Showing 18001 words to 21000 words out of 29671 words
yhu oll```
đź’–đź’–đź’–đź’–đź’–
[2/5, 22:26] Nanameera writer: https://chat.whatsapp.com/BRBJgmCve2uEO7OzFYz8Sj
🌹*TSAKANINMU*🌹
*Story and written by*
*
*Nanameera*
_Tauraruwar royal star_
🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_
*Alk'alaminmu 'yancinmu*
_HaÉ—aka palace_
_Page_ 15&16.
_________Wajejen ƙarfe tara suna zaune suna breakfast ita kuwa Saima ta kasa cin abincin gabaɗaya kanta ya kulle tana cikin tunaninta Daddy ya ce " Saima what's wrong with you?" murmushi ta yi ta ce " nothing Daddy" Samha ta ce " Daddy inason anjima naje supermarket please" yana goge bakinsa ya ce "ok but karkiyi dare" ta ce" insha Allah" tashi ya yi shima Abu Azaad ya miƙe kallonsu Azaad ya yi ya ce " Abu zan biku" girgiza masa kai ya yi ya ce "no babu inda zaka kayi zamanka kaji" maƙe kafaɗa ya yi ya ce" please Abbu" haɗe rai Aliyu ya yi ya ce"kai i'm play with you?" girgiza kai ya yi ya ce "to shiga hankalinka ka koma ka zauna zan siyo maka abun daɗi" shuru ya yi suka fita sannan ya tafi gurin Samha yana zuwa ya faɗa jikinta ya fashe da kuka, rungumeshi ta yi ta ce " ya'isa kaji, muma zamu fita anjima kuma bazai bimuba" shuru ya yi ya cigaba da kukanshi da kyar ta samu bacci ya ɗaukeshi Saima ta ce "gaskiya kina ƙoƙari sai kace ɗanki" kafin ta yi magana Mommy ta ce" au ke bazaki iya yimasa hakaba?" ta ce "tab, ni bazan iya wahala ba inta cewa ɗa ya yi shuru ai wlh sai nayi masa duka" sakar baki Mommy ta yi tana kallonta har ta gama maganar sannan ta ce "Allah ya bamu rai da lafiya naga yanda zakiyi da naki ɗan" mikewa Samha ta yi da Azaad a hannunta ta ce "irinsune waɗanda yayansu ke dukansu" tayi gaba tsaki Saima ta yi ta ce" aikuwa da nayi asara" tashi Mommy ta yi ta ce" ni zanje na shirya saboda inada patient ɗin dazan duba" Ok ta ce sannan itama ta tashi ta shiga ɗakinta.....
Bayan ta idar da sallar azahar tana zaune tana karatun al-qur'ani ta buɗe ƙofa ta shigo, ɗaga kai ta yi ta kalleta sannan ta mayar kan qur'anin, zama tayi gefenta gadon har ta idar da karatun ta ajiye sannan ta kalleta ta ce "ke kuma ina zuwa?" murmushi ta yi ta ce "wlh zanje gidansu Aleeya ne ana birthday ɗin brother'nta" da mamaki Samha ta ce" amma kintambayi Daddy zaki fita?" ta ce" wlh kwata-kwata na manta shiyasa nazo na faɗa miki koda zai rigani dawowa" kallonta Samha ta yi ta ce "to dolene sai kinje?" tashi tayi ta ce" haba Samha idan Aleeya ce ake birthday ɗinki ai ko bata saniba zata zo ni kuma saina kasai yimata kara?" kwanciya Samha tayi ta ce "sai kindawo Allah ya tsare ya kiyaye"
"Ameen" sannan tayi waje.....
Bayan ta gama ɗaukan duk abinda take da buƙata taje counter dan biyan kuɗin akace mata anbiya sosai tayi mamaki taceda mutumin "dan Allah wane ya biya" ya ce "wata mata ce yanzu ta fita tasa baƙar abaya"ok ta ce sannan ta kama hannun Azaad suka fito da sauri.....
Tana ƙoƙarin shiga motarta ta taɓa bayanta ta ce "baiwar Allah" juyowa tayi ta zare face mask ɗin fuskarta, a firgice ta kalleta sai kuma tayi baya cikin rawar murya tana nunata da yatsa ta ce"zaa..za..Zahra" fashewa sukayi da kuka atare tazo ta rungumeta, kuka suke wanda zai karyawa duk wani mai sauraro zuciya, kukane wanda yake fitowa daga ƙasan zuciyarsu kusan 10mns sannan suka fara sauke ajiyar zuciya Samha ce tayi ƙarfin halin cewa" Zahra daman zan sake ganinki a rayuwata?, naɗauka mun rabu kenan har abada" goge hawayen fuskanta ta yi ta ce "ya jikin naki Fateema?" wani kukan taji yana tawo mata ta yi ƙarfin hali ta ce "ai jikina bazai taɓa samun sauƙi ba tun randa na rabu dake jikina yake ciwo har kawo i yanzu kuma har yau ba' saniba a gidanmu" leƙa bayanta ta yi taga Azaad da mamaki ta ce"kinyi aurene?" jawoshi ta yi gabanta ta ce" banyiba wannan ɗan cousin ɗina ne, kefa?" murmushi tayi kafin tayi magana wata yar ƙaramar yarinya wacce bazata huce 2yrs ba Samha ta ce "masha Allah, ya sunanta?" ƙara fashewa ta yi da kuka irin kukan takaicin nan ganin haka yasa Samha ta ce" Zahra lafiya?,ko dai wani abu ya faru ne?" kuka kawai take takasa magana hakan yasa Samha ta ce"please zo muje gidanmu kinji" batayi musu ba ta kama hannunta suka shiga motar Zahra ita kuma ta cewa driver ya tafi gidan.....
Suna shiga gidan ta zaunar da Azaad da yarinyar a parlournta ta zuba musu chocolates a gaba sannan ta kama hannun Zahra suka zauna ta ce "Zahra yimin bayani meya faru bayan rabuwarmu?" cikin mutuwar jiki da kuma takaici tace "abubuwa da yawa sun faru Samha, bayanda naje gida babana ya koreni a lokacin saboda haka Mamana ta kaini gidan sister'nta na zauna har wasu wattani, bayan nayi kusan two months agidan sai.......fashewa tayi da kuka na zallar ɓacin rai ta ce" Samha cewa akai inada ciki" a firgici Samha ta kalleta jikinta banda rawa babu abunda yake ta ce "bangane ba Zahra kina nufin sabida abunda ya faru kika sami ciki?, ko kuwa aure akayi miki?" kamo hannunta tayi ta riƙe ta ce "babu wanda ya yimin aure, cikin jikina ya samune sanadiyyar abunda ya faru dani" cikin kuka Samha ta ce"inna-lil-lahi wa-ina ilaihi raji'unn, to ya kikayi da cikin?" murmushi ta yi ta ce "itace waccan yarinyar da kika gani, Samha Amrah shegiyace batada ub.....wani irin raunataccen kukane ya kwace mata itama Samha na tayata, sosai sukayi kukansu sannan sukai shuru Samha ta ce" wlh bazai yiwu ba dole ya karɓi ƴarsa tunda tanada uba kisan shi nima kuma nasanshi" girgiza kai Zahra ta yi ta ce " no Samha na haƙura yaje shida Allah, nasan Allah zai hukuntashi daidai da laifin daya aikata " tsaki Samha ta yi ta ce " haba Zahra kada ki manta yarinya mace kika haifa ba namiji ba me kikeso yarinya ta faɗa idan ta girma aka tambayeta ubanta?, wlh yanda ya ƙunsa mana baƙin ciki wllh shima sai ya ɗanɗani irin wannan zafin kuma dole abiwa yarinya haƙkinta" shuru Zahra tayi sai kuma ta ce "banaso gidanku suji wannan maganar Samha, yanda tun farko basujiba to banso yanzu suji saboda hakan zai iya kawo hargitsi a tsakaninku kuma dan Allah ki sanarda kowa halinda kike ciki na ciwon zuciya saboda banga amfanin ɓoye musu ba plx" murmushi Samha ta yi ta ce "bazaki ganeba Zahra, ciwon dake damuna nawane ni kaɗai idan har iyayena sukaji to ransu bazai masu daɗiba saboda zasuga akan namiji ciwon zuciya ya kamani it doesn't make sense, saboda haka zanyi managing ciwona har sanda Allah zai ɗauki raina" Zahra ta ce " wannan ba tunani bane Samha ya kamata ace sun sani kodan saboda halin rayuwa, sannan maganar namiji ya samaki ciwon zuciya ai ba kanki farauba saboda haka ki faɗa masu kawai" kallonta Samha ta yi tana goge hawayen fuskarta ta ce"Zahra har yau idan na tuna zuciyata zafi takemin dan Allah dan Annabi Zahra ki yafemin kinji wllh bansan zai aikata hakaba" rungumeta Zahra tayi ta ce "haba Samha ai *Tsakaninmu* babu irin wannan nasan kema da kece irin abunda nayi shi zakiyi saboda haka har abada banayin danasanin abunda na aikata dan kin cancanci fiye da haka agurina" dariya Samha tayi tace "nagode sosai Zahra, yanzu abunda zamuyi kinga yanzu yayi yamma amma idan Allah ya kaimu gobe sai musan yanda zamuyi " tashi tayi tace "ok Allah ya kaimu Samha sauran ki makara dan nasan halinki" dariya tayi ta ce "haba ai wannan da ne amma yanzu ko teacher bazai faɗamin sauri ba" dariya sukayi dukkansu sannan suka fito parlour 'n........
Zaune suka tadda su Azaad suna cin abinci suna wasa abunsu suna ganinsu amma basu kulasuba Zahra ta ce "Amrah taso mu tafi" kallonsu sukayi sai Azaad ya ce "dan Allah ki barta anan kinji" cikin siririyar muryarta ta ce "Mommy ki barni anan plx" murmushi Samha ta yi ta ce"plz ki rabu da'ita ta kwana anan dan Allah" kallonta Zahra tayi ta ce"makarantarfa?" ta ce "dan dai gobe É—aya sai suyi fashi kinji Mommy" dariya ta yi ta ce" shikenan Allah ya kaimu"
"Ameen tace sannan suka fita dan rakata ......
Zaune suke agurin partyn wanda ita duk hankalinta ya yi gida ta kallli Aleeya ta ce" wai Aleeya ba yanzu zamu tafi bane?, nifa ba'a sani ba a gidanmu na fito" tsaki Aleeya tayi ta ce "ke kinfiye tsoro Yazeed nefa kina gani yanzu ya tafi karɓo mana abunsha kuma naga yanzu za'a yanka cake ɗin" kafin tayi magana yazo wajen ya zauna ya ce " sorry na barku ku kaɗai ga abunsha ku sha yanzu zamu tafi" ok suka ce sannan suka ɗauka suka farasha ya ce"i'm coming plx" suka ce ok........
Sosai take mamaki ganin har kusan ƙarfe goma amma Saima bata dawoba gashi su Daddy duk basu dawoba Azaad da Amrah kuma sunyi bacci, tana cikin wannan tunanin ne taji ƙarar shigowa gidan sosai taji relief jin wani ya dawo agidan ta koma tayi kwanciyarta.............
*just manage this lover's saboda yanayi na jiki iya abunda zan iya kenan kutayani da addu'ar samun sauƙi please👏👏*
```Written by```
*Nanameera*
_Love's yhu oll_
🫶🏻🫶🏻🫶🏻🫶🏻
_Tauraruwar royal star ce✍️_[2/6, 21:55] Nanameera writer: https://chat.whatsapp.com/BRBJgmCve2uEO7OzFYz8Sj
🌹*TSAKANINMU*🌹
*Story and written by*
*
*Nanameera*
_Tauraruwar royal star_
🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_
*Alk'alaminmu 'yancinmu*
_Hadaka palace_
_Page 17&18_
__________Bayan ta idar da sallar asuba ta fito dan shiga kitchen har a sannan tana mamaki ina Saima take, lokacin da gari yayi haske tana kitchen bayan ta gama dafa abincin aka buɗe ƙofar a ka shigo duk zatonta Mommy ce yasa bata juyaba ta cigaba da abinda take, tsayawa ya yi abayanta yana ƙare mata kallo ajikinta taji ana kallonta hakan yasa ta juyo sukai ido biyu dashi buɗe baki tayi zatayi kuka ya saka tattausan hannunsa ya rufe mata baki ya juyo da ita gabansa alokaci ɗaya. Kallonsa ta shiga yi kamar munafuka ganin irin kallon da take mai yasa ya ce" dena kallona kona tsokane miki ido" ya fada yana cire hannunsa daga bakinta turo baki ta yi ya ce" wa kike ma wannan abun?" girgiza kai tayi saboda sanin muguntarshi ta ce" ni badakai nakeba wlh" ɗauke kansa ya yi yana murmushi ya ce "zaki sanine yarinya kiyi iya yinki time ɗinkine" juyawa ya yi ya fita ita kuma ta haɗo kayan ta fito.....
Misalin ƙarfe takwas ta fito cikin shigarta ta abaya as usual milk colour ta gaisheda su Daddy sannan ta zauna Mommy ta ce"wai wannan yarinyar ƴar wace?" kallon Amrah ta yi ta ce" Amrah sunanta ƴar ƙawatace jiya sukazo shine Azaad ya ce abarta anan yau zan maidata" Ok Mommy ta ce Daddy ya kalleta ya ce" jeki kirawon Saima" wata irin faɗuwar gaba taji ya saukarmata amma bata nuna ba ta ce"toh" sannan ta tashi jiki a sanyaye ta nufi ɗakin......
Kwance tasameta ta lulluɓa da duvet,sosai taji daɗi aranta ta ƙarasa ta zauna gefenta ta ce" yaushe kika dawo jiya?" dakyar da buɗe baki ta ce" banida lpy ne saida mukaje asibiti sannan nadawo gida" ta ce" Allah sarki sannu meyake damunki" tashi zaune tayi ta ce" wlh zazzaɓi nake yi amma yanzu naji sauƙe bansanma safiya tayi hakaba" tashi ta yi ta ce "ok daman Daddy ne yace nakira ki" ta ce "toh".....
Kallonta sukayi har ta ƙaraso sannan Daddy ya ce"where is she?" ta ce" tana wanka ne yanzun zata fito" ok ya ce sannan ya cigaba da cin abincinsa........
Har kusan azahar tana zaune a É—akinta bata fito tunda safe data fita da gaida su Daddy dan ko breakfast batayi tana É—aki akwance shigowa É—akin tayi tana kallonta ta ce"please Saima zan É—an fita ki zauna da Azaad da Amrah" ok ta ce sannan ta tashi ta fito parlourn......
Kusan 5mins suna zaune a cikin motar sannan Samha ta ce" mu shiga Zahra" Ok ta.ce.sannan suka fito suka shiga gidan......
Zaune suka tadda shi ya hakimce akan kujera yana shan ice-cream hankalinsa kwance, Kallonsu ya yi sai kuma ya miƙe yana waro ido ya ce".Zahra kece?" tana kallnsa ta ce" kayi mamakin ganina ko?" girgiza kai ya yi ya ce" bawai mamakin ganin naki nayiba amma na ɗauka kin mutu" ta ce".toh Allah yafi ƙarfinka kayi zaton ka kasheni amma kuma Allah ya kiyaye ni kodan na tona maka asiri" wata irin mahaukaciyar dariya ya yi ya ce" ay kinyi kaɗan ki tonamin asiri dan idan kika tonan asiri kamar kin tonawa kanki ne kuma ni babu abinda kika isa kiyimin " cikin ɓacin rai Samha ta ce"ok daman tunaninka kenan dayasa kake lalata ƴaƴan mutane?, to kasani wlh awannan karan bazaka shaba dan dole sai an hukuntaka" wani killer smile ya yi ya ce" Samha kenan kinsan har abada bazan iya yimiki rashin mutunciba saboda ina maki kallon masoyiyata da'ace kinada wayewa toda yanzu munyi aure nida ke kuma yanzuma idan ban aure kiba zan auri ƴar biyunki kinga abunda kike gudu ayi dake zanyi da ƴar uwarki kum....wata mari ta ɗauke shi dashi ji kake tasss afusace ya ɗago kai yana kallonta ya riƙe kuncinsa cikin zallar ɓacin rai ta ce" wlh kayi kaɗan ka auri jinina kai baka kai wannan matsayinba kamar yanda na nesanta dakai haka Saima zata nesanta dakai kuma saina tona maka asiri wlh, nasan akwai abubuwa da yawa wanda baka saniba amma ni nasani" yana mata wani kallo ya ce" abu ɗayane zaisa na barki ki fita gidan nan araye saboda ina sonki kamar ynda nake faɗa miki amma kada kiyi tunanin kin mareni zai huce wlh saina rusamiki farin cikinki kinji na rantse" wani banzan kallo tayi masa ta ce "kai ka isa ai wlh kayi kaɗan ka rusamin farin cikina saboda yanzu ba da bace" tana gama faɗin hakan ta kama hannun Zahra sukai waje.......
Tsayawa yayi yana kallon ƙofar da suka bi Mubarak ya fito ganinshi tsaye yasa ya ce "lpy bro?" kallonsa ya yi ya ce "nothing karka damu" ya ce"ok".......
Bayan sundawo gida suna zaune parlourn a gidan su Zahra Samha ta ce "plx Zahra karki saka wannan abun a ranki kinji" girgiza kai Zahra tayi ta ce"i can't Samha wlh duk sanda na tuna da Yazeed zuciya zafi take min sai naji inama ban taɓa zuwa secondary school ba, sai naji inama nice nakamu da ciwon zuciya na mutu ko kuma na kashe kaina, ayau dana sake ganinshi naji kamar na ɗauki wuƙa na caka masa ya mutu idan yaso nima akasheni, Yazeed ya gama cutata babbar cutarma daya kasance ƴa mace na haifa me zancewa yarinyata idan ta girma?, wannan yasa nakejin Allah yasa na mutu na huta" ta ƙarashe maganar tana sakin wani raunataccen kuka. Kamo hannunta Samha ta.yi ta ce"kiyi haƙuri nasan dole akwai raɗaɗi amma ki daure kinji Zahra, yanzu maganar danake miki wlh Yazeed so yake ya auri Saima kuma ta rigada ta yarda dashi hundred percent nayi iya bakin ƙoƙarina amma abanza" cikin tashin hankali ta ce" subhanal-lahi yanzu mene ne mafita Samha dan wlh bazamu zuba ido Yazeed ya aureta ba" murmushi Samha ta yi ta ce" In sha Allah inaso nasamu lokacine na zauna nabata labarin Yazeed na tabbata Saima zata yarda dani" In sha Allah ta ce sannan ta mike dan zubo musu abinci.......
Sai bayan magrib sannan tashigo gidan ganin babu kowa a parlourn yasa tayi shigarta ɗaki tai sallah tayi wanka sannan ta fito, lokacin suna zaune suna cin cake ta zaune gefensu ta ce"lallai yarannan wane ya baku cake?" Azaad na saka wani lomar cake ɗin abakinshi ya ce" Aunty Saima ce ta bamu" ta ce" enyeee ina take aunty Saiman?". ya ce "tashiga ɗaki dan tace batajin daɗi" miƙewa tayi ta ce"lemmme check her" sannan ta nufi ɗakin................
Zaune ta sameta gefen gado tayi shuru kana ganinta kasan tunani take zama tayi gefenta ta ce" Saima lpy kodai jikinne?" girgiza kai ta yi ta ce" no naji sauƙi sosai kawai dai banida kuzari shiyasa" ta ce" ok bari Mommy tadawo sai ta baki magani" kallonta ta yi ta ce" basai ta baniba naji sauƙi sosai" murmushi tayi ta ce" to ko nadafa miki abun. daɗi kamar peppersoup haka?" ɗaga mata kai tayi ta ce"Eh plx wlh daman yunwa nakeji " harararta ta yi ta ce" to sarkin kwaɗayi bazan yiba" langwaɓar da kai tayi ta ce"plx twinny ki taimaka" tashi tayi ta ce"naji zanyi karki cinyeni" dariya tayi ta ce"ni awa na cinyeki" ta ce" ke mana a Saima ta yaya Ayaan yar baƙa" haɗe rai tayi ta ce" Allah kuwan banaso kidaina faɗamin" dariya tayi sannan tayi waje..........
Gama dafa kazar kenan ta zubota a bowl tana fitowa ta tadda Abu Azaad a zaune akan kujera yana danna wayarsa kallonsa tayi ganin yanda yake murmushi ta fahimci da wacce yake wayar ai kuwa ta haɗe rai tazo zata huce ta gabansa ya saka hannu ya jawota, kallonsa tayi ta ce" Allah Abu Azaad ka rabu dani " bowl ɗin hannunta ya karɓa ya buɗe ya ce" wannan na wane?" girgiza masa kai tayi ta ce" A'a wlh na Saima ne batada lpy" kafin ya yi magana Saima tafito tana kallonsu ta zauna kan kujera kusada shi ta ce"shine kika gama dafa naman kika kawowa Abu Azaad bayan kinsan halinsa da nama?" haɗe rai Samha tayi ta ce" to nina bashi ba kwata ya yiba" dariya yayi ya kalli Saima ya ce" tawo mu ci ki rabu da ita" murmushi tayi sannan ta matso suka saka kwanon a tsakiya suna ci, ita kuwa Samha tsayawa tayi tana kallonsu ganin da gaske sun kusa cinyewa sai kawai ta fashe da kuka, murmushi Aliyu ya yi sannan ya gutsuro naman yana kallonta ya ce" haaaaaaa " turo baki tayi sai kuma ahankali ta buɗe bakin ya saka mata naman ta ɗauke kai tana taunawa