Showing 15001 words to 18000 words out of 21146 words
Chapter 6 - Dakarun Musulunci Book 2 By Abdulaziz Sani M Gini.txt
kais, duk inda dare ya riskesu, sai su yada zango zai gari ya waye, sannan suci gaba da tafiya.
Da yake har yanzu Lafirat na fama da lalurar wannna rauni dake bayanta Uzaifat ne ya dinga goyata a bayansa a tsawon kwanaki ukun kuma wani iko na Allah, sai ta kamu da zazzabi mai zafi, har da kumallo, al'amarin da ya dugunzuma hankalin kowa kenan, musamman ma shi Uzaifat domin tattara hankalinsa yayi gaba daya akanta ya rinka jinyarta yana bata magunguna tana sha, kuma ya dinga dura mata abinci da hannunsa.
Da yammacin kwana na uku ne zazzabin Lafirat yayi zafi ainun, har numfashinta ya dinga sarkewa, al'amarin da ya dimauta Uzaifat kenan, bai san Sa'adda ya fara a addu'a yana rokon Allah ya baiwa Lafirat lafiya ba.
Ai kuwabai dade ba da fara addu'ar, sai Lafirat ta samu sauki, har ta bude idanunta ta dubeshi tayi masa murmushi.
Nan take farin ciki ya lullune Uzaifat yaji kamar ya rungume Lafirat, amma sai ya kasa. Bisa mamaki sai Uzaifat yaga hawaye na zuba a idanun lafirat al'amarin daya mutukar bashi mamaki kenan, ya dubeta cikin karayar zuciya yace, yake Lafirat ina dalilin zubar wannan hawaye naki?
A lokacin da Uzaifat yayiwa lafirat wannan tambaya babu kowa a kusa da su, domin Abul shaja'a uwar mayu da yayanta na can gefe daya. Abul shaja'a yana koya musu karatun alkur'ani.
Yayin da Lafirat taji tambayar da Uzaifat yayi mata, sai tayi ajiyar numfashi sannan tace, ya kai gwarzona kayi sami cewa a rayuwata babu wani mahaluki daya taba nuna damuwa da kulawa a kaina sama da kai. Tsananin farin cikine yasa kaga ina zubar da wannan hawaye bisa ganin nuna kulawarka a gareni. Kai kuwa mai ya sa ka damu da rayuwata lhakin kasan cewa bazan iya yi muku komai ba acikin wannan tafiya? Aikina kawai shine na nuna muku hanya, to yanzu ma ga uwar mayu da yayanta ko babu ni su zasu iya nuna muku hanyar.
Lokacin da Lafirat tazo nan a zancenta, sai Uzaifat yayi shiru yana kallonta kawai ya rasa amsar da zai bata.
Lafirat tace ya naga kayi shiru baka ce komai ba?
Uzaifat yayi murmushi yace kiyi hakuri yake Lafirat domin a gaskiya yanzu bazan iya baki amsar wannan tambaya ba, amma idan lokaci yayi zan amsa tambayar, idan muna tare kuma muna raye.
Koda gama fadin haka sai Uzaifat ya mike tsaye ya kara gaba ya bar Lafirat a zaune tana mai binsa da kallo kawai cikin mamaki da wasu wasi. Ba komai taje wasu wasi ba, face wai shin wannan kulawar da Uzaifat ke nuna mata SO ne kk tausayi? Amsar da ta kasa baiwa kanta kenan.
Yayin da Uzaifat ya baro wajen Lafirat sai yaje wajen su Abul shaja'a ya zauna yaci gaba da tayasu karatun alkurani izuwa wani lokaci.
Bayan sun hatatama ne Uzaifat ya dubi Abul shaja'a yace, Yanzu ya kakejin raunin kafarka?
Abul shaja'a yace, ai na warke sumul, shin baka yadda na ke takawa ba sosai yanzu, ga shi ma na daina dogara ice.
Uzaifat yayi murmushi yace, gaskiya ne amma ina neman alfarma mu kara kwana uku a nan domin ku kara samun lafiya sosai, kai da Lafirat.
Koda jin haka, sai Abul shaja'a ya dubi Uzaifat cikin matukar mamaki, yace aini ma warke bana bukatar karin bata lokaci, sai dai saboda ita Lafirat din. Kuma ka tuna cewa, ita Lafirat babu wani abu da zata iya yi mana a cikin wannan tafiya face nuna mana hanya, ko babu ita Yanzu akwai uwar mayu da yayanta.
Uzaifat yace nasan da hk, amma lallai nafi son sai Lafirat ta warke sumul sannan zamu rabu da ita a dajin karshe, bana son mu rabu da ita tana cikin lalura. Ka tuna cewa, ba don ita ba da tuni mun hallaka tun a baya albarka cin ta ne muka kawo izuwa matsayin da muke kai yanzu.
Sa'adda Uzaifat yazo nan a zancensa, sai jikin Abul shaja'a yayi sanyi, bai kara cewa komai ba.
Kamar yadda Uzaifat ya tsara haka al'amari ya kasance, wato sai da suka kara kwana uku a wannan wuri, sannan suka ci gaba da tafiya suka durfafi dajin zarsus. A wannan lokaci kuwa Lafirat ta warke sumul, karfin jikinta ya dawo sosai tamkar ma bata taba yin wata lalura ba.
Sai da suka yi tafiyar sa'a shida sannan suka iso farkon dajin zarsus. Da zuwansu bakin dajin, sai uwar mayu da ke kan gaba ta daina kada fuka fukanta da karfi ta sauko kasa, kuma ta daga hannuna tana mai yiwa su Uzaifat nuni da su tsaya.
Ba tare da gardamar komai ba kuwa suka tsaya cak! Uwar mayu ta dubi gabas da yamma kudu da arewa, sannan ta shauki kamshi da hancinta, kawai sai ta juyo ta dubi su Uzaifat tace, akwai mugayen kunamai anan gabanmu kadan, don haka sai kowa yayi shirin tukararsu. Ina mai gargadinku dacewa, kada ku bi hanyar da kika ga babu sabar macizai akanta a cikin wannan daji, domin itace kadai hanyar da kunamai basa bi saboda a kaidar dajin kunaman da macizan basa faduwa a waje guda.
Tunda dai yanzu banjiyo kamshi macizai ba, sai na kunamai, to mu ratse hanyar su mu bi ta macizai shine kadai hanyar da zamu it tsira daga sharrin su.
Koda gama fadin haka, sai uwar mayu ta wuce gaba, yayata nabiye da ita sannan Lafirat ta bisu sai Abul shaja'a, Uzaifat ne a karshen baya. Dafara tafiyar tasu a cikin dajin na zarsus sukayi kicibus da wata katuwar sabar maciji wadda za'a iya nannade gaba dayansu a cikinta saboda girmanta. Koda ganin wannan sabar maciji, sai dukkaninsu suka cika da mamaki. Abul shaja'a ya dubi Lafirat yace, yake wannan yar sarki shu kuwa wannan maciji mai wannan saba wane irin girma ne da shi haka?
Lafirat tayi murmushi tace ai girmansa ya wuce misali, da kamantawa sai abinda idanun ya gani. Na taba ji mahaifina yace, a duniya kaf irin wannan macijin guda uku ne rak, yanzu daya na can karshen bangon duniya, bangaren kudu. Dayan kuma a bayan birnin sin yake a cikin wani teku, baya fitowa saman tekun sai bayan kowace shekara goma, don ya shaki numfashi kawai. Ina jiye mana yin arba da wannan maciji domin karfin damtsen dana sihir ba zai kwacemu ba.
Gama fadin hakan ke dawuya sai suka fara jiyo wani irin numfashi mai karfin gaske tamkar an yanka shanu dubu a lokaci guda suna kakarin mutuwa. Sannan suka rinka jiyo wani irin huci yana buso musu. Al'amarin da ya matukar razana su kenan, uwar mayu ce tafara juyawa da baya kamat zata ruga da gudu suma yayanta sai suka a da baya, haka ma Lafirat da Abul shaja'a.
Uzaifat ne kawai bai firgita ba, kuma ko gezau Baiyi ba. Kawai sai ya zare takobinsa ya ci gaba da tafiya ya durfafi inda wannan huci ke fitowa. Nan dazuka rasa wanda zai bi bayan Uzaifat, duk sai suka tsaya sukayi cirko cirko suna kallon juna.
Daga can sai Lafirat tayi kundunbala ta bi bayan Uzaifat. Koda ganin haka, sai Abul shaja'a ya bita, sannan ne uwar mayu da yayanta suka biyosu.
Sai dai Uzaifat yayi yar doguwar tafiya sannan ya tsaya yayi gurus bisa abin mamakin da ya gani a gabanku. Ba wani abu ya gani ba face wani narkeken maciji wanda tsawon sa da kaurinsa ya wuce kamu dari biyu. A wannan lokaci macijin ya hadiye wata narkekiyar kunama wacce girmanta yakai na babbar giwa. Kawai macijin yayi lamo a kasa ko kyakkyawan motsi baya iya wa saboda hadiyar da ya fara.
Uzaifat ya tsaya cak! Yana kallon ikon Allah. Jim kadan sai ga Lafirat ta iso wajen, sannan Abul shaja'a da su uwar mayu. Da isowar uwar mayu ta ga saura kadan macijin ya gama hadiye kunamar, sai ta dakawa su Uzaifat tsawa tace, maza ku ruga da gudu mu bar wajen nan kafin ya gama hadiye wannan kunamar dan kanmu zai juyo ya yi loma daya damu.
Dajin haka sai Lafirat, Abul shaja'a da yayan uwar mayu suka falfala da gudun kara gaba. Shikuwa Uzaifat sai ya daka tsalle ya hau kan jelar macijin ya fara tafiya a kansa tamkar ya hau kan katon tsauni. Sannan ya waigo ya dubi uwar mayu yace, idan ba zaki iya tsaya wa ba, ki kallo abinda zai faru ba kuma kiyi takanki.
Koda jin haka sai uwar mayu ta dan ruga gaba kadan ta buya a cikin wata yar duhuwa tana leken a abinda zai faru. Uzaifat ya ci gaba da tafiya akan macijin har ya iso tsakiyar kansa. A dai dai wannan lokacine macijin ya gama hadiye wannan katuwar kunama, kuma a sannane Uzaifat ya daga takobinsa ya cakata a tsakiyar kan macijin. Kawai sai yaji kamar akan dutse ya cakata takobin, take ta karye gida biyu, macijin ya yunkura ya girgiza kansa yayi cilli da uzaifat tabayansa can gefe daya tamkar yafado daga kan dutse mai tsawon gaske. Kafin Uzaifat ya yunkura ya mike tsaye tuni macijin ya juyo da kansa baya ya kawo masa cafka baki bude zai hadiye shi.
Cikin matukar zafin nama Uzaifat ya goce yana mai mirgina jikinsa gefe guda macijin ya hadiyi iska. Uzaifat ya mike tsaye da sauri ya falfala da gudu, aikuwa sai macijin ya sako kansa ya biyoshi suka kasa tsere.
Babu abinda zai mamaki face tazarar da ke tsakanin kan macijin da Uzaifat bai wuce kamu uku ba, kuma a sannan fa karshen jelar macijin a tsaye take a waje daya bai ma fara gudu ba. Uwar mayu dake labe a cikin duhuwa koda ta ga an kasa mugun tsere tsakanin macijin da Uzaifat sai ta firgita ainun tayi fitar burgu daga cikin maboyarta ta falfala da matsanancin gudu har ta zo ta wuce macijin da Uzaifat ta basu tazara mai yawa, saboda kasan cewar ita a sama taje gudun tana kada fuka fukanta. Tsananin tsoro ne ya Janata ta juyo ta sure Uzaifat tayi Sam da shi don ta tserar da rayuwarsa domin gani take cewa, idan hartayi kuskuren haka tamkar ta sayi ajalinta ne, saboda sanin cewa macijin yana da zafin nama na gaban kwatance.
Bayam macijin ya kure iya tsawon sa yana bin Uzaifat da gudu bai cafkoshi ba, sai ya fara gudu a kasa tamkar doki ne ke sukuwa, a sannane fa tazararsa da Uzaifat ta zamo bata wuce kamu daya ba. A duk sa'adda Uzaifat ya waigo baya sai yaga macijin na bude baki daf da shi zai hadiye shi duk da cewa yana falfala azababben gudu.
Al'amarin daya mutukar baiwa Uzaifat mamaki kenan domin shi as saninsa a gaba daya birnin Darul husuf ma babu maguji tamkarsa. Duk sa'adda akayi tseren gudu shi yake zuwa na daya, kuma yana gudu ba tare da ya gaji ba. Kai saboda tsananin baiwar gudun Uzaifat ma ko da dawakai ya kasa tsere basu tazara yake, amma sai gashi yanzu wannan maciji yana gudun ban alajabi fiye da saninsa.
Jim kadan sai Uzaifat yaji macijin ya fara dungurar bayansa, bai aune ba ma sai yaji ya ce rabin rifarsabta bayabda kaifin hakoramsa al'amarin da ya dugunzuma hankalinsa kenan ya tabbatar da cewa, gudu fa ba zai cecishi ba, don haka sai ya fara zulliya yana kauce kauce yana ratsawa ta cikin duwatsu da bishiyoyi ya shia nan ya can ya jurda nan, shi kuwa macijin yaci gaba da binsa a cikin naci.
Sai da suka shafe sa'a guda suna wannan tseren, amma macijin ya kasa kama Uzaifat kuma sakamakon shige da fice da suke yi ta cikin duwatsu macijin ya gabgabje kansa har ya sami raunika, al'amarin da ya kara fusata macijin kenan ya kara kaimi dadagewa don tabbatar da cewa ya lamo Uzaifat, amma sai abu ya faskara.
Haka dai suka ci gaba da wannan tsere har tsawon sa'a shida a wannan lokacine duk su biyun suka jigata ainun, sai ga shi macijin baya iya gudu da karfi, shima Uzaifat haka. Dukkaninsu sai fama haki suke amma saboda naci sunki su daina gudun.
Kwatsam sai suka iso bakin wani matin kogi. Al'amarin da ya dugunzuma hankalin uzaifat Uzaifat kenan, domin ya san cewa muddin suka shiga cikin wannan koni sai macijin ya hallaka shi, domin ba zai iya gudu ba acikin ruwa. Yayinda macijin yaga sun iso bakin wannan kogi, sai ya dai na gudun yaci gaba sa bin Uzaifat a hankli domin yasan cewa anzo inda zai sami nasara. Babu damar Uzaifat ya juyo da baya kuma babu damar ya shiga cikin kogin don bazai kubuta ba.
Cikin karayar zuciya Uzaifat ya tsaya a gaban kogin ya juyo ya fuskanci macijin ba tare da nufin yakarsa ba, don yasan cewa babu abinda zai iya.
Macijin yaci gaba da tunkaro Uzaifat maimakon macijin ya wangame bakinsa ya hadiye Uzaifat, sai ya cillo jelarsa ta kanannade kafafun Uzaifat ya daga shi sama ya dinga makashi a cikin wannan ruwan kogi. Sai Uzaifat ya nutse can kasan kogin sannan macijin ya dagoshi sama ya sake makashi ciki.
Nan da Uzaifat ya fara fita daga cikin haiyacinsa, ya fara jiyo kamshi mutuwa muraran.
Al'amarin su lafirat kuwa, lokacinda suka yi ta gudu a cikin daji har suka yi nisasosai da inda suka Bari wannan maciji, sai Lafirat ta tsaya cak! Ta daina gudun ta juyo ta kallo baya, amma ko duriyar Uzaifat bata ji ba, sai hankalinta ya dugunzuma ainun ta fara shawarar ta koma sa baya. Ganin Lafirat ta tsayane yasa Abul shaja'a da uwarmayu da yayanta ma suka tsaya. Abul shaja'a ya dawo da wajen Lafirat ya dubeta yace, saboda me kika tsaya anan ki zo muci gaba da gudu domin macinjinan bazai daina binmj ba, face muje karshen wannan daji.
Koda jin wannan batu, sai Lafirat ta harzuka ta dubi Abul shaja'a cikin fushi tace, amma ka bani mamaki, yanzu kana nufin kenan mu gudumu bar Uzaifat a can baya bamu san meke faruwa da shiba? Ka tuna fa cewa Uzaifat dan uwanka ne musulmi , ni kuma ba musulma bace, amma na ga bai kamata mu gudu mu barshi ba cikin balai.
Ni kam dolene na koma na kai masa dauki koda zan rasa rayuwata, tunda shi ma yaceci rayuwata a baya, har sau biyu. Idan ma gujeshi a wannan lokacin nayi butulci. Koda gama fadin hakan, sai Lafirat tafalfala da gudu izuwa baya. Abul shaja'a da su uwar mayu suka tsaya suka yi tsuru tsuru suna kallon junansu suka rasa abinda zauyi tsakanin ci gaba dagudu da komawa baya.
Lafirat taji gaba da gudu iya karfinta, harta iso bakin wannan katon kogi. Tun daga nesa ta hango wannan katuwar macijiya tana ta tsoma uwa a cikin koginnan har ya suma bata sani ba. Al'amarin da ya dugunzuma hankalin Lafirat kenan, kuma ya cire dukkan tsoro daga zuciyarta, don haka sai ta daka tsalle ta dane jikinsa ta ci gaba da hawa samansa tamkar kadanfare na hawa bango, har ta iso inda kansa yake bai saniba. Kawai sai ta zare wani karamin gatari da ke cinyarta ta saribidon macijin. Taje ruwan idon ya fashe jini ya kama kwararowa kasa kamar idaniyar ruwa ra balle.
Macijin yayi wani irin ruri bai san sa'adda ya saki Uzaifat ba ya kama matagungun a kasa. Uzaifat ya nutse izuwa kasan koginnan. Koda ganin haka sai Lafirat ta daka tsalle ta fada cikin kogin ta yi nutso kasa tana laluben Uzaifat. Cikin sa'a kuwa sai ta ji ta rukoshi. Lafirat tadago saman kogin ruke da Uzaifat tamkar taruko gawa tana ninkaya. Har izuwa wannan lokaci wannan maciji na ta birgima da matagungun a gefen kogin, kuma ya haddasa gagarumar kura sakamakon birgimar da yakeyi akan rairayi.
Da kyar Lafirat ta fito daga cikin kogin ruke da Uzaifat ta kaishi can gefe daya bakin gaba. Cikin dimaucewa ta shiga danna kirjin Uzaifat sai ga ruwa na fitowa tacikin bakinsa da hancinsa, amma ko motsawa baiyiba, Sam Sam babu alamar numfashi ajikinsa.
Koda ganin haka sai Lafirat ta fada kan Uzaifat tafashe da matsanancin kuka cikin tsananin bakin ciki. Tsawon yan dakiku tana faman kuka, kawai sai taji Uzaifat ya kama kafadarta. Saboda tsabar farin ciki sai ta tasheshi zaune ta rungumeshi kuma ta bushe dadariya, tana mai kankameshi a kirjinta.
A dai dai wannan lokacine Uzaifat ya hango wannan katon maciji ya sandare jikinsa gaba daya ya zama gawa. Uzaifat ya janye jikinsa daga cikin na Lafirat suka fuskanci juna, duk su biyun suna murmushi, yace menene dalilin da ya sa kike zubar da hawayen ki saboda tsammanin cewa na mutu?
Yayinda lafirat taji tambaya sai ta ce dalilin da yasa kaji ka damu da tafiyata da rayuwata sa'adda na kamu da ciwo shine ya sani zubar da hawaye da kuka a lokacin da nake zaton ka mutu.
Koda jin haka sai shima Uzaifat ya bushe da dariya ya rungume Lafirat yace, tabbas kinyi gaskiya, kuma yanzu ne na tabbatar da cewa akwai so da kauna tsakanina da ke.
Gama fadin hakan ke da wuya sai ga uwar mayu da yayanta da kuma Abul shaja'a sun rugo wajen. Cikin sauri gami da alamun jin kunya Uzaifat ya cire jikinsa da ga cikin na Lafirat ya mike tsaye domin a sannane ya dawo cikin haiyacinsa ya tuna cewa haramun ne a gareshi ya rungumi Lafirat a matsayinta na mace, wadda ba muharramarsaba. Uzaifat yace a ransa tabbas, Hakika sharrin soyayya yafi ga haka kuma tabbas idan mace da namiji suka kasaita shedanne na