Showing 18001 words to 21000 words out of 21146 words
Chapter 7 - Dakarun Musulunci Book 2 By Abdulaziz Sani M Gini.txt
ukunsu.
Alhamdulillahi nan zan dakata sai kuma gobe Insha Allahu zaku jini da cigaba nagode.
[17/02, 9:31 pm] Umar Farouq: DAKARUN MUSULUNCI
Littafi na BIYU
Matubuci Abdul Aziz Sani Madakin Gini
Typing Umar Farouq Zango
Cikin tsananin mamaki su Abul shaja'a suka karaso gaban su Uzaifat suka tsaya suna kallon gawar wannan narkeke maciji. Uwar mayu ta dubi Uzaifat tace, tayaya ka sami nasara kashe wannan macijin? Koda ji wannan tambaya, sai Uzaifat ya nuna Lafirat da hannusa yace, ba nine na kashe wannan maciji ba, ga wadda takasheshi, kuma ina badon ita ba da tuni nima wannna macinjn ya hallakani. Itace ta kawo min agajjn gaggawa.
Dan jin haka, sai Abul shaja'a, uwar mayu da yayanta suka sake cika da mamaki, suka kura mata idanu. uzaifat yayi murmushi yace, mamakin me kukeyi? Ai dama dujk tafimu jarumataka, kawai dai don ta sami rauni ne a jikinta saboda haka daga yanzu sau u daina tunanin cewa bata da amfani a cikin wannan tafiya tunda gashi tayi abinda ya gagareni.
Abul shaja'a ya dubi Uzaifat yayi murmushi yace, kaima ba gagararka yayiba, shaafa kayi baka nemi taimakon ubangijinka ba, wanda ya halicceka, kuma ya halicci wannan macinj da Lafirat ta kashe.
Koda jin wannan batu, sai Uzaifat yayi murmushi yace, amma fa kaima ka shaafa da neman taimakon Allah domin bai kamata ka gudu kabarni ba a lokacin da nake artabu da wannan maciji.
Abul shaja'a ya sunkui da kansa kasa cikin alamun kunya. Yace kayi gaskiya ya shugabana. Ina fatan zaka yafeni domin na yi babban laifi.
Nan dai suka zauna gaba dayansu a bakin wannan kofi suka huta, a nan suka kwana sai da gari ya waye sannan suka muke suka ci gaba da tafiya suka durfafi dajin huzurhas inda tsafaffen maridi ke zaune tare da matarsa da yayansa guda biyu.
Tafiya sannu sannu kwana nesa, sai da suka cika kwanaki goma sha bakwai daga ranar da suka fara tafiya sannan suka iso dajin huzurul has.
Da isowar farkon dajin, sai uwar mayu ta daga hannuna tana mai nuni da cewa a tsaya dama itace akan gaba. Ba tare da gardamar komai ba kuwa kowa yabi umarnin ta aka tsaitsaya. Uwar mayu ta kalli gabasa da yamma kudu da arewa ta shaki numfashi, so tayi ajiyar zuciya, kuma tayi shiru ba tare da tace komai ba. Koda ganin haka, sai Uzaifat ya dubeta yace, ya ke yar uwata yaya kika yi shiru baki ce damu komaiba?
Uwar mayu ta sake yin ajiyar zuciya sannan tace, ya kai wannan dan sarki kayi sank cewa, wannan daji da zamu shiga shine mafi hadari daga cikin dazuzzukan uku daomjn a cikinsa ne tsafaffen maridi yake, wanda ake kira da suna zurkas.
Maridi zurkas ya kasance narkeken katon da bazai kwatantu ba da baki, sannan yanada masifaffen karfi na Allah ya isa domin komai kwarin dutse idan ya nausheshi da hannu sai ya dagwargwaje. Kaifin ko tsinin basa tasiri a jikinsa. Zurkas na da karfin sihirin da idan ya bace babu bokan da zai iya ganinsa. Komai yawan rundunar mayaka shi kadai yana iya tarwatsa su.
Shi ma shekararsa hamsin kenan a cikin wannan daji na huzurul has, tunda ya baiyana ya hana shiga da fita. Duk mahalukin da tsautsayi ya kawoshi walau mutum ko aljan ya zama gawa kenan.
Lokacin da uwar mayu ta zo nan a zancenta, sai Uzaifat yayi murmushi yace, ya ke yar uwata ki yi sani cewa, babu wani abintsoro da zai figitani a cikin wannan tafiya, domin koyaushe ina sa ran cewa ubangiji zai fitar da ni daga cikin kowane hali. Shin ki manta ne cewa baya ma kin figitamu da labarin dazuzzukan da muka ratsa kafin mu shigesu, amma sai ga shi mun shige ta cikinsu, kuma sha gumurzu tamkar na zamu Kai labari ba.
Uwar mayu tace, tabbas zancenka dutsena, kuma ina alfahari da irin wadannan makamai nan, domin suna karamin kwarin gwiwa gami da Karin tsoron ubangijin musulunci da dadin imani a gareshi.
Gama fadin hakan ke da wuya, sai uwar mayu ta wuce gaba, sannna yayanta suka bita baya. Abul shaja'a ne ke biye musu, sannan Uzaifat da Lafirat suka jera tare.
Abu kamar wasa sai da suka shafe sa'a tara suna tafiya a cikin dajin huzurul has basu hadu da wani mugun abu ba, face kanan kwari da daidaikun tsuntsaye masu shawagi a sararin samaniya. Al'amarin da ya daurewa su uwar mayu kai kenan suka cika da mamaki, domin ta taba ni a bakin sarki shaaran cewa duk halkitar da ta shiga cikin dajin huzurul has ba zata yi sa'a ba a raye, amma ga shi su yanzu sunyi sa'a tara cif abin da ya samesu. A dai dai wannan lokaci ne rana ke daf sa faduwa, kuna dukkaninsu akwai alamun gajiya a tare sa su. Koda Uzaifat ya lura da hakan sai banga can gabansu ya hango wani wuri mai cike da bishiyoyin masu yawan rassa sannan ga ciyayi masu taushi a wajen tamkar kilishi aka shimfida. Cikin farin ciki Uzaifat ya bada umarni a karasa wannan wuri a yada zango. A guje suka karasa wajen gaba dayansu. Da zuwa sai Abul shaja'a ya kwance a kansa. Ita ma Lafirat ta fiddo wata babbar fatar damisa ta shimfida, ta dubi Uzaifat cikin murmushi mai nuna tsantsar kauna ta ce, zo ka shingida anan ya gwarzona, ina son mu yi yar hira.
Ba tare da gardamar komai ba kuwa Uzaifat yaje ya zauna akan farar damisar itama Lafirat sai ta zauna daf dashi a lokacin da uwar mayu da yayanta suka baje akan ciyawar mai taushi a gefe guda suna hutawa.
Lafirat ta dubi Uzaifat tace, ba ni labarin yadda ake bikin aure a aladarku da addininku.
Koda jin wannan tambaya sai Uzaifat ya kyalkyale da dariya, yace ke kuwa saboda me kikayi mini wannan tambaya?
Lafirat tace, saboda ina son na sami ilimi ne akan al'amarin kafin ya tabbata a kaina, domin a halin yanzu shine burina na biyu a duniya. Fatana na farko shine, na kashe ubana da yar uwata sazirat da hannuna bisa mugun aikin da suka aikata, kuma na dakatar da dukkan barna da suke shukawa a doron kasa. Fatana na biyu shine, na ha na karbi addinina, kuma na zamo abokiyar rayuwarka
Koda lafirat tazo nan a zancenta sai Uzaifat ya tari numfashinta yace, Haba ai sai Yanzu nagane dalilin da yasa kika ki karbar addinina da wuri. Ina tabbatar miki da cewa, zamu iya samun nasarar hallaka mahaifinki da yar uwar ki ba tare da kinyi amfani da karfin sihiri ba.
Ki tuna cewa, duk sihirin da kike takama sa shi mahaifinki ya fiki, to taya kike tsammanin cewa zaki iya hallakashi?
Lokacin da Lafirat taji wannan batu sai zuciyarta ta karaya, tayi shiru ba tace komai ba, tsawon yan dakiku daga can kuma sai ta dago kai ta dubi Uzaifat tace, mahaifina ya taba gaya mini cewa hr abada babu abin da zai iya hallakashi face sihiri. Nayi imani da wannan furuci na mahaifina, shi yasa na sa a raina cewa bazan iya hallakashi ba face da karfin sihiri.
Uzaifat yayi dariya yace, amma dai kin yarda cewa, karfin ubangijin musulunci ya tafi kowane karfi ko?
Lafirat tace kwarai kuwa domin na ga zahiri da idanuna, ni ganauce ba jiyauba.
To tunda haka ne ina mai baki shawara da ki karbi addinin musulunci tun gabanin dama ta wuceki, domin rayuwa bata da tabbas, in mune yau ba mune gobe ba. Ko yanzu idan kika mutu kin mutu ne a matsayin mafita, kuna Allah bazaiyi miki uzuri ba.
Lafirat ta gyada kai tace, tabbas maganarka gaskiya ce, kuma na karbi wannan shawara taka, ina fatan nayi amfani da ita cikin gaggawa.
Koda gama fadin hak, sai Lafirat ta bude salkarta ta kama shan ruwa. Gama shan ruwan ke fa wuya ta dubi Uzaifat, sai ta ga Ashe har ya fara bacci. Kawai sai tayi dariya ta mike tsaye tsam ta koma can gefe daya tayi wat shimfidar dabam ita ma ta kwanta. Kafin cikar sa'a daya gaba dayansu sun bige da bacci, saboda gajiyar da suka sha a baya.
Kash! Rashin sani yafi dare duhu, hakika wannan bacci da su Uzaifat sukayi a wannan wuri shi ne babban kuskurensu.
Shi dai wannan wuri da suka kwanta Ashe wajen shakatawar maridi zurkas ne da iyalansa, kuma kullum sai sun zo wajen su zauna sun huta bayan sun yini suna farauta a adaji.
Har magriba ta kusa yi dayansu daga cikinsu Uzaifat bai farka ba.
Kwatsam sai ga maridi zurkas tare da matarsa maziba da kuma yayansa hiram da hirama, sun durfafo wannan wuri.
Tun daga nesa maziba ta kyallara ido ta hango su Uzaifat a kwance sai ta kama hannun Zurkas da hannun su hirama ta tsai dasu suka tsaya cak! Sannan tace, yau fa mun tsinci tsuntsu daga sama gasasshe.
Cikin mamaki da fushi zurkas ya dubeta ya ce, wannan kuma wace irin maganar banza kikayi haka, ina gasasshen tsuntsun yake?
Maziba tace, dubi can wajen hutawarmu da kyau ka gani. Wasu biladama ne kwance suna shara bacci abinsu.
Zurkas yace, hana maziba shin kin fara makancewa ne? Yaya za'ayi biladama su shigo wannan daji alhalin sama da shekaru talatin suka daina ratsawa ta nan, ba ma biladama ba, hatta aljanu ma sun kauracewa dazuzzukan nan guda uku.
Koda jin wannan batu sai ran maziba ya baci tace, ai idan ni ban makance ba, to kuwa tabbas kai ka makance. Ka tambaya yayanka ka ji ai su yara ne masu kuruciya suna da lafiyar idanu.
Kafin zurkas ya bude baki tuni Hiram yace, ya kai abbana hakika maganar Umma gaskiya ne, akwai biladama a kwance a can wajen hutawarmu, har ma da wadansu aljanu kimanin su dubi daya da doriya. Biladama kuwa basu wuce su uku ba. Tabbas yau zamu sha romo mu more, wai yaushe rabonmu da cin naman biladama da na aljanu? Ai munfi shekara talatin.
Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube zurkas ya dubi maziba, Hiram da hirama yace, ku tsaya anan kada ku biyoni, sai bayan na gama kamasu.
Koda gama fadin haka, sai zurkas yayi girgiza ya bace bat. Bai baiyana a ko ina ba, sai gaban su Uzaifat suna ta shara barcinsu. Nan take zurkas yayi nuni sa hannunsa a garesu sai ga su a cikin wani katon keji na bakin karfe. Zurkas ya ci gaba da kallon su Uzaifat daya bayan daya. Koda ya zo kan Uzaifat, Abul shaja'a da uwar mayu sai ya gane cewa, sun kasance maabota addinin da bai sani ba, ita kuwa Lafirat saibya gane cewa matsafiyace. Nan take ya nisa wata iska daga cikin bakinsa sai barcin Uzaifat, Abul shaja'a da na su uwar mayu ya kara nauyi, ita kuwa Lafirat sai ta farka.
Koda ta gansu a cikin keji a kulle, sai ta mike zumbur a firgice a Sanna ne tayi arba da maridi zurkas. Nan take ta sulale kasa sumammiya saboda tsananin da tayi domin a rayuwarta bata taba ganin halitta mai matukar kwarjini ban tsoro da muni kamarsa ba.
yayinda zurkas yaga Lafirat ta suma sai ya bushe da dariyar mugunta, wadda aminta ya haifar da girgizar bishiyoyin dajin gaba daya.
Nan take ya dauki kejin da yatsa daya ya juya don ya tafi, sai ga maziba da su Hiram sun rugo da gudu izuwa gareshi suna tsalle da murna, amma ita Hirama ba ta farin ciki sosai, domin a rayuwarta babu abinda taje tausayi, sama d biladama. Ko a shekarun baya idan an kama biladama an bata, Sam bata cin namansu, amma tana cin na aljanu.
Lokacin da zurkas ya lura da fuskata Hirama yaga bata farin ciki da wannan garabasa da aka samu, sai ya dubeta ya data mata tsawa yace, ya ke hirama ina mai yi miki gargadi da kada ki kuskura kice zaki kubutarda daya daga cikin wadannan biladama da muka kamo. Ki tuna irin muguwar azabar da nayi miki a shekaru baya, Sa'adda kika kubutar da wadansu biladama daga cikin kejina.
Ki sani cewa, wannan karon idan kika sake aikata hakan ba azaba zan miki ba, zan murder miki wuya ne ki mutu, sannan na dafaki, na cinye namankk domin na huce takaici. Kinji abinda na fada ko bakijiba?
Jikin hirama na karkarwa tace, na ji baya ninka ya abbana.
Nan take suka dunguma su hudun suka nufi gida. Sai da sukayi tafiyar saa hudu, sannan suka iso gidan nasu, wanda ke can sama bisa wani dogon tsauni da ake wa lakabi da hulasul maut.
Ba komai ne yasa ake kiran wannan tsauni da suna hulasul maut ba, face tsananin tsawon sa da fadinsa, domin tua ninka tsaunin dajin mashaarul kais sau uku.
Wani abin alajabi da ya faru shine, a cikin rabin saa maridi zurkas da iyalansa suka gama hawa kan tsaunin suka shige cikin wani katon gida, wanda aka ginashi da zallan itatuwa. Da shigarsu cikin gidan, sai zurkas ya ajiye wannan keji a kasa gefe daya da yake duhu ya soma sai maziba ta kunna fitilun da ke gidan ya haska ke gaba daya.
Su hudun suka zo suka zauna bisa wadansu kujeru domin su huta, dama tun kafin su tafi maziba ta tanadi abinci da ruwan shansu. Man take suka ci suka sha sannan aka shiga tattaunawa akan yadda za a cinye wadannan bakin biladama da aljanu da aka tsinto tamkar dami a kala.
Zurkas ne ya fara magana, ya dubi maziba yace, yake matata Yanzu yaya kike zamu farada wannan naman da muka sami. Shin biladaman zamu farka cinyewa, ko kuwa aljanu? Kinga dai aljanu ne masu yawa zamu iya yin kwana uku muna cinsu, idan muka rabasu gida uku, su kuwa biladama su ukune rak, ko ni kadai aka bar min su kwadayi zasu tayar min.
Kafin maziba ta budi baki ta bada amsa, sai Hirama ta tari numfashinta tace, ai kuwa a fara yi mana dabge da wadannan aljanu kowa yaci ya more, kusan munci nama sosai, inyaso bayan kwana ukun ku dafa biladama kuci abinkj ku uku ku raba dai dai tunda dai ni bana ci.
Koda jin haka, sai zurkas yace, gafara can shashasha, ya za ai mu fara cin nama mara dadi, sannan muzo muci mai dadin da ga baya?
Maziba tace, A'a maigida yarinya fa tana da gaskiya. Ai idan muka fara cin mai dadin, to daga baya muna fara cin mara dadin sai muji ya gunduremu. Shawararta ya kamata mu dauka.
Zurkas yayi tsaki cikin alamun rashin jin dadi yace, to ai shikenan tunda kema kin yarda da hakan.
Duk wannan hira da ake tsakanin zurkas da iyalansa ashe Lafirat tana ji, domin tuni ta dade da farfadowa daga dogon suman da tayi. Koda taji shirin da akayi a Kansu, sai hankalinta ya dugunzuma ta fara kokarin amfani da karfin sihirinta domin ta bude kejin su fita, amma sai sihirin yaki yayi tasiri. Lafirat taci gaba da kokarin tashinsu Uzaifat daga baccin amma sai ta ga sun ki motsawa tamkar sun zama gawa. Al'amarin da ya mutukar kara dugunzuma hankalinta kenan, ta tabbatar da cewa suna cikin mugun yanayi.
A wannan rana dai har dare ya raba sosai Lafirat batayi bacci ba saboda tsananin tsoro, fargaba da tunani, kuma har a sannan babu wanda ya farka daga bacci daga cikjn su Uzaifat basu san ma halin da ake cikiba.
Ita kadai ce a cikin tashin hankali. A wannan lokaci ne nadama tazowa Lafirat, tace Kash! Ina ma na karbi addinin musulunci tuntuni, da yanzu na nemi taimako a wajen ubangijin musulunci ya tserar da mu daga cikin wannan mugun hali. Kawai sai wata zuciyar tace da ita, to ai karbar addinin musulunci ba wani abu bane face ki biya Kalmar shahada.
Har Lafirat ta yumkura zata budi baki ta karanta Kalmar shahada, sai taji wata irin iska mai sanyi ta bugeta takaita kas. Nan take ita ma ta kama barcin dole. Ashe maridi zurkas ne ya buso mata wannan iska kawai sai ya dubeta ya tuntsire da dariyar mugunta yace, wane ke ki ce zaki katse min shirin? Ai tabbas sai mun cinye ku da dai dai kamar yadda muka tsara.
Kashe gari kuwa da sassafe, maridi zurkas ya bude kejin ya debo yayan uwar mayu guda dari biyar ya daddatsa su kamar yadda ake gididdiba nama a mahauta, sannan ya zuba su duka a cikin wat katuwar tukunya K hau dafasu.
Sai da aka shafe sa'a ukucur ana dafa nama ya zamana cewa, yayi luguf luguf sannan maziba ta raba nama izuwa kashi hudu kowa aka bashi nasa rabon.
Koda aka bawa hirama nata rabin, sai ta karba ta mike tsaye ta koma can cikin dakin ta zauna ta faraci.
Tana cikin cin abincin sau idanunta suka ciko da kwalla ta farazubar da hawaye. Ba komai ne yasa hirama zubar da hawaye ba, face tsananin tausayi da takaici.
Nan take zuciyar hirama ta kama tafarfasa kamar zata kone , kawai sai ta aiyana a ranta cewa, komai rintsi da tsanani, kuma koda zata rasa rayuwarta sai taceci wadannan halittu aje cikin wannan keji a daren yau, lallai bazata bari a sake cinye daya daga cikinsu ba.
Alhamdulillahi nan muka kawo karshen wanann littafi na DAKARUN MUSULUNCI littafi na biyu Insha allahu ba da dadewa na zaku jimu da ci ga a cikin littafi na uku.