Showing 3001 words to 6000 words out of 29671 words
kaiwa ba niba nagaji da lallaɓaki karki yarda ɗin wallahi idan har sunana Zainab Ahmad Azaad(Saima) saina aureshi sai dai ace na karya alƙawarin dake *TSAKANINMU* kuma..... Wata kyakyawar tsawa Daddy ya daka musu hakan yasa sukai shuru kowanne yana huci, cikin faɗa ya ce " mene haka ?, bakuda hankali ne ko me?, akan wannan abun shine zaku yarda ku karya amincin dake tsakaninku?, a wane hadisin akace sai kun auri yan biyu kamarku?, wa yay muku dole?, duk wacce ta sami miji tayi aurenta, dan anhaifeku tare bashine yake nufin zakuyi aure tareba banson tashin hankali " Mommy ce ta ce " mene na ɗaga wa juna hankali, idan Saima kinsami miji ya fito itama sanda duk tasamu nata mijin sai ayi nata auren " kallansu Daddy ya yi ya ce " Saima kina son wanda kika faɗa ɗin ?" ɗago kai ta yi ta na kuka ta ce " Daddy wallahi indai Samha bataso na haƙura Allah yasa hakane mafi alkhairi " cikin faɗa ya ce " i asked you kina sonsa ko A'a bawai Samha ta yarda ko bata yarda ba " "Eh Daddy ina sonsa amma nafi son Samha dashi " tashi ya yi ya ce " kice masa ya turo iyayensa suzo ai magana " da mugun mamaki suka kalleshi duka dan basu ɗauka zai yarda ba cikin rawar murya Samha ta ce "Daddy dan Allah karka aura mata Yazeed kaji Daddy please " murmushi ya yi ya ce " Samha kiyiwa ƴar uwarki addu'ar zaman lafiya amma idan har nayi bincike na tabbatar da tarbiyarsu to zan aura masa Saima " dawowa gabansa ta yi ta riƙe ƙafarshi ta ce "
Comments, like and share.
Written by:
*Nanameera*
Meera Love's yhu 💖💖💖💖
[1/31, 10:21] Nanameera writer: https://chat.whatsapp.com/BRBJgmCve2uEO7OzFYz8Sj
💖💖TSAKANINMU💖💖
Story and written by:
*Nanameera*
.....Tauraruwar royal star✨
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_
*Alk'alaminmu 'yancinmu*
*Haɗaka palace*
Kungiyar masu posting ce ba marubutaba.
🅿️....THREE...
Cikin kuka ta ce " Daddy kasan bazan cutarda Saima ba, kuma bazan so ace ta yi danasani a rayuwarta ba please Daddy abar maganar Yazeed dan Allah " ta ƙarasa faɗa tana sakin kuka mai tsuma zuciya, a fusace Mommy tazo gabanta ta ɗagota zatai magana ta wanketa da mari ji kake tass. Abinda bata taɓai mata a rayuwarta ba kenan sai yau, cikin faɗa ta ce " ke wace irin yarinya ce mai baƙin hali saboda ƴar'uwarki ta sami mijin aure shine kike mata baƙin ciki?, to wallahi koda wasa na sake jin kinyi makamanciyar wannan maganar saina ɓata miki rai fiyeda tunaninki, wawiya kawai " tsabar shock ta kasa magana yau ita ake jifa da irin wannan mugayen kalaman?, goge hawayen fuskarta ta yi sannan ta ce " shikenan Daddy, Mommy, Saima kuyi haƙuri In sha Allah haka bazata sake faruwa ba, Allah ya bada zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba mai amfani ku gafarceni idan na ɓata muku rai " numfasawa Daddy ya yi deep down baiji daɗin abinda ya faru ba ya ce " shikenan ya huce karna sake jin antada maganar please idan ba hakaba ranku duka zai ɓaci kar kuce ban faɗa muku ba ku tashi kuban waje " tashi sukai kowacce ta yi ɗakinta tana saƙe-saƙenta, suna shiga ya kalli Mommy ya ce " Maryam karki sake faɗin irin wannan abun ga ƴarki bai daceba " ok yallaɓai ta ce sannan ya ce " Allah ya kyauta " ta ce " Ameen "......
Tunda ta shiga ɗaki take kuka meyasa su Daddy baza su gane mai take nufiba?, meyasa suke tunanin zata yiwa Saima baƙin ciki?, meyasa suka gaza saurararta ?, wannan sune tambayoyin da takewa kanta amma babu mai bata amsa hakan yasa ta tashi ta shiga banɗaki tayi wanka ta shirya ta kwanta...
Ɓangaren Saima ma haka ta kasance tunani take meyasa Samha take haka?, me nai mata takemin baƙin ciki bayan da ba halinta bane, duk ta ruɗe tana cikin wannan tunanin Yazeed ya kirata ta ɗaga suka hau hirar soyyaya sai taji ta manta da wata Samha ma....
Tun wannan ranar Samha bata sake yiwa kowa magana ba hasalima ko parlour bata fitowa kullum tana cikin ɗaki ita kaɗai, yau ma kamar kullum tana zaune akai sallama ta ɗaga ido taga Saima ta jingina da ƙofa ta sauke idonta ƙarasowa ta yi ta zaune gefen gadon ta ce " Twinny meyasa kika canza lokaci ɗaya?, meyasa bakison na auri Yazeed?, meyasa kika guji mu'amula da kowa a cikin gidan nan?, why twinny?, why?" kallonta ta yi amma ba tace komai ba hakan yasa ta ce " meyasa kike ignoring magana dani tun waccan ranar, wallahi banjin daɗi " murmushin takaici Samha ta yi sannan ta ce " babu komai kawai naga ya kamata nabaki dama kiyi rayuwarki karna takura miki nai miki baƙin ciki, idan na ɓata miki rai kiyi haƙuri dan Allah Saima Allah ya zaunar dake lafiya a gidan mijinki " kallonta kawai tayi sai kuma ta ce " Daddy ya ce ki shirya anjima zamu tafi " ok ta ce sannan ta tashi ta shiga banɗaki, girgiza kai Saima ta yi sannan ta yi waje.....
Fitowa ta yi cikin wata abaya peach colour tayi rolling round face ɗinta ta fito tayi kyau kamar ka ɗauka ka gudu, kallonta Daddy ya yi ya ce " Samha komai za'ayi sai kinsa anmakara ko ?" cikin ladabi ta ce " i'm sorry Dad " murmushi ya yi ya ce " Allah ya shiryeki " sannan ya yi gaba, kowacce tafiyarta take daban saɓaninda da zasu riƙe hannun juna su tafi suna nishaɗi....
Kusan ƙarfe takwas na dare suka sauka a garin Ethopia wasu motocine na alharma sukazo kusan goma murmushi Daddy ya yi sannan ya ƙarasa kusada wata ash ɗin mota, wani kyakyawan matashi ne ya fito daga cikin motar kana ganinsa kaga asalin ajebo irin takeaway ɗin nan cikin ladabi ya sunkuya ya faɗa " welcome uncle ya hanya " murmushi Daddy ya yi ya ce " lafiya lao Haidar ya kuke ?" murmushi ɗauke a fuskarsa ya ce " muna nan klao Alhamdulillah, sweet Mommy ina wuni ya hanya " dariya ta yi sannan ta ce " wato sai yanzu ka tuna dani babu komai nasan Ayaan shine mutumina " shafa kansa ya yi ya ce " i'm sorry sweet mommy ban ƙarawa " ok na yafema" thank you ya faɗa.Kallonsu Daddy ya yi ya ce " baku iya gaisuwa ba ?" Saima ce ta ce " ina wuni " cikin sakin fuska ya ce " lafiya lao Saima ya Nigeria da karatu " ganin ya yi mata magana friendly saɓanin yanda yakewa kowa magana yasa ta washe baki ta ce " wallahi lafiya lao Alhamdulillah, ya Azaad da Mommy'n sa ?" suna nan lao ya amsa mata, kallon Samha Daddy ya yi ganin batada niyyar gaidashi yasa ya ce " Samha banji kin gaida yayanki ba?" kwaɓe fuska ta yi ganin irin kallon da Daddy yake mata yasa ta ce " ina kwana " batareda ya kalleta ba ya ce " lafiya "sannan ya ce " Daddy mu tafi muna ɓata lokaci " ok Daddy ya ce sannan sukai gaba. Da Daddy da Mommy suka shiga mota ɗaya da Haidar da Saima suka shiga wata motar, Samha kuwa wata motar ta shiga daban dukda akwai ragowar waje acikin tasu motar Saima ce ta kalleta shikuwa yanda kasan baisan da ita awajenba haka ya nuna, ahaka suka tafi gidansu......
Duk wasu Family na kusa dana nesa sunzo dan tarbarsu, banda murna babu abinda family ɗin keyi, kakarsu wato Fatima wacce suke kirada Mama ta ce " kuje kuyi wanka ku huta sai kuzo ayi dinner ku kwanta tunda dare ya yi " ok sukace sannan aka kai kowa ɗakinsa, bayan sun shirya kowa da kowa yazauna a babban dinning area ɗin gidan sai hira ake banda Samha wacce tun zamanta batace komai ba abincinma da kyar take ci, lura da hakan yasa Yaseer wato mahaifin Haidar wanda ya kasance wane ga Daddy uwa ɗaya uba ɗaya ya kalli Samha ya ce " ƴar biyu meyasa kikai shiru ko har yanzu baki daina miskilanci ba? " kallonsa ta yi ta sunkuyar da kanta, girgiza kai Mama ta yi ta ce " Ke kam kina fama da wannan jarabar taki yarinya kamar wacce aljanu ke shafa kwata-kwata batason mutane anya kana mata addu'a kuwa Ahmad?" murmushi ya yi ya ce " wallahi Mama munayi saidai gyaran Allah lamarinta " to Allah ya sawwaƙe miki kuwa " turo baki ta yi ta tashi tabar wajen tanason zuwa wajensu amma wannan maganar ta tsana..
Wata kyakyawar macace ta shigo wacce aƙalla bazata wuce shekara 23-24 ɗinnan hannunta riƙeda wani kyakyawan yaro wanda baifi three years ba, da murmushi a fuskanta ta gaisheda su Daddy Saima ta ce " Aunty Zaheera yaushe rabo? Ina Azaad ɗin namu ?" murmushi Zaheera ta yi ta ce " wallahi kam kwana da yawa, kin ganshi" ta faɗa tana miƙa mata shi kallonsa Saima ta yi ta ce " wow kasan yaya wallahi kamarku ɗaya dashi " murmushi Haidar ya yi ya ce " ay har nagaji da wannan maganar to ba dole ɗa ya yi kamada ubansa ba " dariya kowa na ɗakin ya yi sannan suka cigaba da cin abincinsu..
Wajejen ƙarfe biyu na dare jikinta ya fara yimata ciwo tun tana daurewa harta fashe da kuka saboda tsananin azabar da takeji gashi babu kowa a kusada ita haka ta ƙaraci ciwonta har aka fara kiraye-kirayen sallar asuba sannan abun ya lafa mata hakan yasa da kyar ta samu tayi sallah sannan ta kwanta saboda matsanancin baccin da takeji..
Kowa da kowa na gidan ya hallara donyin breakfast Haidar ne ya fito hannunsa riƙe da Azaad za'a kaishi makara nta kallonsa Mama ta yi ta ce " yau naga jaraba kabar yaro ya huta acikin ƴan'uwansa kace sai ya tafi makaranta " murmushi ya yi ya ce " Mama kenan wallahi kin fiye rikici banda abinki ba yanzu zai dawo daga school ɗin nagadai ba yau su uncle ɗin zasu tafi ba " banza tai masa ta cigaba da cin abincinta ya ƙaraso cikin ladabi ya ce " Mami , uncle's, Mommy good morning " murmushi ɗauke a fuskarsu suka amsa masa Saima ta kalleshi ta ce " good morning yaya " murmushi ya yi mata ya ce " how was your night ?" fine ta faɗa, Daddy ne ya kalli Azaad ya ce " babanmu sai makaranta " dariya ɗan ƙaramin yaron ya yi ya ce " granny kacema Abu ya barni anan banason school ɗin please " murmushi Daddy ya yi kana ya ɗorashi akan cinyarshi ya ce " karka damu babu inda zaka muna nan tare anjima muje yawo " dariya ya yi yayiwa Daddy kiss a kumatu sannan ya ce " yawwa granny shiyasa nake sonka please idan zaka koma Naija zan biku " ok Daddy ya ce sannan ya fara bashi abinci, Zaheera ce ta fito tasha wata black ɗin abaya ta gaishesu sannan ta zauna dan yin breakfast. Uncle Yaseer ne ya ce " wai ina Samha ne bata fitoba?" cikin ɓacin rai Mommy ta ce " wallahi lamarin Samha ya isheni i don't know what wrong wiz her kullum cikin ignoring mutane take " Mama ce ta ce " gaskiya yarinyar nan ba lafiya ba " Saima ce ta tashi ta ce " bari naje na dubata " ok suka cemata sannan tai gaba ...
Tana shiga ɗakin ta sameta zaune gefen gado ta yi tagumi dan batasan ma tashigo ba, dafata ta yi ta ce " Samha what are you thinking ?" kallonta ta yi ta ce " mefa ?" kizo Daddy na kiranki, ok ta ce sannan ta tashi suka fito...
Sanye takeda riga da wando amma ba matstsuba ta tufke gashinta ya sakko har gadon bayanta sukayi sallama suka shigo, kallo kowa ya bita dashi banda Haidar wanda tun tana shigowa ya yi mata kallo ɗaya ƙarasowa ta yi ta ce " good morning everyone " "morning " suma suka amsa mata, wajen Daddy ta ƙarasa ta ce " Daddy gani " kallonta ya yi ganin yanda ta rame ya ce " Samha what wrong with you ?, meyasa bakya zama cikin ƴan'uwanki ?" ƙasa tayi da kanta bata bashi amsaba ganin haka yasa ya ce " zauna " zama ta yi tana kallonsa ya ɗebo abincin ya miƙa mata, babu musu ta buɗe bakinta ya fara feeding ɗinta domin Allah ya sani yana jin Samha sosai acikin zuciyarsa bayaso wani abun ya sameta kokaɗan saida kawai ya basar. Bayan sungama breakfast ɗinne uncle Yaseer ya ce kowa ya shirya zasu fita, kowa yagama fitowa banda ƴan mazan gidan wanda Haidar ne daman kawai yake ƙasar yakuma fita kallon kowa uncle ya yi sannan ya ce "ina Mamana ?" Mami ce ta ce " let me check her " sannan ta koma cikin gidan dan jin meya hanata fitowa. Kwance ta sameta ta ƙarasa ta yaye duvet ɗin jikinta ta ce " daughter meyasa baki shirya ba ?" da kyar ta ce " Mami i'm not feeling fine " taɓa jikinta ta yi ta ce " subhanal-lahi meyasa baki faɗaba har yayanki ya fita ? " bakinta na rawa ta ce " sai yanzu ya kamani " taimaka mata tayi ta tashi sannan ta ce " bari nakira Son ya kaiki asibiti " tafita takirashi bayan ta faɗa masa ya ce asa driver yakawota asibitin. Fitowa tayi da ita da mamaki uncle ya ce " lafiya ?" jawota tayi saboda yanda jikinta ke shivering ta ce " wallahi batajin daɗi amma nakira Aliyu yanzu driver zai kaita asibiti yana can " kallonta ya yi ya ce " sannu Mamana " kasa amsawa ta yi sai kanta data ɗaga masa Daddy ne ya ce " bari muje nakaita asibitin " murmushi Mami ta yi ta ce " no basai kajeba ai Aliyu na gurinta kawai mu mutafi " ok ya ce Saima ta ce da damuwa " Daddy muje na rakata asibitin " girgiza kai ya yi ya ce " no need mutafi kawai " badan ranta yasoba ta haƙura aka sakata amota suka tafi sannan suma suka kama hanya.....
A harabar asibitin wanda ya kasance mallakinsa ne sukayi parking ya tura nurses suka kawo masa ita kallonta yayi ganin yanda jikinta ya yi weak yasa ya ce rai ahaɗe kamar bai taɓa dariya ba " meyasa tun ɗazu bakice bakida lafiya ba ?" shuru ta yi masa kusan two yasa ya ce " keee! Badake nake magana ba" fashewa ta yi da kuka lokaci ɗaya jikinta ya hau rawa hakan yasa ya ƙaraso inda ta ke ya ce " rufemin baki kona kwaɗa miki mari waza kiyiwa shagwaɓa " turo baki tayi ta ce " ni wallahi babu ruwana dakai ka maidani gida kuma saina faɗawa Mami Allah " ta ƙasara maganar tana sakin wani sabon kukan " kallonta ya yi ganin yanda take kuka kamar wata Baby ya ce " who stop you kije ki faɗa mana kuma dama ni nakawo ki asibitin nan?" shuru tayi masa yatashi ya fita daga ɗakin not too long ya dawo hannunsa riƙeda injection ya ce " tashi tsaye " kallon abinda yake hannunsa ta yi ta fashe da kuka ta ce " dan Allah Abu Azaad kada kayimin allura wallahi bana so " tamke fuska ya yi dukda dariyar data bashi ya ce " ni sa'an wasanki ne ?, i'm play with you ?" girgiza masa kai tayi ya ce " ohyaa ɗauke hannunki ko ki daku " ganin da gaske bazata tsaya ta daɗin raiba yasa ya ce " shikenan na fasai miki tafi ki kwanta " gogen hawayenta ta yi ta ce " thank you " sannan ta huce gefensa har yanajin hucin jikinta saboda yadda temperature ɗinta tayi high. Bayan ta kwanta kusan two minutes sannan yazo gefenta ya zauna a hankali ya yi ƙasa da trouser ɗin jikinta batareda ta sani ba, cikin dabara ya saita allurar ajikinta batayi auneba taji ya tsira mata wata azabbabiyar ƙara ta saki tana kuka murmushi ya yi ganin ta tashi yasa ya rungumeta ya ce " sorry kinji ban ƙarawa kiyi bacci " kuka ta hauyi cikin two minutes kuma allurar ta fara aiki ajikinta nan da nan bacci ya ɗauketa, saida ya tabbatar baccin ya yi nisa ya ɗagata dan kwantar da ita yaji ta riƙeshi cikin magagin bacci ta ce " Abu kabarni anan " murmushi ya yi sannan ya komar da ita ƙirjinsa yana shafa kanta yana kallon cute face ɗinta shikaɗai ya saki wani smile har saida beauty point ɗinsa suka loma ya ce " rigimammiyata "
Comments, like nd share.
Written by:
*Nanameera*
Meera Love's you 💋💋💋💋💋[1/31, 10:21] Nanameera writer: https://chat.whatsapp.com/BRBJgmCve2uEO7OzFYz8Sj
💖💖TSAKANINMU💖💖
Story and written by:
*Nanameera*
.....Tauraruwar royal star✨
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_
*Alk'alaminmu 'yancinmu*
_Haɗaka palace_
Kungiyar masu posting ce ba marubuta ba.
Page Four.
Wajejen bayan sallar isha'i suka shigo gidan bayan ya yi parking ya kalleta rai ahaɗe ya ce " sauka " babu musu ta sauka ya ce " keee !!" juyowa ta yi ya kalleta ya ce " wane zai ɗaukar miki maganin ?" turo baki ta yi sannan ta ɗauki ledar maganin ta yi gaba..
Tana shiga shima ya yi sallama ya shigo kallonsu Mama ta yi ta ce " sai yanzu " zama ya yi ya ce " wallahi kuma nagaji " sannunku Mama ta faɗa, da gudu yazo ya rungumeshi ya ce " welcome Abbu " kiss ya mishi a kumatu ya ce " thank you Son " Mami ce tafito ta ce " au daughter zonan kici abinci " tashi ta yi ta ƙasara wajen Mamin ta zaune aƙasan kujera shafa kanta ta yi ta ce " ya jikin naki?" da sauki ta amsa mata daidai nan Saima ta fito daga kitchen da sauri tazo ta dafata ta