Showing 1 words to 3000 words out of 21146 words

Chapter 1 - Dakarun Musulunci Book 2 By Abdulaziz Sani M Gini.txt

DAKARUN MUSULUNCI

LITTAFI NA BIYU 2

Marubuci:- Abdul Aziz Sani Madakin Gini

Typing:- Umar Farouq Zango.

A can birnin Darul Husuf kuwa, lokacin da kwanaki bakwai suka cika sai mutanen birnin suka taru a fada domin ganin yadda za'a fito da gawar sarki a masa jana'iza, a wanna lokaci gidan sarautar yayi tsit ba'a jin komai face sautin iskar dake kadawa. A can kofar turakar sarki kuwa shulaifa da muzaira ne a gefe daya a tsaye yayinda sauran bayi da kuyangin gidan suma sukayi sahu sahu, kowa kansa a sunkuye, a gefe guda kuma sauran yan majalisar sarki ne suma sunyi sahu sahu kowa kansa a sunkuye.
Bayan wasu wani lokaci sai kawai akaji karar bude kofar turakar sarki, sai kowa ya dago kai domin ganin yadda za'a fito da gawar sarki. Kwatsam ba zato ba tsammani sai aka ga sarki ya fito yana takawa da kafafunsa cikin koshin lafiya, bai doshi ko ina ba sai inda matansa suke, wato inda mulaifa da shulaifa ke tsaye. Yana zuwa gaban su ya tsaya sannan ya dubi muzaira yace kinyi mamakin ganina a raye ko, wannan kadan daga ikon Allah kenan, gubar da kika bani gashi bata kasheni ba. Koda gama fadin haka sai muzaira ta sulale kasa sumammiya.

Lokacin da sarki uwaisul karni yada matarsa muzaira ta sulale kasa sumammiya, sai ya dubi dakaru ya ce, ku dauketa ku kaita kurkuku ku kulleta. Nan take kuwa wasu dakaru biyu suka cika wannan umarni. Faruwar hakan ke da wuya, sai shulaifa ta ruga ga sarki uwaisul karni ta rungumeshi cikin farin ciki, tana mai godiya ga Allah da ya tserar da rayuwarsa. Sarki uwaisul karni ya janye jikinsa daga cikin na shulaifa, sannan ya dubi wani hadiminsa yace, kaje kayi shela a gari cewar kowa ya hallara a fada yau da yamma bayan sallar la'asar. Hadimin ya risina yace, an gama ya shugabana.
Bayan anyi sallar la'asar kuwa, sai fadar ta cika ta batse da jama'a, ya zamana cewa duk inda mutum ya duba babu abinda zai gani face kawunan bil adama rututu, babu masak tsinke.

Jim kadan da gama taruwar jama'a, sai ga sarki uwaisul karni ya fito Fes da shi yaci ado yana takawa a cikin koshin lafiya, a wannan lokaci yana sanye ne da fararen tufafi, farin rawami da farin takalmi fade, ya shafe gemunsa da sajensa da kunshi, sai kyalli suke tamkar matashin saurayi.
Duk da cewa sarki uwaisul karni ya fara manyanta idan mutum ya ganshi a wannan lokaci, sai yayi zaton cewa, saurayine saboda kyan jikinsa da kuma koshin lafiya. Koda jama'ar gari suka ga sarkinsu ya fito da karfinsa cikin koshin lafiya, sai sika cika da tsananin farin ciki suka rude da kabbara. Har sarki uwaisul karni yaje ya zauna akan karagar mulki basu daina kabbara ba. Jim kadan sai sarki uwaisul karni ya mike tsaye ya fuskanci alumma. Nan take fadar tayi tsit tamkar babu wani abu mai rai a wajen. Uwaisul Karin yayi gyaran murya, sannan yayi sallama irin ta addinin musulunci, ya fara bayani kamar haka...

"Yaku jama'ar wannan birni namu mai albarka, kuyi sani cewa, abinda ya faru gareni ishara ce babba garemu baki daya, domin Allah ya nuna ikonsa cewa, rai da mutuwa duk a hannunsa suke.
Matata muzaira ta zuba min guba a cikin abincina na ci, amma si gashi ban mutum ba, duk da cewa na sha bakar wahala tamkar zan mutu. Wannan ya isa hujja a garemu da zamu sake jajurcewa akan addinin Allah, mucire tsoron abokan gaba daga cikin zukatanmu, mu tare su da dukkan karfin mu.
Ina son ku sani cewa, a lokacin da na kwanta jinyar rashin lafiya bisa wannan lalura data sameni nayi wani mummunan mafarki da ya tayar min da hankli. Ba wani abu na gani ba a cikin mafarkina, face an nuna mini cewa, dakarun da muka tura yaki izuwa birnin shumbul suna cikin mugun hali, domin makiya sun kamasu, mutum biyune kacal ba a kamasu ba, wato Uzaifat da Abul shaja'a.

Ukashat kuwa an nuna mini cewa ya guji 'yan uwansa ya sabi Allah, kuma ya hada kai da makiyan mu. Kun sani cewa, a rayuwata ban taba yin mafarkin da bai zamo gaskiya ba, saboda haka bani da wata tantama akan wannan mafarki don haka zama bai samemu ba m. Dolene muyi gagarumin shiri mu kaiwa 'yan uwanmu dauki, tun gabanin su hallaka.
Bisa wannan dalilin yanzu na bada umarni ga dukkanin mayakan wannan kasa tawa, su yi shiri daga nan zuwa kwana uku domin mu je mu yakin karshe da wadannan abokan gaba namu. Lallai ba zamu dawo ba face mu ko su.
Yayin da sarki uwaisul karni yazo nan a zancensa, sai fadar ta sake rudewa da kabbara. Nan take sarki yayi addu'a tare da gaba dayan jama'ar dake fadar suka nemi sa'a da taimako a wajen Allah. Bayan an shaga adduar ne fadar ta watse kowa ya kama gaban sa.
Lokacin da sarki uwaisul karni ya shiga cikin gida, sai ya wuce kai tsaye izuwa dakin shulaifa.

Da shigarsa cikin dakin saiya isketa a zaune tana ta zubda hawaye. Koda ganinta a cikin wannan hali sai hankalinsa ya dugunzuma ainun ya karasa gareta da sauri ya zauna daf da ita, ya kama kafadunta suka fuskanci juna, yace, yake matata me ya faru kike faman kuka? Shin na bata miki rai ne, ko kuwa wani ya bata miki ne gidan nan.
Koda jin wannan tambaya sai ta dubeshi ta ce, ba wanine ya bata min rai ba kuma ba kai bane, abinda ya sa kaga ina zubar da wannan hawaye ba komai bane, facw bakin labarin da na ji daga bakin ka, wanda kayi dazu fada cewar, dana ukashat ya hada kai da makiya Allah. Ina jin wannan batu sai na kaimu da tsananin bakin ciki, kuma na tausaya masa matuka domin abin tausayine shine a matsayin musulmi kuma dan sarkin musulmi na wannan babban birni ace ya kauce hanyar gaskiya ya kama ta karya. Ni babban abinda yafi damuna ma a yanzu shine, rashin sanin matsayinsa a wajen Allah.
Lokacin da sarki uwaisul karni yaji wannan tambaya, sai yayi ajiyar zuciya, sannan yace, idan har Ukashat bai yi ridda ba, har yanzu shi musulmi ne, amma akwai hukunci a kansa bisa laifin daya aikata wanda aka nuna min a mafarki. Abu na farko sai an nuna mini cewa yasha giya, kuna sannan yayi zina. Koda jin haka sai shulaifa tayi salati ta sake fashewa da kuka cikin matukar bakin ciki. Uwaisul karni ya mike tsaye yace, mene ne abin kuka? Ai kawai zainfuskanci hukuncine kamar yadda Allah ya shar'anta muddin na sameshi a raye, saboda haka ina mai shawartarki da ki daina zubar da hawayen ki a banza domin tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa ke duka.
Koda gama fadin haka, sai sarki uwaisul karni ya mike tsaye ya fice daga cikin dakin yabar shulaifa tana mai ci gaba da kukanta, ko waigota bai sake yi ba.
Kamar yadda sarki uwaisul karni yayi bayani, haka alamura suka kasance, domin sai da aka shafe kwana uku cur ana ta shirye shiryen yaki sannan aka gama kimtsawa.

A ranar kwana na ukunne da yammaci dakarun kasar gaba daya suka gama hallara a fada. Nan take sarki uwaisul karni ya fuskancesu yayi musu nasihohi da wa'azi kamar yadda ya saba yi musu a duk sa'adda za'a fita yaki, sannan ya dubi waziri yace, ya kai waziri ga amanar kasata nan a hannunka, mu zamu tafi yaki, sai Allah ya dawo damu. Ka ji tsoron Allah, ka tafi da mulkinka bisa adalci da gaskiya kwatan kwatankwacin yadda zaka iya kuma kuci gaba da tayamu da addu'a akan Allah ya bamu sa'a da nasara.
Sa'adda sarki uwaisul karni yazo nan a zancensa, sai waziri ya numfasa, yace, da izinin Allah zan kasance mai rike wannan amana bisa gaskiya da tsoron Allah, kuma ni da sauran jama'a zamu kasance cikin yi muku addu'a daga yau, har izuwa ranar da Allah zai dawo daku, idan kuma kun sami shahadane a can, to muna yi muku fatan samun rahamar Allah. Koda jin wannan batu, sai murna ta kama sarki uwaisul karni, ya rungume waziri, sannan suka yi bankwana.

Sarki yaje ya kama dokinsa ya hau, har ya kada linzamin dokin sai yi gaba, sai waziri ya kira sunansa yace, ya shugabana ya za'ayi da matarka muzaira wacce kasa aka kaita kurkuku. Baka yanke mata hukuncin komai ba, har yanzu bisa laifinta? Sa'adda sarki uwaisul karni yaji wannan batu, sai ya gyada kai, kuma yayi ajiyar numfashi yace, kuci gaba da ajiye ta har izuwa lokacin da zan dawo daga wannan yaki idan kuma ajalina ya riskeni a can wajen yaki, wanda duk ya gajeni shine zai yanke mata hukunci dai dai da laifinta.
Koda gama fadin hakan, sai sarki uwaisul karni ya sakar wa dokinsa linzami yayi gaba. Nan take dakaru sama da guda dubu arba'in bisa dawakai, alfadarai da rakuma suka bishi a baya du.... tamkar kaza da 'ya'yanta suka nufi kofar fita daga harabar gidan gaba daya. A wannan lokaci gaba daya jama'ar gari sunyi cincirundo a kofar fadar suna yi musu jinjina, gami da addu'ar nasara, sai kabbara suke tayi musu.

Allahu Akbar! Musulunci da dai yake. Hakika in da mutum na tsaye a wannan lokaci yana ganin yadda dakarun suka sa niyyar wannan tafiya da zuciya daya, bisa dogaro da Allah ba tare da shakkar mutuwa ba, da kuma yadda iyalansu suke tayasu da addu'a ba tare da bakin cikin rabuwa ba, ko kuka ba, dole ne zuciyarsa ta sosu koda kuwa ya kasance Arne.
Haka dai wannan tawaga taci gaba da tafiya, jama'a na yi musu rakiya a baya, har suka isa can bayan gari. Anan ne masu iyali suka rinka bankwanan karshe da iyalansu suna rungumar juna da sumbata, amma dayansu bai rushe da kuka ba, sai dai kaga kwalla a idanu. Nan dai aka gama yin sallama, sarki ya jagoranci dakarun suka nausa cikin dajin. Tun ana hangensu, har suka bace bat.
Wannan shine abinda ya faru a birnin sarki uwaisul karni, bayan ya tashi daga jinyar cutar da ya kwanta sakamakon gubar da matarsa muzaira ta zuba masa a abinci yaci.


* * * * * *
Al'amarin Uzaifat, Abul shaja'a da Lafirat kuwa, lokacin da Lafirat tahau kan dokinta na tsafi taci gaba sa tafiya, su kuma suka bita a baya suna tafiya da kafafunsu cikin sauri sauri, gudu gudu sai da suka yi tafiyar sa'a uku cur, amma basu iso dajin mashharul kais ba. A dai dai wannan lokacine Uzaifat da Abul shaja'a suka fara gajiya, suka fara tafiyar sarsarfa.
Kamar Lafirat tasan abinda ke faruwa garesu sai ta tsaida dokinta ta juyo taga halin da suke ciki. Koda ganin haka, sai ta sauka daga kan dokin ta jashi izuwa Kar kashin wata bishiyata tsaya daf da ita, Uzaifat yace, me yasa kika tsaya a nan? Koda jin wannan tambaya sai Lafirat tayi murmushi tace, ai koda mun ci gaba da tafiya, sarewa zakuyi domin yanzune ma muka ci rabin tafiyar, nan gaba sai munyi kamarta sannan zamu isa dajin na daya, wato dajin mashharul kais inda muggan tsuntsaye suke, ga shi kuma tun yanzu naga kun gaji. Lallai akwai bukatar mu yada zango domin ku huta kuma muci abinci, tunda rana na daf da faduwa sai mu bare idan dare yayi, sannan mu ci gaba da tafiya tunda dai za'a sami hasken farin wata a wannan lokacin.
Ba tare da gaddamar komai ba, su uzaifat suka amince da wannan shawara. Nan take suka kwance jakunkunansu sukayi shimfida suka zauna. Ita ma Lafirat sai tayi tata shimfidar a can gefe daya ta zauna kuma ta dauko soyayyen nama ta ajiye a gabanta. Maimakon ta fara ci, sai ta dubi su uzaifat ta ce, Bismillanku fa ha nama. Cikin tsananin mamaki Uzaifat ya dubeta, kawai sai yayi murmushi, yace Mun gode. Nan take Uzaifat da Abul shaja'a suka fiddo dabino suka kama ci.
Lafirat ta dubesu tayi murmushi, sannan ta budi baki tayi bismillah ta fara cin wannan soyayyen nama dake gaban ta.

Al'amarin da ya mutukar baiwa Uzaifat mamaki kenan, har suka kasa cin dabinan nasu suka tsaya suna kallonta kawai. Koda Lafirat taga sun zuba mata idanu, sai tace, lafiya naga kun kura min ido haka, shin ba kwajin kunyata ne a matsayina na 'ya mace? Uzaifat yayi ajiyar zuciya yace, ki gafarcemu yaje wannan 'yar sarki, kiyi sani cewa tsananin mamaki ne yasa muka kura miki idanu. Manene dalilin da yasa kika yi bismillah a lokacin da zaki ci wannan nama alhalin baki kasance musulma ba?
Sa'adda Lafirat taji wannan tambaya, sai tayi murmushi tace, ai na gaya muku na koyi yadda duk aladar ku take ta musulmi kuma aladace wadda take mutukar burgeni duk da cewa ban karbi addininku ba amma ai nayi imani dashi a cikin zuciyata, kawai dai ina jiran lokaci ne dazan karbeshi, don haka bai kamata kuyi mamaki ba, saboda kunga ina yin wasu abubuwa cikinsa. Ina tabbatar muki da cewa, na iya salloli biyar da kuje a rana, kuma nayi zurfi a cikin karatun littafi mai tsaki, amma saboda sanin cewa, ina taammali da tsafi shi yasa bana yinsa.

Sa'adda Lafirat tazo nan a zancenta sai yarima uzaifat yace, ai gwara da bakya yinsa, domin baki da tsaki, kuma ina mai shawartarki da kada ki sake yunkurin yin wani abu makamancin hakan face kin karbi addininmu, saboda kin san cewa ruwa da wuta basa haduwa.
Lafirat tayi murmushi, tace, na karbi shawarar ka, kuma zanyi aiki da ita.
Haka dai suka ci gaba da hira suna cin abincin har suka kammala. Basu bar wajen ba sai da su Uzaifat sukayi sallar isha sannan suka mike suka ci gaba da tafiya a cikin daren domin an sami hasken farin wata a wannan lokaci kamar yadda Lafirat da fada. Basu gushe ba suna tatafiya har tsawon sa'a biyu, a wannan lokaci dajin yayi tsit ba ajin komai face kukan kananan tsuntsaye da kwari. In banda hasken farin watan da Ya gauraye dajin gaba daya ba dole ne mutum ya razana da dajin, saboda yawan duhuwarsa gami da dogayen bishiyoyi da manyan duwatsu da tsaunika. Suna cikin tafiya ne kwatsam sukaga wani katon shuri a gabansu mai girman gaske, tamkar katon dutse aka ajiye.

Shurin ya cika hanyar gaba daya babu ta inda za'a wuce face anji ta kansa. A jikin shurin akwai wasu manyan hudoji wadanda mutum na iya shigewa cikinsu, hudojin na da yawa babu adadi. Koda sukayi arba da wannan shuri sai suka ja suka tsaitsaya, kamar hadin baki, ai duk su ukun suka zare takubbansu suka kura idanu ga shurin suna jira suga ko wani abu zai fito daga cikinsa. Tsawon dakika dari da a shirin basu ga komai ba.
Uzaifat ya dubi Lafirat yace, me kika sani dan gane da wannan shuri? Lafirat ta gyada kai tace, ban san komai ba, asalima ban taba ganinsa ba anan, ma'ana bai taba wanzuwa ba sai yanzu da muka ganshi. Abinda naje zargi shine, duk yadda akayi mahaifina yasan da zuwan mu don haka shine ya turo mana wannan shuri, lallai ba a rasa wani mugun abu ba a cikinsa mai mugun hadari.

Kafin Lafirat ta gama rufe bakin ta kuwa, sai sukaga wadansu irin aljanu kanana masu suffar bil adama suna fitowa daga cikin hudojin shurin suna shawagi a saman shurin, tamkar anan ruwan fari. Banbancinsu da bil adama shine, rafkeken kai mai surar shanty, sai kuma wadansu irin fuka fukai irin na jemage sannan kowannensu yana da hannaye hudu, kafafu hudu. Bakunansu dogayene ga tsini tamkar allura.
A dai dai wannan lokacine tsautsayi ya biyo da wani shawo zai gifta ta saman shurin kawai sai daya daga cikin aljanu yayi sama ya cakeshi da tsinin bakinsa. Taje ya zuke jinin jikin shagon ya fado kasa tim sa sandare tamkar gawar da ta kumbura take shirin yin bundiga.

Koda Lafirat, Uzaifat da Abul shaja'a suka ga abinda ya faru ga wannan shaho, sai hankalinsu ya dugunzuma ya tashi, domin sun san cewa, suma abinda zai samesu kenan da zarar miyagun aljanun sun farmusu. Babban abin tashin hankalin shine, yawan aljanun ya wuce daruruwan dubbunai, sai dai ace miliyoyi, sannan suna ta wani irin kara mara dadin ji, wacce ka iya dodar da kunne, ba shiri su uzaifat suka fara to she kunnuwansu kuma suka dimauce basu san sa'adda suka rikito kasa ba daga kan dawakansu.
Koda aljanun suka ga haka, sai suka taho da gudu izuwa Kansu suka yanyamesu suna kawo musu suka da tsinin bakinsu ta ko ina, cikin tsananin zafin nama Uzaifat, Abul shaja'a da Lafirat suka shiga kare harin da aljanun suke kawo musu da takubbansu. A duk lokacin da takubbansu suka hadu da bakin aljanun, sai kaji kamar karfe da karfe ne suka hadu, kuma har tartsatin wutane ke tashi. Tsananin zafin naman aljanun be yasa su uzaifat suka kasa saran jikinsu.

Ana cikin wannan gumurzu ne daya daga cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login