Showing 27001 words to 29671 words out of 29671 words

Chapter 10 - TSAKANINMU BOOK 1 by Nana meera.txt

Unknown   

26 Jun 2024

5766

kalleta ta ce" da gaske bazaki faɗawa kowaba ?" ta ɗaga mata kai. Miƙewa ta yi daka kwancen ta kamo hannunta tana facing ɗinta ta ce" twinny i'm sorry, i'm very sorry wlh ban taɓa zaton haka zai faru dani ba sanda kike faɗamin ban saurare ki ba sai Yanzu da babu abunda faɗawar zai amfanamin, wlh twinny nayi danasani bansan haka yakeba, ban ɗauka so yake ya cutar daniba banji maganarki ba saboda ƙawa data ruɗeni gashi yanzu natashi cikin tutar babu ni ban auri wanda nake soba kuma yanzu ko wanda bana soma bazai aureni ba, bansan me zan faɗawa su Daddyba wlh bansani ba, ji nake inama Allah ua ɗauki raina na huta da irin wannan ranar" ta ƙareshe maganar tana wani irin kuka mai tsuma zuciya, itama kanta Samhan kuka ta ke dan ko bata faɗa mata ba tagane inda zancen nata ya dosa, tana goge hawayen fuskarta ta ce" tun yaushe?" ta ce" tun randa nace miki zani birthday gidansu Aleeya wanda kuma a zahiri Yazeed ne ya gayyacemu birthdayn bayan munje ganin yanayin wajen yasa nace nidai mu tashi mu tafi amma sai ya ce bari ya kawo mana abun sha wanda tunda nasha bansan inda kaina yakeba sai da na farka na ganni a asibiti kima ya yimin gargaɗin karna kuskura na faɗawa kowa idan ba haka ba ya yimin video kuma zai sakeshi kowa ya gani" ta faɗa tana cigaba da kukanta kamar ance Mommy ta mutu. Sabida mutuwar jiki Samha kasa cewa komai ta yi amma deep down ji take inama taga Yazeed yanzu da wlh sai ta kasheshi idan yaso itama a kasheta, shuru kowannensu ya yi suna tunanin mafita musamman Samha kusan 10mins sannan ta ce" karki kuskura Mommy ta ganki a tsukinnan koda zaki fito ki dinga sake hijab saboda kai tsaye zata gane, sannan karki ce mata bakida lpy kome ki keji ki faɗamin zan miki please Saima coz bansan ya zata ɗauki al amarinba kuma kinga ta nada depresion to kaga aje ya tashi more espicially Daddy zani wajen Zahra zamusan abun yi amma this time around dole sai an hukunta Yazeed" ɗago kai ta yi da sauri ta ce" twinny ya ce zai watsa video na please ki taimake ni" kamo hannunta ta yi ta ce" karki damu kinji nasan me zanyi kedai ki tabbata kinyi abunda na ce miki" gyaɗa mata kai ta yi ganin yanda jikinta ya ɗauki zafi yasa ta ce" ki kwanta bari na dafa miki abinci kici sai kisha magani" komawa ta yi ta kwanta ita kuma ta tashi ta fito dan shiga kitchen.......















*Ethopia*


Zaune suke gefenta suna taɓa hira sosai yaji daɗi dan rabonda suyi hira da ita har sun manta tana murmushi ta ce" Abu Azaad idan na mutu wa zaka aura?" kallonta ya yi sai kuma ya ce" please Zaheera banson irin wannan maganar wane ya ce miki mutuwa zaki yi?, yanzu ba gashi kina samun sauƙi ba kuma maganar ma kirasa gaban wa zaki yi sai Azaad wannan ai ba daidai bane" murmushinta mai kyau ta yi ta ce" i'm sorry kawai daman akwai wacce nakeso idan na mutu ka aura kuma inason kamin wannan alfarmar kaji" ya ce" dan Allah dan Annabi abar maganar nan kinji" little Azaad ne ya ce" ummina bazaki mutu ki barni ba ko?" wasu hawayene suka gangaro kuncinta ta ce" Eh Azaad amma idan na mutu ka dinga yimin addu'a kaji Love" fashewa yaron ya yi da kuka ya ce" Abbu ka cewa Ummi karta mutu" jawoshi ya yi kan cinyarsa ya rungumeshi ya ce" Ummi wasa take maka kaji yarona " shuru ya yi yana sakin ajiyar zuciya not too long bacci ya yi awan gaba dashi...........










Mama ce tashigo parlour hannunta riƙeda plate as usual ta zauna tana kallonsu ta ce" oh yarinyar nan Allah ya yaye miki wannan ciwo wlh bakiga yanda kika rameba duk kinyi ƙashin wuya idanuwa sun faffaɗa, shi kuma mijin naki ya yi wani zuru-zuru dashi da ɗan.... Allah dai ya kyauta" murmushi Zaheera ta yi ta ce" Ameen Mama" bata sake cewa komai ba ta fara cin abinci ta wanda aikinta kenan kullum..............


*Nigeria*




Shigowa ta yi da plate a hannunta ta zauna gefenta ta fara tashinta daga bacci, buɗe ido ta yi ta ce" tashi kici abincin sai na baki drugs ɗinki kafin Mommy ta dawo" babu musu ta tashi ta zauna ta miƙa mata abincin, saurin ɗauke kanta tayi ta ce" please twinny ki ɗauke banaso" cikin lallashi ta ce" idan na ɗauke me zakici?" ta ce" wlh komai banaso kawai ki barni haka" haɗe rai ta yi ta ce" wlh baki isaba kici ko kaɗanne banson su Daddy su dawo kuma kinga it's almost magrib".... Da kyar ta lallaɓata taci kaɗan sannan ta bata drugs ɗin ta kwanta ta lulluɓeta da duvet sannan ta fito parlour ta zauna............


Bata daɗe da zama ba taji ƙarar buɗe gate lokaci ɗaya taji gabanta ya faɗi da sallama ta shigo ai kuwa ta rungumeta tana murmushi ta ce" welcome Zahra" murmushin ta mayar mata sannan ta ce" thank you"zama sukayi bayan sun gaisa ta ce "ina Amrah?" ta ce" wlh tana gida wajen Mommy zasu unguwa da har ta ce zata biyoni taga Azaad bansan me ta tuna ba ta ce A'a.." dariya Samha ta yi ta ce" Allah sarki ay Azaad yafi three weeks da komawa gida" ta ce"wlh ban sani ba shida Dad ɗinsa suka tafi" ta gyaɗa mata kai. Zahra ta ce" daman wajenki nazo inason zamuyi wata magana" Samha ta ce" ina jinki " ta ce" daman yayan Abbanmu ne ya dawo daga saudia dan kusan shekarar sa uku baya Nigeria shine yazo gidanmu kuma wacce ya fara gani ita ce Amrah ya tambaya ka ce masa ƴata ce, sai yake faɗa ya ce a matsayinsa na maɗaurin aurena a ce har nayi aure ba'a sanar dashi ba kodan saboda ba shida ɗane, sai suka faɗa masa duk abunda ya faru toh daman Genaral ne na sojoji shine ya ce na faɗa masa inda zasu sami Yazeed zasu kamashi, shine na ce bari nazo naji shawarar ki" shuru Samha ta yi lokaci ɗaya kuma hawaye ya kawo fuskarta da mamaki Zahra ta ce" Samha lpy?, ko maganar dana faɗa ce ta ɓata miki rai?" girgiza kai ta yi ta ce" dan Allah Zahra ki faɗawa uncle ɗinki wlh zan kaisa inda zai samu Yazeed saboda bazan iya rabuwa da Yazeed ba yanzu maganar dana ke miki Yazeed yama biyunina fyaɗe kuma ta samu ciki" da sauri ta miƙe tsaye ta dora hannu a ka ta ce" mun shiga uku wai Saima kike nufi?" gyaɗa mata kai ta yi ta fashe da kuka ta ce" amma garin yaya haka ta faru?" riƙe hannunta ta yi suka zauna sannan ta bata labari kamar yanda Saima ta bata, sosai tasha kuka dan tasan raɗaɗin irin haka ta ce" zanje na faɗawa uncle ɗina kuma nasan zasu ɗauki mataki amma yanzu ya za'ayi da cikin jikinta?" ta ce" shine abinda nake tunani yanzu saboda banso ko kaɗan Daddy ko Mommy su san wannan maganar" Zahra ta ce" yanzu dai mafita ɗaya ce shine ayi abortion nashi " ta ce"banso tayi abortion saboda ko mene za'a mata dole zai nuna ta rasa virgin nata kuma duk wanda ya aureta zai dinga yi mata gori" Zahra ta ce" shikenan yanzu dare ya yi amma in sha Allah zuwa gobe zan shigo ko muhaɗu a makaranta da'ita koda batajin daɗi karta zauna a gida ita kaɗai tunani zai mata yawa " tashi ta yi ta ce" ok zamu zo taren" daga haka sukai sallama ta rakota parking lot sannan ta koma........






Suna zaune suna cin abincin dare banda Saima Daddy ya ce" Mamana" ɗago kanta ta yi ta ce" na'am Daddy" ya ce" ku shirya in sha Allah next week zamu tafi Ethopia mu duba Zaheera sabida jiya Aliyu yacemun jikinta ya yi sauƙi amma ɗazu kuma ya ce ya sake tashi yanzu ma indiya zasu kaita" ta ce" tom Daddy Allah ya bata lpy" ya ce" Ameen"... Mommy ta ce" wai ina Saima ne?" da sauri ta ce"bacci take" ta ce"jikin nata ne ya tashi?" ta ce"A'a kawai kwanciya ta yi"Mommy ta ce" gobe idan zan fita asibiti sai mu tafi tare na dubata acan" ji tayi gabanta yayi wata muguwar faɗuwa ta tashi Mommy ta ce" abincinfa?" ta ce" na ƙoshi sai da safe" suka ce " Allah ya tashe mu lpia" Ameen ta ce sannan tayi gaba.........












Mommy ce ta kalli Dad ta ce" nifa kwana biyu ban yarda da yaran nan ba kamar akwai abunda suke ɓoyewa babu son a sani" ya ce" i think so, dan duk sun canza mu'amalarsu kuma basu yadda da kowa" ta ce" idanma wani abun suke ɓoyewa zan saka musu ido" ya ce" better" sannan ya tashi ya ce" zaki samu zuwa Ethopian ne?" ta ce" gaskiya banjin zani" ya ce" ok" sannan ya yi gaba...........






*Ethopia*


Sosai daren jikinta ya tashi hankali tashe sukai asibiti da'ita, bayan an dubata tana kwance amma babu alamar da rai jikinta a haka suka kwana har safe sannan suka shirya dan tafiya india......








Little Azaad na zaune jikin Zaytoon tana bashi abinci kamar wanda aka tsikara ya ce" Aunty" ta ce"na'am" yana murmushi ya ce"wlh so nake naga aunty Samha" ta ce" sure?" ya ce"yeh" dariya tayi ta ce" ka bari idan Abbunka ya dawo sai ka faɗa masa" ya ce" yaushe zasu dawo?" ta ce"i don't know, amma ka tambayi Mami" tashi ya yi da gudu ya yi hanyar kitchen tana kiransa amma ya yi mata banza.........








Ayaan da Asaad ne suka shigo ta ce" yaya ya jikin aunty Zaheeran?" ya ce " wlh ba naceba amma sunje indian" ta ce" Allah ya bata lpy" ya ce" Ameen".........


*Nigeria*


Gama shiryawarsu kenan sun saka wata abaya blackiston colour iri ɗaya sunyi kyau sosai suna fitowa parlour tace" muyi a hankali kar su jimu" Saima ta ce"twinny kawai mu faɗawa Mommy wlh tsoro nakeji" ba tareda tayi magana ba ta kamo hannunta suka fito. A harabar gidan suka tadda drivern su yana ganinsu ya taso cikin girmamawa ya ce" sannunku da fitowa" Samha ta ce" yawwa, yau basai ka kaimu ba kayi zamanka" ya ce " toh" sannan sukai waje kuma tayi hakane saboda kaga su Mommy su ankare sun fita...........








Suna fita bakin titi suka tadda Zahra tana jiransu, a baya tasa Saima sannan ta shiga gaba sukayi gaba.....
Bayan sunyi nisa ta ce" yanzu mene abunyi?" Samha tace" muje makaranta" ok ta ce sannan suka ɗauki hanyar BUK ɗin.....




Sanda suka ƙarasa Saima tayi bacci hakan yasa suka barta a motar, kai tsaye office ɗin Sapwan suka huce......




Zaune suka tadda shi suka gaisa da fara'a ya ce" Fateema kin ɓuya" ta ce" wlh kam" ya ce" wannan ƙawarki ce?" ta ce" Eh sunanta Zahra" ya kalli Zahra ya ce" nice to meet yhu" ta ce"thanks".. Ina Azaad ya tambaya, tana murmushi ta ce" Allah sarki ay ya koma Ethopia kusan three weeks ago" ya ce" amma bakida kirki shine baki faɗamin ba?" ta ce" wlh tafiyar tasu ce urgent shiyasa" ya ce"ok amma duk sanda ya zo you let me know" ta ce" in sha Allah" ... Basu daɗe suna hira ba ta ce zasu tafi ya rakosu har waje sannan ya koma........








Har suka gama abunda zasuyi bata farka ba Zahra ta ce" yanzu zan tafi gidan uncle gobe zamu haɗu" ta ce" ok" suka shiga motar ta ajiye su a gida ita kuma ta wuce.............


A hankali take tafe da'ta saboda yanda jikinta ya yi weak, suna shiga parlour suka tararda Daddy da
Mommy tsaye sai zagaye parlourn suke, gabanta taji ya faɗi tayi ƙarfin halin cewa Daddy lpy na........... Marin daya sakar mata yasa bata ƙarasa faɗar abuda ke ranta ba ita kuwa Saima ɓuya tayi bayanta tana kuka cikin tsananin ɓacin rai ya ce" Samha mene ne wannan?" ya faɗa yana nuna mata sachet ɗin maganin, kasa magana ta yi sai kuka da take Mommy tazo gabannsu ta ce" ba magana ake muku ba?" cikin kuka Samha ta ce" dan Allah kuyi haƙuri ku gafarceta wlh ba laifinta bane" da mamaki Mommy ta ce" bangane ba?" ganin duk sun rikice yasa Daddy ya ce" Mamana zo nan" babu musu ta ƙarasa gabansa ta tsuguna ya ɗagota ya ce" tell me what happened?" durkushewa ta yi agurin tana kuka kamar ranta zai fita Mommy ta ƙaraso wajenta tana kallonta ta ce" Samha dan Allah ki faɗa mana mene ne ya faru Dan Allah" ta ƙarashe maganar tana kuka, zama Samha ta yi ta jingina da kujera sannan ta ce"..........."




*India*






Da gudu likitocin sukayo kanta wajen su biyar ciki kuwa harda Aliyu banda zufa babu abunda yake haɗawa jikinta sai rawa ya ke ta ce" Abu Azaad!!" riƙe hannunta ya yi ya ce" na'am Ummu Azaad" tana jan numfashi ta ce" please ka kula da Azaad kaji ka faɗa masa ina sonsa kuma ya dinga yimin addu'a sannan ka cewa Mami da Abba da Mama da Zaytoon da Asaad da Ayaan duka su yafemin kai ma ka yafenmin" baisan sanda ya fara hawaye ba ya ce" dan Allah Zaheera ki daina faɗin haka wlh babu abunda zai sameki zaki warke kamar baki yiba" a hankali ta furta" Abu Azaad ina sonka, ina sonka" yana kuka ya ce" nima ina ƙaunarki Zaheera" cikin sarƙewar murya ta fara faɗin kalmad shahada har ƙarshe, sai kuma numfashi n ya fara tafiya computern na ƙara within one second kuma tayi shuru, kallon computern ya yi sai kuma ya kalli Zaheeran ganin idanunta a rufe yasa ya ce" Zaheera! Zaheera" shuru yaji bata amsaba wani likita yazo ya ja bargon ya rufe fuskarta sannan ya kama hannun Aliyu wanda banda kallo babu abinda yake ya jashi sai dai kafin sukai bakin ƙofar ya yanke jiki ya waɗi ƙasa sukayi kansa da sauri...............


*Nigeria*






Tunda ta fara bada labarin banda zufa babu abunda Daddy ke yi ita kuwa Mommy sai kallonsu take Samha ta ce" Daddy babu irin magiyar da banyi muku ba akan Yazeed amma babu wanda ya saurare ni gashi yanzu ya lalata mata rayuwa a banza" ta faɗa tana cigaba da kukanta. Banda ina lil lahi babu abunda Daddy ke furtawa Mommy kuwa tashi tsaye tayi kamar zata tafi ɗaki sai kuma ji sukai timmmm ta waɗi ƙasa..,........






Banda kuka babu abunds suke a asibitin barema Saima jikinta sai rawa yake kusan 20mins sannan likitocin suka fito da sauri suka tafi wajensu Daddy ya ce" doctor ya jikin nata?" likitan ya ce" Alhaji ku shiga ku ganta" da sauri sukayi ɗakin da aka kwantar da itan amma suka tsaya durus ganin wata likita tana rufe fuskarta cikin rawar murya Daddy ya ce" do..doch....doctor me ya faru?" ba tareda ta kallesuba ta ce" i'm sorry Allah ya mata rasuwa" wata irin ƙara suka saki yana juyowa ya ga duk sun suma Saima sai bleeding take, da gudu likitan ta yi waje suka shigo da yawansu aka ɗaukesu banda Daddy wanda yama kasa kukan sai kallo kawai ................
_Allah ubangiji ya jiƙan dukkan bayinsa wadanda suka rigamu gidan gaskiya idan tamu tazo yasa mu cika da imani_

```End of book one```


*Shin ya rayuwarsu Samha zata kasance bayan babu ran mahaifiyarsu?*
*Shin da gaske Zaheera ta mutu kuma idan ta mutu ya su Aliyu da little Azaad zasuji?*
*Shin mene ne zai faru da Saima?*
*Shin za'a hukunta Yazeed ko A'a?*
*Shin Samha taza auri Sapwan ko A'a?*


*Duka zaku samu amsar tambayoyinku a littafin TSaKANINMU book 2 wanda kuma isn't free its 400#, 300# For first 20 people18 slot remaining make your payment via 9086030007 Hauwa lawan opay digital service evidence via 09086030007 whatsapp only*








_Muhaɗu a book two_


_Tauraruwar royal star ce✍️_

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login