Showing 9001 words to 12000 words out of 29671 words
abun ya faru ne?" girgiza kai ta yi ta ce " kedai kice mini kin amince please sister " numfasawa ta yi ta ce "idan baifi ƙarfina ba zanyi amma idan yafi ƙarfina to saidai kiyi haƙuri " murmushi ta yi ta ce " nasan bazaifi ƙarfinki ba ma wallahi " girgiza kai ta yi ta ce " ohyaa ina jinki " gyara zama ta yi ta ce " ina kibawa Sapwan dama please karki ce A'a, nasan kinsani bashida wata matsala to please kibashi dama koda sau ɗayane arayuwa you will never regret kinji " shuru ta yi tana kallonta ta ɗora da faɗin " nasamo miki saurayi kin watsamin ƙasa a ido to dan Allah karki yimin haka yanzu kinji sister " ta ƙarashe maganar tana zubarda hawaye itama kukan take ta kama hannunta ta riƙe cikin nata ta ce "
Comments, like and share.
Written by
*Nanameera*
Meera Love's yhu🫶🏻🫶🏻🫶🏻🫶🏻🫶🏻🫶🏻
[1/31, 10:21] Nanameera writer: https://chat.whatsapp.com/BRBJgmCve2uEO7OzFYz8Sj
💖💖TSAKANINMU💖💖
Story and written by:
*Nanameera*
.....Tauraruwar royal star✨
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_
*Alk'alaminmu 'yancinmu*
_Haɗaka palace_
Kungiyar masu posting ce ba marubuta ba.
🅿️...SIX.
__________Cikin sanyin murya tafara magana " haba Saima kinsan haka kawai bazan ƙi abinda kike soba amma kin kasa fahimta ta kwata-kwata bazaki tsaya ki fahimce niba kina ganin kawai dan banaso ki auri wanda ranki yakeso ne yasa nake haka " gogen hawayen ta tayi ta ce " shikenan Samha bazan sake takura miki nace kiso waniba In sha Allah " tashi tayi zata tafi ta ce " shikenan yanzun me kikeso ayi ?" ki kula shi koda sau ɗayane ta bata amsa, murmushi ta yi ta ce " shikenan i will do so saboda ke " rungumeta tayi ta ce " thank you twinny " dariya tayi ta ce " no thanks kinji " zama tayi ta ce " yawwa bari nabaki card ɗinshi saiki kira shi kinji kinga yadda muna komawa sai asa rana musha biki " murmushi ta yi batace komai ba.....
Shigowar su kenan daga india Zaitoon ta ce " Daddy da gaske su Samha sunzo?" kallonta Mami ta yi ta ce " da ƙarya za'ay miki?" da gudu tayi hanyar ɗakin datasan suke zama idan sunzo, suna zaune tashigo da gudu ta rungumesu tana ihuu murmushi Samha ta yi ta ce " gaskiya Zaitoon Allah ya shiryeki kiga yanda kika shigo da gudu " zama ta yi tana dariya ta ce "wallahi i'm so happy shiyasa yaushe kuka zo?" Saima ce ta ce " kusan two weeks kenan jibi ma zamu koma " haɗe rai ta yi ta ce " chaɓ wallahi baku isaba banda rashin mutunci basai kuyimin wayaba ai saina tawo nabarsu Daddy amma gaskiya banji daɗiba " dariya Samha ta yi ta ce " come down sarkin faɗa ai munada yau, da gobe ko kuma kibimu Naija kiyi ko one month ne " dariya takeyi sosai kamar mahaukaciya saida tayi mai isarta sannan ta ce " waye zai barni naje Nigeria?, ai kozan ɗige wallahi nasan Daddy bazai bariba wannan " tashi Saima ta yi ta ce " bari naje gurin Mama sai kun fito" ok suka ce sannan tayi waje ....
Gyara zama ta yi ta ce " babbar yarinya matar manya " tsaki Samha tayi tana nunata da yatsa ta ce " kinga banaso Zaitoon wallahi zan miki rashin mutunci " murmushi ta yi ta ce " tuba nake babbar yarinya banƙarawa " tashi ta yi ta ce " daɗina dake bakida hankali wani time ɗin " miƙewa itama ta yi ta ce " naji ɗin " gaba tayi tafita daga ɗakin itama ta bita.
A parlour suka tadda Daddy, Uncle Yazeed, Uncle Ajeeb(Daddyn Zaitoon),Yaya Haidar, Mama, Zaheera, little Azaad,Ayaan, Asaad, Mami dakuma Mommy sai hira suke gwanin ban sha'awa.
Zama sukai Zaitoon ta ce " Mama wai ina naman da kikace kin ajiyemin rannan?" dafa ƙirji Mama ta yi ta ce " astgfirullah kaji ƴa ni zakiyiwa sharri ƙiri-ƙiri yaushe nace na ajiyemiki wani nama " kallonta Zaitoon ta yi ta ce " lahh Daddy dan Allah ba agabanka data kirani ta faɗaba?" murmushi Daddy ya yi ya ce " A'a ni ban ganiba yaushe?" dariya suka hau yimata hakan ya ƙona mata rai ta haɗe rai ta ce " gaskiya Mama ki daina ƙarya da girmanki gaskiya ki daina naga... Cikin faɗa Uncle Yaseer ya ce " kidanku Zaitoona uwartamu kike cewa tana miki ƙarya?" fashewa Mama tayi da kuka tana share hawaye ta ce " Allah yaso agabanku ne da saikuce naimata sharri haka duk suke zagina ɗaya bayan ɗaya itakuwa waccen mai kamada zabiyan ko kulani batayi gaba takeyi dani saboda ina faɗa mata gaskiya ta faɗa tana nuna Samha " murmushi Ayaan ya yi ya ce " kai Mama Samhan ce take gaba dake ?" harararsa ta yi ta ce " to munafiki kaji nasako baki dakai?, sai kabari idan na kulaka ko na kula ubanka sai kayi magana " dariya suke mata little Azaad ya ce "Mama kedaina yiwa mutane rigima kullum sai nasa teacher ya zaneki " kallonsa take tunda ya fara maganar tana shan yogurt saida tashanye na bakinta sannan ta ce " to kai kuma waya sako dakai ?, yaro sai kinibibin tsiya wallahi daga kai har iyayenka kufita daga harkata " dariya ya kyalkyale chan kuma ta kalli su Daddy ta ce " kunaji na" fuskar su asake suka ce " munaji Mama " ajiye apple ɗin hannunta ta yi sannan ta ce " kunsandai mahaifinku ya daɗe da rasuwa ya barni daku, kuma cikin ikon Allah gashi duk kun tara zuri'a yanzu abu ɗayane ya rage shine naga kun aurar da waɗannan yaran dan kaf ɗinsu sun isa aure " murmushi Uncle Yaseer ya yi ya ce " In sha Allah Mama nan bada daɗewa ba zasuyi aure dukansu " murmushi ta yi ta ce " yawwa Allah yayi muku albarka " Ameen suka amsa dukansu....
Cikin dare tasake farkawa da zazzaɓi mai zafi ko ɗan yatsanta ta kasa ɗagawa tazama kamar gawa sai rawar sanyi take dukda blanket ɗin data rufa sai kusan ƙarfe huɗu sanna sannan ta iya miƙewa daga kwance tashiga banɗaki tayi wanka ta ɗauro alwala tafara sallolin nafila kafin lokacin asuba ya yi. Bayan ta idar da sallah tahau shirya kayanta saboda yau ne zasu koma Naija saida ta gama haɗa komai nata lokacin gari ya fara wayewa sannan tafito dan taya su aikin abubuwan breakfast...
Misalin ƙarfe sha biyu na rana suka isa airport ɗin kasancewar akwai kusan mintuna goma kafin jirgin ya tashi hakan yasa suka zauna suna bankwana da kowa na family ɗin Mama na kuka ta ce " shiyasa nake cewa maka Ahmadu ka dawo kusada mu cikin danginka wallahi banason rabuwa da jikokina " rungumeta sukai suna kuka suka ce " zamuyi missing naki granny " rungumesu itama tayi sai rera kukansu suke itama Zaitoon tabi bayansu sunata kuka, Daddy ne ya ƙaraso yana goge kwallar idanunsa ya ce " mene haka kukeyi?, sai kace zamu mutu, In sha Allah nan bada jimawa ba zamu sake dawowa dan Allah Mama ki daina kukan nan" sakinta sukai ta goge hawayenta ya ce " yawwa ko kefa " Azaad ne ya kalli Daddy ya ce " Daddy kamin alƙawarin zaka tafi dani Naija idan zaku koma please zan biku?" murmushi Daddy yayi ya ce " ok sweetheart ka tambayi Abbunka?" ɗaga masa kai yayi ya ce " ya ce naje ai zaka sani makaranta ko?" dariya Daddy yayi ya ce "me kyau ma kuwa " wajen Samha ya je ya ce " aunty Samha ai zaki zama Mommy na ko?" ɗaukansa tayi ta ce" In sha Allah my son kaɗaukeni kamar Mommynka" dariya ya yi ya ce " thank you so much" suna cikin hira aka sanar jirgi zai tashi hakan yasa suka tafi suna ɗagawa juna hannu cikeda kewa da begen juna haka har jirgin su ya lula sararin samaniya sukuma suka koma gida.
```Wannan kenan```
Comments, like and share.
Written by
*Nanameera*
Meera Love's yhu 🫶🏻🫶🏻🫶🏻🫶🏻🫶🏻🫶🏻[1/31, 10:21] Nanameera writer: https://chat.whatsapp.com/BRBJgmCve2uEO7OzFYz8Sj
💖💖TSAKANINMU💖💖
Story and written by:
*Nanameera*
.....Tauraruwar royal star✨
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_
*Alk'alaminmu 'yancinmu*
_Haɗaka palace_
Kungiyar masu posting ce ba marubuta ba.
🅿️.....0️⃣7️⃣..
*Nigeria*
___________Bayan Sallar isha'i suna zaune Azaad ya yi shuru, murmushi Daddy yayi ya ce" Babana lafiya?" Kwaɓe fuska ya yi ya ce " granny ina Aunty Samha?" murmushi sukayi yaji ta ce " gani nan my son naje dafama indomie ne " cikeda murna ya ce " yawwa Aunty amma tare zamu ci?" zaunar dashi tayi akan cinyarta ta ce " Eh mana yanzu buɗe bakinka" buɗe bakinsa ya yi tafara bashi yana ci yana bata har suka gamaci dariya Saima ta yi ta ce " ok Auntynka kawai kasani ko?" murmushi ya yi ya ce " no kema nasanki kawai nafi sonta" tafa hannu ta yi ta ce " lallaima yaron nan wato kafi sonta ?" turo baki yayi ya ce " Aunty na zaki kunnamin game a system ɗinki ?" riƙe hannunsa ta yi ta ce "Eh mana zo muje " tafiya sukayi Mommy ta ce " oh su Samha anyi ɗa" dariya Daddy ya yi ya ce " naga yanda zatayi dashi idan zata tafi makaranta itada bata shiryawa da wuri " tashi Saima ta yi ta ce " wallahi kam gobe akwai kallo, Daddy, Mommy good night " ok good night suka amsa mata....
Tunda ta tashi take cukwi-cukwin makaranta bayan ta shirya ta kalleshi ta ce " yawwa son tashi mutafi Daddy zai kaika makaranta" toh ya ce sannan ta kama hannunsa suka fito....
Bayan sun gaida Daddy Azaad ya ce " granny ina Mommy?" murmushi Daddy ya yi ya ce " Mommy nada patient tafita tun asuba " riƙe hannun Daddy ya yi ya ce " granny nima Doctor zan zama irin Abbuna da Mommy" jan kumatunsa ya yi ya ce " toh Allah yabada sa'a sweetheart " Saima ce tafito ta ce " Daddy muntafi " ok sai kun dawo ya amsa musu sannan ya kama hannun Azaad sukai waje shima "....
Tunda suka shigo makarantar taji gabanta ya faɗi kai tsaye ta shiga cikin ajinsu cikin rashin sa'a tasamu Sir Sapwan yana musu lectures yana kallonta tayi maza ta ɗauke kanta ta tafi ta zauna kowa yayi mamakin dabai koreta ba kamar yanda ya saba. Bayan sun fito daga lecture suna zaune da Aysha wayarta ta yi ringing ɗagawa ta yi takai kunne cikin cool voice ɗinshi ya ce "please Samha idan babu takura idan antashi ki tsaya a parking lot "ok ta ce sannan ta kashe wayar, kallonta Aysha tayi ta ce " lafiya kuwa Samha?" murmushi tayi ta ce " lafiya lao Aysha kina bani labari " girgiza kai tayi sannan ta cigaba da bata labarin...
Tunda ta hango Saima suna hira da Yazeed taji ranta ya gama ɓaci har suka ƙaraso gabanta, murmushi ɗauke afuskarsa ya ce " A'a Samha ya kike?, ya karatu " wani banzan kallo tayi masa sannan tayi gaba abinta. Sosai ran Saima ya ɓaci dakyar ta kalleshi ta ce " Dan Allah kayi haƙuri beb, wallahi halin Samha sai ita narasa mene ne matsalarta " murmushi ya yi ya ce" haba karki damu ai nasan halinta tunba yanzu ba" da mamaki ta ce " A ina kasan halin nata?" dariya ya yi ya ce" a bakinki mana " ok tace sannan sukai gaba......
Tsaye ta sameshi yana danna waya tayi sallama da murmushi ya amsa sannan ya ce " please mushiga mota mana" shuru tayi nawasu sakanni sannan ta ce "ok " buɗe mata yayi sannan ya zagaya ya zauna shima, kallonta ya yi ya ce " Samha " ɗago kai tayi ta ce " na'am " cikin nutsuwa ya ce " Samha nasan kin sani, amma sunana Sapwan Muhd Kabeer ni haifaffen garin Kano ne amma mahaifiyata ƴar ƙasar Ethopia ce wato ƙasar kakanninku, ina rayuwa within Nigeria and Ethopia har nagama Jami'a kuma nafara lecturing kasan cewar shine muradina. Tun ranar dana fara ganin ki naji inasonki amma kuma ganin yanda kike mu'amula da mutane yasa nakasa furta miki har kike tunanin na tsanekine, banzo da maganar wasaba idan har kin amince dani to banaso mu wuce five months bamuyi aureba ina fatan zakiban haɗin kai " murmushi ta yi ta ce " shikenan babu matsala Allah yasa hakan ne mafi alkhairi " kallonta ya yi ya ce "kin amince Samha?" ɗaga masa kai tayi ya ce " amma ban taɓa zatoba nagode sosai Samha In sha Allah zuwa next week zan turo iyayena" dariya tayi sannan ta ce " toooh! Kuma daga haɗuwa sai turo iyaye bamu sababa bamuyi komai ba?" dariya shima ya yi ya ce " wallahi duk namanta saboda zumuɗi, Allah ya nunamin ranar dazan ganki matsayin matata " Ameen ta amsa tana rufe fuska ganin ya kunna motar yasa ta ce" ina zakaje kuma?" yana reverse ya ce " gida zan kaiki kuma ko kince nabarshi bazan barshi ba" dariya ta yi ta ce " Allah sarki to ay ni ba gida zaniba zanje ɗauko Azaad a makaranta" ok sai mu biya mu ɗaukoshi ya faɗa......
Fitowar su kenan daga Jifatu store Azaad sai murna yake suka shiga mota dan komawa gida, bayan yayi parking ya kalleta ya ce " wai a ina kika samo balaraben yaro?" murmushi tayi ta ce " wallahi ɗan yayana ne muka tawo dashi daga Ethopia " yana kallon Azaad ya ce " Masha Allah ya sunanka?" cikin sakin fuska Azaad ya ce" my name is Azaad Aliyu Yaseer " dariya ya yi ya ce " woww masha Allah sannunka " kallon Samha ya yi ya ce " to madam sai gobe?" Eh sai gobe ta bashi amsa sauka sukayi daga motar sannan yabawa Azaad kayanshi da yayi masa shopping sukai sallama ya tafi su kuma suka shiga gida.......
Har dare suna ɗaki suna bacci bayan sunci abinci saida su Daddy suka dawo sannan suka fito Azaad ya ce " Mommy sannu da zuwa" murmushi tayi masa tana ɗaukansa ta ce " yawwa yarona ya kake?, ya zaman Nigeria ?" yana cire ɗankwalin kanta ya ce " ina nan klao gurin Aunty Samha kuma tabani chocolates dayawa masu daɗi " dariya Daddy ya yi ya ce "wato dai gurin Aunty Samha kazo ko?" Eh mana tunda tana bani chocolate kuma ta kunnamin game nayi a system ɗinta " kama hannunsa Mommy tayi ta ce " muje muyi dinner " ta ajiyeshi kan kujera sannan ta ce " zauna bari nashiga ciki na fito " ok yace mata sannan yacigaba da wasansa.......
Yau kusan ƙarfe takwas ta fita saboda lecture safece da'ita ita kuma Samha sai 12pm har kowa ya fita ita kuma tana bacci bayan ta shirya Azaad kiran wayarsa ne ya farkar da'ita bayan ta ɗaga jin muryarta ya ce " badai bacci kikeba?" tashi tayi zaune sannan ta ce " wallahi kam yau banida lecture safe shiyasa" dariya ya yi ya ce " ai kuwa kiyi sauri ki shirya dan yanzu sha ɗaya ta kusa, zan kiraki anjima " ok ta ce sannan ta kashe wayar ta hau shiryawa...
Zaune suke a restaurant amma kwata-kwata takasa cin abincin ganin yanayinta yasa Aleeya ta ce " wai Saima me akai miki naga ranki a ɓace?" tsaki ta yi ta ce " wallahi sai naiwa Samha rashin mutunci dan wallahi abinda takemin ya isheni akan Yazeed saidai mu yanke zumuncin dake *TSAKANINMU* dan saboda ita bazan rabuda Yazeed ba idanma baƙin ciki takemin saidai ta mutu amma wallahi saina aureshi " dariya Aleeya ta yi ta ce " Ai sanda nake faɗa miki baki saurareniba kina ganin kamar inaso ne na haɗaki da ƴar uwarki wallahi ko kaffara bazan miki Samha baƙin ciki take miki bataso taga kin auri wanda zaki huta shine kawai damuwarta " shuru ta yi nawasu mintuna sannan ta ce " ai kuwa taci ƙarya ta kwana da yunwa kuma bari nakoma gidan wallahi yau saidai ayita ta ƙare dan nagaji akan Yazeed babu abinda bazan aikata ba" wai ke har saikin bari ankoma gida?, ay yanzu ya kamata kije kisameta kiyi mata tijara agaban kowa wallahi bazata ƙaraba " Allah ko? Saima ta tambaya, tsaki ta yi ta ce " to zauna ni nafi zarginma so take ita ta auri Yazeed ɗin shiyasa take waɗannan abubuwan gwanda kije yanzu ki taka mata birki " tashi ta yi ta ce " zo mutafi wallahi yau saidai na yanke alaƙar dake *TSAKANINMU* dan saina sauke mata buhun rashin mutunci idan har tana tunanin zata auri Yazeed ne " kama hannunta ta yi sukai waje......
Comments, like and share.
Written by
*Nanameera*
```Meera Love's yhu```🫶🏻🫶🏻🫶🏻🫶🏻🫶🏻🫶🏻🫶🏻
[1/31, 10:21] Nanameera writer: https://chat.whatsapp.com/BRBJgmCve2uEO7OzFYz8Sj
💖💖TSAKANINMU💖💖
Story and written by:
*Nanameera*
.....Tauraruwar royal star✨
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_
*Alk'alaminmu 'yancinmu*
_Haɗaka palace_
Kungiyar masu posting ce ba marubuta ba.
🅿️......0️⃣8️⃣...
____________Ahanya suka haɗu da Yazeed wanda daman wajenta zashi ganin yanayinta yasa ya ce " baby what's wrong?" kallonsa ta yi ta ce " please muje ka rakani " ok ya ce sannan sukayi gaba.....
Tsaye take itada Sir Sapwan suna taɓa hira Saima ta ƙaraso da tawagarta da murmushi Sapwan ya ce " A'a ƴar biyu ce anan ko kinzo sada zumunci ne?" wani kallo ta yi masa ta ce " A'a nazo yanke zumunci ne" bai fahimci inda ta dosaba ta kalli Samha ta ce " inason magana dake idan da hali" da mamaki ta ce " idan maganar sirrice kibari sai mun koma gida mana" zatayi magana Aleeya ta jata gefe ta raɗa mata wani abu sai kuma suka dawo tana huci ta ce " daman warning nakeso nayi miki saboda na fuskanci baƙin ciki kike yimin da kuma hassada saboda na sami mijin