Showing 27001 words to 29277 words out of 29277 words

Chapter 10 - Mugunta 1 Complete Hausa Novels By Khairat.txt

KHAIRAT   

13 Mar 2026

12

zuwa cikin gidan, suna shiga suka zazzauna a kan tabarma suka gaisa da su kawu Bello.
Bayan wani lokaci sai ga Ladiyo ta fito a cikwikwiye cikin gumi da alama ko wanka bata yi ba.
Tana fitowa ta fara washe musu baki tana gaishesu, amsawa suka yi sannan suka fara gabatar da abinda ya kawo su.
Kawu Bello ne ganin rashin dacewar zaman Ladiyo a wurin ganin duk masu gemu ne a wurin ya sa shi faɗin, "Ladiyo ki shiga daga ciki mana ay bai kamata ki tsaya anan ba."
Kallon banza ta bishi da shi kafin tace "Ƴar ka ko tawa? Ina ruwanka da ni? Wato salon ana bada kuɗin ku yagi rabonku ko? Toh wallahi ina nan sai an yi komai a gabana." Ts ƙarashe tana wani juyar da kai haɗe da murguɗa baki.
Rasa mai kawu Bello zai ce ya yi, kawai ya ja bakinsa ya yi shiru.
Malam Isyaku sam bai ji daɗin abinda ya faru ba, amma ganin baƙi yasa sa ya yi shiru dan yanzu Ladiyo ta faɗa mai maganar da ta so.

Buɗe taron da addu'a aka yi sannan aka fara gabatar da abinda ya tara su a wurin, Babban yayan Alhaji Gabatari, wato Alhaji Aminu ne ya nemar wa Gabatari auren Nabeela.
Ladiyo tayi charaf tace"Ay an riga da an gama kawai ku gayi nawa kuka zo da shi da kuma ranar da kuke son ayi bikin."
Sakin baki Alhaji Aminu ya yi da sauran mutanen wurin dan ganin wannan lamari na Ladiyo.
Kallon juna Alhaji Aminu da Alhaji Ahmed abokin Alhaji Gaɓatari.

Ganin yadda Ladiyo tayi babakere a kan lamarin, yasa suka amince a kan nan da kwana ishirin da ɗaya za'a ɗaura aure, sannan kuma suka bada kuɗin tambaya naira dubu ɗari biyar.
Suma ne kawai Ladiyo bata yi ba sakamakon ganin wannan zunzurutun kuɗi, ai kuwa suna ajiye wa tayi saurin ɗauke kuɗin ta maƙe su a hammata.
"Ai Alhaji kuje kawai, auren Nabeela da Alhaji kawa an riga da anyi ne." Ta faɗa tana miƙe wa har da taka rawa sannan tayi cikin gidan da kuɗin.
Alhaji Aminu da Alhaji Ahmed ne suka kalli juna suna murmushi.
Sallama suka yi kafin kowa ya tafi harkokin gabansa, shi dai kawu Bello cike da takaicin matar yayan nasa ya tafi yana Allah wadai da abinda tayi.
Shi kuma malam Sani aminin malam Isyaku ya same shi yace "Kaga dai yadda tayi komai ba tare da ko kunyar idanunmu ba, dan haka ya kamata ka gyara ɓarakar da take gidanka, na bar ka lafiya." Ya ƙarashe yana barin wurin.

Ladiyo kuwa a cikin gida hauka ne kawai bata yi ba, sakamakon ganin wannan zunzurutun kuɗaɗe.




********************************


*_Nafee da Farouk _*

Ko kaɗan Nafee ta ƙi barin Farouk ya fita, ko sallah ma s gida ta umarce sa ya yi shi kuwa da yake an riga an shanye shi, ba abinda ya isa ya yi.
Yanzun ma tana jikinsa ta maƙale mai kamar mayya, shi ya rasa wannan jaraba irin ta Nafee ace kusan duk bayan wasu awanni sai ta buƙaci namiji? Gashi ita kamar ba mace ba haka yake jinta, wallahi a ƴan kwanakin nan ya yi missing ɗin Ummu Kulsum, ga kyau ga hankali ga shi ta san ta yadda take gamsar da shi ko ba tare da sun yi sex ba.
Ita kuwa Nafee banda muguwar ƙazanta da rashin sanin ya kamata ba abinda ta iya sai kuma yawan buƙatarta kamar me.
Wallahi har ga Allah ya fara gajiya da Nafee, kwana uku da aure har ta ɗauko ƴar aiki dan ita tace ita ba baiwa bace dan haka ba ruwanta da wani aiki.
Haka ma ta ɓangaren girki ko cokali bata ɗaga wa, Ummu ce ta zama kukun sun ita take girka musu na safe, na rana da na dare har na da wasu tsirface-tsirfacen Nafee duk ita take yi.




(Kaɗan ma ka fara gani Farouk)





********************************


*_Ummu_*

Lallashin Mu'ayyad take ta faman yi dan kwana biyu ya sako ta a gaba banda rigima ba abinda ya iya.
Dare ne ga wata uwar gajiya da ta tara dan Nafee yau girke-girke ba wanda bata sata ba, har meat pie ta sata yi duk dan ta wahalar da ita.
Gashi dare ya yi maimakon ta huta sai ma wata sabuwar gajiyar da Mu'ayyad yake son ɗaura mata, ringing ɗin wayarta ne ya tayar ta ita taje ta ciro ta a chaji, number Farouk ce wadda ta yi saving da Abban Mu'ayyad.

Ɗaga wa ta yo kafin tace komai taji muryar Nafee, ki dafo min tea ki kawo min yanzu.

Kamar zata kurma ihu haka ta dafa tea ta juye a flask ta dauki hijabi da Mu'ayyad ta nufi sashen Nafee.
Su na zaune a falo su na kallon wani American film ta shiga ta samesu, Nafee ta yi luff a jikin Farouk wanda ya lulluɓe ta a bargo da alama ko kaya babu a jikinsu.
Ajiye tea ɗin ta yi ta miƙe da niyyar fita, "Ɗumamamin meat pie a microwave ki kawo min nan." Taji muryar Nafee cike da izza.
Kitchen ta nufa ta aikata abinda aka sa ta kafin ta bar sashen.
Tana fita ta shaqi wata iska mai daɗi, dan indai tana sashen Nafee bata iya numfashi da kyau dan ba ƙaramin tsoronta take ji ba.
Tana shiga sashenta ta lallaɓa Mu'ayyad ya yi bacci finally ita ma dai ta samu lokacin kanta.






Sai mun haɗu a next page more comment more typing ✍️


Khairat ce ✍️ 🤍



Love you all 💞 🥰😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈



By


Khairat ✍️🤍

https://chat.whatsapp.com/Js1xb4FBd2v0o5mxXpssVr. (Posting room)



My WhatsApp group comment section 👇 👇 👇 👇
https://chat.whatsapp.com/FYbZw86FTfQDpyIkILlMuN





Wannan page ɗin ma sadaukar da shi zuwa ma karanta littafin MUGUNTA da masu comment, ina godiya I love you lodi lodi🙈❤️‍🩹💋♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️.





💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.

_With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.🤌💪_





BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM


Page 49-50


*END OF BOOK ONE*

Haka ana kiran asuba ta farka kamar birkitacciya, alwala ta ɗauro ta tayar da sallah.
Tana jin Mu'ayyad na maganganunsa tayi mai shiru.
Ko ƙarasa azkhar baya yi ba ta fara gyangyaɗi, ay kuwa ta koma gado taja blanket tayi baccinta.



********************************



*_Ladiyo_*

"Ayiririri nanaye." Abinda take ta faman faɗa tana juyi kamar mahaukaciya, "Nabeela? Kinga rabo ko? Hehehe dubu ɗari biyar ba wasa ba." Ta ƙara faɗa tana shinshina kuɗin.
"Wallahi ƙamshi suke, amma wallahi ko zanyi yawo tsirara sai kin aure Alhaji, ga gidan hutu? Ay gwara kawai ko me za'a yi ayi." Ladiyo ta faɗa tana kallon Nabeela.
Nabeela dake zaune tana danna waya ko kallon Ladiyo bata yi ba bare ta amsa mata.
Haka dai Ladiyo ta ƙarasa shirmenta ta kwashe kuɗin ta sa a wata ƙaramar jaka ta rataya a ƙugunta.
Gyale ta saka ta fice daga gidan,
Bata wuce ko ina ba sai kogon bokan kan tudu.
Tana isa ta tarar da Delu na fitowa daga kogon tana saka kayanta, kallon banza suka bi juna da shi kafin ko wacce ta nufi inda zata.
Ladiyo ta cire kayanya ta ajiye a wurin kamar yadda dokar wurin ta tanadar, ita kuma Delu ta nufi hanyar barin dajin.

"Ma gaishe ka ɗan gidan uwar kowa, bokan da babu kamar sa duk faɗin duniya." Ladiyo ta faɗa tana shiga ciki.
"La'ananniyar Allah da Manzonsa , tsinanniya ƴar wuta kuma kafira, me ke tafe da ke." Boka ya faɗa yana wata ƴar ɗariya.


"Boka ƴar wuta kuma, ay baka san tsakanin bawa da ubangijinsa ba."
"Haba Ladiyo, ni da ke fa duk munsan ƴan wuta ne, meye na mai da zance kuma?"

Shiru Ladiyo tayi kafin tace, "Boka ka san me ke tafe da ni ay, babu wata mafita?"
Boka ya yi shiru kafin yace "Kinga Delu da ta fita daga nan? Toh ƙarar ki ta kawo, tana so a lalata auren yarinyar wajenki, a dagargaza miki rayuwa, amma tunda kin zo sai ki fanshi kanki." Ya ƙarasa da wani makirin murmushi.

Shiru Ladiyo tayi ta rasa me zata ce kafin chan kuma sai tayi kamar zata yi magana sai tayi shiru.

"Baza ki fanshi kanki ba? Ni zan fara aikin da aka sa ni tohm."
"Da me zan fashi kan nawa?"

Wata ƙofa ya nuna mata, babu musu ta tashi ta shiga shi kuma ya bi bayanta.

********************************






*Ayaman*


Ayaman kuwa sai ma sha Allahu, dan rayuwa tana tafiyar mata yadda take so, yanzun ma zaune suke su biyu a rumfar inna suna ta hira, dariya take yi sosai dan innar Anas akwai abin dariya ga kuma uwa uba ƙaunar da take nuna mata.
Jikinta yayi luff alamar hutu da kwanciyar hankali sun tabbata, ga wata ƙiba ta ban mamaki da tayi, haske kam ba'a magana dan dama tun chan Ayaman fara ce sai dai Ladiyo da taso ta kawar da farin sakamakon ɓaƙar azabarta.
Sallamar Anas taji, bayan sun gaisa da Inna Ayaman ta gaishe sa, wani kallo ya bita da shi ko ba komai zai samu ladan wannan baiwar Allah r dan ganinta ma kawai na sa shi farin ciki, ledar tsire ya miƙa mata.
Amsa tayi sannan ta miƙa wa Inna, "Ay ni bana cin tsire ko kin manta ciwon sukari da nake da shi." Cewar innar Anas a lokacin da Ayaman ta miƙa mata tsiren.
Innar Anas ce tace "Ku tashi ku bani wuri dare ya yi." Ta faɗi hakan ne ganin yadda Anas ke bin Ayaman da kallo.
Da sauri Anas ya miƙe yana yiwa mahaifiyarsa sallama dan dama ya ƙagu, rufo ƙofar gidan ya yi ya yi mata sallama sannan ya shige sashensu.
Sai da safe Ayaman tayi wa Inna kana ta shiga sashen.
Tana shiga ta ga Anas a bakin ƙofar kamar jiranta yake, ay kuwa ya yi wuff ya chafe ta ta faɗa jikinsa.

Saƙonni suka fara aika wa junansu kafin suka rufo kofa.






********************************


_*Nafee*_

Ita kuwa Nafee sai san barka dan rayuwa tayi dai-dai, sai fachaka take yi a dukiyar Farouk a gefe ɗaya kuma tana tunanin raba Farouk da Ummu.

Yanzu ma shirin tafiyarsu yawon cin amarci suke inda zasu ziyarci ƙasar Dubai daga nan su wuce Spain.

A ɗayan ɓangaren kuma ta kama duk wata ragamar gidan a hannunta, babu mai yin wani abu sai da izininta, ta kori ƴan aiki ta mai da Ummu a matsayinsu, yayin da ta shanye Farouk bashi da bakin magana ko mai tayi dai-dai ne.




_*Ummu Kulsum*_

Baiwar Allah, tana kitchen sai aiki take ga Mu'ayyad a bayanta sai rigima yake dole yasa sai da ta goya sa.
"Ummu" ta jiyo muryar Nafee.
Amsa wa tayi sannan ta fita zuwa wurin ta, tana falo duk ta birkita wurin kamar ba yanzu ta gama gyarawa ba.
"Ina fruit salad ɗin?"
Kame-kame ta fara yi kafin tace "Baba mai gadi bai kawo ba."

Cillo mata ɗari biyar Nafee tayi kafin tace "Ki je ki siyo." Sannan ta cigaba da abinda take.
Ɗaukar kuɗin tayi ta zira takalminta ta fice.

Tsuru tayi a ƙofar get ta ma rasa ta ina zata fara neman fruit, kallon jikinta tayi , jaga-jaga kamar ƴar aiki, ko da yake ƴar aikin ce.

Hawayen da bata so fitowarsu bane suka fara zirya a lallausan kumatunta, ta gaji har ga Allah ta gaji, gani take dama kar ta koma cikin gidan wace irin rayuwa ce wannan? Haka ta cigaba da yiwa kanta tambayoyi kafin ta fita bakin titi dan bata san inda zata nufa ba.
Ƙiiiiiiiiiiiiiiiii ƙarar mota ta bigi kunnena a lokacin da na juya zan bar wurin.




*Ladiyo*
Sai wurin tara na dare suka fito daga wannan ɗakin, tafiyar talala ta ke yi yayin da boka ke ƙyalƙyala dariya.
Wani farin haske ne ya fito daga bangon kogon na dama, neman mafaka Ladiyo ta shiga yi dan jikinta ko ƙyalle babu.
Wannan hasken wurin boka ya nufa , kafin kace me babu boka babu alamarsa a wannan kogon.
Duhu mai tsanani ne ya baibaye wurin wanda ko tafin hannunka baza ka iya gani ba.
Wata uwar ƙara Ladiyo ta saki kafin kuma diff kamar anyi ruwa an ɗauke, kogon ya yi shiru kamar babu wani ɗan Adam da ya taɓa rayuwa a wurin.


_*Delu*_

Tana dawowa daga wurin boka ta shigo gidan da aka fara gyara musu amma ba'a kammala ba, duk da haka suke zaune sai ɗan zani da aka yafa a ƙofar gidan.

Da masifa da banbami ta shigo gidan babu ko sallama, ta ajiye mayafinta ta shiga ɓanɗaki.
Sai da ta fito sannan ta lura da fuskarta da ta gani a cikin ruwan.
" Wayyo!" Ta saki wata uwar ƙara tana taɓa wurin, fuskar ta kumbura kamar fanke sai idanunta da suka yi jaa alamar taruwar jini.

Ɗakin Mariya ta nufa da gudu dan ɗauko mudubi ta kuma tabbatar wa fuskar tace ba ta aljana ba.
Abinda ta gani ne ya tsayar da ita chakk, "Mariya?" Ta faɗa cike da mamaki, waje tayo da gudu tana salati da sallalami.










Alhamdulillah a nan muka kawo ƙarshen book one, book two zai fara zuwa gobe in Allah ya kaimu domin jin wannan chakwakiya, shin waye ya ɗauke boka? Me yasa Ladiyo tayi ƙara? Me Delu ta gani har ta firgice? Sannan wannan zaman lafiya na Ayaman zai daure? Kar ku manta da alwashin da Ladiyo ta ci a kan Ayaman, na gode da gudunmawar da kuke bani a ko yaushe Allah ya saka da alkhairi.



Khairat ce ✍️ 🤍




Love you all 💞 🥰

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login