Showing 9001 words to 12000 words out of 21146 words
Chapter 4 - Dakarun Musulunci Book 2 By Abdulaziz Sani M Gini.txt
kansa sama don ya ga iyakar tsawon bishiyar, amma sai ya ga ashe bata da karshe. Zagaye da bishiyar tun daga kasanta har izuwa inda ido ka iya gani wata matattakala ce, yace a ransa, to wai shin wane ne ya gidan wannan matattakala haka, kuma a yaushe akayi wannan gagarumin aiki? Duk yadda akayi dai ba aikin bane na mutane sai dai aljanu.
Koda gama aiyana haka, sai Uzaifat ya haukan matattakalar benen a jikin bishiyar ya fara hawa yana yin Sama batare da sanin inda zai je ba. Haka dai ya ci gaba da hawa matattakalar yana kara yin sama, har tsawon sa'a biyu, amma kuma sai ya ga ya kasa kure matattakalar, kuma har a sannan bai je karshen bishiyar ba, al'amarin da ya kara bashi mamaki kenan.
Haka dai Uzaifat yaci gaba da hawa matattakalar dake jikin bishiyar har ya sake shafe wata sa'a biyun. Kwatsam sai ya tsinci kansa a gaban kofar wani makeken gida, a sannane ya gane cewa, ashe gidana akan saman bishiyar. Abin mamakin shine, gidan an ginashi ne da zallan duwatsun wuta, kuma ya kasance mai girman gaske. Yaya akayi wannan gida ya zauna daram akan bishiya? Amsar da Uzaifat ya kasa baiwa kansa kenan.
Alhamdulillahi nan zan dakata sai Allah ya kaimu gobe.
Zanyi amfani da wannan dama dan sanar muku da cewa Insha Allahu gobe za'ayi sadakar bakwai ta yayata. Ina mai gode a gareku kuma ina muku Fatan alkhairi.
UMAR FAROUQ ZANGO
[12/02, 7:57 pm] Umar Farouq: DAKARUN MUSULUNCI
LITTAFI NA BIYU
MARUBUCI ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI
TYPING UMAR FAROUQ ZANGO
Uzaifat ya kasa kunnensa a jikin kofar, amma sai yaji shiru tamkar babu kowa a cikin gidan, ko sautin gyare baiji na. Ya dubi kofar gidan da kyau wadda aka yita da zallan karfe mai kaurin gaske, ya tabbatar da cewa ba zata ballu ba da karfin tsiya, sai kawai ya sa hannunsa ya kwankwasa kofar. Shiru baiji ance komai ba, sai ya kara kwankwasawa da kotar takobinsa. Wannan karon sai yaji ance, wanene nan yake kwankwasa mana koda haka da sanyin safiya?
Muryar Sam irin ta mutane ba ta aljanu ba. Batare da fargabar komai ba Uzaifat yace, nine bakon ku Uzaifat dan sarki uwaisul karni. Na zo ne ku bani abokan tafiyata Abul shaja'a da Lafirat. Idan kuwa kun taba lafiyar su, sai na kashe duk wani mahaluki da ke cikin gidannan, sannan na ruguje gidan naku gaba daya na konashi.
Koda jin wannan batu, sai aka kyalkyale da dariya. Dariyar dai ta matace wadda ta kasance sirirya mai dadin sauraro. Nan take kofar ta bude da kanta, shi kuwa gogan naka, sai ya ruke takobinsa tsirara a hannu ya kunna kai ciki.
Da shigar Uzaifat cikin wannan gida, sai ya tsinci kansa a cikin wata makekiyar fada kasaitacciya, wadda ko a labari bai taba jin mai kawatuwarta ba. Wadansu kyawawan 'yan mata ya gani kimanin su dubu uku a tsaitsaye, sunyi sahu biyu dama da hagu sun ci ado da wani Korean tufafi duk iri daya mai gaske da kyalkyali, kuma mai daukar ido sai kamshi suke.
Wani abin mamaki shine, gaba dayan 'yan matan kammaminsu iri dayane Sak, tamkar an tsaga kara. A nan saman wani gini mai tudu an ajiye wata luntsumemiyar karagar mulki.
Zaune akan karagar wata kyakkyawar budurwa wace ta gaban kwatance wadda kyawunta ya ninka na ragowar 'yan matan sau goma. Tana da cika haiba da matukar kyawun dirin jiki da kyawun sura. Babu wani da namini da zai ga wannan budurwa bai kamu da sha'awarta ba, amma bisa mamaki tana hada ido da Uzaifat, sai ta ga ya daka mata harara bai na damu da kyanta ba, bare taka hankalinsa ta rudeshi.
Koda ganin haka, sai kyakkyawar budurwar ta mike tsaye daga kan karagarta ta taho ga Uzaifat a lokacin da wadannan kuyangi nata suka dare suka bata hanya. Koda ta zo daf Uzaifat sai ta tsaya ta kura masa idanu tana murmushi, kuma tana kallonsa sama da kasa sannan ta kewayashi tana mai dada yi masa wani irin kallo, wanda za'a iya fassarashi da kallo ne na sha awa ko na hilata.
Asannane ta dawo gaban Uzaifat suka fuskanci juna ta dubeshi cikin tattausan murmushi mai karya zuciya tace, haba gwarzo uban sadauka, haba jaurmin jatumai saboda me zaka shigo fadar sarauniyar kyau ta matan duniya, kana turbine fuska alhalin ba a bakin ciki a fadata, kuma ba a yunwa da kishirwa anan, sannan ba a rashin lafiya ko wata lalura da ka iya kefa mutum cikin damuwa? Ka sani cewa, wannan gidana nawa aljannar duniya ce, babu wani abu na jin dadin duniya da babu shi, duk wanda ya dace ya shigo nan bazai tsufa ba kuma bazai mutuba har abada.
Koda sarauniyar tazo nan a zancenta, sai Uzaifat ya daka mata tsawa, yace, ke munafukar Allah karya kike yi, babu wannan rayuwa da kika siffanta a wannan duniya tamu. Ubangijin musulunci shi kadai ne ya shirya wannan rayuwa ga bayinsa, wadanda suka bishi a bayan rayuwar su ta duniya, wato a can makomarsu aljanna.
Ina so ki sani cewa, duk wannan kawar taku da kyawunnan naki bai burgeni ba, kuma ban yarda cewa ku mutane ne ba. Maza ki fito min da abokan tafiyata su Lafirat don tabbas kune mini kuka daukko su daga can inda na barosu, ko kuma yanzunnan na hallakaku ke da kuyangin naki.
Koda gana fadin haka, sai Uzaifat ya daga takobinsa sama, sannan ya budi baki da nufin zai kwala kabbara, kawai sai yaga wanna kyakkyawar sarauniya ta fashe da kuka. Nan take ta dauki Wata 'yar karamar wuka da ke cake a jikin tuffa bisa wani teburi ta yanki damtsen hannunta.
Take wajen ya dare jini ya zubo cikin fusata ta dubi Uzaifat, tace, shin yanzu ka yarda cewa ni bil adama ce kamarka? Jikina irin nakane, zuciyata irin takace. Ina son ka sani cewa asalina na kasance 'ya ga sarkin birnin hindu, aljanune suka satoni suka kawonj nan saboda a duniya babu Wata 'ya mace mai kyawuna. Ka saki jikina ka yarda dani a sannane zan iya gaya maka yadda zaka iya saduwa da abokan tafiyar ka, ka ceto rayuwar su domin suna can a cikin halin tsaka mai wuya.
Sa'adda sarauniya tazo dai dai nan a zancenta, sai jikin Uzaifat yayi sanyi, yaji kamar abinda ta fada gaskiyane, amma duk da haka sai yaji zuciyar sa tana wasuwasi akan hakan. Nan dai sarauniyar ta baiwa kuyanginta umarni da akai Uzaifat izuwa masaukinsa ya huta. Nan take wasu kuyangi hudu suka kama Uzaifat suka ja shi suka kai shi izuwa cikin wani kasaitaccen daki daban mai dauke da wani luntsumemen gado, suka zaunar dashi akan gadon, sannan suka fita suka barshi.
Jim kadan sai ga wasu kuyangin biyu daban, sun shigo da manyan farantan abinci guda biyu. Farantin farko a cike yake da nama kaji kala uku soyayyu gasassu da kuma farfesu. Shikuwa faranti na a cike yake da 'ya 'yan itatuwa kamar su, tuffa lemon zaki ayaba baure da fasadabur.
Bayan kuyangi biyu sun ajiye farantan biyu a gaban Uzaifat sai suka fice daga cikin dakin suka barshi shi kadai.
Uzaifat ya dubi wannan abinci yaji yana shaawar ci, amma kuma sai yaji hankalinsa bai kwanta ba da abincin, kawai sai yayi bismillah gami da karanta wata addu'a ya hau abincin da ci, hat sai da yakoshi.
Wani abu da Uzaifat ya lura da shi shine, lokacin da ya fara wannan adduar sai ya jiyo kamar ana ihu a can wajen dakin da yake ciki, amma kuma da ya kammala addu'ar sai ya dai na jiyo ihun. Bayan Uzaifat ya kimtsa cikinsa sai ya sake yin wata adduar ya tofa a gabas da yamma kudu da arewa da sama da kasa, sannan ya mike kafafunsa akan luntsumemen gadon yayi kwanciyarsa.
Abinka da gajiyayye, kuma ga shi ya ci ya koshi, nan da nan barci ya kwasheshi bai sani ba.
A can fadar wannan sarauniya kuwa tana zaune tare da kuyangin ta sai ga wata kuyangarta ta taho daga bangaren dakin da aka kai Uzaifat.
Da zuwan kuyangar sai ta zube kasa gaban sarauniyar tace, ya ke uwar mayi ta aljanu ai hakanmj ya cimma ruwa, tuni wannan bako yaci wannan abincin da muka kai masa, don haka dafin dake cikin abincin yayi tasiri a jikinsa, ya zama gawa akan gado.
Koda jin wannan batu sai uwar mayi ta bushe da dariya, sannan tayi girgiza ta juye izuwa wata mummunar halitta mai kama da ta dodanniya, ba kyan gani. Suma sauran kuyanginnata sai duka suka zama irinta.
Uwar mayu ta dubi wadansu daga cikin kuyangin ta tace dasu, kuje ku dauko wannan bakon ku kaishi can dakin da muka kulle abokan tafiyar sa dayazo yana nema, si da daddare za'a hadasu su ukun ayi mini romonsu na sha lagwada.
Koda jin wannan umarni sai wadannan kuyangi suka ce, an gama ya shugabarmu.
Nan take mayun aljanun su uku suka bude duka fukansu suka tashi sama suka nufi inda wannan faki yaje, wanda Uzaifat ke kwance a ciki.
Mai makon su shiga dakin ta cikin kofa sai suka ratsa ta cikin gini tamkar danshi ya tsattsafo daga cikin kasa. Take suka baiyana a gaban gadon da Uzaifat ke kwance. Koda suka durfafi Uzaifat sai sukaji wani irin gagarumin zafin wuta na fesowa. Ba shiri suka ja da baya cikin alajabi. Daga can sai suka sake yunkurawa a karo na biyu don su daukko Uzaifat ai kuwa sai suka kara jin wannan zafi ya feso musu tamkar jikinsu zai narke.
A dimauce suka sake rugawa da baya, ba tare da sun kara jarrabawa ba a karo na uku suka fice daga cikin wannan dakin da gudu suka je gaban uwar mayu suka zube suna gaki. Sarauniyar mayu ta daka musu tsawa tace, wannan kuma wane irin shashancin banza ne haka? Ina bakon naman da nace ku dauko a hada da wadancan a dafa mini don suyu luguf da wuri kafin dare yayi?
Koda jin wannan tambaya sai daya daga cikinsu ta dubeta tace, ya shugabata ai al'amarin yafi karfin mu domin sau biyu muna kokarin dauko shi, amma da mun kusanceshi si muji mugun turirin wuta na fesowa zai narkar damu. Koda jin haka, sai uwar mayu ta buga tsaki ta dubi wasu zakwakuran kuyangin nata guda biyu tace, maza kuke ko daukko shi tunda wadannan ragwayen sun kasa.
Nan take kuyangin suka tafi cika umarni. Jim kadan sai ga su suma sun dawo a guje suna haki kamar ransu zai fita suka fadi gaban sarauniya suka yi bayani kamar yadda na farko sukayi. Koda jin wannan batu sai uwar mayu ta mike zumbur a fusace a bude fuka fukanta ta nufi wannan daki inda Uzaifat ke kwance. Ai kuwa sai gaba dayan kuyangin nata suka bita a bata du domin su ga abinda zai faru.
Da shigarta cikin dakin, sai suka iske Uzaifat a kwance yana ta shara bacci abinda, bai ma san abinda ke faruwa ba. Kai tsaye uwar mayu ta durfafi Uzaifat tana karanta wasu dalasiman tsafi. Sai da yarage saura bai fi taku uku ba ta isa daf da shi, sai taji wani irin mugun hucin zafi gami da wata iska mai karfin gaske sun buso mata sai gani akayi an watsota baya tamkar an janyo ta da kugiya sannan aka fyada ta da bango ta fado kasa a mutukar galabaice, kuma rabin fuskarta UA kone.
Koda ganin wannan abu da ya faru, sai gaba dayansu suka firgice ainun, ba shiri suka dauke sarauniyar tasu suka fice da ita daga cikin dakin, suka maida ita can fadartata suka zaunar da ita akan karagar mulkinta. Sarauniyar mayu ba ta dawo cikin haiyyacinta ba, sai bayan dakika dari uku. Koda ta bude idanunta taga kanta a raye, sai ta yi ajiyar zuciya ta hau kallon kuyangin nata daya bayan daya, dagacan sai ta numfasa tace. Yanzu ya zamu yi da wannan shaidanin bako? Tabbas idan har ya farka daga barcin da yake yi bamu hallaka shi ba. Shi zai hallakamu, kuma ya dauki 'yan uwansa.
Alhamdulillahi nan zan dakata sai Allah ya kaimu gobe.
[13/02, 8:50 pm] Umar Farouq: DAKARUN MUSULUNCI
LITTAFI NA BIYU
MARUBUCI ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI
TYPING UMAR FAROUQ ZANGO
Sa'adda kuyangin suka ji wannan tambaya sai duk sukayi shiru suna nazari. Daga can sai mafi shekaru daga cikinsu wata tsohuwa yar shekara dubu biyu da dari shida tayi murmushi tace, ya shugabata ina da dabara. Abinda ya kamata muyi shine, mu banka wuta aikin dakin da wannan bako yake ya zamana cewa ko da ya farka daga barcin ba zai iya fitowaba face wutar ta babbakeshi.
Su kuwa sauran yan uwan nasa guda biyu sai mu daukesu tun yanzu mu yayyakasu mu zuba a tukunya a fara dafasu. Koda jin wannan shawara sai uwar mayu ta cika da farin ciki tace, an gaisheki tsohuwa jalziba hakika kinzo da shawarar da zata fisshemu, in ba dan keba bamusan yadda zami da wannan shaidanin bako ba. Hakika masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce duk wanda ya rigaka kwana dole ne ya riga ka tashi. Nan take uwar mayu taba da umarni aje a dauko Abul shaja'a da Lafirat daga cikin wani daki mai duhun gaske wanda ko tafin hannu mutum baya iya gani a cikinsa.
Nab take kuwa aka je aka fiddo Lafirat da Abul shaja'a sai gasu a daure tamau da wasu irin sarkoki na tsafi wadanda ko yaushe juya wa suke a jikinsu suna kanannadesu. Kallo daya mutum zaiyi wa Abul shaja'a da Lafirat a wannan lokaci ya gane cewa basa cikin haiyacinsu domin idanunsu ma a lumshe suke kuma suna tangadi kamar zasu fadi kasa tamkar wadanda suka sha giya suka bugu.
Bayan an zo dasu Lafirat gaban sarauniyar mayu an watsar da su, sai aka dauko wata katuwar tukunya aka dorata bisa murhu aka zuba ruwa a cikin tukunyar aka watsa cefane a ciki, sannan aka kunna wuta ana dafa cefanen.
A sannane uwar mayu ta dubi sarkin fawarta wata garjejiyar aljana tace, yanzu kece da aiki, sai ki je ki debo kayan aikinki ki fara.
Kafin uwar mayu ta rufe bakinta tuni sarkin fawa ta bace bat ta sake baiyana dauke da wata katuwar akwatin karfe. Koda ta bude akwatin sai ga wukake da adduna da gatari iri iri a ciki sama da kala dari, amma gaba dayan wadannan makamai a dakushe suke, saboda tsabar yawan saran kasusuwan aljanu da dabbobi da akayi da su. Koda uwar mayu ta lura da dakushewar makaman sai ta dakawa sarkin fawa tsawa tace me yasa kika bar kayan aikinki babu washi haka?
Sarkin fawa tace, ki gafarceni ya shugabata ki tuna cewa rabonda mu sami abinci afarutar da muke fita yau shekara guda Kenan, shiyasa na shaafa bam wasosu ba. Sarauniyar mayu tace maza ki wasosu yanzu da sauri.
Nan take sarkin fawa ta shiga aikin wasa makaman ta cikin gidan gaba daya ya cika da Karar karafa kai kace a makera kake.
Duk da cewar Abul shaja'a da Lafirat na cikin gushewar hankali a wannan lokaci da sukaga ana wasa wadannan muggan makamai za'a yankasu, a daddatsasu sai da hankalinsu ya dugunzuma suka kamu da tsananin tsoro. Dama tuntuni Lafirat ta karaya tun a Sa'adda aljanu suka shammacesu sukayi musu surar shirwa sukayi sama da su lokacin da suke zaune acan dajin da Uzaifat ya tafi ya barsu.
A wannan lokaci babu irin kokarin da Lafirat batayi ba, don ta cecesu da karfin sihirinta amma sai sihirin nata yaki yayi tasiri saboda karfin sihirin aljanun yafi nata, bisa dole ta rungumi kaddara ta zuba ido kawai.
Shakuwa Abul shaja'a tun Sa'adda aljanu suka sokeshi sukayi sama dashi sai yaji bakinsa ya rufe ruf ya kasa yin addu'a kuma yaji wata irin muguwar kasala ta baibayeshi idanunsa ma dakyar yake iya bude wa. Suna j suna gani akayi ta tafiya dasu a sama, har aka iso dasu wannan isa aka jefasu cikin dakin duhu aka kullesu.
A dai dai wannan lokaci da sarkin fawa ke wasa wukakenta ne Uzaifat dake barci acan daki yake wani mummunan mafarki mai ban tsoro.
A cikin mafarkin ne aka nuna masa cewa sun shiga cikin wani bala'i na halin tsaka mai wuya suna daf da rasa rayuwarsu. Kawai sai Uzaifat ya kama mutsu mutsu da jikinsa. Tuni a wannan lokaci an baka gagarumar wuta a cikin wannan daki da Uzaifat ke kwance ta kama ko ina saura kiris ta kama gadon dayake kwance akai. Tiririn hayaki da zafin wuta ne yasa ya farka a firgice ya mike tsaye zumbur kawai saiya ga babu ta inda zai wuce ya fita daga cikin wannan dakin face ta cikin wutar, gashi kuma wutar ta fara kama gadon da yake har tana kawowa kafarsa barazana.