Showing 1 words to 3000 words out of 29277 words

Chapter 1 - Mugunta 1 Complete Hausa Novels By Khairat.txt

KHAIRAT   

13 Mar 2026

7

https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB
*(Posting room)*









*My WhatsApp group comment section*👇👇👇👇



👇https://chat.whatsapp.com/JL5uulBkRqf3E8JFFxJm8v







MUGUNTA 😈😈😈




by




Khairat 🖤🖤🖤




💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️




Allah ya sa yadda na fara lapiya na gama lapiya.. Allahumma Ameen🙏




BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM



Page 1-2




Dare ne sosai, dan a lokacin kusan karfe biyu na dare, a cikin kungirmin dajin hazdabe da ke garin dan masaki a ƙarƙashin karamar hukumar Bagwai ta jihar Kano.
Zaune ta ke gaban mutumin dake gaban ta,tsohone mutumin kuma kato, shirgegen ,baƙin mutum.
Jikinsa butubutu wanda idan aka gaya ma bai taɓa wanka ba tsaf zaka yadda saboda baqinsa har sheƙin dauɗa ya ke , ya dago ya kalle ta cike da mamaki yace

"Kin binne layar da na baki?"


Da kai ta amsa mai alamar "Ehh" cike da tsoro da Kuma firgici a tattare da ita, zufa duk ta gama rufe mata fuska,ya kalli wani kwano a gabansa wanda ƙoƙon kan jaki ne,aka ɗinke sa da wani baƙin zare.

Dagowa ya yi ya kalle ta, buɗe bakinsa wanda da alama bai taɓa ganin wani abu wai shi brush ko asuwaki ba.
Ƙyalƙyalewa da dariya ya yi a lokaci ɗaya kuma ya haɗe rai kamar ba shi ya yi dariyar ba.

"BARQAAANNN!!!!!!"

Ya faɗa cikin murya mara daɗin sauraro wadda cikin amo ya yi ta har sai da kogon da suke ciki ya amsa wanda duk cike yake da kayan tsaface - tsaface,kawunan dabbobi da kuma zanen mutane a jikin bangon dutsen.

Wata ƴar tsana ya ɗauko mai kama da mutum sak, "kalli wannan ƴar tsanan ki gani." Ya miƙawa Ladiyo wannan ƴar tsanan.

"Tabbas kamar yadda kike so, Ayaman zata wahala a rayuwa, amma kuma zata yi kyakkyawan ƙarshe." Ya faɗa cikin alamar gargaɗi.

Baki buɗe ta karɓi ƴar tsanan tana kallo, kalmar da boka ya faɗa na cewa zata yi kyakkyawan ƙarshe shi ne ya tsaya ma ta a rai, lallai bata ga ta zama ba........








******************************* "Wasshh Allah na, na gajiii."

Wata kyakkyawar budurwa da aƙalla ba zata wuce shekara 20 ba ta faɗa ta na zama a kan ƙaramar kujerar dake tsakar gidan, karkashin bishiyar mangwaro.

Gida ne mai tsarin ginin bahaushe na asali, tsakar gida mai ɗauke da ɗakuna biyu sai ɗakin soro(wanda yawanci na samari ne).

Sai banɗaki babba na amfanin kowa, da madafa babba , a ƙarƙashin bishiyar mangwaron mai bada wata ni'imatacciyar iska mai dadin gaske, ta zauna.

Duk da gidan talakawa ne amma ko Ina na cikin gidan a sha re yake tsaf.
"Kulululu" cikin wannan budurwar ya yi Kara a lokacin da ta kalli madafar tasu , flask ne a ciki na jollop din shinkafa da taji attaruhu da manja a ciki,sannan kuma ta kalli gefen tulin kayan wankin dake tsakar gidan.
Tuno kalaman inna ladiyo kafin ta fita ta yi, ta ce ko da wasa kar ta taɓa ma ta abinci Kuma ta yi wankin da aka kawo aikatau wanda ko sisi bata samu daga kuɗin aikin .

Taba idonta ta yi taji damshin hawaye,kallon tsakar gidan da ta yi ne ya tuno ma ta da lokacin da aka shimfiɗe gawar innar ta, nann take wani hawaye ya zubo ma ta a idanu .
Mutuwa bata ma ta adalci ba, ta ɗauke ma ta mahaifiya a lokacin da ta ke tsananin buƙatar ta.

Kuma har yau bata daina mamakin Ladiyo ba , kasancewa Ladiyon aminiyar innar ta ce wadda a lokacin da ta ke da rai ta ga gata da ƙauna a wurin Ladiyo, bayan mutuwar innar ta komi ya chanja.

Tashi tayi ta fara wankin tunda tasan bata da wata mafita da ta wuce wannan ,zafin da ta ji hannunta ya yi shi ya tuno ma ta da ciwon da taji da safe a lokacin da ta ke haɗa wuta.
Durƙushewa tayi ta fara tunani, shikenan ita rayuwar ta a haka zata ƙare, cikin yiwa Ladiyo da ƴaƴanta bauta?
Ganin tunanin ba shi ne mafita ba ya sa ta tashi ta nufi madafar tasu ta buɗe flask din, tuni yawun ta ya tsinke dama rabonta da abinci tun jiya da yamma da tsahare kawarta,ta kawo mata abincin bikin da su kayi har yanzu gurin magriba ake neman kira,wanko hannunta ta yi tazo ta zauna ta fara cin shinkafar nan ko zafi bata ji,

"AYAMAN"

taji an daka ma ta tsawa daga bayanta juyawar da zatai ta hada ido da inna ladiyo tana hura hanci kamar zakanya ......





Masu karatu ya kuke ganin wannan sabon labarin kuwa? Meye ra'ayin ku? Ku ajiye min a comment section. Muje zuwa 🏃🏃🏃🏃🏃




https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB

*(Posting room)*










*My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇*

https://chat.whatsapp.com/JL5uulBkRqf3E8JFFxJm8v







😈😈😈MUGUNTA 😈😈😈





by





Khairat 🖤🖤🖤






💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️



BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM



Page 3-4


AYAMAN!!!! Ta ji an daka ma ta tsawa daga bayanta juyawar da za tai ta hada Ido da inna ladiyo tana hura hanci kamar zakanya

"Uban wa yace ki taɓa min abinci bayan na ce miki kar ki taba?"

Inna Ladiyo ta fada, fuskar nan kamar hadari, kame-kame AYAMAN ta fara yi a kokarin ta na kare kanta amma sai dai jin saukar lafiyayyun maruka ta yi a duka kunchin nata guda biyu ,kuka ta fashe da shi tana ji tana gani inna Ladiyo ke jibgar ta kamar Allah ya Aiko ta .

Dayake inna ladiyo irin matan nan ne jibga-jibga.

Ayaman kuwa tun tana kuka da iya karfin ta har muryar ta ta dashe.
Sai da Ladiyo ta gaji dan kanta sannan ta ƙyale Ayaman, ta tashi ta shige dakin ta, ba jimawa ta fito ,ta shige bandaki ta yi wanka ta fito wanda duk jiqa-jiqa ne ,tana fitowa ta ji sallamar malam isyaku baban Ayaman,kuma mijinta, ya shigo.

Koh kallon inda yake Bata yi ba tai shigewar ta daki,malam isyaku kuwa ya kalli inda Ayaman ta ke kwance duk ta jigata ,kamar zai yi magana sai kuma ya fasa ya shige dakin inna Ladiyo...


********************************
Zaune yake gaban halwar tsafin sa,wadda wata kwarya ce sai farin abu kamar ruwa a cikin ta,can yana cikin tsaface-tsafacen sa, a cikin wannan abun mai kamar ruwa,sai ga wasu dokuna farare biyu sai kuma baqi guda daya sun zagaye sa,ta ke wannan fararen dokunan suka rikide suka koma wata halitta mara kyaun gani.
Tsugunawa wannan halittun sukayi , sukayi sujjada a garesa (wa'iyazubillah) wani yare suka fara ma junansu kafin wannan halittun suka bace baaattt!!! basu ba alamunsu,dariya ya kece da ita yana faɗin "BARQAAANNN kayi kaɗan kayi jayayya da ni kafin kuma ya dakata da dariya sakamakon ganin wani baqin hayaki yana fitowa daga wannan kwaryar.
Sai ga wata mummumar mata ta fito ta cikin qwaryar,kamar ta daya da wannan bokan,"me ya hada ka da BARQAAANNN? Ta fada fuskar nan kamar hadari, hade fuska ya yi ya cigaba da aikin sa,matar kuma buɗe baki ta yi zata tambaye sa sai Kuma ta fasa ta yi wasu irin surqulle ta koma siffar tsaka ta bi bangon kogon ta fice....




********************************



"Ladiyo? Wai Ina ladiyon ne?"

Wata mata wacce baza ta wuce shekara 35-40 ta faɗa tana karasa shigowa dakin,inna Ladiyo ce ta fito daga dakinta tana masifa yayin da malam isyaku ke biye da ita,
"Mallam wallahi yau ba kai ba abincin nan, wannan shegiyar ƴar ta ka ta ci da rabonka."

Inna Ladiyo ta faɗa tana tura daurin kanta gaban goshi irin ba mutuncin nan, Delu ce ta tsaya tana kallon ikon Allah kafin ta kuma rangada sallama,sai a sannan ne Ladiyo ta lura da ita ,

"Ahh deluwa sannu da zuwa."

ta faɗa tana washe dashashun hakoranta ,

"Yawwa Ladiyo ta faɗa tana kallon malam isyaku a wulaqan ce , Ladiyo ce ta jata zuwa dakin ta da sauri suka rufo kofa.
"Ya ake ciki ne kawata?"
Ladiyo ta fada tana zama akan gadonta na ƙarfe, cike da murna da kuma MUGUNTA delu ta ce

"Wallahi yau nake jin an fasa bikin lamin binta,."

" Kai Amma ma sha Allah haka muke so."
Ladiyo ta faɗa fuskar nan kamar anyi ma ta bushara da gidan Aljanna,
"Toh yanzu da usainan za ayi bikin koh kuwa ? " Ladiyo ta tambaya.

"Bamu tabbatar ba gaskiya amma dai ko ma mene ne bokan nan ya iya aiki wlh." Delu ta ƙarasa cikin mamaki.


" Ay aikinsa kamar yankan wuqa haka yake ." ladiyo ta faɗa,ta numfasa sannan tace "Ni yanzu babbar matsala ta wannan yarinyar, Ayaman , kinga duk bayan wahalar da mukasha da zuwa gurin boka aikin nan be yiba,har yanzu samari sai zuwa suke ita kuma Nabila(yar ladiyo) har yanzu shiru sai mazan banza da suke bin ta ga kuma rashin kunya wlh gaba daya ta raina ni a gidan na." Ta ƙarasa cikin yanayin damuwa.

"Toh Ina inusa( ɗan inna ladiyo )yanzu?" Delu ta fada tana kallon ladiyo,
"Hmmm wannan yaron ay sai a hankali,yanzu fa har dai ya shigo garin nan shike nan na shiga uku daga sata,sai dabanci da yake koyawa yaran mutane yanzu dai har mai garin be kyale ba fah."

"Chabb Ladiyo Anya ba uwar yarinyar nan Ayaman ce ta yiwa yaran ki tsafi ba?" Kinga fah duka ƴaƴan ki su ukun ,Nabila yawon banza,Inusa dabanci,ga kuma nafisa da ta shiga yawon duniya,gaskiya ya kamata ki duba lamarin nan Anya ba sa hannu?" Delu ta ƙarasa tana kallon Ladiyo...






Sa hannu Kuma delu? Toh masu karatu ya kuke ganin wannan labarin?


Khairat 🖤 🖤 🖤....🖊️🖊️🖊️



Nagode,love you all 😘❤️

https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB

*(Posting room)*







*My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇👇*


https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8








😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈


by



Khairat 🖤🖤🖤


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM.

Page 5-6



_____________"Gaskiya ya kamata ki duba lamarin nan Anya ba sa hannu?"

Inna delu ta fada tana kallon Ladiyo,shiru Ladiyo ta yi sannan tace"Lallai biri ya yi kama da mutum,amma indai haka ne, nasan matakin da zan dauka." Ladiyo ta faɗa sannan suka cigaba da firar su wacce duk yawancin ta munafunci ne da irin sharrin da suke haɗawa a gari..

*AYAMAN (p.o.v)*



Tana nan a gurin har aka kira sallar isha sannan ta samu da tashi daga wurin ta rarrafa zuwa akurkin dakinta wanda ko arzikin plaster bai samu ba.

Zama ta yi ta fara kuka me ban tausayi,sai da ta yi me isar ta sannan ta tashi ta dauro alwala,ta dawo dakin ta tayar da sallah,bayan ta idar ne ta daga hannunta sama tana kuka ta fara miqa kukan ta ga Rabbil Arshil Azeem sai da taji zuciyarta ta fara yi ma ta sanyi sannan ta rakuɓa ta kwanta a kasan dakin wanda duk kasa ne,ta lulluba da Wani zaninta.

"Hasbunallahu wani'imal wakeel" Ayaman ta faɗa sakamakon jin saukar wani ruwan sanyi a jikinta,

"Dan ubanki Zaki tashi ko sai na qara zuba miki ruwan?"
Inna Ladiyo ta faɗa tana zaro idanu, rarraba idanu Ayaman ta shiga yi kafin ta bi kofar dakin da kallo wanda Inna Ladiyo Bata Dade da fita ba.
Saukar hawaye taji a fuskarta, ta yi sauri ta goge su tana girgiza kai tana faɗin
"Ba wannan ne lokacin da ya dace nayi kuka ba." tashi ta yi da sauri ta fita daga dakin inda suka yi kichibis da inna ladiyo da bokitin ruwan sanyi zata ta shigo ɗakin saurin tsugunawa kasa ta yi hadi da cewa"Inna ina kwana?'

Harara Ladiyo ta watsa mata mai cike da tsana sannan ta ce "Da ban kwana ba Zaki ganni ne? Munafukar Allah da manzonsa sai wani sim-sim ta ke da kai,ki wuce kije ki ɗebo ruwa Nabila zata yi wanka kuma kinsan ba ruwa a gidan kika kwanta kikai ta sharar bacci."
"Toh inna".
"Keh! Ni fa ba innar ki bace,innar ki ta daɗe da macewa ta bar mana ke annoba kawai."
Ladiyo ta faɗa tana tofar da yawu kamar taga wata ƙazanta a wurin.
Ayaman ta kalli kanta sai asannan taga yadda kayanta suka jiƙe ga sanyin asuba me razana gangar jiki,a sanyaye ta tashi ta nufi gurin randar su ta ruwa,ruwa ta ɗiba ta shiga banɗaki ta fito ta yi alwala ta koma dakinta.
Tsayawa ta yi tana kallon dakin da duk ya jiƙe,rakubawa ta yi a gefe ta buɗe ƙullin kayanta, ta ciro wata doguwar riga ta atampa wacce duk ta koɗe,sakawa tayi sannan ta mayar da hijabin da ke jikin ta,ta tayar da sallah.




********************************


Tafiya take tayi a jikin bango, a siffar tsaka har sai da ta karaso wani gida,madaidaici ne gidan mai shegen kyau duk da kasancewar sa ƙarami.
Shiga ta yi cikin gidan,ta shige har ɗakin matar gidan wacce bata daɗe da haihuwa ba,ɗan jariri ne sabuwar haihuwa a kusa da ita,wannan tsakar ce ta lallaba har sai da ta kusa zuwa kusa da jaririn sai kuma ta koma baya da gudu kamar wacce wani abun ya kawo wa hari.
Ƙara yunƙurin zuwa kusa da yaron ta yi Amma kamar dazu ta kuma yowa baya,sai da ta yi hakan yafi a kirga kafin ta koma gefe ta tsaya tana kallon matar,charaff ! Suka hada Ido, murmushi wannan matar tayi kafin ta dauke yaron ta fita a dakin,tsakar ce ta tsaya tana kallon matar kafin wani lokaci Kuma ta bace baaattt.....



********************************




Tafiya take cikin nutsuwa,hannun ta riqe da bokitin ruwan data debo daga borehole din garin.
"Wallahi ita ce,kin ganta nan duk ta tsufa a gida har yanzu kusan shekarar ta 20 ba mijin aure." wasu mata suka faɗa yayin da suka zo wucewa.
A ranta taji zafin abun sosai,amma in ta tuna aure lokaci ne sai hankalinta ya kwanta.

"Assalamu Alaikum." ta faɗa yayin da ta ke shiga cikin gidan nasu inna Ladiyo da Nabila ta gani a tsakar gidan suna zaune.

Kamar jira Nabila ta ke yi ta hau zaginta, ta uwa ta uba wai tun dazu ɗebo ruwa sai kace an aiki bawa garinsu,ita dai Ayaman bata da tacewa sai dai ta yi kasa da kanta dan tasan koh hauka take baza ta iya faɗa da nabila ba saboda nabilan irin jikin inna Ladiyo gare ta, saboda haka tasan duka zata sha kuma koh bakomi Nabilan ta girme ta.
"Ba zaki wuce ki ƙarasa ɗeban ruwan koh kuwa kin tsaya kina kallon mutane kamar kin ga wasu sabbin halittun?" inna Ladiyo ta fada tana kallon Ayaman, wucewa ta yi ta ɗauki bokiti ta fice daga gida.









Toh fah!!! Lallai inna ladiyo,toh Allah ya kyauta,masu karatu mene ne ra'ayin ku a kan wannan littafin???





More comment more typing......




Khairat 🖤🖤🖤🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️ ....

https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB
*(Posting room)*





*My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇*


https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8










😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈.




by


Khairat 🖤🖤🖤


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️



This page is specially for you zainabu ta 😅❤️



BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM


Page 7-8

Tana tafiya hannunta riqe da bokitin da zata debo ruwan,har ta iso gurin borehole din garin, duk gurin ya cika, saboda manya da yara haka ake diban ruwa tsayawa ta yi tana kallon su yayin da wasunsu ke faɗa akan diban ruwa .

"AYAMAN!!"
Taji muryar tsahare babbar ƙawarta tana Miko ma ta hannu,miƙa ma ta bokitin ta yi ita kuma ta ɗebo ma ta ta bata.
Gaisawa suka yi kafin suka fara tafiya,tsahare babbar ƙawar Ayaman ce duk da Ayaman din ta girme ta dan tsahare bata fi shekara 15 ba.
Amma a haka suke ƙawance da yake tsahare yarinya ce mai hankali da halin manya.

Tafiya suke su na hira sama-sama " Ina ladiyo har yanzu tana nan tana gallaza miki ke kuma kina ƙyale ta koh?" Ay na sani ko baki fada dan ganin ki da sanyin safiyar nan nasan akwai lauje cikin naɗi tsahare ta fada tana kallon Ayaman.

Numfasa wa Ayaman ta yi kafin tace cikin sanyin muryarta " wallahi tsahare abun yana damuna yanzu jiya da naci abincinta baki ga dukan da ta yi min ba, gashi in nayi aikatau ita ta ke karbe kudin ,ga rashin tausayi duk abubuwan sunyi min yawa tsahare yanzu wallahi ba kiji ciki na yadda yake min ciwo ba saboda yunwa." Ayaman ta fada tana zubar da kwallar da ta taru a cikin idonta,haƙuri tsahare ta bata kafin suka yi sallama.

Tun daga kofa take Jin kamshin ƙosai yana tashi,da sauri ta shiga gidan ta tarar da Inna Ladiyo tana suyar kosai a tsakar gidan.

"Assalamu Alaikum. Ayaman tayi sallama tana karasa shigowa cikin gidan,hararar da inna Ladiyo ta aika ma ta ne yasa tai ƙasa da kai ta fara cewa " dama inna layi na tarar a gurin diban ruwan shiyasa... "

"Shiyasa kika yi uwar ki koh ?" Inna Ladiyo ta faɗa tana kallon Ayamam, rasa me zata ce Ayaman ta yi tsuru-tsuru a gurin,can da ta gaji ta shige dakin ta....



Zan cigaba in Allah ya kaimu gobe... Nagode





BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM

Continued to page 7-8

Tana shiga dakin nata taji muryar inna ladiyo cikin masifa tana fadin " Dan ubanki da kika shiga dakin waye zai karasa miki aikin?
Sauri tayi ta fito ta dauki tsintsiya ta share tsakar gidan tass, ta janyo ruwa a rijiya ta fara wanke kwanikan da ba da ita aka ci abincin ba, bayan ta gama ne ta tafi wurin dabbobin inna ladiyo ta share wurin su,tana cikin Sharan ne yaro yayi sallama ya kawo aikatau na surfe kwano 3,inna ladiyo ta amsa ta amshi kudin.

Tana fitowa daga wurin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login