Showing 6001 words to 9000 words out of 29277 words

Chapter 3 - Mugunta 1 Complete Hausa Novels By Khairat.txt

KHAIRAT   

13 Mar 2026

15

tunda kinga baba baya so."
"A'a Ayaman, gobe kya tafi." tun daga haka suka cigaba da hirar su har dare ya tsala suka kwanta abubuwa da yawa a cikin zuciyar su.









*Bayan wayewar gari*

A bangaren su Ayaman tun da suka tashi ita da tsahare suka yi sallah suka kama aikin gida basu suka kammala ba sai wajen bakwai na safe sannan sukayi karin kumallo suka shirya domin zuwa gurin maigari.

Bayan mahaifin tsahare ya gama shiryawa suka fito daga gidan suka ɗauki hanyar fadar maigari su uku dan umma tana gida bata biyosu ba.



*A bangaren LADIYO*


Bayan ta tashi Bacci taga rana ta taake sosai, tsaki ta yi ta tashi ta fita daga ɗakin. Tana fita tsakar gidan taga yadda rana ta fito sosai kamar ba sanyi ake ba.

Botiki ta dauko zata debi ruwa a randa taga ya qare, tsaki ta kuma yi, ta zauna akan botikin cike da jin haushi ta furta "Zaki dawo ki same ni ne." kafin ta ja kuma jan wai tsakin ta fita da botikin ta ɗebo ruwa ta yi wanka ta dafa taliya.

Ta zauna tana ci kenan bafade ya yi mata sallama, amsawa tayi kaana ta dauki mayafi ta leqa.
" Lapiya malam?" Ladiyo ta tambaya ganin ba fade a qofar gidan Kuma tasan ita ba laifin da tayi.
" Lapiya kalau, maigari ne ya aiko ni ana neman ki a fada." ba faden ya fada yana kokarin tafiya.
"Dan Allah tsaya ta tsayar da shi, me nayi? "

" In kinje fada kya sa ni." wannan ba faden ya fada kamin yayi wucewarsa ya bar Ladiyo tana tunanin me ta aikata har ake neman ta a fada.

Komawa gidan ta yi ta ƙarasa cin taliyar ta sannan ta saka hijabi ta fito ta kama hanyar fada...







*Bangaren delu*



Bayan ta kammala gyaran gidan ta chanchada kwalliya da kayan sallan ta, doya da kwai ta soya wacce tasa malan surajo ya siyo.

Suna zaune a tsakar gidan tana bama mijin nata abinci a baki a lokaci daya kuma wani farinciki ne fal a zuciyarta.

"Gaskiya dole na koma wajen boka na kan tudu domin aikinsa yana yi sosai." Delu ta faɗa a zuciyarta tana kallon yadda malam surajo yake nuna ma ta kulawa, mutumin da bai sakin fuska da murmushi shine yau har da fara'arsa .

"Ahh ah."inna wannan dabgen ake ja a gidan nan." Mariya ta fada tana fitowa daga ɗakin, nima a zuba min nawa." ta faɗa tana miqo kwano.
"Sai yanzu kika tashi mariri yar baba." malan surajo ya fada yana washe baki.
Cike da mamaki Mariya ta amsa da "Eh baba na tashi."

" Toh sannu da tashi, delu a zuba mata abincin mana." malan Surajo ya faɗa yana kallon delu wacce ta ke ta washe baki dan ji ta ke kamar yau sallah a gurin ta.

A haka delu ta yini cikin annashuwa da farinciki Dan Gani take kamar wahalar ta ta yanke.....







Sai mun hadu a next page ... Love you all 😘 ❤️




Khairat 🖤 🖤 🖤 🖊️ 🖊️https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB
*(Posting room)*



*My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇*



https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8



*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈






Written


By




Khairat 🖤🖤🖤





Dedicated to MUGUNTA hauda novel readers.




BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM




Page 13-14









A haka delu ta yini cikin annashuwa da farinciki Dan Gani take kamar wahalar ta ta yanke....







*LADIYO*


Tana tafiya tana ta faman tunanin me yasa ake neman ta a fadar maigari.

Tana isowa cikin gidan maigari aka yi mata iso zuwa inda maigari yake, zuwan ta wurin ke da wuya ta hango su Ayaman zaune cikin ɗakin.
Wata uwar harara ta aika wa Ayaman wanda yasa cikin Ayaman ya kaɗa.

Zubewa ta yi ta kwashi gaisuwa kamar ba abinda ta gani wurin maigari, bayan an amsa gaisuwarta ne, maigari ya nemi sanin ko wacece ita a wajen Ayaman.
Bayani ta yi akan cewa ita ce abokiyar zaman maman ta tun kafin ta rasu.
"Ina mahaifin ta?" Maigari ya kuma tambaya.
"Ranka ya daɗe, mahaifinta yana wajen zaman banzan da ya saba, ba aikin fari bare baƙi." ladiyo ta fada tana qara russunar da kai.
Maigari ne ya yi umarni da a je a kira mahaifin.
Bayan malam isyaku ya iso ya miqa gaisuwa wurin maigari sannan ya yi bayanin matsayin sa a wajen Ayaman.

Ayaman aka bukaci tayi bayani akan me yasa batason zaman ta tare da su Ladiyo, ta fara bayani kamar haka:
"Allah ya baka yawan rai, inna Ladiyo ta kasance kishiyar uwa mai mara tausayi da imani a gareni, tun bayan rasuwar mahaifiyata wacce aminiyar inna ladiyo ce." Ta numfasa kafin cigaba kamar haka.
"Inna ladiyo da ƴaƴanta sun daɗe suna cizguna min a rayuwa kuma na dade Ina jurewa, ina neman alfarmar a nema min wani gurin zama ba wai gidan mu ba." Ayaman ta karasa fada cikin muryar kuka.


Maigari ya numfasa kafin ya kalli Ayaman da take ta sheƙar kuka tsahare na rarrashin ta.
Maigari ya kuma kallon Ladiyo da malam Isyaku da suka yi tsuru-tsuru a gurin, sannan yace" malam isyaku kaji abinda ta fada ko"? .

"Naji ranka ya dade, muna neman afuwa kuma zamu gyara insha Allah ."

Maigari ya koma kan Ladiyo yace "ke baki ce komai ba."

"Ranka ya dade ay malam ya gama magana, muna neman afuwa kuma baza mu ƙara ba." ta karasa fade tana russunar da kai.

"Ayaman, kinji me iyayen naki suka fada, zaki haƙura ki koma gidan da zama ko koh, ki bi ra'ayin ki."


"Na hakura ranka ya dade" AYAMAN ta fada tana ƙara matsar kwalla.

"To Masha Allahu, dama maslaha muke nema Kuma tunda kin ce kin yafe Kinga shikenan komai yayi daidai" maigari ya fada yana washe baki.

Anan wurin su AYAMAN suka kammala sulhu suka koma gida, a hanya ne tsahare ta fadawa AYAMAN abinda tayi bata kyauta masu ba, kamata ya yi taqi hakura har sai an hukunta su ladiyo.

AYAMAN dai shiru tayi tana kallon tsahare na masifa dan ta rasa abin fada, dama chan bata so aka kai su Ladiyo gaban Mai gari ba.

Haka suka karasa kan hanya inda tsahare da baban ta suka kama hanyar gidan su, ita ma Ayaman suka shige gida...



*DARE*

Tun komawar su AYAMAN gida ladiyo ke ta nan nan da ita tana lallaba ta har dare ya yi suka kwanta.



(An ya kuwa ladiyo)






*DELU*


A bangaren delu kuwa sai mulki ake zubawa a gidan, dan yanzu malam surajo ya zama tamkar bawan ta (wa'iyazubillah Allah ya cigaba da tsare mu).

A yanzu ma kuwa zaune ta ke kan tabarma da nama gashashshe a gaban ta tana ta cillawa baki, hade da lemo na kwalba da ta ke kurba a hankali, yayin da malam surajo ke zaune gaban ta Yana mata firfita.

Yaro ne ya shigo gida ya gaishe su kafin ya ce ana sallama da Mariya, baki delu ta washe kafin ta ce " wane yake sallamar da ita? "Alhaji gabatari ne."

Fara'ar ta ce ta qaru, kafin tace " je ka ce tana zuwa."
"Toh" yaron ya fada yana fita.

"Mariya! Mariya! Ina kike be yar baba?" Delu ta daga murya tana Kiran Mariya.

"Gani inna."

"yawwa maza je ki shirya alhaji Gabatari ne ya zo."

"Dan Allah mama" Mariya ta fada tana daka tsalle kafin ta shige ɗakin da gudu.

Dariya delu ta yi sannan ta juya ta kalli malam surajo, "Kai kuma ka wani zauna kana kallo na , dallah ka tashi ka bani wuri ka wuce kayi bacci."

Sumsum malam surajo ya tashi ya shige dakin ya kwanta kamar wani wanda ake controlling, delu shewa tayi kafin ta ce "lallai malam na kan tudu ba wasa ba." sannan kuma ta ƙara sheqewa da wata dariyar.

Mariya ce ta fito cikin shaddar ta blue da mayafi red hade da takalmi da jaka duk red, ga shi ta ci Wata uwar kwalliya da acuci.

"Kai, Ma sha Allah, wannan kyau haka maririn baba, kinyi chass abinki." Mariya cike da jin dadi ta kalli uwar ta ta kafin tai ma ta sallama ta fita.
Tana fita kofar gida ta tarar da alhaji gabatari jingine gaban motar sa kirar golf irin ta kayan miyan nan.
Wata farar shadda ce a jikin shi, sai gilas da ya ƙwama a fuskar shi.
Cike da zumudi Mariya ta karasa kusa da shi, Dan ba'a taba kiran Mariya ba wai ana sallama da ita ba.
Alhaji gabatari ne ya bude bakinsa wanda in ban da warin sigari ba abinda yake, yace "Barka da fitowa gimbiya sarautar mata, fatan kina lapiya."


Wani farrr Mariya ta yi da Ido, kafin ta bude dashashun hakoran ta tace "yawwa alhaji , Ina lapiya ya kasuwa."

"Lapiya kalau mariri." alhaji gabatari ya kuma fade.

A haka suka cigaba da hirar su har dare ya tsala suka yi sallama.

Mariya na shiga gida ta ga delu ta dade da bacci, ita ma ta shige dakinta ta kwanta ba tare da ta damu ta sauya kaya ba.



Asuba ta gari!!!







*AYAMAN*



MAFARKI



Wata mata ta hango, zaune akan wata kujerar karfe wacce duk ta yi tsatsa ta lalace, kallon qurilla matar ta ke yi wa Ayaman wanda ya sa tai maza ta tashi ta fara gudu.
Tana cikin gudun ta fara hango wani haske mai matukar kyau, ta nufi hanyar da zai kaita wurin hasken ne wannan matar ta riqo kafarta da wata kaca ta qarfe, ihu ta fara yi tana neman taimako.

Yayin da wannan matar ke dada janyota, kusa da ita , tazo gab ta ita ne ta farka daga mafarkin.

"Hasbunallahu wani'imal wakeel." Ayaman ta fada tana tashi a firgice, kanta ne taji ya sara mata.
"innalillahi wa'inna i'laihi raji'un." ta faɗa cikin tashin hankali, addu'ar da taxo bakin ta kawai take yi kafin ta ji ciwon kan ya ragu.
Kiran sallar asuba da taji ana yi ne yasa ta tashi ta fita tsakar gidan nasu, hasken farin wata, da Kuma niimatacciyar iskar asuba ne yasa ta lumshe Ido.
Ta Dade a tsaye a wurin kafin ta shiga bandakin da ko arzikin fitila bai samu ba, tsarki tayi kafin tayi alwala ta fito.

Dakin ta koma tana tuna mafarkin da tayi.
Raka'atanul fajir ta fara yi kafin taji iqama a masallacin unguwar tasu sannan ta tada sallah.

Bayan ta idar da sallah ta yi azkhar sannan ta fito tsakar gidan, randa ta duba Taga da ruwa a ciki .
Kwanika ta debo ta fara wanke wa, tana yi tana mitar kazantar Ladiyo dan wasu kwanikan har sun bushe ba'a wanke ba.
Shara tayi bayan ta kammala wanke-wanken, sai da ta sha re gidan tsaf sannan ta zauna ta huta dan a lokacin takwas ta kusa .

Bokiti ta dauko zata debi ruwa, Taga ruwan ya qare, "ya salaam." ta fada tana dafe kanta da hannu. Harga Allah bata son debo ruwa Dan wannan ranar safiyar da zafinta.

Ba yadda ta iya, haka ta dauki bokitin ta fita debo ruwa.


Kamar kullum gurin borehole din nasu a cike yake da mutane manya da kanana ana ta diban ruwa.

"Wallahi na riga ki baki Isa ba" wata yarinya wacce bata wuce shekara 10 ba ta fada tana ture wata budurwa wacce ta Kai kusan shekara 15.
"Ni sa'ar ki ce Amina? Iyi ." wannan budurwar ta fada tana hararar yarinyar.
"Ehh din ay ke kika zubar da girman ki shiyasa muka bi muka ta ke shi." yarinyar ta fada tana murguda baki irin na marasa kunya.

Nan fa fada ya kaure tsakanin yarinya da budurwa. Ayaman ta tsaya tana kallon I kon Allah taji an fincike bokitin hannun ta.
"Anas?"

"Ayaman."

Kallon shi take kafin ta gaishe shi , amsawa anas ya yi kafin ya amshi bokitin yace taho muje, "Ina zamu kuma? "

Binshi tai suka tafi, Mai ruwa ta samo mata ya kai shi har gida, amsar ruwan ta yi ta rinqa cika ko Ina na gidan har sai da ya cika taf.
Fitowa ta yi Taga anas har ya sallami mai ruwan, " nagode sosai ." Ayaman ta fada da wani murmushi a fuskarta.
"Bakomi, yiwa kaine" Anas ya fada yana mayar ma ta da martanin murmushin.

"Bari na shiga gida sai anjima"

"Dan tsaya Ayaman." tsayawa ta yi kafin ta cigaba da cewa "ya maganar mu ta waccan ranar"?

Rufe fuska ta yi ta shige gida da gudu, yayin da anas yayi tafiyar da Yana dariya.

Tana shiga gidan ta bige inna ladiyo wacce ke wanke fuskar ta, Dan da alama daga bacci ta tashi.
" Kam bala'i!! , tass !! inna ladiyo ta wanke fuskar Ayaman da Mari, " ba Kya Gani ne da Zaki buge ni?"

"Kiyi hakuri inna" Ayaman ta fada tana ƙasa da kai .

Tsaki ladiyo ta yi sannan ta wuce ta shige dakinta, sum sum AYAMAN ta wuce ta shiga dakin ta ta zauna akan zanin dake shimfide a kasa...










More comment more typing ✍️✍️



Love you all 😘 ❤️




Khairat 🖤🖤🖊️ 🖊️ 🖊


️https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB
*(Posting room)*



*My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇*


https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8







*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️



😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈





By





Khairat 🖤🖊️✍️




This page is dedicated to aunty Reemah ❤️





BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM



Page 15-16




Tsaki Ladiyo ta yi sannan ta wuce ta shige dakinta, sum sum Ayaman ta shige na ta dakin, zama ta yi a kan shimfidar zanin dake shimfide a kasan dakin.

Tunanin Anas ne ya fado ma ta a rai, wani lallausan murmushi ta saki tana qara jin soyayyar Anas a ranta, wadda bata ta'ba sanar Mai ba.
Tun mahaifiyar ta na da rai Anas ke hidima da ita,yana nuna ma ta ƙauna da so wanda bata fahimta ba a wannan lokacin, a gaskiya in ta yi rashin Anas ta yi babban rashi, Amma taya Ladiyo zata bari ya aure ta.

Tana yawan mamakin irin qeta ta ladiyo, qiri-qiri ladiyo ke dakile maganar auren ta da zarar ta taso, kusan Maza uku ne suka zo neman auren ta, ladiyo ke zuga malam isyaku ya hana auren.
Haka bayan rasuwar mahaifiyar ta, dangin ta su adda asiyah ƙanwar innar ta, tana iya tuna me ya faru sosai a ranar.
"Nifa babu inda za'a kai min 'ya, haka kawai, ku barmin ɗjya ta Ina da matar da zata kula da ita." malam isyaku ya karasa fada yana kallon su addah Asiyah ɗaiɗai.

"Haba malam isyaku, ay abun bai kai haka ba, naga Ayaman duk diyar mu ce, tunda ay 'ya'yan Zainab (mahaifiyar Ayaman) duk 'ya'yan mu ne koh koh?"
Adda suwaiba, babbar yayar inna ta , ta numfasa sannan tace "batun matar ka ay ba wanda bai san halin ladiyo ba, auren ta na farko, ta kori kishiyar ta, ta gallaza ma mijin nata daga karshe ya mutu wanda mutane ke zargin ita ta kashe shi, gashi wani irin uƙuba ne bata bawa Zainab ba duk da cewa ita ta ma ta sanadiyyar shigowa cikin gidan?"

"Wallahi ƙarya ce,munafikan banza da hofi kawai, wannan wace irin jaraba ce , habaa." Ladiyo da ta fito daga dakinta tana riqe da zani a hannu ta fada tana tura daurin dankwali gaban goshi.

Ta cigaba da fadin "Kuma yarinya tana nan, ko yanka naman ta zamu yi mu ci dole ku bar ta a nan." ta tsaya a kan tabarma da su addah asiyah da addah suwaiba da sauran yan uwan mahaifiya ta ke zaune.

"Kehh Ladiyo ki shiga tai tayin ki wallahi, Dan ruwa ba sa'an kwando bane, yawwa."Addah Asiyah ta fada tana miqewa daga zaman da take.
Yatsina fuska ladiyo ta yi sannan tace"wannan Kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login