Showing 3001 words to 6000 words out of 21146 words

Chapter 2 - Dakarun Musulunci Book 2 By Abdulaziz Sani M Gini.txt

aljanun ya cakawa Abul shaja'a tsinin bakinsa a cinya. Abul shaja'a bai san sa'adda ya kurma uban ihu ba ya sulale kasa sumamme. Kafin aljanin ya zuke jinin Abul shaja'a tuni Uzaifat ya kwalla kabbara ya tsargeshi gida biyu. Nan take aljanin yayi bindiga tamkar mushen gawa ya fashe kuma ya kone kurmus, ya zama toka.
A dai dai wannan lokacune, wani aljanin dabamya make Lafiratda jelarsa yayi mata mugun rauni a gadon bayanta, ita ma ta sulale kasa sumammiya. Koda ganin abinda ya faru sai Uzaifat ya ci gaba da kwalla kabbara yana sarana aljanun, suna babbakewa da tarwatsewa a sama. Koda aka jima a haka, sai aljanun suka ga cewa m, Uzaifat ya zame musu alakakai, kuma indai aka ci gaba da wannan gumurzu a haka, sai ya karar dasu gaba daya duk da cewar, yawansu ya wuce kima, domin lokaci guda yana saran guda dari.

Da yaga yana samun wannan nasara, sai ya sunkuci takobin Abul shaja'a wato ya hada guda biyu ya ci gaba da ragargazar aljanun. Fa dai aljanun suka ga Uzaifat ya Karar da sama da rabinsu, sai suka juya gaba dayansu da gudu suka koma wannan shuri sukayi ta shigewa cikinsa.
Kafin Uzaifat ya ruga inda shurin yake sun gama shigewa cikinsa gaba dayansu. Ai kuwa Uzaifat na zuwa kan shurin sai ya daga takobinsa guda biyu sama yana mai yin kabbara har sau uku, sannan ya sari shurin da dukkan takunban biyu. Faruwar haka ke da wuya sai gaba daya shurin ya kama da gagarumar wuta, sai ga wadannan aljanu da ke cikin sa suna narkewa tamkar an dafa dalma. Nan da nan duk suka zagwanye dayansu bai tsira da rayuwarsa ba.
A wannan lokacine hankalin Uzaifat yakoma kan Abul shaja'a da Lafirat ya yarda takubban hannunsa ya ruga garesu. Koda ya je Kansu ya tsaya sai ya ga haryanzu duk su biyun a sume suke, babu wanda ya farfado, al'amarin da ya matukar dugunzuma hankalinsa kenan. Kuma ya rude ya rasa wanda zai fara baiwa agajin gaggawa daga cikinsu.

Cikin hanzari ya ruga ya dauko sallar ruwan sa ya zuba musu aka a tare. Faruwar hakan ke dawuya, sai duk su biyun suka farfado suna masu yin numfashi sama sama kamar zasu mutu. Uzaifat ya dubi raunin dake jinyar Abul shaja'a ya ga wajen ya fafe yayi rami mai zurfi da fadi kuma har yanzu jini bai dai na bulbulowa daga ciki ba, sannan kuma ya dubi raunin dake bayan Lafirat yaga shima ya dare yayi tsawo, amma bai kai na Abul shaja'a muni ba, amma kuma ita ta fishi jin jiki, don tunda ta kofa tayi rufe da ciki ko motsawa bata sake yi ba, sai ci gaba take da numfashi sama sama.
Cikin matukar karfin hali Abul shaja'a ya dubi Uzaifat yace, maza ka fara baiwa Lafirat again gaggawa kada ka damu dani, domin zan iya yiwa kaina wani abun.
Koda gama fadin hakan, sai Abul shaja'a ya cire rawanin kansa ya daure raunin jinyar tasa tamau don tsaida jini. Cikin gaggawa Uzaifat ya dauko jakar guzurinsanya budeta ya fiddo wani garin magani ya zuba a cikin raunin Lafirat, koda maganin ya shiga cikin raunin taji wani irin zugi da radadi ya shigeta, sai ta kankame jikin Uzaifat ta rafka ihu.

Da kyar ta iya jurewa ya gama sa mata maganin, Uzaifat ya umarceta da kada ta motsa, taci gaba da rub da ciki. A sannane Uzaifat yaga hawayen wuya ya zubo daga Lafirat, nan take yaji ya kamu da tsanannin tausayinta.
Uzaifat ya mike tsaye ya koma wajen Abul shaja'a ya kwance rawanin da ya daure wannan raunin nasa, sannan ya debo garin wannan magani zai zuba a cikin raunin amma sai hannunsa ya kama karkarwa ya kasa zuba maganin saboda sanin irin mugun zafin da zaiji. Koda gamin haka sai Abul shaja'a ya kama hannun Uzaifat ya ruje da kyau yace, Haba ya shugabana bai kamata kaji tausayinta ba, Ashe inda dates kafar tawa ne ya kamata ba zaka iya ba? Maza kasa mini wannan magani domin mu yi maganin zafin ake cikinsa.

DAKARUN MUSULUNCI
LITYAFI MA BIYU
MARUBUCI ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI
TYPING UMAR FAROUQ ZANGO.


Koda gama fadin hakan, sai Abul shaja'a ya rungume Uzaifat shi kuma sai ya sa masa garin maganin a cikin raunin. Ai kuwa Abul shaja'a bai san sa'adda ya kwada kabbara da karfin gaske ba, muryarsa ta amsa kuwwa ta cikin dajin gaba daya, al'amarin da ya janyo gaba daya tsuntsayen dake dajin suka firgice suka tashi daga kan bishiyoyi suka kama guje guje a sama ba tare da sanin inda suka dosa ba. Kai hatta dabbobin dake kwance a cikin ramukansu sai da suka farka daga barci a firgice, suka kama fitowa suna gudu da neman matsera.
Faruwar hakan ke da wuya sai Lafirat ta juyo da kanta ta dubi Uzaifat cikin karfin hali tace, nagode yakai wannan gwarzom jarumi, hakika ka ceci rayuwata a karo na biyu, ban san dame zan saka maka ba. Yanzu gashi ni da abokin tagiyarka mun samu wannan lalura ina mai baka shawara daka hakura da ci gaba da yin wannan tafiya, inyaso mu koma can baya izuwa gidana domin muyi jinya, inyaso bayan mun sami lafiya sai mu sake fitowa.

Abinda yasa na baka wannan shawara shine, lallai kana bukatar gudunmawarmu a cikin wannan tafiya, yinta kai kadai abune mai hadari. A yanzu idan kace zamu ci gaba da wannan tafiya a haka, wahala zata maka yawa domin jinyar mutum biyu zaka yi a lokaci guda, kuma idan wata masifa ta afko maka ba zamu iya kare ka da komai ba face ma mu zamo maka matsala.
Yayinda Lafirat tazo nan a zancenta, sai Uzaifat yayi ajiyar zuciya yace, yake wannan 'yar sarki ki tuna cewa, bata lokacina a cikin wannan tafiya dai dai yake da salwantar rayuwar 'yan uwana da kuma tarwatsewar birninmu, domin kuwa su sarki Sha'aran suna nan akan shirin zuwa su yakemu, kuma muddin dan uwana ukashat zai tona wadannan layu da aka binne a jikin katangar birninmu sai sun sami nasara a kanmu, kinga kenan banga ta zama ba. Ba zamu koma da baya ba, kuma bazan barku a ko ina ba, har sai mun isa dajin karshe tare da ke kamar yadda mukayi alkawari da farko.

Na dogara da ubangijina, kuma nasan tabbas nasan zai taimakeni har na sami nasarar abinda nasa a gabana.
Koda gama wannan furuci sai Lafirat ta kira dokinta na tsafi, yazo daf da ita ya tsaya sannan ta dubi Uzaifat tace, taimaka min ka dorani akan dokina. Uzaifat yace indai kina so na ci gaba da taimakonki bisa halin da kike ciki, sai dai ki ajiye komai na harkar tsafinki.
Koda jin haka, sai Lafirat tayi murmushi tace na amince da hakan. Nan take tayi nuni da hannunta na hagu ga wannan doki nata, ya bace bat.
Faruwar hakan ke da wuya sai Uzaifat ya sunkuya ya dauki Lafirat ya goyata a bayansa ya daureta da rawaninsa tamkar uwa ta goya danta. Abul shaja'a dake zaune akas sai ya dubeshi yayi murmushi yace, to ni kuma ya zakayi da ni yanzu? Ka goya Lafirat a bayanka, ni kuma akan wuyanka zaka dorani?

Maimakon Uzaifat ya bashi amsa, sai ya tafi izuwa ga wata bishiya ya karyo reshenta daya dan dogo ya dawo wajen Abul shaja'a ya mika masa, yace, ungo wannan ka dogarashi ka yi tafiya da kafarka domin kai namijine, cikin tsananin mamaki Abul shaja'a ya dubi Uzaifat yace, haba yarima ya za'ayi kace na mike na taka kafata ina da wannan sabon raunin?
Uzaifat yace ai kashinka bai tabu ba zaka iya takawa. Koda gama fadin haka sai Uzaifat ya juya yaci gaba da tafiya yabar Abul shaja'a a zaune a wajen, kawai sai Abul shaja'a yaga Lafirat ta waigo tana yi masa dariya. Nan take Abul shaja'a ya fusata ya kama wannan ice dake hannunsa da kyau cikin tsananin juriya ya yunkura ya tashi tsaye da kyar, sannan ya fara dogara sandar yana dogarawa da kyar yana cijewa, a wannan lokaci ji yakeyi kamar kafar zata gutsure saboda tsananin zafi da zugin da yake ji.

Haka dai ya jure ya ci gaba da dogarawa yana bin Uzaifat a baya har hawayen wahala na zubo masa. Koda Uzaifat ya juyo yaga halin da yake ciki, sai da tausaya masa, amma sai ya dake bai nuna ya ji tausayin nasa ba.
Haka dai suka ci gaba da tafiya, bayan 'yan sa'o'i sai suka tsaya su huta, sannan su ci gaba da tafiya, har dai suka iso bakin dajin masaharul kais. Da zuwansu sai Lafirat tace, ya kai gwarzon jarumi kada ka shiga cikin wannan daji yanzu, mu zauna anan tsawon kwana uku, domin ni da Abul shaja'a mu kara samun sauki. Komai kankantar taimakon da zami iya baka yana da muhimmanci. Na tabbata cewa, nan sa kwana ukun zamu iya samun karfin jikinmu, mu iya agazawa da wani abin.
Sa'adda Uzaifat yaji wannan batu, sai ya yi shiru baice komai ba, ya dubi Abul shaja'a. Abul shaja'a ya jinjina kai yana mai yi masa nuni da cewa ya karbi wannan shawara ta Lafirat. Ba tare da gardamar komai ba Uzaifat ya je jikin wani dutse ya tsugunna ya sauke bayanta ya dubi raunin nata yaga ya fara kamewa, amma kuma akwai bukatar tayi mata addu'a ya tofa akan ciwan. Har ya yunkura zai fara adduar sai ya tuna cewa, ai Lafirat ba musulma bace, don haka sai ya fasa, ya dawo wajen Abul shaja'a ya tsugunna ya kwance raunin yaga shima nasa ya fara kamewa harma yafina Lafirat warkewa. Cikin mamaki Uzaifat ya dubi Abul shaja'a yace yaya akayi raunin naka naga yayi saurin warkewa haka.
Abul shaja'a yayi murmushi yace, albarka cin addu'a ne ya kawo haka. Me yasa ka fasawa yiwa Lafirat addu'a dazu alhalin da naga kayi niyyar yin haka? Koda jin wannan tambaya, sai Uzaifat yayi shiru bai ce komai ba, kuma ya juya ya dubi Lafirat wacce ke can gefe daya a zaune, tsakanin su akwai tazara bata jiyo abinda suke tattaunawa.

Uzaifat ya juya ya sake fuskantar Abul shaja'a yace, kasan cewa Lafirat ba musulma nace, don haka banga dalilin da zai sa nayi mata addu'a ba. Abul shaja'a yace, wannan gaskiya ne, amma ina Fatan ta samu lafiya da wuri, domin tana da mutukar muhimmanci a cikin wannan tafiya tamu.
A dai dai wannan lokacine Lafirat tayi tati ta kira sunan Uzaifat. Cikin sauri Uzaifat ya mike tsaye ya ruga gareta yace, me kike bukata? Lafirat tace, ina mutukar jin kinshirwa, kuma na duba salka ta naga babu komai a ciki. Uzaifat na jin haka, sai ya duba tasa salkar ya ga itama ko digon ruwa babu a cikinta, kawai sai ya sake rugawa wajen Abul shaja'a ya duba tasa salkar, ita ma babubkomai a ciki. Nan fa hankalinsa ya dugunzuma ya rasa me zaiyi. Kawai sai ya dubi Abul shaja'a yace, ya zama dole na shiga cikin wannan daji na mashaarul kais domin neman ruwan sha tunda wajen dake da ruwa a bayanmu yana da nisa sosai. Zan tafi na barka a nan tare da Lafirat. Ka sani cewa, Lafirat ba zata iya yiwa kanta komai ba, amma kai da sauran kwarinka.

Koda wani abu zai taso muku kayi iya kokarinka wajen kare lafiyar ku, kafin na dawo.
Koda gama fadin haka, sai Uzaifat ya koma wajen Lafirat ya tsugunna a gabanta, ya ce, zan shiga cikin dajin mashaarul kais domin na samo mina ruwan sha, zaku ci gaba da zama a nan har dawo. Koda jin wannan batu, sai idanun Lafirat suka zazzaro ta dubi Uzaifat cikin tsananin damuwa da fargaba tace, in dai saboda ni zan tafi neman wannan ruwa ka barshi zan iya jure kishirwata har tsawon kwana ukjn da zamuyi anan. Uzaifat yayi murmushi yace, haba Lafirat yaya za'ayi ki rayuwa tsawon kwana uku cikin kishi, ai bazaiyiwu ba. Ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai sameni, da izinin ubangijina. Na yi miki alkawarin zam dawo nan da sa'a uku. Ga Abul shaja'a nan zai debe miki kewa kafin na dawo, kuma na tabbata cewa, zai iya baki kariya dai dai gwargwado.

Sa'adda lafirat taji haka, sai ta yi yake tace, bazai iya debe min kewar da zaka iya debe min ba, kuma bazai iya bani kariyar da zaka iya bani ba. Babu abinda zan iya cewa tunda nasan cewa bazan iya hanaka tafiya ba, amma zan kasance a cikin tsananin bakin ciki idan har baka dawo ba kariskeni a raye ba.
Koda jin wannan bayi, sai Uzaifat ya cika da tsananin mamaki, yace ni fa ban fahimci komai ba dan gane da duk wannan bayani naki ba.
Lafirat tayi murmushin yake tace, ai bazaka fahimta ba, domin lokacin fahimtar baiyiba. Fatana kawai shine, ni da Kai mu sake saduwa, kuma mu rayu har zuwa lokacin da zamu cika burikan zukatanmu. Maza ka tafi neman wannan ruwa domin ka dawo da wuri, kasan cewa yanzu fa lokaci abune mai mutukar muhimmanci a garumu.
Uzaifat yace, kwarai kuwa, nan take ya mike tsaye ya juya ya nufi hanyar da zata kaishi cikin dajin mashaarul kais. Koda ya juyo ya hada ido da Lafirat, sau yaga idanunta sun ciko da kwalla sannan fuskarta na nuna tsananin damuwa karara. Kuma tana yi masa kallo mai dauke da alamar tambaya. Kawai sai Uzaifat ya ji tsikar jikinsa ta tashi gaba daya, zuciyarsa ta buga da karfi, ya kaimu da was wasu gami da jimami a ransa, nan take yaji kamar bazai iya tafiya baya bar lafirat a cikin wannan hali ba, amma sai ya daure ya juya ya kunna kai cikin wannan dajin na mashaarul kais, bai yarda ya sake juyowa sun hada idanu da Lafirat ba, kada zuciyarsa ta karye.

Bayan kamar dakika dari uku da sittin da tafiyar Uzaifat, Abul d Lafirat na zaune shiru dayansu baice kala ba, sai dai su kalli juna su kau da kai, kuma ga shi akwai tazara a tsakanin su, koda zakuyi magana da juna sai dai su daga murya.
Kawai sai Lafirat ta yafito Abul shaja'a da hannunta tana mai nufin ya taso ya dawo inda take. Ba tare da gardamar komai ba kuwa Abul shaja'a ya dauki wannan dogon icen da yake dogarawa ya mike tsaye da kyar ya dogara yana tafiya a hankali har ya isa inda Lafirat take, ya zauna daf da ita.

Lafirat ta dubeshi cikin murmushi tace, hakika mutanen birninku sunyi babbar sa'a.
Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama Abul shaja'a yace, ke kuwa saboda me kika fadi haka? Lafirat tayi murmushi ta ce, saboda kun sami magajin sarkinku yarima uzaifat domin na fuskanci cewar, yana da dakakkiyar zuciya ta rashin tsoro irin ta mahaifinsa, kuma sannan yana da tausayi da adalci ga tsagwaron jarumta. Akwai alamun cewa, nan gaba zai iya yin shahara a duniya, idan har ajali bai yi masa gaggawaba. Uzaifat mutumne irin wanda kowace 'ya mace lo son ta mallaka domin zai share mata hawayenta a duk sa'adda yaga yana zuba.
Wai shin kuwa Uzaifat na da macen da yake son aura a rayuwarsa? Koda Jin wannan tambaya, sai Abul shaja'a yayi murmushi yace, ai Uzaifat bai taba yin soyayya ba, duk cewa 'yan matan garin mu da yawa sun shiga mugun hali bisa kamawa da sonsa. Abinda ya kan gaya musu shine, bazai taba yin soyayyaba, ko Aure face yacika burin mahaifinsa, wato yaci birnin shumbul da yaki.

Koda jin wannan batu, sai Lafirat ta cika da farin ciki ta kama murmushi, kuna ta yi shiru batace komai ba. Shi kansa Abul shaja'a da ya ga tana wannan murmushi sai da ya tsargu yace a ransa, anya kuwa babu soyayyar Uzaifat a cikin zuciyar Lafirat?
Idan ma akwai zan gane nan gaba, domin an ce somi somin hauka zuba da yawu ne. Ga ma aiyana hakan ke dawuya a cikin zuciyar Abul shaja'a sai kawai sukayi gaba daya dajin ya kama girgiza kasa na neman darewa ta rufta dasu ciki, al'amarin da ya mutukar dugunzuma hankalin Lafirat da da Abul shaja'a kenan suka kama kalle kalle da hange hange ko zasu ga abinda ke shirin aflo musu amma shiru basu ga komai ba. Cikin karfin hali Abul shaja'a ya mike tsaye yan dogara wannan ice da hannun hagu, sannan ya zare takobinsa da hannun dama ya tsaya yana saurare.

Ita kuwa Lafirat da tasan cewa bazata iya komai ba, sai ta zuba idanu kawai tana sauraron abinda zai wakana. Doke dai tasan cewa, cikin biyu sai abu daya ya faru. Ko su hallaka, ko kuma su tsira da rayuwar su.
Kwatsam ba zato ba tsammani sai ga wani garjejen maridi ya durfafosu, wanda hucin isar bakinsa ta haddasa karamar guguwa, ashe karfin takun sawayensa ne ya haddasa wannan girgizar kasa.
Girman kansa kuwa ya kai na wani dan babban dutse wanda karti shirin bazasu iya rabashi da kasa ba. Maridin yana da manyan idanuwa kwala kwala guda hudu, biyu a kwan girar ido, biyu kuma a daman girar. Yana da wawakeken baki tamkar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login