Showing 15001 words to 18000 words out of 29277 words
Ta yi shiru tana tunani ta jiyo muryar Saratu dillaliya, fitowa ta yi taga har ta yi ma kanta masauki a ɗaya daga kujerun falon.
Saratu na ganin Ummu Kulsum ta yashe baki ta fara ma ta kirari kamar ƴar maula, gaisawa sukayi da Ummu Kulsum sannan ta fara fito da kayan dake cikin jibgegen buhun ta.
"Ay in gaya miki Hajiya wannan atamfofin ƴan cotouno ne, ga kyau ga sauƙi." Saratu ta ƙarasa maganar tana washe baki.
Duba atamfofin Ummu Kulsum tayi kafin ta zaɓi guda biyu ta chake wa Saratu kuɗinta a hannu.
Bayan sunyi sallama da Saratu ta dauko Mu'ayyad wanda ke gurin mai aikin ta, abincinsa ta ba shi sannan ta kuma miƙa ma ta yaron ita kuma ta koma ɗaki ta kwanta zuciyarta duk ba daɗi.
********************************
*Ayaman(p.o.v.)*
Bayan ta gama kukan nata ta tashi ta kama wankin nan ba ji ba gani, har sai da ta kammala sa cikin mintuna ƙalilan.
Abincin da Inna Ladiyo ta dafa ta bata , ta zauna ta ci ta koshi ta yi wa Allah godiya.
Tana nan zaune har Ladiyo tayi ficewar ta ɗan Nabila na yin wanka ta fice sai ya zamana ita kaɗai ce a gidan.
Tunanin maganar da suka yi da Ladiyo ce ta dawo ma ta, Anas dai mutumin arziki ne ga hankali da nutsuwa, kuma yana da rufin asirinsa daidai gwargwado, dan da shi da mahaifiyarsa ne kaɗai aka sani shiyasa ba wanda ya bashi ƴarsa aure.
Gashi mahaifiyarsa ba lafiya ce ishashiya ce da ita ba, tana buƙatar taimakon wani, gaskiya zata amince ta aure shi ko dan taimakon baiwar Allahn nan .
Da ta gaji da tunanin ta fara karanto ƙur'ani wanda ke kanta dan rabon ta da islamiyya tun mahaifiyarta na da rai, bayan rasuwar ta Ladiyo ta katse islamiyyar.
********************************
*Farouk*
Yana fita daga gidan, gidansu ya nufa, a falo ya tarar da Hajiyarsu ana ma ta tausa, tana kallo tana cin kayan marmari.
Gidan kam dan tsaruwa ya tsaru, dan ya fi gidan Farouk girma da tsaruwa wanda bayan rasuwar mahaifinsu ne aka ƙara tsara gidan, su uku ne a family ɗinsu, babbar mace ce sunan ta Halima tana New York City da zama ita da iyalanta, sai mai bi ma ta , Raihana, tana garin Abuja da zama, sai Farouk ɗan auta, wanda ke zaune a Kano kusa da mahaifiyarsa.
Da sallama ya shiga falon, zama ya yi kusa da Ammi , murmushi dattijuwar matar ta yi, sannan ta shafa kanshi,
"Babana (haka take kiransa dan sunan mahaifinta ne da shi)ya aka yi ne?" Matar ta tambaya tana sakin sabon murmushi.
"Ina kwana Ammi" Farouk ya gaishe ta cike da ladabi.
"Lafiya ƙalau babana, ya Iyali?"
"Suna lafiya"
"Masha Allah."
"Bari na tafi office ana jira na"
"Toh babana, Allah ya bada sa'a."
"Ameen, zan dawo zuwa dare"
"Toh, Allah ya kaimu."
"Ameen ya faɗa yana ficewa."
Ammi ce ta ƙura masa ido san da yake fita, sai ya yi ma ta kama da ubansa sak , "Allah ya maka rahama Aliyu" ta faɗa tana tuna lokutan su tare.
Farouk ya na fita bai zame ko ina ba sai gidan Nafee, horn ya yi mai gadi ya buɗe mai, gaisawa suka yi da mai gadin sannan ya nufi cikin gidan.
Ya na shiga falon ya tarar da Nafee zaune ta na breakfast, daga ita sai wata yaloluwar riga a jikinta.
Baba Asabe ce ke ta kai kawo a falon ta na gyaran gidan, ya na shiga falon ya tsaya ya ƙura wa Nafee ido kamar tsohon maye.
Idanunta sun kumbura alamar ta yi kuka har ta gode wa Allah, matsawa kusa da ita ya yi ya rungumo ta jikinshi yana faɗin
"my love fushi kika yi ne naga ko kallo ba ishe ki ba?"
Kawar da kanta gefe ta yi ta na turo baki gaba, murmushin gefen baki ya saki ya na matsawa gefe, ya ce "tunda ba zaki hakura ba bari na je wurin Amrah ita zata lallaɓe ni."
Zumbur ta juyo jin ya yi maganar Amrah, "kar ka sake min maganar wannan ƴar iskar a gida na , kaji na gaya ma." Ta faɗa cike da jan kunne da masifa.
Suna nan wurin ya bata hakuri suka jima suna hira kafin ya tashi ya nufi office ɗinsu.
Nafee kuwa rai ya yi ƙal , dan Farouk ya gaya ma ta yau zasu tattauna da mahaifiyarsa a kan batun auren su, haka nan ta wuni cikin farin ciki.
********************************
*Ladiyo da Delu*
Ladiyo na gama wankan ta shirya ta nufi gidan Delu, a tsakar gida ta tarar da su ita da Mariya sun zube soyayyar kaza wadda aka baɗa ma yajin tafarnuwa a kai.
"Duniyar Allah." Ladiyo ta faɗa ta ƙarasa shiga cikin gidan.
"Ladiyo kece tafe?" Delu ta faɗa ta na yagar cinyar kaza.
"Ni ce fa Delu." Ta amsa ma ta tana ɗaukar naman ta kai baki, "waii wannan daɗi, Allah turo min da naira in more arziki na." Ladiyo ta faɗa kamar ta taka rawa.
Mariya da Delu kam ban da dariya ba abinda suke yi.
Zama Ladiyo ta yi da kyau, sannan suka haɗu su uku suka cinye kazar, bayan sun gama ci Delu ta yi ma malam surajo umarnin miƙo musu da lemu a ɗaki.
Ba musu ya tashi ya nufi ɗakin, duk ya wani susuce , ya rame ya fita hayyacinsa Delu sai abinda taga dama take yi.
Lemu biyu ya miƙo musu, ya na komawa inda ya ke zama, wanda bakin kitchen ne.
"Naga ka miƙo lemu biyu ka aje, da yawa zaka miƙo ay." Delu ta faɗa mai tana kallon sa .
"Ya ƙare ne " malam Surajo ya faɗa kamar zai yi kuka.
"Sai kaje ka siyo." Delu ta faɗa cikin halin ko in kula.
"Wai dan Allah Delu ta kike so na yi ne, duk kuɗin dake wuri na sai da na kashe su a kan ki da wannan yarinyar, sannan kin hanani fita in samo, sai bauta da na zauna nake miki a gida, hatta gonar gadon mu da aka raba kuɗin na hannunki kin hanani, ya kike so na yi ne?." Malam Surajo ya ƙarasa faɗa cikin kuka wanda duk wani mai imani zai taya sa , dan a halin da ya ke ciki ya gwammace mutuwa a kan rayuwar da ya ke.
"Wannan kuma matsalar kace ba tawa ba, matsala ta ita ce ka nemo min lemu na sha." Delu ta faɗa cikin halin ko in kula.
Ladiyo da ke zaune kam , lemun ta dauka tana shan kayanta, dan duk wannan batun ba damunta ya yi ba.
More comment more typing.......
A taya mu sharing please.
Khairat ✍️
https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB
*(Posting room)*
*My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇👇*
https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
😈😈😈* MUGUNTA* 😈😈😈
By
~Khairat~🖤💙
BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM
Page ~25-26~
Sai da ta dire kwalbar lemun sannan ta kalli inda Delu take tace "ke kam ki kyale shi haka mana, da wanne zai ji, habaa deluwa."
"Kin ga fa Ladiyo babu ruwanki a harka ta, wannan matsalata ce da mijina dan haka ba ruwanki."
Iya ƙuluwa Ladiyo ta ƙulu, ranta ke tafarfasa wai ita Delu ke gaya ma haka.
Mariya da ta gaji da diramar ta tashi ta shige ɗakinta tana mitar wannan lamarin.
Su Ladiyo kuwa saboda rashin zuciya, zama ta yi ta cigaba da cin kazar har sai da ta koshi, sannan suka ɗau hira ita da Delu.
Malam Surajo na gefe yana kallon su, gaba ɗaya ya rasa me ke mai daɗi duk ya susuce ya fita hayyacinsa.
Hira tai hira har suka kai wurin la'asar suna hira dan dama sallah ba damun su ta yi ba.
Abinci suka nema suka, bayan sun ci suka dasa hirar tasu hade da fatan yau da dare zasu kai wa a bokan kan tudu ziyara.
*Ayaman(p.o.v)*
A bangaren Ayaman kuwa zamanta ta yi tana harsaso irin rayuwar da zasu yi ita da Anas, tabbas in tace bata san Anas ta yi ƙarya, rayuwarsu mai cike da nishaɗi da kaunar juna take harsashe.
Kwatsam tunanin mafarkinta ya dawo ma ta a rai a lokacin da ta yi ido biyu da wata murtukekiyar tsaka mai girman ƙadangare ta ƙwalalo ma ta idanu.
"A'uzu bi kalmatil lahi tammat min sharri ma kalaq." Ta faɗi a ranta saboda ba ƙaramin razana ta yi da ganin wannan halittar ba.
Tsoro ne ya kamata sosai ganin tsakar bata daina kallonta ba.
Hijabinta ta dauko a ɗaki ta saka ta fice daga gidan. Tana fita bata zarce ko'ina ba sai gidan su tsahare, da sallama ta shiga gidan, Innar su tsaharen ce ta fito daga banɗakin tana amsa sallamar.
Dire butar hannunta ta yi tana faɗin, "Ayaman kece tafe, sannu da zuwa."
"Ni ce inna, ina wuni?"
"Lafiya ƙalau ya mutanen gidan?"
"Su na lafiya."
"Toh ma sha Allah."
Zama ta yi a tabarmar dake tsakar gidan su na taɓa hira da Inna, "Inna yaushe tsahare zata dawo?" Ayaman ta tambaya ta na tsince shinkafar da Inna ta auno.
"Ta kusa dawo wa Ayaman, nan kusa." Inna ta bata amsa.
"Toh Allah ya kaimu."
"Amin."
Hirar su suka cigaba da yi har Ayaman ta daura ma ta girkin dare , su na cikin girkin Ayaman ke neman shawarar Inna a kan maganar auren Anas.
"Ya kike gani inna?"
Inna taja numfashi sannan tace "Ayaman, a rayuwar nan in kana abu dole ka nemi zaɓin Allah domin shi ne mai kowa mai komai, sannan Anas ba shi da wani aibu, yana da sana'ar sa, ba sata yake ba ko cutar wani, ga mahallin da zai aje ki , gaskiya a gani na ki amince da maganar auren nan, ko kin huta da rayuwar da kike fuskanta a yanzu." Inna ta ƙarashe maganar tana kallon Ayaman.
Shiru Ayaman ta yi tana nazarin maganganun inna, tabbas haka zancen yake in ta yi auren zata huta da rayuwar gidansu.
Nan Inna ta cigaba da bata shawarwari har ta kammala girkin suka ci tare sannan Ayaman ta yi ma ta sallama ta tafi.
Tana fita daga gidan aka kira sallar magriba, dan haka kanta a ƙasa ta fita daga gidan sakamakon mazan da ke wucewa domin shiga masallaci.
Wasu maza wanda aƙalla zasu yi sa'anin mahaifinta ne suka zo wucewa ta gaishe su, "yanzu ace malam Isyaku ya bar yarinya ta riƙa ta zama riƙaƙƙiyar kubewa, duk ta zama wata uwa a unguwa wannan ai bai dace ba." Ɗaya daga cikin mutanen ya faɗa, ɗayan kuma yace "Hmm, wa ya sa ni ko akwai abinda suka shirya shiyasa suka ƙi aurar da ita, koma dai mene muna nan muna zuba ido."
Wucewa ta yi ba tare da ta kalli ko inda suke ba duk da ta san da ita suke kuma taji me suke cewa.
Tana mamakin yadda mutane ke ma ta wata fahimtar daban, ita a ganinta aure ay lokaci ne kamar yadda mutuwa take .
Da sallama ta shiga gidan duk da ba kowa, ta tsaya a banɗaki ta yi alwala ta zo ɗaki ta dauko zanin da take sallah da shi.
A tsakar gida ta shimfiɗa ta yi sallar kasancewar akwai wutar lantarki dan sun ci sa'a an gyara musu.
Tana zaune a kan zanin har aka kira sallar Isha'i ta yi sallar ta.
Tana idarwa kam bayan ta gama zikiri ta shige ɗaki ta yi kwanciyar ta dan cikinta a koshe yake bata jin yunwa kuma tunda Ladiyo ta fita ta san sai sanda ta ga damar dawowa.
********************************
* Nafee(p.o.v)*
"Ke wallahi aikin mutumin nan yana ci, yau gashi da kansa yazo yake faɗa min zai yi magana da mamansa a kaina, kinsan mun daɗe muna fama da shi a fara maganar auren sai yau dai Allah ya yi." Nafee ta ƙarasa maganar cike da jin daɗi.
Ta ɗayan ɓangaren Lubna tace " ai ke kike wasa da tsafi, baki ji me bahaushe yace ba tsafi gaskiyar mai shi."
Hira suka cigaba da yi a kan yadda zasu shirya abubuwa dan Nafee ji take kamar an yi ma ta hajji da Umrah.
********************************
*Farouk(p.o.v)*
Yana isa office ya tarar da aiki ya yi mai yawa, dan mataimakin nasa bai yi abinda ya dace ba dan tafiyar da harkokin kamfanin.
Sai da ya gama mitar kuma ya fara aikin, har wurin la'asar yana abu ɗaya, sallah ce kawai ke tayar da shi.
Gidansa ya wuce bayan sallar la'asar.
A falo ya tarar da Ummu Kulsum tana turaren wuta, dan bata bari mai aiki ta yi ma ta.
Gaishe sa ta yi ya amsa ciki-ciki, dinning ya nufa ya bude kular abincin, masa da miyar taushe ya gani.
"Oh shit!!, wai me yake damun ki ne, jahilcin da baki gama ba a kauye shi zaki zo ki dasa min a gida? Mtcwwww."
Wullar da kular ya yi, sai ga waina ta yi ɗaiɗai a ƙasa, miyar ta biyo bayanta.
Fuuu ya wuce ɗakinsa kamar iska, kallon dinning ɗin Ummu Kulsum ta yi tana zama turuss a kan kujera.
Kuka ta fashe da shi mai ciwo, ita meye laifinta? Dan kawai daga ƙauye aka kawo ta shi ne ta yi jahilci? Ace kusan shekara ɗaya kana rayuwa da mutum amma baka taɓa samun farin ciki ba? Sai yaushe kenan?? Ta tambayi kanta cikin kuka.
A gaskiya ta fara gajiya da halin Farouk, ba zata ga murmushinsa ba sai in dare ne ya yi yana nemanta? "Na jure da yawa wallahi." Ummu Kulsum ta kuma faɗa tana kuka.
Mop da tsintsiya ta dauko ta gyara gurin dan Allah ya sa ta aiki ƴar aikinta wani wuri da tuni a gabanta zai yi wannan abin.
Bayan ta gama gyara gurin ta shige ɗakinta ta kullo ƙofa, tana tunanin raba ta da aka yi da masoyinta aka aura ma ta Farouk da sunan zumunci.
*Asalin su Farouk*
Love you all 💞💋 ❤️
More comment more typing ✍️
Khairat ✍️https://chat.whatsapp.com/IiFZaLvHaXWJSlqsXgayfB
*(Posting room)*
*My WhatsApp group comment section 👇👇👇👇👇*
https://chat.whatsapp.com/EF8H5r2xZU81B9Fj9qafY8
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈*
By
*Khairat 💞💙*
BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM
Page 27-28
*Asalin su Farouk*
Mahaifin Farouk Alhaji Aliyu Umar Datti ɗan asalin garin Katsina ne a kaita local government.
Ya taso cikin gata inda ya kasance shi kaɗai ne ɗan Fateema da Umar, dan shima sai da aka jima sannan aka haife sa.
Ya yi karatunsa na boko da Arabi a nan kaita inda ya tafi babbar University a lokacin wadda ita ce University of Lagos.
A nan makaranta ya hadu da Amina, har ta kai su da fara soyayya mai karfi, Amina ƴar asalin garin Lagos ce inda aka haife ta take.
Bayan kammala karatunsu ne Farouk ya gabatar da kansa a wurin iyayen ta har ta kai ga ya tura manya domin nemo mai auren Amina.
A lokacin an sha gumurzu kafin iyayen Amina su amince da auren dan sun so Amina ta auri wani ɗan uwanta.
An daura aure da kimanin sati biyu aka dauko Amina daga Lagos zuwa gidan Aliyu dake Katsina bayan nasihohi masu ratsa zuciya da iyayenta suka yi ma ta.
Watan Amina biyu a gidan Aliyu ta fara laulayi inda bayan cikin ya cika wata tara da ƴan kwanaki ta haifo santaleliyar ƴar ta mai kama da ubanta, aka raɗa ma ta suna Halima wanda sunan mahaifiyar Amina ne.
Halima taga gata iya gata a wurin iyayenta da kakkaninta kasancewar ta jikar farko a family ɗin.
Halima na da shekara biyar Amina ta kuma haifar ƴa mace wadda taci suna Raihana.
Bayan haihuwar Raihana ne suka koma garin Kano da zama saboda sauyin wurin aiki da Aliyu ya samu.
Amina sai da ta jima dan sai da Raihana ta kai shekara goma sannan ta haifo ɗa namiji wato Farouk.
Amina da Aliyu suka haɗa kam ƴaƴansu suka raina har suka kawo karfi, Halima ta yi aure da kwanaki kaɗan Allah ya amshi ran Aliyu sai gidansa na gaskiya.
A lokacin sunyi baƙin cikin rashin uban nasu amma suka yi tawakkali suka rumgumi ƙaddararsu.
A haka rayuwa ta cigaba da nisawa har Raihana ta kammala karatunta ta yi auri inda ta auri ɗan mataimakin shugaban kasa su na zaune a Abuja.
Lokaci zuwa lokaci Fateema tana kawo wa jikokinta ziyara, a wannan zuwa ta taho da wata budurwa wadda tace jikar aminiyar ta ce wacce mahaifiyar ta ta rasu tana da tarbiyya da hankali dan haka take son haɗa ta da Farouk.
A lokacin hauka ne kawai Farouk bai yi ba dan ya gama shirinsa zai auri Nafee sai ga Ummu Kulsum ta shigo.
Hajjo (Fateema) ta yi amfani da ƙarfin ikonta har aka ɗaura auren Farouk da Ummu Kulsum.
Tun daga lokacin Farouk yake ƙullace da Ummu Kulsum na ganin ta yadda an daura auren bayan jan kunnen da ya yi ma ta.
Tana zaune an lulluɓe ta da mayafi ta yi shiru tana tunanin wannan sabuwar rayuwar da zata shiga, kawai taji an ja ma ta mayafin aka cillar a ƙasa.
A yatsine yake kallon ta kamar ya ga wani abin ƙi, ya buɗe baki da kyar yace "Finally kin yadda an daura auren, har an kawo ki gidan nan,