan ya ce.
"Duk tsiyar ki dai ba za a taɓa sauya wa tuwo suna ba,ni ɗin dai da ba kya so ni ne uban yarinyar,to don haka ki dena wani zaƙewa da yi min shisshigi a lamura na,idan haihuwar kike so kema ki dage ki haifi naki."
Kallon Abbas Barirah ta yi ranta a matuƙar ɓace,cikin tsananin ɓacin rai ta ce masa.
"Inda za ka tabbatar da cewa ita haihuwa ta Allah ce ba ta mutum ba kenan tinda ka haihu ni ban haihu ba. Allah ya na bawa wanda ya so ya hana wanda ya so,kuma shi ɗin ne dai ya baka mu kuma da muke so bai bamu ba,ba dan komai ba sai dan hakan ya zame mana aya a rayuwarmu."
"Oho dai,duk wannan rawar kan da kike yi nine dai uban ƴar,kuma sisina ba zai yi ciwo ba,tinda ba a nemi shawarata ba balle izinina aka kawo min mata nan wajen."
Barirah bata sake kula Abbas ba saboda ɓacin ran da ya dasa mata,wanda ya fi na da. Shehu da Malam Idris na dawowa Abbas ya buga tsaki ya ci gaba da habaici da surutai na kore kunya da hauka. Cikin ɓacin rai Malam Idris ya kalle shi ya ce.
"Kai dai Abashe an yi mugun miji kuma azzalumi,yanzu ace matar ka za ta haihu ko tsinke ba ka siya mata ka ajiye ba,sannan ka tasa masu taimaka maka a gaba da rashin arziƙi? Da ace yarinyar nan za ta bani dama alƙur'an ba za ta koma gidan ka ba,daga asibiti sai gidan iyayenta,dan ko ka ƙi sakin ta sai na maka ka a kotu ka sake ta dan dole."
Dariya Abbas ya fashe da ita sannan ya ce.
"Ai dama na san sai kun yi gulmata tinda kuka fita tare,wato har ya baka labarin ban siyi ko tsinke ba ko? To ban siya ba ɗin sai me? Ko ni na saka shi kashe kuɗin sa? Dama ai ba domin Allah suke taimakon ba tinda har suke iya yayata abinda suka yi mana."
Ganin haukan na Abbas azimun ne sai kowa ya bawa banza a jiyarsa,shi kuwa tunda ya ga ta haihu lafiya,an fito da jaririya ya ganta ya yi mata addu'a,sai kawai ya bawa nurse ita ya wuce gida. Ya na isa gida ana kiran assalatu. Bai wani damu ba ya shige ɗakinsa ya kwanta,cike da tinani da soyayyar jaririyarsa bacci mai mugun nauyi ya ɗauke shi..........
[9/14, 7:31 AM] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: MUGUN MIJI.
RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 6.
Gari na wayewa likita ta duba Fauziyyah da jaririyarta ta tabbatar da lafiyarsu ƙalaou,sai ta rubuta musu sallama da magungunan da ya kamata ta dinga sha. Babu ɓata lokaci Barirah ta haɗe kan kayan su da dama ba wani yawa ne da su ba. Ragowar madarar da Fauziyyah bata shanye ba,Barirah ta sa ta a gaba ta zuƙe ta ƙara mata da ruwa sannan ta ɗauki jaririyar. Malam Idris da Shehu ne suka taya Barirah ɗaukan kaya suka yi sallama da matan dake kwance a ɗakin suka tafi. Suna tafe a cikin mota Fauziyyah ta lula cikin tunani mai zurfi,lokaci zuwa lokaci Barirah ke taɓo ta da hira. Cikin sanyin murya Fauziyyah ta hau yi musu godiya da addu'o'i har da kukanta. Barirah ce ta ce.
"Babu komai Fauziyyah yi wa kai ne. Amma fa dole ne ki sanar da yayan ki haihuwar da kika yi,domin ba zai yu a ce kaf dangin ki basu san halin da kike ciki ba."
Ajiyar zuciya Fauziyyah ta sauke kafin ta ce.
"Tun ɗazu tinanin da nake ta yi kenan,sai dai ina tsoron abinda zai je ya zo,kin san sharuɗa da rashin azziƙin da Abbas ya yi wa dangina,bana so a maimaita abinda ya faru a baya."
"To ki zauna kar ki sanar da su saboda kina tsoron Abbas. Ta ya za ki sulluɓo sabuwar halitta zuwa duniya ki bari har muguntarsa ta nakasa ki ko ta shafi ƴar ki babu wanda ya san me kuke ciki a dangin ki."
Tinawa da abubuwan da suka faru a baya,da iyayenta da ta yi ne ya yi sanadiyyar zubar hawayenta har da shessheƙar kuka. Tausayinta ne ya kama su gaba ɗaya,a hankali Shehu ya ce.
"Ki yi mata a hankali don Allah da wanne za ta ji? Kar ki damu Fauziyyah idan baki son sanar da kowa abinda ke faruwa,babu matsala, za mu yi ta taya ki da addu'a,ba kuma za mu gaji da baki taimakon da ya dace ba,har zuwa lokacin da Allah ya nufa."
Muryar ta suka ji ta na faɗin lambar waya,cikin sauri Shehu ya zaro wayarsa ya fara latsawa,sake maimaita lambar ta yi,shi kuma ya duba ya ga cas ta cika,shima sai ya karanto mata sai ta ce.
"No Yah Abdullah ce."
Suna gab da isa unguwarsu Shehu ya kira layin wayar Abdullah,ta jima ta na ringing kafin a ɗauka,da sallama aka amsa wayar,cike da mutuntawa Shehu ya amsa sallamar sannan ya ƙara da cewa.
"Barka da asuba Alhaji,suna na Shehu Usmanu maƙoci ga ƴar'uwarka Fauziyyah...."
Abdullah a can ɓangaren sai ya yi saurin taran numfashin Shehu da faɗin.
'Na gane sunan ka,ban taɓa mantawa da karamcin ka a gare mu ba na kula da Fauziyyah da kake yi kai da iyalinka. Ina fatan dai lafiya kuke ko? Ya Fauziyyah?'
Gyara zama Shehu ya yi ya zayyane wa Abdullah duk abinda ke faruwa da ya sani, sannan ya ƙara da cewa.
"To yanzu ma muna hanyar komawa gida daga asibiti,shi ne ta bamu lambar wayarka ta ce a sanar da kai haihuwar."
Ran Abdullah a matuƙar ɓace ya ce.
'Na gode sosai Malam Shehu,Allah Ya saka muku da mafificin alkhari kai da duk wanda suka taimaka wa ƙanwata. Da izinin Allah zan zo garin kanon,wannan karon dole ne na kawo ƙarshen mugun zaman da Fauziyyah take yi a gidan Abbas. Yanzu ka tura min account No zan tura maka wani abu,a yi mata siyayyar duk da ta dace,sannan kuma ku ɗauki kuɗin asibiti da kuka kashe,kar ka ce min ah ah don Allah ku karɓa,Allah Ya biya ku da kyakkyawan sakamako."
Godiya Shehu ya yi sosai shima,sannan ya kashe wayar,suna gamawa ya juya ya kalli inda suke,sai ya gan su tsaye a ƙofar gidan nasu,ashe har sun isa. Zayyana musu yanda suka yi da Abdullah ya yi,sai Malam Idris ya ce.
"Alhamdu Lillah,Allah Ya sa ƙarshen wahalar kenan. Ni dai bana buƙatar ko sisi,wannan yarinya ai ta cancanci taimakon duk wani mumini."
"Wannan gaskiya ne Malam Idris. Allah Ya saka da alkhairi. Mu je ciki ko?"
Godiya Fauziyyah ta sake yi wa Malam Idris sannan ta ce wa Shehu.
"Don Allah Yaya kar ka sanar da Abbas Yah Abdullah ya san halin da nake ciki,duk abinda za ka siyo kawai ka kawo a matsayin ku ne kuka yi min,idan ya sani ba zai bar hankali na ya kwanta ba."
Jinjina kai kawai Shehu ya yi,da haka suka tattara suka yi hanyar shiga cikin gidan. Su na zuwa suka ji ƙofar a rufe,sai Shehu ya lalubo makullin gidan ya saka ya buɗe,ya na buɗewa ya sake murɗa ƙofar,sai ya ji ta a rufe. A ƙufule Barirah ta ce.
"Ka dena wahal da kan ka,rufe wa ya yi ta ciki tsabar rashin mutunci,kawai ka zagaya ta baya ka haura ka buɗe mana sakata."
"Ki rage zafin rai Baby,da alama be san za mu dawo yanzu ba."
Cikin sauri Fauziyyah ta ce.
"Haka ne ma,da ya san za mu dawo na san da ba zai saka sakata ta ciki ba."
Barirah ji ta yi kamar ta kifa mata mari,Abbas ɗin za ta ba wa uziri? Ai ba domin ma ba da uziri ya zamo wani ɓangare na addini ba,da babu abinda zai sa ta yi shiru ta bashi uzirin. Ƙwafa ta yi ta fallawa Fauziyyah harara,cikin sauri ta yi ƙasa da kanta saboda gano katoɓarar da ta yi. Zama suka yi a dandamalin ƙofar gidan Shehu na ta gwada kiran layin Abbas ɗin, wayar na ta ringing amma ba a ɗauka ba. Tin ƙarfe bakwai da rabi suke zaune a wajen har takwas da minti ashirin Abbas bai buɗe musu gidan ba. Tsananin takaici ne ya sa Shehu zagayawa ta baya ya haura cikin gidan sannan ya isa bakin ƙofa ya buɗe musu suka shiga. Cike da masifa Barirah ta ce.
"Da ka bi shawarata tin da farko ai da bamu yi zaman jiran mara mutuncin nan ba a cikin sanyin safiyar nan,ga yarinya nan sai atishawa take yi da alama sanyi ya kama ta."
Abbas ne ya fito daga shi sai dogon wando,haɗaɗɗe kuma kyakkyawan jikinsa irin na Models ɗin nan maza ya bayyana a gaban su Shehu,da sauri Barirah ta ɗauke idanuwanta daga kallon sa ta shige ɗakinta da jaririyar a hannunta. Rai a ɓace Abbas ya ce.
"Da ina da makami da fitowa zan yi na raɗe duk shegen da ya hauro min gida ta katanga,wannan ai karya dokar zaman tare ne,uban wa ya ce ka hauro min gini kamar wani ɓarawo?"
A hasale Shehu ya ce.
"Ubanka ne ya sa ni hauro maka ginin ɗan iska mara mutunci kawai. Ka san Allah daga yau na dena ɗaga maka ƙafa, tuɓewa zan yi mu daku ni da kai,mu ci uban juna da kyau,duk wanda ya ji a jikinsa ya kiyayi ɗan'uwansa. Shashasha mara hankali kawai. Kai yanzu ba abin kunya bane mutane su ji labarin abubuwan da kake aikatawa? To ka sani a yau ba sai gobe ba zan je har gidan tsohuwar ka na sanar da ita duk iskancin da ka ke yi wa ƴar mutane."
Cikin wani irin yanayi na tashin hankali Fauziyyah ta kalli Shehu da ransa ya kai ƙololuwar ɓaci,Abbas kuwa jikinsa ne ya yi mugun sanyi saboda yanda ya ga Shehu na magana har wata kumfar masifa da bala'i na fita daga bakinsa,tabbas ya sani idan aka bar shi da Shehu mugun duka zai yi masa,dan shehu irin mazan nan ne dirarru gajeru masu ƙirar ƙafi. Kyakkyawan ustaz ne fari tas da shi,ya na da sauƙin kai sosai,da kunya mai tsanani,amma fa idan aka kai shi maƙura ba ya da daɗin sha'ani. Baki na rawa Fauziyyah ta ari bakin Abbas sarkin girman kai ta ci masa albasa.
"Don Allah Yaya ka yi haƙuri kar ka sanar da Hajiya abinda ke faruwa,idan ta ji labari ciwon ta zai iya tashi."
Hararar da Shehu ya banka mata ne ta sanya ta tashi daga gabansa ta koma gefen ɗakinta ta rakuɓe,Barirah ce ta fito goye da jaririya ta wuce su ta kunna gas ta ɗora ruwan wanka. Ta na gamawa ta koma ɗaki ta zauna ranta na suya,cikin ranta take ayyana.
'Dole ne na bi umarnin miji na a wannan karon,na gaji matuƙa da tausaya wa matar da bata san ina ne yake yi mata ciwo ba ballantana ta sha masa magani. Ana neman a taimaka mata,ta na bin bayan ja'irin mijin nata da bai ƙi ta faɗi ta mace ba.'
Wayar Shehu ce ta yi ƙara alamar shigar saƙo,duba wa ya yi,sai ya ga saƙon daga bankinsa ne,kuɗin da Abdullah ya tura masa ne suka sanya shi zaro ido waje,cikin sauri ya bar wajen ya shiga ɗaki, ya jima suna tattaunawa da Barirah kafin ya fito fuskarsa a haɗe,machine ɗinsa ya ɗauka ya bar gidan. Sai a lokacin Fauziyyah ta shiga ɗakinta ba tare da ta tanka wa Abbas ba. A ƙofar ɗakin Barirah Abbas ya tsaya ya na faɗin.
"Malama ai sai ki bani ƴata tinda ba ke kika haifa min ita ba ko?"
Ko motsi Barirah bata yi ba,ballantana ta tanka shi. Jira take yi ya yi gigin shiga ɗakin nata ta illata shi ta nuna masa mata suna suka tara. Ita ba Fauziyyah bace ballantana ya kai mata wargi. Shirun da ta yi masa ne ya hasala shi ya koma ɗakinsu ya samu Fauziyyah ya hau surfa mata masifa,ita kanta a wannan karon ta rasa inda ta samu ƙwarin guiwar ƙin bin umarninsa na karɓo yarinyar. Haka ya ƙaraci faɗan sa da cin alwashi kala-kala amma bata motsa ba. Wanka ya yi ya wanke bakinsa,sannan ya saka kayansa masu kyau ya fesa turare,kallonsa kawai Fauziyyah take yi tana jin sabuwar ƙaunarsa na ratsa zuciyarta,haushin kanta ta ke ji sosai akan yanda take kasa controlling zuciyarta akan Abbas. Namiji ne shi da bashi da tausayi,bashi da kulawa. Zuciyarta ta gama tabbatar mata da cewar baya sonta a yanzu. A duniya idan wani ya ce mata Fauziyyah Abbas zai juye ya dawo maƙiyin ki watarana to fa tabbas da ta saka bakin bindiga ta harbe shi,saboda ta na da yaƙinin yanda Abbas ya so ta,ya nuna mata kulawa a baya,ba zai taɓa gudunta ba. Ya yi mata alƙawurra kala-kala,sai gashi ya kasa cikawa,ta haifa masa yarinya kyakkyawa,amma ko sannu bai yi mata ba,ballantana magana mai daɗi ta sannu da dawowa daga asibiti ta haɗa su,ƙarshe sai ma rashin mutunci da azziƙi da yake ta tafka mata. Ajiyar zuciya ta sauke a daidai lokacin da ya bar ɗakin ya ɗauki makullin machine ɗinsa ya bar gidan.
Wajen mai sayar da shayi ya nufa aka soya masa ƙwai huɗu, indomie biyu,sai shayi haɗin kauri,ya karɓa ya ɗauki hanyar shago.
Shehu kuwa tinda ya fita kasuwa ya wuce kai tsaye,mayanka ya je ya tarar ana ta gyara raguna da shanu har da akuyoyi da raƙuma,wajen mai siyar da naman rago ya tafi ya siyo rabin rago,sannan ya wuce wajen masu kayan miya ya siyi kayan miya,da maggi da duk abinda ake buƙata,daga nan sai ya wuce wajen masu awo,ya siyi buhun shinkafa,katan ɗin taliya da sauran kayan abinci. Yana kammalawa ya biya ɗan dakon da ya yi masa dako ya taya shi jerawa a saman machine,sai ya ɗauki hanyar gida.
Shehu na isa gidan sai ya tarar Barirah har ta yi wa jaririyar wanka,ta sake ɗora wani ruwan saboda mai jego. Kitchen ɗin su ya shiga ya saka naman nan a babban fridge ɗin su,sannan ya kai sauran kayan abicin madaidaicin store ɗin su dake cikin kitchen ɗin ya jibge. Ya na gama ajiye kayan Abbas