Showing 15001 words to 18000 words out of 29671 words
*
*Nanameera*
_Tauraruwar royal star_
🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_
*Alk'alaminmu 'yancinmu*
_Hadaka palace_
Page.11&12....
__________tana masa wani matsiyacin kallo ta ce " wacece ex ɗin taka?" wani killer smile ya yi ya ce " kemana Samha ai nasan har abada baki taɓa mance *TSAKANINMU* ba kamar yanda nima bazan mantaba, nasan har yau har gobe kina sona kamar yanda nake sonki dan dalilin son da nake miki yasa naji inason biyuninki Saima" sosai gabanta yake faɗuwa amma ta dake cikin faɗa da kuma nuna zallar ɓacin rai ta ce " lier!, ƙarya kake domin ni na daɗe da mance alaƙar dake *Tsakaninmu*, bana fatan sake tuna irin wannan alaƙar sannan ina gargaɗinka Yazeed ka fita a harkar Saima idan ba haka ba wllh saina fasa kwan idan yaso kowama yaji, naƙi faɗane saboda na rigada nayi maka alƙawarin zan riƙe maka sirri amma wllh da tuni kowa ya ji kuma yanzuma idan baka fita harkan ƴar uwataba wllh zaka sha mamakina i will show you the other side of me" ta ƙarashe maganar tana nunashi da yatsa.
Zama ya yi akan kujera alokacin mood ɗinsa ya fara canzawa ya ce " who stop you Samha?, kije ki faɗawa duk wanda kike tunanin zaki faɗawa amman karki manta ƴar uwarki ma na hannu idan kuma ciwon zuciyar naki kikeson ya dawo sabo bismillah " tsugunawa ta yi ta haɗe hannayenta biyu ta ce cikin rauni " please Yazeed kada ka cutarda Saima she can't take it nasan halin twinny, kasan na sanka farin sani kuma da zarar naiwa Saima bayani wllh kona sakan ɗaya bazata sake kulaka ba saboda haka please and please ka fita a rayuwarmu ka rabu damu " wata irin dariya ya hau yi saida ya yi mai isarsa sannan ya ce " Samha kenan, kin san nasan duk abinda zaki iya wllh haka kawai bazaki zo ki tsuguna a gabana ba, kinsan ina sonki sabida haka zan rabu da Saima idan har zaki dawo gareni " a firgice ta tashi daga tsugunon tana masa wani kallo ta ce " macuci, mayaudari, azzalumi kawai, wllh har abada ni dake banso na sake ganinka acikin rayuwata ba Yazeed naso munyi rabuwa irinta har abada saboda kwata-kwata bakada imani a cikin zuciyarka, kuma idan kana mafarkin ina sonka to ka sani kaci ƙarya kodada na sakan ɗaya banasonka kuma bazan taɓa sonkaba" tashi ya yi yana mata tafi yana zagayeta sannan ya ce " maƙaryaciya kawai, idan baki sona meyasa kika faɗi hardasu ciwon zuciya Samha?, nasani har yanzu kina sona so kawai muzo mu rufawa juna asiri kinji" goge hawayen fuskanta ta yi ta ce " har abada wlh zan tafi amma ka sani wata rana zakayi danasani alokacin da bazata amfaneka ba" dariya ya yi yana gaba yace " muje na saukeki" tsaki tamasa sannan tayi waje......
Bayan ta dawo gida ta zauna ita kaÉ—ai sai tunani take irin abubuwan da suka faru a wancan lokacin Azaad ya yi sallama ya shigo, haurowa ya yi ya zauna gefenta ya ce " Aunty Samha kizo inji wannan mutumin mai kayan daÉ—i" murmushi ta yi tana shafa kansa ta ce "ok to kaje kace ganinan zuwa" da gudu ya fita ita kuma ta tashi dan gyarawa.
Tunda ta fito yake kallonta sanye takeda wata atampa brown colour ɗinkin rigada skirt tasa veil batayi kwalliya ba lip gloose kawai tasa da kwalli amma sai ka rantse wata kwalliyar tayi tayi kyau sosai, zama tayi kujerar kusada shi ta ce " sannu da zuwa" murmushi ya yi ya ce " yawwa sweetheart ya kike ya ɗan naki?" tana wasada fingers nata ta ce " muna nan klao Alhamdulillah" ya ce " daman zuwa nayi naji ina muka dosa akan maganarmu?" da mamaki ta ce " wace magana kuma ?" gyara zama ya yi ya ce " najiki shuru bakice na turoba " turo baki ta yi ta ce " tab ni dai babu ruwana wllh kabari saina gama school kawai" zaro ido ya yi ya ce " haba ai kya tausayamin aca har saikin gama degree kuma bayan yanzu kika shiga gaskiya i can't " kwaɓe fuska ta yi ta ce " tab nikuwa bazanyi aure ba sai na gama degree sannan" zaiyi magana akayi horn hakan yasa ya yi shuru, bayan Daddy ya yi parking ya kallesu yana ƙarasowa Sapwan ya tsuguna cikin girmamawa ya ce " barka da zuwa, ina wuni " fuska a sake Daddy ya ce " lafiya lao alhamdulillah sannunka" daga haka ya shiga gida. Tashi ya yi ya zauna tana masa dariya ta.ce " dan Allah kalli yanda kayi wani kamar mara gaskiya" dariya ya yi ya ce " Kee Daddy fa ai dole nayi kamar mara gaskiya" murmushi ta yi ta ce " to gaskiya ka tafi kaga Daddy ya dawo" tashi ya yi ya ce " ok ai tafi zanyi kar najawo Daddy ya yi miki duka" dariya ta yi ta ce " haba ai wuce nan wllh koda ina ƙarama Daddy baya dukana bare yanzu" ya ce " ok tom ki gaishemin da Mommy, Saima dakuma Azaad" ok ta ce sannan ya tafi parking lot ɗin gidan ita kuma ta koma gida...
Tana shiga ta tararda Daddy zaune shida little Azaad yana masa hira, tsugunawa ta yi ta ce " Daddy sannu da zuwa" kallonta ya yi ya ce " Samha waye wanda yazo gurinki?" aɗan firgice ta ce " lecture mune" ya ce " what bring him here?" shuru ta yi bata bashi amsaba ya kalleta ya ce " to banson tara samari ki tsaya kiyi karatu cox ba yanzu zan aurar da keba" sosai ta yi mamakin furucinsa saboda bai taɓa cewa Saima ba yanzu zai aurar da itaba sai ita?" yana mata wani kallo ya ce " understood?" ɗaga masa kai ta yi ya ce "ok tashi kije" tashi tayi Azaad ya yi sauri ya bi bayanta suka shiga ɗakinta......
Dadaddare tana kwance Saima ta shigo ɗakin ta zauna gefenta ta ce " twinny wai ɗazu menaji Daddy na cemiki?" tashi ta yi zaune tana facing ɗinta ta ce " wai cewa ya yi nacewa Sapwan ya dakata saboda ba yanzu zai aurar daniba" da mamaki ta ce " tab ɗijan to amma meyasa ni bai cemin haka ba?" ɗaga kafada ta yi alamar batasaniba ta ce " kinga ki rabu dashi wllh idan yaga kina kula shi to da kansa zaice miki ki cemai ya turo" murmushi ta yi ta ce " wai kuwa Yazeed ya turo da iyayen nasa?" girgiza kai ta yi ta ce" A'a wallahi wai Daddynshi baya ƙasarnan to sai ya dawo zai faɗa masa" ta ce " ok Allah ya dawo dashi lafiya" murmushi ta yi ta ce " Ameen, nikuwa na manta na faɗa miki munyi waya da Zaheera ta ce na gaisheki" lokaci ɗaya mood ɗinta ya sauya ta ce " oh ina amsawa" murmushi tayi ta ce " ya kamata ki kira Mama dan da mukayi waya saida tayi kamar zata cinyeni saboda ke" dariya ta yi ta ce " insha Allah zan kirata da Zaitoon da Mami In sha Allah" murmushi Saima ta yi ta ce " harda Abu Azaad" wata uwar harara ta maka mata sannan ta ce " na rantse akan wannan abun da kikemin sai ranki ya ɓaci to" dariya ta yi ta miƙe ta ce "ok good night dear" ok ta ce sannan ta fita ta ja masu ƙofar....
Washe gari bayan sun shirya suna breakfast Azaad ya ce " Aunty Saima kibani aron laptop ɗinki plx" tana goge bakinta da tissue ta ce " ok ka bari mudawo daga makaranta kaji kaga yanzu zamu makara " murmushi ya yi ya ce " tom amma promise?" gyaɗa masa kai ta yi ta ce" yeah!" ya ce "thank you " tashi sukai suna fitowa parking lot ɗin gidan akayi horn da mamaki mai gadin gidan yatafi ya buɗe ƙofar, wasu motocine suka shigo guda biyu, bayan sunyi parking wasu guards suka fito daga ɗaya motar da sauri suka buɗe masa ƙofa, fitowa ya yi cikin shigar sa ta suit baƙaƙe wanda sukai matuƙar amsar farar fatarshi cikin yanayinsa na son kamewa yake kallonsu, da gudu Azaad ya tafi yana wangale baki ya ce "oyoyo Abbunaaaa " ya faɗa yana faɗawa jikinsa ɗaga sa sama ya yi yana dariya ya ce"
_Written by_
*Nanameera*
```Love yhu oll```💖💖💖
[2/2, 20:10] Nanameera writer: https://chat.whatsapp.com/BRBJgmCve2uEO7OzFYz8Sj
🌹*TSAKANINMU*🌹
*Story and written by*
*
*Nanameera*
_Tauraruwar royal star_
🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_
*Alk'alaminmu 'yancinmu*
_HaÉ—aka palace_
_Page_ 13&14..
________Ya ce " na'am yaron Abbu" yana murmushi ya ce " Abbu dama zakazo shine baka faɗa mana ba?" saukeshi ya yi ya ce " saboda inason nayi suprising naka shiyasa " kama hannunsa ya yi suka nufi entrance ɗin gidan suna isa inda su Saima suke da murmushi Saima ta ce " welcome Abu Azaad, ina kwana " shafa kansa ya yi ya ce " lpy lao Saima ya kike ya karatun?" tana murmushi ta ce " wllh Alhamdulillah, irin wannan zuwa haka babu notice".ya ce "wallahi kam zuwan ne yazo abazata shiyasa amma ai munyi waya da Daddy" ta ce "ai kuwa Daddy bai faɗa mana ba, Azaad zo mutafi school" ɓuya ya yi abayan Aliyu ya ce "A'a ni wajen Abbu zan zauna " dariya ta yi ta ce " to kaje ka faɗawa Auntynka" da gudu ya ta yi inda Samha take tsaye kamar an dasata ya kama hannunta ya ce " Aunty zo muje wajen Abbu please" rasa yanda zatayi yasa ta tace toh sannan suka tafi. Suna zuwa ta kalleshi ta ce " good morning " ya ce" morning ya kike" tana wasa da fingers nata ta ce "lafiya klao ya Zaheera?" ya ce " she is fine" ta ce "masha Allah" kallonta Azaad ya yi ya ce" Aunty ni bazani school ba yau kinji "waro ido ta yi ta ce " saboda Abbunka yazo?" ɗaga mata kai ya yi yana kwabe fuska ta yi murmushi ta ce" kazo mutafi idan mundawo ma ai zamu tarar dashi kar kayi fashi kaji Love" turo baki ya yi lokaci ɗaya kuma ya fashe da kuka ya ce cikin zallar shagwaɓa" ni i'm not going to anywhere i swear" dariya sukayi duka Aliyu ya ce " shikenan yau ɗaya dai kayi fashi amma gobe zaka school ko?" gyaɗa masa kai ya yi Saima ta ce " wato saboda kaga Abbunka shine zaka mana rigima ko?, ai zai tafi ya barka ne" shuru ya yi mata bai kulataba Samha ta ce" ok tom sai mundawo kaji" da murmushi a fuskarsa ya ce "ok bye Aunty ki gaishemin da uncle Sapwan kice masa Abbuna yazo" da sauri Aliyu ya kalleta ta yi murmushi ta ce "ok zan faɗa masa kaji " daga haka sukai gaba sukuma suka shiga entrance ɗin gidan....
Bayan sun shiga mota Saima ta kalleta ta ce " wai meyasa bakison yiwa Abu Azaad magana?" kallonta ta yi ta ce " kamar yaya banason yi masa magana?" gyara zamanta ta yi tana facing nata ta ce " ina lura dake duk sanda zaku haɗu kina ignoring yi masa magana kuma kinsan isn't good idan Daddy yaji kinsan ranki sai ya ɓaci" harararta ta yi ta ce " to ai seki faɗa masa uwar sa'ido" murmushi ta yi ta ce " ko duk saboda kada Zaheera ta gane kune?" da mamaki ta ce " wai Saima what's wrong with you ne?, how mad you are kike haɗani da Abu Azaad?, banso wllh zan fara yi miki rashin mutunci " ta ƙarashe maganar tana galla mata harara, dariya ta hau yi kamar mahaukaciya ita kuwa Samha saboda takaici ko kallonta batai yiba ahaka har suka ƙarasa makarantar.....
Misalin ƙarfe biyu bayan sun fito daga masallaci wayarta ta yi ƙara bayan ta ɗaga ya ce "ya kike sweethear?" murmushi ta yi ta ce "i'm fine and you" ya ce " i'm fine too ina Azaad" dariya ta yi ta ce "wllh yana gida wai Abbunsa yazo saboda haka bazashi school ba harda kukansa" murmushi ya yi ya ce " Allah sarki ai ɗa da mahaifi sai Allah banga laifinsa ba" ta ce "ok hakama zaka ce?" ya ce" Eh mana, ya maganarmu kin faɗawa Daddyn kuwa?" lokaci ɗaya gabanta ya faɗi saboda tunawa da abinda Daddyn ya ce mata, jin ta yi shuru yasa ya ce " naji kinyi shuru lpy, ko baki jina ne?" cikin ƙarfin hali ta ce " umh yanzu ina jinka, dama bansamu na faɗa masa bane sai yau idan mun koma gida" ya ce " ok dan Allah kiyi ƙoƙari ki faɗa masa kinji" ta ce" In sha Allah i will do that " ya ce "ok " daga haka sukayi sallama.....
Wajejen la'asar suka koma gida bayan sun gyara sunci abinci suna zaune a parlour Saima ta ce "wai inasu Abu Azaad na jisu shuru?" Samha na operating laptop ɗinta ta ce "maybe sunyi nisa ne" ko rufe bakin batayi ba sukayi sallama suka shigo, da gudu Azaad yazo ya rungumeta tana murmushi ya ce " Aunty mun dawo" jawoshi ta yi gabanta ta ce " ina kukaje" da hannunsa yake mata indicating ya ce "mukaje asibiti sai kuma mu kaje shopping mall" ta waro ido ta ce " kace yawo kukasha, wait.. Ina tsarabata" tashi ya yi yaje gaban Aliyu ya ce " Abbu ina ledata" miƙa masa ya yi ya dawo ya zauna akan cinyarta ya ce "yawwa Aunty kinga komai biyu na siyo sai mu raba ko" rungumeshi ta yi ta na murmushi ta ce " Allah sarki my son yana son Auntynsa, to kabari sai zamu kwanta sai muci ko muna game" ɗaga mata kai ya yi ya ce " accepted" kallonsa Saima ta yi ta ce "ok kaida Auntyka kayiwa shopping ko?" turo baki ya yi ya buɗe ledar ya ɗauko wata chocolate ya miƙa mata ya ce " to kema gashi" dariya suka hau yi Saima ta haɗe rai ta ce " wane ya cemaka ni kwaɗayayyiya ce?" shuru ya yi ya mayarda chocolate ɗin cikin ledar ya kwanta jikin Samha, murmushi Aliyu ya yi ya ce "ok karki damu ni nayi miki shopping ki rabu dasu" tashi ta yi ta koma gefensa ta zauna tana murmushi ta ce " thank you Abu Azaad" ta kalli Azaad ta ce "ohya gashinan da baka siyonba Abbunka ya siyon" turo baki ya yi ya ce " ni ina ruwana, Aunty tashi mu tafi ɗaki muyi bacci" ok tace sannan ta miƙe ya rike hannunta suka shige ɗakinsu.....
Da daddare suna zaune suka dinner Daddy ya ce " Doctor amma zaka ɗan jima anan ko?" murmushi ya yi ya ce " Eh zanyi kamar one-two week inaga" buɗe baki Mommy ta yi ta ce " no ina wani daɗewa a one week gaskiya kayi ko one month ne ka taimaka kashiga asibitina dan akwai patient ɗin da suke buƙatar irinku" ya ce "ok In sha Allah zanga nayi ƙokarin haka" ta ce "yawwa ko kaifa" dariya Azaad ya yi ya ce " Abbu ka bari kayi one year kaji" murmushi Aliyu ya yi ya ce "idan ka gaji da Naija sai mu koma tare daman gidan ya yi shuru" kwabe fuska ya yi ya ce " Abbu da Aunty Samha?" ɗago kai ta yi ta kallesu sai kuma ta yi ƙasa da kai Aliyu ya ce "idan zata bimu sai mu tafi tare" murmushi Saima ta yi tana kallonta ta ce " haba ai zata biku mana" harararta Samha ta yi ta ce " school ɗinfa?" Azaad ya ce " ai akwai universities dayawa a ethopia " ta ce " dan Allah kayi haƙuri ka barni" murmushi kowa ya yi sannan suka cigaba da cin abincinsa.....
Wajejen ƙarfe sha biyu na dare ta miƙe ta fito parlour dan ɗaukan ruwa, zaune ta ganshi yana operating laptop ɗinshi a parlour'n tazo ta huceshi bayan ta dawo zata koma ya ce "keee!" juyowa ta yi taga bama ita yake kalloba hakan yasa ta dawo ta tsaya ta ce" gani" yana duba wayarsa ya ce " matsa a kaina" ta gane me yake nufi yasa ta tsuguna ta ce "gani to ni bacci nakeji" yana kallonta ya ce " who stop you?" turo baki tayi yana kallonta ya ce " wane Sapwan?" ɗago kai ta yi ta kalleshi sai kuma ta ce " wane Sapwan ɗin?" yana mata wani kallo ya ce " ina miki wasa?" kwaɓe fuska ta yi ta ce " wllh bansan me kake nufi ba" harararta ya yi ya ce " Samha kinsan ni ba abokin wasan ki neba ko?, ki faɗamin gaskiya ko na ɓata miki rai wlh" fashewa ta yi da kuka ta ce " ni wallahi bangane ba" tashi ta yi zata gudu ya fincikota ta waɗo jikinsa zata tashi ya matseta hakan yasa ta yi shuru tana ajiyar zuciya yana kallonta ya ce " yanzu faɗamin waye shi kuma mene alaƙarki dashi?" shuru ta yi tana kallonsa ya ce " saina tsokane miki idanunki kike kallona" kwanciya ta yi a ƙirjinsa ta ce " lecture'n makarantar mune fa" ya ce " shine yasa kike kulashi har Azaad yasanshi?" ta ce " kawai fa makaranta ya taɓa kaimu shine fa ya sanshi" bige mata baki ya yi ya ce " wallahi duk ran'da nasake ganin ki da wani saina karya ƙafarki tunda ke bakida hankali" yana faɗa yana squeezing bakinta daidai nan Saima ta buɗe labulen windows ɗinta, murza idonta ta yi dan tabbatar da abinda take gani gaskiya ne, saboda mamaki ta kasa rufe bakinta saboda yanda taga Samha kwance jikin Abu Azaad shikuma ya ranƙwafa kansa daidai fuskarta yana mata magana, sosai tayi mamakin amma tayi shuru ta tsaya tana ƙare musu kallo sannan ta sauke labulenta ta koma ta kwanta cikeda mamaki...
_Written by_
*Nanameera*
```Love