Showing 18001 words to 21000 words out of 29277 words

Chapter 7 - Mugunta 1 Complete Hausa Novels By Khairat.txt

KHAIRAT   

13 Mar 2026

10

ya yi kyau..." Ya faɗa yana cilla ma ta kaza wadda bisa umurnin Ammi ya siya.
Ɗago kai ta yi ta ga yana ficewa daga ɗakin, "Ikon Allah." Ta faɗa a ranta.

Tashi ta yi tana kallon ɗakin, gaskiya iya tsaruwa ya tsaru amma dimm gabanta ya faɗi sanin ba wani zaman daɗi zata yi a gidan ba.

Haka ta yi ta hakuri da zama da Farouk, wata ranar ya dawo a bige ya neme ta ta ƙarfi, wata rana ya kawo matan banza har sai da abin ya dame ta ta gaya wa Ammi sannan ta tsawatar mai, shi ne ta ɗan samu sauƙin matan da yake kawo wa.

A haka har ta haifi Mu'ayyad, a haka kuma Farouk bai daina abin da yake ba sai dai ma ƙaruwa da yake.


Wannan kenan...


*Cigaban labari*


A karo na ba adadi Ummu Kulsum ta kuma fashe wa da wani kukan tuno rayuwar ta da ta yi a garin su, ga masoyinta da aka raba ta da shi ganin shi ba kowa bane .
Da ta gaji da kukan ta tashi ta ɗauro alwala a banɗaki ta yi nafila tana kai ƙaran Farouk wurin Allah.






********************************



*Ladiyo*



Tana nan har bayan sallar Isha'i a gidan Delu, sai wurin ƙarfe tara na dare sannan suka yi shirin zuwa wurin boka Barqaan.
A hankali suke hawa kan tsaunin gudun kar wata ta fado wani abu ya same ta.
Kamar yadda al'adar da kuma tsarin Barqaan yake, ba'a shigar mai kogo da kaya dole ka cire su , ka ajiye har sai ka fito.
Babu tsoro ko kunya su Ladiyo suka aikata abinda aka umarce su kafin suka shiga cikin kogon.
Boka Barqaan yana nan cikin kogon zaune cikin kazanta da ɗoyi wanda su Ladiyo basa ji sakamakon rufewa da idanunsu ya yi wurin neman taimako.

Bayan ya gama ƴan tsubbace tsubaccen sa ya juyo ya kalli su Ladiyo, kamar wanda suke bautamai haka suka fara russunar da kai hade da kirari a garesa.
Maganganu suka yi na lokaci mai tsawo sannan ya dauko wata ƙaramar baƙar laya a cikin ƙoƙon jakin da ke wurin ya miƙa wa Ladiyo yana faɗin "Wannan shi ne ƙarshen matsalar ki, ki yi aiki da shi zaki bani labari."
Ya juya wurin Delu yace, "Duk abinda kike aikatawa ina ganin ki ta ƙwaryata, abinda zance shi ne ki bi a hankali ." Daga nan ya ja bakinsa ya yi shiru.

Sumsum suka fice daga kogon bayan biyansa da suka yi da mutuncinsu.






********************************


*Ayaman*


Baccinta take cikin kwanciyar hankali kawai taji alamar ana tashin ta daga bacci, a ɗan razane ta ja bargon ta rufe kanta tana karanto ayoyin Alkur'ani.

Kuma jin ana jan zanin da ta rufa da shi ta ji ana yi, da sauri ta ja ta kuma tofa addu'a kusa da ita.

Again aka kuma jan zanin, ta yi ta maza ta miƙe zaune, wayam babu kowa a ɗakin, chan ta hango wani abu kamar mutum a tsaye ya tunkaro ta.
Duk addu'ar da ta zo bakinta take yi har wannan abin ya cimma ta....





Love you all 💞 💙




More comment more typing ✍️






https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB
*(Posting room)*


*My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇*

https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8
😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈



By




Khairat 💞💙


Page 29-30




*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*




BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM



Lokaci na ta shuɗewa, abubuwa na ƙara haɓaka, ta ɓangaren Ayaman ma haka.
Lamura sai ƙara gaba suke dan yanzu Ladiyo ta yi yadda ta yi aka sa ranar aurenta da Anas, har yanzu bata gama mamakin Ladiyo ba har sai da ta ga saura watanni uku bikinta da Anas.

Tashi ta yi daga kan zanin da take sallah, tsayawa ta yi ta na kallon tsakar gidan, gari ya waye tangararan, rana ta fara fitowa alamar za'a yi rana mai zafi.
Ruwa ta ɗebo a randa ta shiga banɗaki, bayan ta fito ta fara aikin gidan, ta gama ta yi wanka tasa kaya.

Abin kari Ladiyo ta miƙo ma ta dan ba laifi ta ga sauyi sosai daga wurin Ladiyo wanda bata gama yadda da shi ba.
Ta kammala cin abincin ta fice zuwa gidan su tsahare dan bikin saura kwanaki uku.
Ta na shiga gidan ta tarar da tsahare ana shafa ma ta kurkur dan shi ne abinda yawancin ƴan garin ke amfani da domin gyaran amarya.
Bayan ta gaisa da Innar su tsaharen da wasu daga cikin ƴan uwansu tsahare, ta zauna aka fara fira tana taya su ayyuka har aka kammala gyaran jikin.

Wuraren ɗaya na rana suka fita rabon katin biki , sun zagaya gidaje da yawa na ƴan uwa da abokan arziki sun raba kati.
Sai ana kiran magriba suka shiga gidansu tsahare a gajiye.
Innar su da sauran ƴan uwa da suka fara zuwa na ɗaki su na gabatar da sallar magriba.

Bayan sun idar da sallah suka ci abinci sannan Ayaman ta yi ma ta sallama da niyyar gobe da wuri zata fito domin za'a yi sa lalle.



*******************************

*Farouk*

Ta ɓangaren Farouk da Ummu Kulsum abu sai ƙara tabarbarewa yake, dan yanzu an sa ranar auren Farouk da Nafee.
Ummu Kulsum ta yi kukan har ta gaji, har ga Allah ta gaji da rayuwar gidan Farouk, ga Amminsa ma kamar shi ta daina bata kulawa kamar da.
Dan akwai ranar da ta je gaishe ta, ta amsa ma ta ciki ciki kuma ta tashi ta bar falon.
A ganin Ummu Kulsum ba laifi ne ba dan ta shiga ɗakin Ammi dan ta saba da hakan, mafi yawancin lokuta Ammin da kanta take jan ta ɗaki tai ta bata haƙuri saboda ta san zaman da suke ita da Farouk .
Amma a wannan lokacin tana shiga ɗakin,Ammi ta hau ta da faɗa da masifa, "Banda tsabar munafirci, meye kuma na shigo min ɗaki? Tsaya kiji bazan dauki wannan abin ba dan haka fitar min a ɗaki!." Ammi ta ƙarasa cikin faɗa.

Cikin tsoro Ummu Kulsum tace "Kiyi haƙuri Ammi, na zata ba laifi ne dan na shigo ɗakin ki ba."

"Tunda na uwarki ne ay dole baza ki ɗauka laifi ne ba, fita kafin ki ƙarasa ɓata min rai."
Ammi ta faɗa tana rufe idanu irin na wanda ke masifa.

Sumsum Ummu Kulsum ta fita daga ɗaki tana mamakin me ya samu Ammi.

Ta ɓangaren Ammi kuwa, hakanan taji ta tsani ganin Ummu Kulsum a kusa da ita, babu dalili ko ɗaya.

Ummu Kulsum ta zauna a falon cike da zullumi, dan dama ta zo ne domin gayama Ammi halin da take ciki sai gashi ta tarar da Ammi a wani yanayi da bata taɓa ganin ta ba.




********************************


*Nafee*

Yanzu kam Nafee ranta fess an sa ranar aurenta da Farouk sai bankar magungunan mata take ita ala dole sai ta koma budurwa, ga Lubna dake gefe tana ƙara zuga ta.

Su na zaune a falon Nafee, Lubna na kallon wayarta sai ƙawar Lubna Zainab tana cin kayan marmari, ita luma Nafee ta na jujjuya wani abu a hannunta.

"Lubna anya kuwa?" Nafee ta faɗa cikin rashin yadda da tantama tana juya maganin a hannu.
"Nafee, kina tantama ne? Tsaya kiji wannan maganin sai da na tsallake rijiyoyi biyar kafin na amso miki su."
Lubna ta numfasa sannan ta cigaba da faɗin, "Wannan ɗan ƙaramin, hmm." Ta faɗa ta a ɗaga sa sama.
"Cika aiki kenan, in dai kika yi amfani da shi, hmmm wai inji mai ciwon haƙori ba'a magana kawai." Lubna ta ƙarasa faɗa tana yin alamar rufe baki kamar zip.
Haka suka cigaba da hirarsu,su na ta shewa kamar an yi musu hajji da Umrah.





********************************


*Ladiyo*

Abubuwa su na tafiyar ma ta yadda take so, dan yanzu ta sa malam Isyaku a gaba har sai da aka sa ranar auren Ayaman.
Matsalarta, Nabila sai Yunusa amma wannan bai dame ta ba kamar Ayaman, ta tsani ganinta cikin farin ciki ko walwala.

Ita da Delu ne suke kiɗansu suke rawarsu..












Love you all 💞 💙



More comment more typing ✍️


Khairat ✍️🤍https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB
*(Posting room)*


*My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇*

https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8


*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈


By



Khairat 💞






BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM



Page 31-32


Ita da delu ke kiɗansu su na rawarsu...

Dan ayanzu haka, alhaji Gabatari ya nemi auren Mariya kuma Delu ta yi uwa ta yi makarɓiya sai da aka yadda da shi.

Rayuwa ta yi ma ta sumul, bata da wata damuwa, dan yanzu ma Alhaji Gabatari ya aiko masu aikin gini zasu rushe gidan ayi musu sabo dal.
Ta ɓangaren Malam Surajo kam ba'a magana, dan yanzu duk ya susuce duk wanda ya sanshi a baya ya ganshi yanzu sai ya kasa gane shi.
Har ranar auren Mariya da aka sa bai da masaniya a matsayin sa na mahaifinta, sai lemu da Delu ta bashi tace an saka rana.

Yanzu ma masu aiki ne ke ta fama da aiki, dan an ruguje gidan tass , Delu ta shigo gidan da yake a gidan wasu ƴan uwanta suke zaune kafin a kammala aikin.
Washe baki ta yi tace "Sannun ku da ƙoƙari , kuna ta fama, kai sannunku sannunku." Ta ƙarashe maganar tana kallon ma'aikatan.

Wani saurayi ne ya amsa ma ta suka gaisa cikin mutunci.
Bayan ta gama zagaye gidan, ta fito tana mamakin wannan duniyar da ake ƙoƙarin gina musu.

Kichibis ta yi da Ladiyo a hanya tana ta zabga sauri kamar ƴar maula.
"Ahh ah , Ladiyo sai ina kuma?" Delu ta tambaya tana tsare Ladiyo da idanu.
"Gidanki na yi
niyyar zuwa, sai...." Sauran maganar ta maƙale ma ta a maƙoshi sakamakon ganin gidan Delu a ruguje dai aiki ake.

"Wallahi da gaske ne, wayyo!" Ladiyo ta faɗa kamar zautacciya.

Delu kam tsayawa ganin ikon Allah ta yi, dan ganin Ladiyo ta yi kamar mahaukaciya sai ɗaura hannu a kai take.
Koma dai mene Delu tasan baƙin ciki ne Ladiyo ke nuna wa ƙarara.
Wucewar ta ta yi ta bar Ladiyo na ta kwasar drama ita da leburorin.

Gida Ladiyo ta koma zuciyarta cike da baƙin ciki, taya Delu zata samu wannan duniyar ita kuma ta na nan zaune? "Kai bazai yiwu ba!" Ta faɗa a karo na ba adadi.

Nabila ce ta shigo gidan, kallon Ladiyo ta yi wacce duk ta susuce saboda ruɗewa.
"Toh fah, Ladiyo lafiya kika zauna anan kike ta surutai kamar sabuwar kamu?"
Shiru Ladiyo ta yi tana kallon Nabila, kai duk yadda za'a yi ma sai dai Nabila ta auri Alhaji Gabatari ko kuma kowa ya rasa.

Gaya ma Nabila abinda ke faruwa ta yi suka tsaya suna shawarwari, a ƙarshe dai suka yanke cewa Ladiyo zata samu bokan kan tudu su zanta.




*Ayaman*

Shirye shiryen biki suke ba abinda ya dame su, dan yanzu ma kiɗan kwarya ake ta zabgawa a tsakar gidan su tsahare ana ta rausayawa.

Sai wurin la'asar aka kammala kiɗan ƙwaryan, mutane sun fara raguwa tunda an kammala bikin yau saura kuma gobe da za'a ɗaura aure.

Bayan sun gama hutawa suka kama hanyar gidan yayar tsahare, su kusan tara dan ba laifi ƴan uwan tsahare sun zo da dama.

Hirarsu suke cikin kwanciyar hankali har dare ya tsaga, dan Anty Nusaiba ba ruwanta akwai hira.
Da asuba da suka farka basu koma bacci ba suka shiga shirye shirye, gidansu tsahare suka nufa dan a chan ne amarya zata shirya.

Wurin ƙarfe goma na safe aka ɗaura auren tsahare wanda asalin sunanta Fatima ita da angonta Usman.

Biki kam ya yi biki dan kofar gidansu tsahare ya cika tanƙam da mutane ana shaida daurin aure yayin da mata ke cikin gida suna ta hidimar abinci.

A ƙuryar ɗaki Ayaman ta sami tsahare ta yi shiru kamar mai tunani, kallonta Ayaman ta yi kana ta girgiza kai hade da murmushi.
Zaunawa kusa da ita ta yi ta fara lallaɓa ta , kamar jira take tsahare ta saki wani kuka mai ban tausayi.
Da ƙyar Ayaman ta rarrashe ta, ta ɗauko ma ta kayan da zata saka, girgiza kai tsahare ta yi sannan ta miƙe ta dauko wata atamfa mai ruwan toka da ja , ta miƙa ma Ayaman guda ɗaya ita kuma ta saka ɗaya.

Riga sa skirt ne wanda ake ya yi tsahare ta ɗinka musu, ga ɗinkin ya yi matuƙar kyau, shiryawa suka yi aikuwa atamfar ta zauna daram a jikin Ayaman abin ka da farar fata.

Fitowa sukai kamar ƴan biyu kowa sai yabawa yake, wata mata ce ta bude baki tace "kai ma sha Allah, Asma'u(babar su tsahare) wannan ƴan biyun naki kamar turawa, kai ma sha Allah, Allah ya nuna mana naki." Ta ƙarasa faɗa tana kallon Ayaman.

Sunkuyar da kai Ayaman ta yi , suka cigaba da gaisawa da ƴan uwa.



Wuraren ƙarfe shida na yamma, motar daukar amarya ta iso, duk da ba wata mai tsada bace amma babu laifi.

Haka aka kwasa aka tafi kai amarya bayan nasihohi masu ratsa zuciya daga iyayenta da danginta.
Ayaman da tsahare sun sha kuka iya kuka, dan da ƙyar aka raba su, ita a ganin tsahare barin Ayaman da zata yi, kamar zai bawa Ladiyo damar cigaba da cisguna ma ta.
Ita kam Ayaman tana tunanin kewar ƙawarta mai ɗebe ma ta kewa a duk lokacin da taji duniyar ta yi ma ta zafi.

An kammala biki lafiya an kai amarya gidan mijinta wanda babu karya Usman ya yi bajinta, dan ɗaki falle ɗaya da madafa sai tsakar gida da banɗaki wanda a wannan kauyen irin wannan ginin sai ƴar gata.

Ga kayan ɗaki da aka ma ta daidai gwargwado anyi ƙoƙari, dan akwai samiru kusan ishirin da sauran kayan amfani na ƴa mace.




********************************

*Bayan wata biyu*



*Ayaman*

Kwana biyun nan ta rasa mai ke damunta, ta yi wani fari na ban mamaki da qiba, ita dai ta alaƙanta hakan da abubuwan da Ladiyo ke bata.
Yanzu ma Ladiyo ce ta shigo ɗakin ɗauke da wani kwanon rubutu a hannunta, miƙa ma Ayaman ta yi "Maza shanye ki bani kwanon."

Karɓar kwanon ta yi , ta sa dai-dai bakinta ta furta Bismillah a hankali, "Dan ubanki ba na hanaki wannan Bismillahn ba? Ko ke daƙiƙiya ce da baki gane hausa?". Ladiyo ta faɗa ta na kwace kwanon.

Matse bakin Ayaman ta yi ta ɗura ma ta rubutun har wani yana zubowa.








********************************

*Farouk*

Farouk kam yanzu kwata kwata ya daina kwana a gidansa, ya tare a gidan Nafee wacce yanzu ita kaɗai yake gani a duniyar shi.

Yanzun ma kuwa shirye-shiryen biki suke yi abinsu.

"Kalli wannan dress ɗin bae." Nafee dake kwance kan cinyarsa ta faɗa tana miƙa ma sa wayar.

Amsa ya yi ya kalla, ya ɗan taɓe baki kaɗan yace "Ta yi." A takaice.

Cigaba da kalle kalle a wayarta ta yi har zuwa wani lokaci ta tashi ta shiga ɗaki.






Sai mun haɗu a next page, more comment more typing ✍️ 💙.




Love you all 💞






Khairyy ✍️🤍https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB
*(Posting room)*



My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8



*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️




😈😈😈 MUGUNTA 😈😈 😈




By



Khairat 💞



BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM


Page 33-34





**Ummu Kulsum**


Ta ɓangaren Ummu kuwa, ta mayar da al'amuran ta zuwa ga ubangiji dan ta yi imani shi zai kawo ma ta mafita.

Yanzu ma tana zaune a ɗakinta duk abun duniya ya ishe ta, muryar wata mata ta ji a bayanta,
"Kar ki damu Ummu, damuwar da kike ciki kaɗan ce ga wacce zaki fuskanta nan gaba...."

Saurin juyawa ta yi domin ganin mai magana, sai taga wayam babu kowa.
Saurin tashi ta yi ta fita daga ɗakin, shiru ta yi ta kasa taɓuka komai, ƙwanƙwasa gidan da ake yi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula.
Leƙawa ta yi taga baba maigadi baya nan, slippers ta saka sannan ta fita ta buɗe gidan.

Masu aikin gini ta gani, bayan sun gaisa ne suke sanar da ita cewa maigidan ne ya aiko su.
Shiru ta yi na wani lokaci kafin taji horn ɗin motar Farouk.

Bayan ya shigo gidan ya bawa masu aikin umarnin fara abinda ya kawo su, wurin bayan gidan suka nufa suka fara aiki.
Kangon dake kusa da su aka ruguje katangar aka hade da cikin gidan.
Ummu na gefe tana kallon ikon Allah, dimm zuciyarta ta buga kar dai ace auren Nafee Farouk zai yi, "Innalillahi wa'inna i'laihi raji'un."
Ta faɗa cike da tsoro, bin bayan Farouk ta yi cikin gidan, ɗakinsa ta nufa bakinta da sallama.
Kofar ta ƙwanƙwasa kafin ta tura ta shiga ciki.
A zaune ta tarar da shi a kan gado, "Sannu da zuwa Abban Mu'ayyad."
Ko kallon iskar da ta kwaso ta bai yi ba bare ya amsa.
Shiru ta yi sannan ta cigaba da magana, "Nace wannan masu aikin lafiya dai naga sun fara ruguje katangar gidan nan."
"Tunda ubanki ne ya siyamin filin sai ki hanani kinji." Farouk ya dakatar da ita .
"Kuma ki shirya, nan da sati biyu za'a ɗaura min aure da Nafeesa."

Shiri Ummu ta kasa mayar mai da amsa, wani baƙin ciki ne ya taho ya tare ma ta maƙoshi, kafin ta tashi jiki a saɓule ta fice daga ɗakin.
Tsaki Farouk ya yi kafin ya cigaba da danne danne a wayarsa.....



********************************




*Ayaman(p.o.v)*




Mamakin yadda jikinta ya yi wani sumul ya yi haske take yi, ga wata ƙiba ta ban mamaki da ta yi.

Indai tana lissafi yau saura kwana sha uku bikinta da Anas.

Ladiyo ce ta shigo gidan kamar an hankaɗo ta, Nabeela na biye da ita.
Ɗaki suka shige ko kallon inda Ayaman take basu yi ba, wannan halin Ladiyo na bin bokaye yana matuƙar damun ta , shirka ƙiri ƙiri kuma baka da bakin magana.

Haka dai ta zauna a wurin na wani lokaci kafin nan ta shige ɗaki.




********************************


*Nafee (p.o.v)*

Ta ɓangaren Nafeesa kam sai bankar magungunan mata take yi, duk ta bi ta rikice akan dole sai ta mallake Farouk, ga kuma ƙawayenta da ke gefe suna zuga ta .

Ga shirin biki da take yi babu kama hannun yaro abubuwa dai ba'a cewa komai.









*Bayan sati ɗaya*


*Nafee da Farouk*


Yau take ranar dinner kamar yadda suka tsara , amarya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login