Showing 12001 words to 15000 words out of 21146 words
Chapter 5 - Dakarun Musulunci Book 2 By Abdulaziz Sani M Gini.txt
Al'amarin da ya mutukar dugunzuma hankalinsa kenan ya fara tunanin dole ne yasan abinyi cikin gaggawa don ceto rayuwarsu.
A can fadar uwar mayu kuwa a wannan lokaci sarkin fawa ta gama wasa wukakenta na saran nama don haka sai aka fara dauko Lafirat aka dorata akan wani katon teburin karfe, aka kwance sarkar da aka daureta da ita.
Lafirat ta dubi Abul shaja'a suka hada idanu a Lokacin da hawayen takaici ya subuto mata bisa cewa zata mutu bata cika burinta ba na duniya. Koda Abul shaja'a yaga zubar wannan hawaye a idanun Lafirat sai yaji ya kamu da tsananin tausayinta inda yana da ikon ceton rayuwarta da yayi. Sarkin fawa ta dauki wani faskeken gatari mai fadin kai ta daga sama da nufin ta fara datse kan Lafirat kawai sai akaga jarumi Uzaifat ya taho da gudu a sama tamkar an harboshi daga cikin baka ya doki kirjin sarkin fawa da kafarsa.
Take sarkin fawa ta yi sama ta naku da gini ta fado kasa, jini na zuba ta cikin hancinta da bakinta, ko shurawa batayi ba. Koda ganin haka sai gaba dayan kuyangin uwar mayu suka kwashi wukaken sarkin fawa suka fakwa Uzaifat aka ruguntsume da a azababben yaki. Ita kuwa uwar mayu o motsawa batayi ba daga kan karagarta ta mulki. Maimkon ta razana da ganin Uzaifat ma sai harde kafafu ta zuba ido domin taga iya Kar jarumtakarsa.
Lafirat kuwa sai ta fado kasa daga kan wannan tebur da aka dorata sakamakon hautsinin yakin da ke afkuwa a fadar, shi kuwa Abul shaja'a har a sannan yana daure cikin sarkar tsafi.
Uzaifat ya ci gaba da kaiwa kuyangin sarauniyar mayu sara da suka da takobinsa suma suna kai masa, ya zama tamkar shaidani a tsakiyarsu. Duk Sa'adda takobinsa ta hadu d makamansa sai dai kaga tartsatsin wuta na tashi gami da hayaki. Nan fa suka kasa yi masa illah, shima ya kasa kashe ko da guda daya daga cikinsu ne.
A wannan lokaci ne hankalin Uzaifat ya dugunzuma domin yasan cewa muddin aka ci gaba da wannan fafatawa a haka zai gaji su kuwa kuyangin sarauniyar mayu ba zasu gaji ba, tunda su ba mutane bane.
Da zarar ya gaji kwa yasan cewa sai sun sami nasara akansa sun hallakashi. Hakika lokacin da sarauniyar mayu dakuyamginta suka ga Uzaifat tsulum ya fito da ga cikin wannan daki a sama kamar tsunsu sai da suka cika da tsananin mamaki yadda akayi ya kubuta daga sharrin wutarda suka banka wa dakin. Abinda basu sani ba shine, karfin addu'a ce kawai ta kubutar dashi.
Lokacin da Uzaifat ya tabbatar da cewa lallai idan ya gaji kuyangin uwar mayu zasu sami nasara a kansa, sai ya farakaranta wata addu'a ta musamman a cikin zuciyarsa yana mai neman taimakon Allah. Nan take kuwa yaji wani irin sabon karfi da zafin nama suna shigarsa. Ita kanta takobinsa sai ta sauya launi ta zama ja jajir tamkar an gasa ta a wuta. Da zarar ya makamansu sai ka ga makaman nasu sun guntule duk aljanar da ya sari jikinta kuwa sai ya ga ta kama da wuta ta soye kurmus ta zana toka, sabanin da idan ya sari jikinsu basa jin komai tamkar ya sari karfe.
Kuyi min hakuri nan zan dakata Insha Allahu zan dora gobe.
Naku a kullum da koda yaushe UMAR FAROUQ ZANGO
[14/02, 9:09 pm] Umar Farouq: DAKARUN MUSULUNCI
LITTAFI NA BIYU
MARUBUCI. ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI
TYPING UMAR FAROUQ ZANGO
Kafin kuyangin uwar mayu su ankara tuni Uzaifat ya kashe sama da rabin su. Koda uwar mayu taga abinda ke faruwa, sai ta kwalla uban ihu ta mike tsaye zumbur daga kan karagarta, Al'amarin yasa ragowar kuyangin nata suka ja da baya kenan. Shi ma Uzaifat sai ya juyo ya fuskanci uwar mayu, bisa mamaki sai yaga hawaye na zuba a idanunta.
Cikin tsananin takaici da bakin ciki uwar mayu ta dakawa Uzaifat tsawa, duk da kasancewar sa jarumi mai dakakkiyar zuciya sai da hantar cikinsa ta kada, domin bai taba jin kakkausar murya mai among ba tamkar uwar mayu. Uwar mayu tadubi Uzaifat tace, yakai wannna hatsabibin biladama kayi sani cewa, yau ka yanke min burin rayuwa, kuma ka haddasa min bakin cikin zuciya.
Kasani cewa wadannan kuyangi nawa da kashe gaba dayansu ya'yana ne na cikina wadanda ban sami damar haihuwarsu na sai bayan shekara dubu da dari daya ina faman neman haihuwa.
Ba wani bane ya samo min magani haihuwar ba, face sarki sha'aran ibini Naukib na birnin shumbul bisa sharadin cewa, zan zauna a wannan dajin nayi masa gadon hanya na tsawon shekara sittin, sannan ya yantani na koma can ainahin kasata ta haihuwa inda na baro iyayena da kakannina.
A tsawon shekara sittin da zanyi a cikin wannan daji, sarki sha'aran ya tabbatar min da cewa zan haifi yaya dubu uku kuma daya zan tafi dolene na bar masa guda dubu daya da dari biyar, yanzu gashi ka kashe dubu daya daya da dari biyar din, kaga kenan koda na hallaka ka idan zantafi, sai dai na tafi ni kadai ba tare da da ko daya ba.
Daga cikin yayan nawa yanzu ka kashe mafi soyuwa a raina, wadda itace yata ta farko mafi shekaru daga cikinsu, mai bani shawara bisa dukkan alamurana.
Ni kam yanzu da na koma kasarmu ba tare da dan da na haifa ba, gwara ma nima na rasa rayuwata, domin yau shekara ta dubu uku kenan da yin aure ban taba haihuwaba, har na gaji da gorin dangin miji, sannan na samu haihuwar kuna na rasa.
Ya zama dole a gareni yanzu na yi maka kisan gilla domin na huce wannan takaici daka jefani a ciki. Koda gama fadin haka, sai uwar mayu ta zare wata sharbebeyar takobin tsafi dake rataye a bayanta. Ita dai wannan takobi sauya launi take yi ita kadai tana zama kala kala kuma tartsatsin wuta gami da hayaki na tashi a jikinta, tun gabanin ayi sara da ita.
Nana take uwar mayu ta daka wawan tsalle a sama tadira a gaban Uzaifat. Saboda nauyinta sai da gidan gaba daya yayi girgiza tamkar zai ruguje. Kawai sai ta kaiwa Uzaifat mummunan sara da nufin ta fille masa kai cikin zafin nama shi ma ya sa ta sa takobin ya tare saran.
Koda takubban biyu suka hadu sai akayi wata irin gagarumar tsawa, wacce ta firgita sauran yayan uwar mayu suka dimauce suka kama guje guje a cikin fadar.
Tartsatsin wutar da ya zubo kasa kuwa sakamakon haduwar takubban sai ya haddasa gobara a fadar ko ina wuta ta kama ci ganga ganga. Nan fa suka ci gaba da kaiwa juna sara da suka cikin tsananin zafin nama juriya da bajinta babu sassauci.
Nan da nan fadar ta yamutse gaba daya dirkokin gini suka rinka karyewa suna ruguzowa kasa. Duwatsu da aka yi ginin gidan da su suka rinka farfashewa suna ruburbushewa. Kai shi kansa Uzaifat bai taba ganin tashin hankali irin na wannan rana ba.
Sai da aka shafe sa'a uku cur ana wannan gumurzu dayansu bai sami nasarar illata daya ba. A sannane Uzaifat ya tuna cewa ya shaafa dayin addu'a don haka sai ya fara kiran sunayen ubangiji tsarkaka yana mai neman taimakon sa.
Faruwa hakan ke dawuya sai yaga ya raba takobin uwar mayu gida biyu bata san Sa'adda ta saki takobin ta fadi kasa ba, sannan ta ja da baya a tsorace.
uzaifat ya tsaya cak rike da tasa takobin yana kallonta kawai. Ita ba tayi yunkurin gudu ba ko afka masa shima haka. Cikin fushi uwar mayu ta dubi Uzaifat tace, idan ka isa ka yarda wannan takobi tana mu gwada yar kashi ni da kai. Nan rantse da ababan dogarona Saina karairaya ka, nayi gutsin gutsin da sassan jikinka.
Yayin da Uzaifat yaji wannan batu, sai ya yi murmushi, sannan yace, yake wannan muguwar aljana kiyi sani cewa koda wannan takobi ko babu sai na yi nasara akanki da izinin ubangiji na, domin kuwa kina kan bata mabaiyani.
Koda gama wannan batu sai Uzaifat yayi nifa da takobinsa ya karanta wata addu'a ya tunkari uwar mayu b tare da shakkar komaiba.
Koda ganin haka, sai uwar mayu tafara murmushin mugunta domin tasan cewa ta farat daya zata gama da Uzaifat, don haka sai ita ma ta tunkareshi.
Suna haduwa ta kai masa wawan naushi da hannuna guda a fuska, cikin matukar zafin nama na ban alajabi ya sunkuya kasa bata sameshi ba, sai ta naushi dirkar gini mai kaurin kamu ashirin. Take dirkar ta rushe, fadi kasa kafin uwar mayu ta sake kaiwa Uzaifat wani naushi tun Uzaifat ya dunkule hannunsa ya gabza mata naushi a cikin ta tadurkushe kasa tana mai kurma ihu sakamakon tsananin zafin da taji tamkar yayan hanjinta sun karkatse.
Shi kansa Uzaifat sai ya cika da tsananin mamaki bisa yadda ya sami wannan gagarumin karfi. Uzaifat ya sa kafarsa ya sake gabzawa uwar mayu naushi a fuska ta kuga da baya.
Nana take Uzaifat ya take wuyan uwar mayu da kafarsa tafara kokarin mutuwa bata san Sa'adda ta budi baki ba tace kayi min rai ya shugabana. Ina son ka amsa mini tambaya guda daya kafin ka kashe ni.
Koda jin haka, sai Uzaifat ya dauke kafarsa daga kan wuyanta a lokacin da ta dawo gwauron numfashi tamkar wadda ta farfado daga suma. Uwar mayu ta dubi Uzaifat a lokacin da idanunta suka kada sukayi jawur tamkar an gasa dan buda a wuta, ta ce, kai kuwa yaya akayi ka sami wannan gagarumin karfi haka? Shin kana tsafine ko kuwa kana da wani boyayyen sihirin?
Yayinda Uzaifat yaji wannan tambaya sai ya yi murmushi sannan yace, ni bana tsafi, kuma bani da sihiri. Wannan karfi da kika ga na samu yazone daga ubangijina, domin ya nuna fifikon gaskiya akan karya.
Sa'adda uwar mayu taji haka, sai tayi ajiyar zuciya tace, Hakika ubangiji da ya baka wannan karfi shine ubangijin gaskiya, domin yau shekara ta arba'in da biyar a wannan daji duk biladaman da yayi karo da ni, sai na ga bayansa domin ina da karfin sihirin tsafin da babu mai irinsa a duniya face sarki sha'aran.
Koda jin wannan batu sai jikin Uzaifat yayi sanyi da kansa ya kama Ka fadar uwar mayu ya tasheta tsaye suka fuskanci juna, sannan yace ki karbi addinina yanzu ni kuma na yi miki alkawarin zaki koma kasarki tare da ragowar yayanki, domin ki huta da gorin fangin miji.
Uwar mayu tayi murmushi tace bani addinin naka ina marhaba dashi.
Nana take Uzaifat ya biya mata Kalmar shahada ta mai mai ta. Duk wannan abu dake faruwa ragowar yayan uwar mayu na durkushe a can gefe daya kuma a takure suna kallo tamkar ace kyat su fita da gudu. Abul shaja'a da Lafirat ma suna kallon duk abinda ke Faruwa, suna alajabi.
Uwar mayu na gama karanta Kalmar shahada sai wannan sarkar tsafi data daure Abul shaja'a ta bace bat, duk abubuwan tsafin dake cikin fadar suka bace tamkar basu taba wanzuwa ba a wajen.
Uzaifat ya dubi uwar mayu yace, yake wannan aljana kiyi sani cewa daga kin zama yar uwar mu musulma, don haka ina maiyi miki nasiha da kada ki sake cin naman mutum ko na dan uwanka aljan. Ki sani cewa, wannan maita da Allah ya baki ba don kiyi barna bane, sai domin ki zamo tamkar likita ga jama'ar ki tunda kinada baiwar ganin abinda su basu da ikon gani a cikin jikinsu.
Yanzu abinda nake so dake shine ki musuluntar da yayanki kamar yadda na musuluntar dake.
Kafin uwar mayu ta budi baki gaba dayansu suka karanta Kalmar shahada, al'amarin daya jefa Uzaifat Abul shaja'a cikin matukar farin ciki kenan.
Ita kanta Lafirat sai da ta ji ta kamu da farin ciki duk dacewar itaba musulma bace. Uwar mayu ta dubi Uzaifat tace, yanzu menene dalilinku na ratsowa ta ciki wadannan muggan dazuzzuka alhalin shekara da shekaru biladama sun dai na shigo wa saboda sanin masifun dake cikin su? Dajin wannan tambaya sai Uzaifat ya kwashe labarin su tsaf ya zaiyanewa uwar mayu dan gane da tsohuwar gabar dake tsakanin birnin shumbul da birnin Darul Husuf da kuma duk abubuwan da suka faru garesu tun daga lokacinda suka fito yakishi da dan uwansa Ukashat da kuma labarin da Lafirat ta basu na hadin kan da Ukashat ya baiwa sarki sha'aran don aje aci birnin su da yaki.
A karshe ya sana da ita cewa yanzu suna sone suje can birnin shumbul domin ceto rayuwar yan uwansu da kuma rayuwar luhaira yar likita abu sharaz sannan su sato yarima Ukashat don kada yaje ya tono wadannan layu guda hudu da aka binne akasan katangun birnin Darul Husuf.
Lokacin da uwar mayu ta gama jin wannan bayani, sai tayi shiru kuma ta sunkui da kanta kas, tana jin jina al'amarin cikin damuwa. Daga can sai ta dago kai ta dubi Uzaifat tace, hakika akwai gagarumin aiki agabanku domin ita Lafirat tasan irin masifun dake cikin sauran dazuzzukan da zaku ratsa ku isa birnin shumbul.
Shidai dajin mashaarul kais ka gama da shi tunda ka shigeshi harka fafata yaki dawasu daga cikin muggan tsuntsayen cikinsa harka hallakasu. Tabbas yanzu wadannan tsuntsayen duk inda suka ganka bazasu kasance ka ba, domin sun tsorata ainun, lafiya kalau zaku wuce ta cikin dajin. Inda zaku fuskanci matsala shine, aicikin dajin zarsus inda muggan kunamai da macizai suke da kuma dajin Huzurul Has inda tsafaffen maridi yake tare da matarsa da yayansa biyu.
Bisa tarihi sama da shekaru hamsin baya babu wani mahaluki da ya taba ratsa wadannan dazuzzuka biyu ya wuce a raye, walau mutum ko aljan, face da izinin sarki shaaran bin Naukib.
Koda uwar mayu tazonan a zancenta, sai Lafirat ta taso daga inda take zauneta taho gaban Uzaifat tatsaya tace, tabbas abinda uwar mayu ta fadi yanzu gaskiya ne.
Uzaifat yace babu komai mu zamu ratsa ta cikin dazuzzukan biyu, kuma mu wuce a raye da izinin Allah.
Uwar mayu tace, ya kai wannan gwarzon jarumi kayi sani cewa yau shekara arba'in da biyar kenan ina tare da mutane da aljanu a wanann daji ina kashesu da cinyesu. Lallai wannan aiki dana ai nata ba karamin zunubi bane don haka inaso na share zunubina da aikata aikin alkhairi saboda haka nima yanzu na sallama rayuwata bisa yi muku rakiya a cikin wannan tafiya har mu isa birnin shumbul. Idan Allah yasa kun sami nasara akansu kuma ni da ya'yana rayuwar mu, shikenan sai na cika burina. Idan kuma muka hallaka, ina fata mutuwarmu ta zamo sanadin samun rahama a wajen ubangijin musulunci. Koda jin wannan batu sai Uzaifat yaji kaunar uwar mayu ta shiga zuciyarsa, abu san Sa'adda ya rungume ta ba.
Alhamdulillahi nan zamu dakata sai Allah ya kaimu gobe zamu dora.
Zanyi amfani da wannan dama domin na mka sakon godiya dafatam alkhairi ga dukkan mutanen gidanna, muna godiya bisa nuna hadin kai da goyon baya da kuma kara mana kwarin gwiwa da kuke da wadanda suke bin mu ta DM da kuma kira duka muna godiua. Muna jin korafe korafen ku kuma Insha Allahu zamu ci gaba da gyara domin ganin kun samu nishadi da farincki. Haka zalika kuma ina mai neman afuwarku a duk lokacin da kuka ga nayi karamin typing to bawai da gangan nayi bane, akwai uzurin da yake zuwane ni kuma sai naga da naki yin postin gwara nayi ko yaya yake don ganin duka kun samu nishadi da farin cikin.
Na barku lafiya naku a kullum da ko da yaushe
UMAR FAROUQ ZANGO
[16/02, 9:25 pm] Umar Farouq: DAKARUN MUSULUNCI
LITTAFI NA BIYU
MARUBUCI ADBUL AZIZ SANI MADAKIN GINI
TYPING UMAR FAROUQ ZANGO
Nan dai Uzaifat Abul shaja'a Lafirat da Uwar mayu da yayanta suka fice daga cikin gidan suka yi ta sauka kasan bishiyar da gidan ke kai, ta kan wannan matattakala. Koda fara saukarsu sai gidan yaci gaba da rushewa yana neman zubowa kasa. Cikin hanzari suka ci gaba da saukko wa da gudu, aikuwa suna gama sauka kasan bishiyar da gidan ke kai, sai ta nutse izuwa cikin karkashin kasa ta bace bat.
Ba tare da bata lokaci ba kuwa suka afka cikin dajin mashaarul Kais suka kama tafiya ba kakkautawa. Ai kuwa suna cikin tafiyar ne suka ga irin wadannan manyan tsuntsaye na ta shawagi a samansu, amma da zarar sunyi kasa kasa sunyi arba da Uzaifat sai suke yin sama su lulaka ba sa sake dawowa.
Haka dai su Uzaifat suka ci gaba da tafiya, har tsawon kwana uku a cikin dajin mashaarul