Showing 6001 words to 9000 words out of 29671 words

Chapter 3 - TSAKANINMU BOOK 1 by Nana meera.txt

Unknown   

26 Jun 2024

5768

ce " twinny ya jikin naki?" kallonta ta yi ta ce " dasauki Alhamdulillah " murmushi ta yi ta ce " wai Mama bakiga takwararki bane ?" cikin masifa Mama ta ce " to sallamammiya ita data shigo ta kulani ne?, ko saboda ni nafi kowa barbaɗa saina hau kulata " dariya kowa yake yi hakan ya ƙara tunzurata ta ce " A'a nifa ba mahaukaciya bace da zaku dinga yimin dariya " little Azaad ne ya kalleta ya ce " ke granny kin iya comedy wallahi " mitsi-mitsi ta yi da ido ta ce " kai karkaga ina cemaka mijina wallahi ranka ne zai ɓaci dan ko ubanka bai isaba bare kuma kai " ɗagowa Haidar ya yi ya ce "gaskiya Mama babu ruwana a wannan zance karki sako dani kije can ki ƙaraci rikicin tsufanki " ta buɗe baki zatayi magana kenan Daddy da uncle suka shigo sai wasu maza biyu a bayansu waɗanda bazasu huce shekaru 30 ba tana ganinsu ta fashe da kuka da mamaki Daddy ya ce " Mama lafiya kedawa ?" cikin shasheƙa ta ce " yanzu ace kamar ni Aliyu ya zauna yana zagi shida wannan ɗan nasa " da mamaki Daddy ya ce " Aliyu kuma shi Aliyun?" baki buɗe kowa na parlour'n yake kallonta sanin halinta yasa uncle ya ce " Aliyu koda wasa karka sake shiga har karta ka riga kasan halinta yanzu sai addu'a " girgiza kai ya yi ya ce " ni bansan meyasa takeson yimin sharri ba wallahi agaban kowanefa ko yaushe na zageta bansani ba " murmushi Saima ta yi ta ce " sai haƙuri yaya " tsaki yayi ya ce "shiyasa fa bana shiga harkarta kwata-kwata " wata uwar dariya aka sheƙe da ita kallo ɗaya ya yi masa ya ce " wai dan Allah Ayaan yaushe zakayi hankali?" shigowa ya yi ya ce " gobe, mutanen Naija saukar yaushe ?" ya faɗa yana kallon Samha, murmushi ta yi ta ce " wallahi tun rannan akace kana india " eh wallahi aiki ya riƙeni bansan kun zoba, ɗaga masa kai kawai tayi dan har sannan batajin daɗin jikinta kallon Saima ya yi ya ce " A'a kace harda baƙalli akazo, wai dan Allah uncle awane asibiti aka caka maka ?" haɗe rai tayi ta ce " Allah yaya Ayaan banaso kadai naimin " dariya ya yi ya ce " Allah Daddy akoma asibitin wannan ba ƴar familyn mu bace ƴarinya baƙaƙirin " yanda ta haɗe rai kamar zatayi kuka zaka kane batason yanda yake tsokanarta, daga baya Asaad ya ce " sorry rabu dashi kinji Saima ai kowa yaganki yasan ke familynmu ce kuma ai baiwace da Allah ya yoki chocolatey kinji stop worring kinji "murmushi ta yi ta ce " yawwa yaya Asaad kuma In sha Allah sai ya auri baƙar masa wacce tafini baƙi kuma ƴar talakawa " dariya ya tuntsire ya ce " lallaima yarinya ni bakisan ƴar shugaban ƙasar America zan auraba " Uncle ne ya ce " kai kutashi kubawa mutane guri sai surutu kamar kunci aku " kallonsa Mama ta yi ta ce " A'a karka matsawa jikokina kabarsu idan basuyi hiraba mai zasuyi kaji ɗa " murmushi Daddy ya yi ya ce " hajiya Mama Allah ya baki haƙuri " tashi tayi ta ce " ai gaskiyace da son samune ai su auri junansu " dariya Ayaan ya yi ya ce " tab ai kuwa wannan baƙallin zata daɗe bata sami mijiba " kallonsa Mama tayi ta ce " kaji sallamammen ɗa to in bansa ka aureta ba " tab wallahi bazai yiwu ba kawai ni tasawa agaban mota zan aura " tsaki Mama tayi ta shige ɗakinta dan ita lokacin kwanciyarta yayi.....












Daddy ne ya kalli uncle Yaseer ya ce " wai kuwa har yau yaya bai dawoba ?" ajiyar zuciya ya sauke ya ce " wallahi bai dawoba yace nanda two weeks zai dawo amma ai zaku jirashi " gyara zama Daddy ya yi ya ce " ba lallai ba saboda su Samha zasu koma makaranta next week to kaga akwai buƙatar mutafi kafin sannan " Zaheera ce tashigo ta tsuguna ta gaidasu sannan ta ce " Saima inasu Mami " miƙewa ta yi ta ce " yanzu suka shiga ciki da Samha " ok tace sannan ta koma part ɗinta.....












Zaune yake yana operating laptop Zaheera ta miƙa masa kofin coffee ɗin amsa yayi ya ce " thanks " zama tayi gefensa ganin kusan ten minutes amma bai bar abinda yake ba yasa ta ce " Abu Azaad " batareda ya kalletaba ya ce "uhmm " cikin damuwa ta ce " meyasa bakason kulani ?, kwata-kwata tunda mukai aure baka shiga harkata yaushe rabonda wani abu ya haɗani dakai ?" kallonta yake tunda ta fara maganar Allah ya sani yana son kyautata mata amma kwata-kwata bashida feelings ko kaɗan ƴa mace bata gabanshi ganin yayi shuru yasa ta ce " kayi shuru " daidaita nutsuwarsa yayi sannan ya ce " Zaheera i'm sorry amma tun bayan munyi aure nima nakejin haka bansan meyasaba kiyi haƙuri idan da rabon watarana nadawo kamar da sai kiga Allah ya yayemin " goge hawayen idonta ta yi ta ce " Abu Azaad na yarda dakai domin son da nake maka yasa nayarda na aureka dukda nasan baka sona alharma kayi min " da damuwa ya ce " Zaheera banason kina irin wannan maganar amma narasa meyasa kika saka haka aranki fiyeda komai " cikin shasheƙar kuka ta ce " Abu Azaad kana sona ?" kasancewar bai iya ƙaryaba yasa ya ce " bazan miki ƙaryaba Zaheera ina ƙaunarki amma bantaɓai miki so irinna aure ba " goge hawayenta tayi ta ce " shikenan hakanma nagode sosai Abu Azaad amma dai kanason Azaad ko ?" murmushi yayi ya shafa kan yaron wanda yake bacci hankalinsa kwance ya ce " kin taɓa ganin ubanda baya son ɗansa?, inason Azaad, ina jinsa araina " murmushi ta yi ta ce " nagode sosai Abu Azaad " rufe system ɗin yayi ya jawota jikinsa ya ce " faɗamin yanzu me kike so?, kwanciya tayi aƙirjinsa ta ce " nadinga jin ɗuminka akoda yaushe shine muradina " dariya ya yi yana ƙoƙarin zame ƴar rigar baccin dake jikinta hakan yasa nayi musu saida safe najawo musu ƙofar....












Kamar jiya haka yauma jikinta ya dinga ciwo sai zufa take haɗawa lokaci ɗaya taji tanajin wata irin ƙishirwa hakan yasa ta lallaɓa ta fito dan ɗaukan ruwan batareda ta luraba ta shiga wani ɗakin wanda aka ƙawatashi da kayan more rayuwa bata kalli kowaye akwance ba taje takwanta jikinta sai rawa yake jin mutum ya danneshi yasa ya buɗe ido yana ƙarewa kyakyawar fuskanta kallo tashi yayi zaune yana kallonta dakyau mamakin abinda ya shigo da ita ɗakinsa yake , shima ji yayi ya takura awancan yasa yadawo ɗakinsa tun kan yayi aure, yanda jikinta ke rawa yasa yakai hannunsa jikinta sosai yaji temperature ɗinta tahau sosai kuma kamar tafara fita hankalinta tashi yayi ya dudduba amma bai sami magani ko injection ba hakan yasa ya ɗauketa ya direta a toilet, without second though ya fara ciremata kayan jikinta itakuwa batamasan abinda yakeyiba saida ya rage daga ita sai pant da bra sannan ya kunna musu shower wata irin zabura tayi ta shige jikinsa tanajin kamar zata waɗi sosai shima ya rungumeta tsam ajikinsa, kusan ten minutes sannan ya ɗauketa kamar ɗazu ya fito da ita towel yasa ya goge mata jikinta sai a sannan ta fara gane ina take, bayan ya gama gyarata ya rasa mezai bata tasa kasancewar babu kayan mata aɗakin, hakan yasa ya ɗauko mata armless ɗin riga da boxer ya samata sannan ya jata bakin gado shikuma ya koma banɗakin...










Some few minutes ya fito cikin sabuwar shiga zama yayi gefenta ya kalleta ya ce" me kika fito yi da daddare ?" turo baki tayi ta ce " ni ruwa zansha " tashi yayi ya fita ya kawo mata ruwan bayan ta gama sha ya ce " to tashi ki tafi " kwaɓe fuska ta yi ta ce " ni tsoro nakeji saidai ka rakani " kallonta ya yi sai kuma ya yi kwanciyarsa ya ce " saidai ki kwana anan indai ni zan rakaki " yana gama faɗa ya juya mata baya. Kallonsa ta yi ganin bashida niyyar rakata yasa ta fashe da kuka tana cewa " Abu Azaad please kazo ka rakani wallahi tsoro nakeji " yana jinta yayi mata banza har tagaji ta fara gyangyaɗi azaune can kuma saita kwanta gefen gadon yanaji ta kwanta dama yasan asalin matsoraciyace yayi wani murmushi sai kuma ya ce "mmmyywww " ai da gudu tazo ta ƙanƙameshi tana cewa " Abu Azaad mage please ka fita da ita " juyowa ya yi ya kalleta ya ce " to ina ruwana ta kama mai tsoronta " kwaɓe fuska tayi ya ce " kina yin kuka ni kuma zan kirata " turo baki tayi ta ce "ai ni ba kuka nace zanyiba " ɗauke kansa ya yi yana wani cute smile, kusan five minutes yaji saukar numfashinta alamun ta yi bacci blanket ya ja musu kana yayi musu addu'a bacci ya ɗaukeshi.......










Bugun ƙofar da akeyi yasashi ya farka sosai yayi mamakin lokaci dan tun bayan sallar asuba ya koma bacci, miƙewa ya yi jin yadda ake knocking ɗin yasa ya ce " waye ?" murmushi ta yi ta ce " Abu Azaad ni ce "kallon ƙofar yayi sai kuma ya kalli Samha wacce take bacci hankalinta kwance ya rasa meya kamata yayi ga Zaheera abakin ƙofa jin ansaƙe knocking ɗin yasa ya ce "












Comments, like nd share.










```Written by```
*Nanameera*














Meera Love's yhu🫶🏻🫶🏻🫶🏻🫶🏻
[1/31, 10:21] Nanameera writer: https://chat.whatsapp.com/BRBJgmCve2uEO7OzFYz8Sj


💖💖TSAKANINMU💖💖








Story and written by:
*Nanameera*






.....Tauraruwar royal star✨




*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*






_Haɗaka palace_
Kungiyar masu posting ce ba marubuta ba.






🅿️...0️⃣5️⃣....






____________Cikin sauri ya ce " i'm coming " ƙara jamata duvet ɗin sannan yaje ya buɗe, rungumeshi Azaad yayi ya ce " Abbu good morning " da mamaki ya ce " ina mamanka?" dariya yayi ya ce " taje kitchen gurin Mami " ɓoyyiyar ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce " ok jeka taso uncle Ayaan kaji love " da gudu ya tafi shikuma ya koma ɗakin yasa key, kallonta yayi sannan ya hau tashinta ɓuɗe ido ta yi ta ce " dan Allah Abu Azaad kabarni " haɗe rai ya yi ya ce " tashi ki fita " tura baki tayi sannan ta sakko daga kan gadon tasa bedroom slippers sannan ta yi waje....












Fitowarta kenan daga kitchen ta kalleta ta ce " Samha meya kaiki ɗakin yaya Haidar ?" shuru ta yi bata bata amsaba ta kuma cewa " kinyi shuru naga.... Shigowar Daddy yasa ta yi shuru kallonsu ya yi suka gaisheshi sannan ya ce " meya faru na ganku haka ?" Saima ce ta ce " Daddy ina tambayarta ne meya kaita ɗakin yaya Haidar " kallonta Daddy ya yi ya ce " ba magani ya bataba ?" da sauri Samha ta ce "Eh Daddy magani na karɓa " gaba yayi bai sake bi takansu ba yana tafiya Saima ta ce " to ina maganin ?" harararta ta yi ta ce " bansani ba uwata " tana gama faɗin haka tayi gaba abinta, girgiza kai ta yi ta ce " Allah ya shiryeki twinny " sannan itama ta koma kitchen ɗin....












Sai kusan azahar sannan tafito cikin wata sky blue ɗin riga da wando tasa wani baby hijab tayi kyau sosai Asaad ne ya kalleta ya ce " wow Samha wallahi kinyi kyau abinki kamar sarauniya mijinki yayi dace wallahi " kallonsa tayi tai murmushi ta ce " kai yaya Asaad banson sharri Allah" dariya ya yi ya ce " wallahi da gaske nake miki " zama ta yi ta ce " niban yarda ba bakaine kace black beauty tafi kyau ba Saima tafine kyau saboda kaga batanan to wallahi yanzu zata fito zamu supermarket kuma wallahi saina faɗa mata " tashi ya yi ya ce " bari kiga na gudu dan Saima tafi ƙarfina " kallonsu ta yi ta ce "wace Saiman ?" gaba yayi bai bata amsaba ta kalli Samha ta ce " dan Allah meya cemiki ?" dariya ta yi ta ce " bansani ba kije ki tambayeshi mana " kwafa tayi ta ce " bari mudawo " tashi sukai suka fita dan zuwa shopping mall ɗin.....












Bayan sunga ɗaukan duk abinda suke so sukazo wajen biyan kuɗi samusu kayan aleda akai sannan Samha ta miƙa ATM card ɗinta me abun ya ce anrigada anbiya da mamaki ta ce " waye kuma ya biya ?" daidai lokacin yazo zai fita ya ce " wancan mutumin mai black ɗin riga shine ya biya " ok tace sannan ta kama hannun Saima dan suje suga wanene ...










Zai shiga mota ta ce " bawan Allah " juyowa yayi mutuwar tsaye tayi saboda mamaki ta nunashi da yatsa ta ce " kaine " murmushi ya sakar mata ya ce " Fatima Ahmad Azaad kina lafiya " rungume hannu tayi a ƙirji ta ce " lafiya lao ko kayi zaton saboda banshiga lecture'n kaba zanyi lalura ne ?" murmushi ya yi yana girgiza kai ya ce " Samha kenan " da wani mamakin ta ce " ina kasan sunana ?" kallonsu ya yi ya ce " Samha kenan kin ɗauka bansan komai nakiba ?, nasanki fiyeda ƙima hatta biyuninki nasani Zainab Ahmad Azaad amean Saima " ranta ahaɗe ta ce " meyasa ?, mekakeso awajena ?" murmushi ya yi ya ce " soyyayarki da kuma yardarki su nake buƙata karki ce A'a please " kallon kazama mahaukaci tai masa ta ce " ni Samha kake so?, amman dai kana hauka ko?" dariya ya yi sosai wadda ta ƙara fidda asalin kyansa sannan ya ce " Samha ina sonki na koreki daga lecture ɗina ne saboda nayi testing naki bawai dan banasonki ba ko na tsaneki please Samha kiyi accepting ɗina koda sau ɗaya ne kinji " kama hannun Saima ta yi ta ce " mutafi please " gaba sukayi sannan Saima ta ce " haba Samha wai mene matsalarki?, wallahi kowa yasan Sir Sapwan bashida matsala yanada ilimi, kyau, kuɗi addini dan Allah ko sau ɗayane kiyi accepting nasa idan yaso idan bai mikiba sai ku rabu " kallon ta farayi tunda ta fara maganar saida ta idar sannan ta ce " please Saima leave me alone kinji " tana faɗin hakan ta cikata tayi gaba.....












Dawowa tayi gurinsa ta ce " sorry Sir kasan halin Samha sai ita please kayi haƙuri " murmushi ya yi ya ce " babu komai Saima nagode " sosai taji daɗi ta ce " yanzu kabani lambarka In sha Allah zansa ta kiraka " card ɗinshi ya miƙa mata da rafar dollar ta kalli kuɗin ta ce " la wallahi nagode kabarshi " haɗe rai ya yi ya ce " bani na baki ba karɓi mana " gaba tayi ta ce " wallahi nagode sosai " tashige mota suka ja, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya shiga tashi motar yana fatan Allah yasa ta amince dan ba ƙaramin so yakewa Samha ba.....












Tunda suka shigo yake kallonsu har suka ƙaraso gabansa Saima ta yi murmushi ta ce " yaya ina zuwa ko asibiti?" murmushi ya yi ya ce " no unguwa zani ina kikaje?" da fara'a ta ce " wai shopping mall mukaje " gaba ya yi ya ce " sannunki " murmushi tayi itama sannan ta yi ciki ......












Zaune ta tadda ita gaban su Mami tana nuna musu abinda ta siyo murmushi Mami ta yi ta ce " sunyi kyau sosai daughter " zama Saima ta yi ta ce " Mami wai yaushe jidderh zasu dawone gashi har zamu tafi?" murmushi Mami ta yi ta ce " maybe next week Saima amma ku yaushe zaku koma ?" ruwa tasha ta ce " chab mufa maybe weekend mukoma saboda kinsan monday zamu koma school " da mamaki Zaheera ta ce " kaii !! gaskiya ya yi huri dayawa bama next week ba ?" dariya ta yi ta ce " wallahi kimsan school sai ahankali dole mu koma da huri za'a kafe mana jarrabawa " ok Allah ya bada sa'a Ameen ta amsa sannan suka tashi danyin sallah...












Sallama tayi ta shigo ɗakin kallo ɗaya Samha tayi mata ta ɗauke kai zama tayi gefenta ta ce " Samha meneyi miki dayasa kwata-kwata bakya kulani?, nayi miki shuru dan naga ko gajiya kikai amma har yau baki buɗi baki kince Zaheera ya kike ba meyasa Samha ko nayi miki laifi ne?" kallonta Samha ta yi ta ce " ayyah kiyi haƙuri ummi Azaad abubuwane sukayi min yawa kinji amma ai yanzu gashi ke kin yimin kuma naji daɗi nagode sosai dan Allah kiyi haƙuri " murmushi ta yi ta ce " babu komai Samha nice da godiya sai anjima " tashi ta yi itama ta ce " bari nashiga toilet agaidamin Azaad " ok ta ce sannan ta fita......










Ahanya suka gamuda Saima ta ce " A'a ummi Azaad daga ina haka ?" murmushi ta yi ta ce " wallahi gurin Samha naje naji menayi take fushi dani " dariya ta yi ta ce " kemadai sai kace bakisan halin Samha ba watarana fa ko Mommy bata kulawa tafiye nunƙufurci, nima yanzu wajenta zani " sai kindawo ta faɗa sannan ta yi gaba.....












Babu kowa a bedroom ɗin sai ƙarar zubar ruwa hakan yasa ta zauna gefen gadon dan jiranta, kusan seven minutes sannan tafito sanyeda towel kallonta ta yi ta ce " ke kuma daga ina?" kwanciya ta yi kan gadon sannan ta ce " kedai shirya sai kiji ko mene ne " ok ta ce sannan ta hau shiryawa...












Zama ta yi kusada ita ta ce " to gani " tashi ta yi ta riƙe hannunta ta ce " Samha dan Allah dan Annabi ina neman alharma awajenki karki ce A'a kinji twinny kodan zumuncin dake *TSAKANINMU* ki yarda please " da mamaki ta ce " wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login