Showing 24001 words to 27000 words out of 29277 words
Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈
By
Khairat ✍️🤍
BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM
Page 41-42
Sai da ta daɗe tana masa wani irin rikitaccen salo kafin ya yi sauri ya ture ta.
"Pls mana my dear." Nafee ta faɗa tana wani kashe murya.
Gaskiya shi gani yake baze iya barin wani abu ya shiga tsakaninsa da Nafee ba, dan Allah na gani yasan Nafee karuwa ce, tun ba yau ba, amma shi kansa ya rasa yadda zai hana aurensa da ita .
Cikin fushi ta kuma jawosa ya kufce, kamar wani yaro ya rasa mai zaiyi ma, tsaki ta yi kafin ta daka masa wata irin tsawa kamar uwarsa.
Haka ya biye mata har ta biya buƙatarta, ko hauka yake yasan Nafee ba budurwa bace amma ya rufe bakinsa tsit!!!
(Su Nafee wannan iko )
********************************
*_Ayaman_*
Bayan wani lokaci Adda Asiya ta kora mutane ganin dare ya yi , sannan aka bar Ayaman ita kaɗai tunda ba wasu ƴanuwa da ƙawaye take da su ba.
Su na tafiya Ayaman taji shigowar su innar Anas, bayan sun gama bata haƙuri duk a ganinsu kukan rashin gida take ita kuwa tasan kukan me take.
Bayan sun fita ta miƙe ta leƙa ta taga, hasken farin wata ne tarr ya fito ya haskaka ilahirin garin.
Ƙarar wutar nefa ce ta bugi kunnenta kafin taji mutanen unguwar sun ɗau kuwwar "Nepa!!!" Da alama sun daɗe basu ga wutar nefa ba.
Ƙare wa ɗakin kallo ta yi , banda "Ma sha Allah." da "Allah ya saka da alkhairi." babu abinda take faɗa.
Ta leƙa kitchen da banɗakin, gaskiya sun mata kyau bata taɓa tsammanin haka su Adda Asiya suka kashe kuɗi ba.
Ta koma ɗakin ita dai komai ya yi mata wallahi, agogon dake jikin bango ta kalla, da yake ba sabawa da agogo tayi ba sai bata gane ƙarfe nawa bane.
Alwala ta ɗauro kafin ta rama sallar isha'i da ake bin ta.
Muryar Anas taji yana gaisawa da mahaifiyarsa kafin ya yi mata sallama .
Ya shigo sashen nasu bayan ya rufo kofa.
Ƙara ɗuƙufar da kanta ta yi jin muryarsa a ɗakin, "Waalaikumus salaam." Ta amsa masa sallamar.
"Amarsu ta ango." Ya faɗa yana ƙara washe baki.
Shiru suka yi na wani lokaci kafin ya tashi ya umarce ta da su gabatar da raka'a biyu dan su godewa Ubangiji ga wannan ni'ima tasa.
Bayan sun idar ya fito da ledar tsirensa wanda sai tashin kamshi yake ga ɗumi alamar bai daɗe ba, sai kuma lemon zaƙi da kuma fanta guda ɗaya.
Buɗe fantar ya yi ya miƙa wa Ayaman, girgiza kai ta yi alamar a'a, takura ta ya yi har ta amsa ta kurɓa ta ajiye.
Tsiren ya ɗauko zai kai bakinta, kamshin turarensa da kuma kamshin tsiren ya haɗe mata sai jin tashin zuciya ta yi kafin kace me ta fara amai.......
********************************
*Ladiyo*
Cike da tunani kala² ta koma gida, kanta duk ya yi zafi, wai taya za'a ce Ayaman ta tafi gidan ni'ima haka?
"Wallahi bazai yiwu ba, ko zan tafi tsirara sai na hana Ayaman zaman lafiya!!"
Sai mun haɗu a next page more comment more typing ✍️
Khairat ce ✍️ 🤍
Love you all 💞😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈
By
Khairat ✍️🤍
*(Posting room)*
https://chat.whatsapp.com/Js1xb4FBd2v0o5mxXpssVr
*My WhatsApp group comment section 👇👇👇*
https://chat.whatsapp.com/FYbZw86FTfQDpyIkILlMuN
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
_With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.🤌💪_
BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM
Page 43-44
_____________Haka Ladiyo ta gama surutanta har ta jira shigowar Nabila gidan.
"Toh ni mai kike so nace Ladiyo?" Nabila ta faɗa tana kurɓar yoghurt ɗin hannunta.
"Bangane mai zaki ce ba? Kin manta alwashin da naci a kan Ayaman? Wallahi bazan bar ta ta zauna lafiya ba." Ladiyo ta ƙarashe cike da takaici.
"Ba ma wannan ba, kinsan Alhaji Gabatari yana so ya turo a fara maganar auren mu."
"Ayiririri , lallai ne kice su Nabila sai gidan Alhaji." Ladiyo ta ƙarashe cikin shewa.
Firarsu suka cigaba da yi kafin dare ya tsala suka nufi makwancin su.
********************************
*_Ummu Kulsum _*
Tun da ta zauna a falon bata kuma motsawa ba illa kallon tv da take wanda shima ba ganesa take ba.
Kukan Mu'ayyad ne ya tasar da ita ta nufi ɗaki, dan kwantar da shi.
Ta kwantar da shi a gadonsa kenan tana tofa mai addu'oi sai jin shewa da kuma muryar masu kawo amarya.
Ita a ganinta ana kawo amarya gurin uwargida domin sanin juna amma ko hauka take tasan ba zai yiwu ba.
Chan taji muryar wata mata da alama irin maroƙiya ce sai kirari take yiwa amarya Nafeesa wacce ta laɓe luff a cikin lifayarta purple color.
Tsaye tayi tana sauraron matar ta window tana faɗin "Ki shiga ki fito da munafuka Nafeesa, kin ci dubu sai ceto mata ƙwalli ɗaya a gidan Farouk Datti, yanzu Farouk zai san ya yi aure wallahi." Matar ta ƙarshe cike da tsiwa da kuma shaƙiyanci.
Haka suka sallame ta da kuɗaɗe kafin aka shigar da amarya sashinta.
Haka ta zauna a ƙasan tiles ta rasa me ke mata daɗi, wani yanzu Farouk zai san ya yi aure, hawayen da bata shiryawa ba ne suka taho ta kuncinta.
Wannan kalaman sun mata zafi, ita kanta ta san ta kamu da son Farouk tunda ba tun yau suke tare ba, bugu da ƙari Farouk mugun ɗan wanka ne wanda a kallo ɗaya zai iya sace zuciyar mace.
Tana nan a zaune a wurin har taji shigowar tawagar ango da abokansa, leƙa wa ta yi ta taga ta hango Farouk sai sheƙi yake cikin dakakkiyar shaddarsa ruwan madara mai kyau da tsada.
Tana tsaye har ta ga fitowar su tare da ƙawayen amarya sun wuce sai Farouk da ya biyo bayansu.
Karaff suka haɗa ido da Farouk, sakin wani makirin murmushi ya yi kana ya mata blowing kiss.
Alwala ta ɗauro ganin zaman bai da wani amfani sannan ta tayar da sallah.
Ita kanta bata san adadin raka'ar da ta yi ba ta fara jin bacci.
Kayan bacci ta sauya sannan ta kashe fitila ta kwanta.
Ihun da Nafee take yi duk ya bi ya takura ta,da take bangon dakinta da na Nafee katanga ɗaya ce dan a manne suke.
Mamaki falll a ranta, "Dama haka amarya take a daren farko?" Tambayar da ta yi ta sako wa kanta kenan babu mai amsa mata.
Gaba ɗaya ta kasa baccin ga Mu'ayyad da ya dame ta da rigima ta rasa ta meye, tashi zaune ta yi duk ta rasa me ke mata daɗi da yaron zata ji ko da wannan mutanen?
********************************
*_Delu_*
Cikin kuka Mariya ta shigo gidan tana bubbuga ƙafa, "Wallahi Inna sai na aure Alhaji Gabatari, taya zai ce ya fasa aure na?" Ta ƙarasa maganar cikin kuka.
"Ya fasa aurenki kamar ya?" Delu ta zabura tana tambayar ta.
"Wallahi cewa ya yi ya fasa aure na wai da Nabila zai yi auren."
"Wace.. Nabeelan...?" Delu ta tambaya a ɗan tsorace.
"Nabeelan Ladiyo mana, wannan munafukar ƙawar taki." Mariya ta faɗa cike da rashin kunya.
"Kam bala'i Ladiyo......." Delu ta saɓi mayafinta ta fice daga gidan.
********************************
*_Ayaman_*
Haka suka kwanta cike da tantama a ranta, amai? Ta ya ya? Sune tambayoyin da take ta yiwa kanta.
Anas kuwa banda lallaɓata ba abinda yake dan har ga Allah ya na matuƙar son Ayaman.
Sai mun haɗu a next page more comment more typing ✍️
Khairat ce ✍️🤍
Love you all 💞🥰
😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈
By
Khairat ✍️🤍
https://chat.whatsapp.com/Js1xb4FBd2v0o5mxXpssVr
*(Posting room)*
*My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇*
https://chat.whatsapp.com/FYbZw86FTfQDpyIkILlMuN
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
_With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.🤌💪_
BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM
Page 45-46
---------------------------------------------------
Ƙarar bige kwanikan ne ya fito da Ladiyo babu shiri, "Wani ɗan...." Sai kuma tayi shiru sakamakon ganin Delu tana huci kamar zakanya.
"Aw Delu, kece kike wannan ɗayan aikin sai kace taɓabɓiya?"
"Uwarki ce taɓabɓiya Ladiyo, ni za ki yi wa wannan rashin amanar? Ki juyar da hankali Alhaji ya koma kan ƴar ki? Toh wallahi ko sama da ƙasa zata haɗe ba zai yiwu ba."
"Hehehe." Ladiyo ta kece da wata irin dariya kana ta cigaba da faɗin
"Ashe a kan wannan ƴar ƙaramar maganar kika kwaso jiki kika zo min gidan da tsohon daren nan, toh bari kiji gobe in Allah ya kaimu Alhaji Gabatari zai turo a nemar masa auren Nabeela."
In ran Delu ya kai dubu to ya gama ɓaci, ta juya bayanta taga tunkunyar da suke girki ta ɗauko ta tayo kan Ladiyo.
Cike da dabara Ladiyo ta juya bayan Delu ta kwace tukunyar ta rafka mata a kai.
Kafin kace me faɗa ya kaure tsakaninsu, ita Ladiyo ga girman jiki ga ƙarfi, ita kuma Delu ga ƙanƙantar jiki ga kuri.
Mutane ne suka fara shigowa gidan duk da dare ya yi dan ganin mai ke faruwa, Baba Lami ce wata dattijuwa a layinsu ta shigo tana faɗin "Ku rabu da karnuka su cinye kansu, ji kaina wannan munafukan sun addabe ni haka ina ji ina gani suka daƙile auren Binta saboda tsabar munafinci."
Haka kowa ya fara ja da baya yana tofa albarkacin bakinsu, a ƙarshe dai Delu ganin Ladiyo na ƙoƙarin kashe ta ta samu hanyar tsira ta fice tana faɗin "Allah ya isa kuma sai ta rama."
Ladiyo kuwa ranta fess ta doke shegiya haka ta rufo kofarta.
********************************
*_Farouk da Nafee _*
*Bayan wayewar gari*
Taɓa sa da taji yana yi ne ya tasar da shi, "Good morning angona." Nafee ta faɗa tana shirin kai mai kiss.
Saurin tashi ya yi daga gadon ya shige banɗaki ya kullo kofar.
Brush ya fara yi kafin ya yi wanka, sai da ya kammala wankan ya ga babu towel bare wasu kayan, gashi wallahi mugun kunyar Nafeesa yake ji dan jiya ta shayar da shi ruwan mamaki.
Tsayawa ya yi na kusan minti goma sannan ya mayar da kayansa ya fito.
A kan gadon ya tarar da ita tana ƙoƙarin magana ya yi saurin ficewa daga ɗakin.
Direct sashen Ummu Kulsum ya nufa, ƙwanƙwasa ƙofar ya yi dan a kulle take kuma babu mukulli a hannunsa.
Ummu ce ta zo buɗe masa sai Mu'ayyad da ke bayanta yana tafiya a keken koyon tafiya, "Ina kwana." Tayi saurin gaishesa haɗe da russunar da kai.
Bai amsa mata ba ya ɗauki Mu'ayyad suka nufi ɗakinsa.
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta kullo ƙofar.
Aikinta ta cigaba da yi a kitchen har ta kammala, shigowarsa kitchen ɗin ta ji shi da yaron a hannunsa ya na ta mai wasa.
Ya sauya kaya ya sa wasu ƙananan kaya na shan iska.
"In kin kammala abincin ki kai ɓangaren Nafeesa muna jiranki." Abinda ya faɗa kenan sannan ya yi ficewarsa daga sashen.
A falo ya tarar da Nafee ta na kallo, kallonsa ta yi kafin tace "Wannan yaron fa?"
"Ai kin san ɗa na ne ko kuwa."
"Ko ma jikanka ne wallahi mayar da shi wurin uwarsa zaka yi, dan baze zo ya ɓata min sababbin kujeru na ba."
Shiru Farouk ya yi, dan Nafee kam tsoro ta fara bashi.
Ƙwanƙwasa ƙofar da ake yi ne ya ja hankalinsu zuwa wurin, "Waye?" Farouk ya tambaya.
"Ni ce." Ummu ta mayar mai cikin sassanyar muryarta.
Buɗe ƙofar ya yi ya bara damar shigowa falon, "Ina kwana?" Ummu ta gaisar da Nafee.
Ko kallo bata ishe ta ba ta cigaba da kallonta.
"A ina zan ajiye abincin?" Ummu ta kuma tambaya.
"A kan uwarki, baki ga dining ba?" Nafee ta bata amsa a zafafe.
A hankali Ummu ta tashi daga tsugunon ta nufi dining ta ajiye abincin.
Har ta yi hanyar fita ta ji muryar Farouk "Zo ki ɗauke yaron."
Ɗaukar Mu'ayyad ta yi suka fice daga sashen.
Tana shiga sashenta ta zauna tana tunani, yanzu da wannan mutanen zata zauna?
********************************
*Ayaman*
Da asuba ta farka, alwala ta ɗauro kafin tazo ta tashi Anas, ya shirya ya fice zuwa masallaci, ita kuma ta tayar da sallah.
Ta na cikin azkar taji shigowar Anas, "Ina kwana?"
"Lafiya ƙalau Ayaman, ya kwanan sabon wuri?"
"Alhamdulillah."
Komawa ɗaki ya yi ya kwanta, ita kuwa Ayaman ta yi tsuru dan ba saba baccin safe ta yi ba.
Kan kujera ta koma ta kwanta ta na tunanin wai ita ce a kujera yau, tunda take a rayuwa bata taɓa ganin kujeru na falo a gidansu ba sai dai wani gidan amma yau ita ce a nata kujerun.
Ikon Allah kenan kowacce irin ƙaddara Allah ya baka akwai sakayya in dai kayi haƙu.
Bacci ne sama² ya fara ɗaukarta, ta gyara kwanciyarta ta fara bacci.
Taɓa ta da taji ana yi ne ya yi saurin tayar da ita, Anas ne ya na sakin wani lallausan murmushi a fuskarsa.
Tabbas Anas kyakkyawa ne mai kyakkyawar zuciya, "Ayaman!" Taji ya ambaci sunanta.
"Na'am."
Kallon kallo suka tsaya yi kafin ta yi saurin janye idonta ta miƙe, wani uban jiri ne ya kwasheta yarap ta faɗi a kan kujera.
Anas ne ya bita da sannu kafin ya ɗebo mata ruwa a zatonsa ko rashin ruwa ne.
Muryar mahaifiyarsa taji ta na ƙwallamai kira, ya na isa ta miƙa mai flask ɗin ruwan zafi da na abinci.
Ɗauka ya yi ya na godiya, buɗe kular ya yi a gaban Ayaman tuni yawunta ya tsinke kafin kace me ta fara jin soyayyar doya da ƙwan ko jiran tayi brush balle shan tea ko cikinta ya warware ba.
Tsayawa Anas ya yi ya na kallonta, shi duk a tunaninsa yunwa ce take kuwa yaji wani tausayinta ya ratsa shi.
Ruwan lipton ɗin ya ɗebar mata a kofi ya sa sugar, sannan ya miƙa mata.
Sai da ta tayar da doyar tass sannan ta juya ta ga yadda Anas ke kallonta.
"Sannu." Ya faɗa cikin tausashiyar murya.
Ƙasa ta yi da kai dan sai yanzu ta ga aika²r da ta yi, flask ɗin wayam babu komai ita kanta tayi mamakin yadda ta iya cinye wannan uban abincin.
Kitchen ɗin ya shiga yaga babu komai na gara da aka kawo wa Ayaman, shiru ya yi dan ya san ba zai iya komawa yace wa mahaifiyarsa babu abinci ba.
Wurin idi mai shayi ya nufa, "Ahh ahh ango? Kaine da safiyar nan ina amaryar?" Idi mai shayi ya tambaya cike da munafinci.
"Bacci take bata tashi ba." Anas ya basa amsa.
"Ah ya kamata ta huta kam da wannan gajiyar ay sai da hutu." Idi mai shayi ya ƙarasa ya na wata shaƙiyiyar dariya.
Ayaman kuwa wanka ta yi ta saka wata sabuwar atamfa duk da leda ce amma kuma ta yi kyau, fita ɓangaren mahaifiyar Anas tayi suka gaisa cikin mutunta juna.
Hira suka fara sama-sama kana Anas ya shigo ya tarar da su, zama ya yi a kan bokiti yana faɗin "Nima ayi hirar da ni."
Anan zamu dakata sai Allah ya kaimu, more comment more typing ✍️
Khairat ce ✍️ 🤍
Love you all 💞😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈
By
Khairat ✍️🤍
https://chat.whatsapp.com/Js1xb4FBd2v0o5mxXpssVr
*(Posting room)*
*My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇*
https://chat.whatsapp.com/FYbZw86FTfQDpyIkILlMuN
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
_With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.🤌💪_
BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM
Page 47-48
----------Hira suka fara yi sama-sama kana Anas ya shigo yace "Nima ayi hirar da ni."
Ƙasa Ayaman tayi da kanta ta kasa magana, ta na jinsu su na hira iya kaci in abin dariya suka yi ta yi in na girgiza kai ne shi ma ta yi.
Chan zuwa hantsi Anas ya shirya ya fita nema, yayin da Ayaman ke ƙoƙarin taya mahaifiyarsa wasu ayyukan.
Su na kammala girkin innar Anas ta umarce ta da ta ɗauko flask ta zuba musu nasu, haka kuwa aka yi bayan sun gama komai da komai suka zauna ƙarƙashin rumfar innar Anas su na taɓa hira.
Kayan saƙa Inna ta ɗauko tana yi yayin da Ayaman ke kallon komai kuma ta fara yunƙurin iya wa.
********************************
*_Ladiyo_*
Gari na wayewa ta fara kichiniyar yadda zata gyara gidan da kuma girki domin tarbar baƙi.
Wurin Habu mahauci ta nufa domin siyo nama, ai kuwa ta samu anyi sabon yanka dana haka aka zuba mata namanta ta yi gaba.
Tayo sauran chefanen kama daga lemukan kwalba, kayan miya, shinkafa da sauransu.
Tana isa gida ta ɗaura tunkuya ta hau aiki gadan-gadan.
Nabeela na ɗaki tana kwance ko tunanin taya mahaifiyarta aiki bata yi ba, hasali ma ita ba iya wani aikin gida tayi ba dan tun tasowarsu da ƴanmatanci Ayaman ce baiwarsu dan ita take komai a gidan, dan its Nabeela bata ƙi wanka ma Ayaman tayi mata ba.
Zuwa bayan azahar Ladiyo ta kammala wasu daga cikin ayyukan, shinkafa da waken da tayi duk ta chaɓe tayi ta ruwa, miyar kam ƙarni kamar me ita s ganinta tayi komai dai-dai.
Sabuwar tabarmarta ts ɗauko ta shimfiɗa a ƙarƙashin bishiyar mangwaron da ke tsakar gidan, ra ɗauko komai ta ajiye sa inda ya dace.
Tana aiki tana magana ita kaɗai, "Ay wallahi Nabeela tayi goshi, kai kai kai ." Sai kuma ta cigi yatsa kamar taɓabɓiya.
Wuraren la'asar Malam Isyaku da amininsa sai wani ƙaninsa da sai da aka sha gumurzo kafin ya yadda yazo dan Ladiyo ba irin wulaƙancin da bata musu, daga tace ɗangin matsiyata sai tace masu ƙashin tsiya abubuwa dai iri-iri.
Wani yaro ne ya shigo ya same su a kan tabarma su uku, "Ina wuninku, wai ana sallama da malam Isyaku."
"Toh maza je kace yana zuwa." Ladiyo tayi charaf ta amsa mai.
Haka kuwa aka yi, Malam Isyaku ya mike ya fita, manyan mutane ne su huɗu sun sha babbar riga wadda daka gani kasan sai an sa kuɗi mai yawa za'a iya siya.
"Assalamu Alaikum." Malam Isyaku ya faɗa ya na miƙa musu hannu domin suyi musabaha.
"Waalaikumus salaam." Suka amsa suna gaisawa cikin mutunta juna.
Iso ya yi musu