Showing 21001 words to 24000 words out of 29671 words
a hankali dariya Saima ta hau yi, saida tayi mai isarta sannan ta ce".
```Ayi haƙuri dani lover's yau banida caji ayi manage wannan plz```
_Written by_
*Nanameera*
```love's yhu oll```
🫶🏻🫶🏻🫶🏻🫶🏻
[2/8, 00:27] Nanameera writer: https://chat.whatsapp.com/BRBJgmCve2uEO7OzFYz8Sj
🌹*TSAKANINMU*🌹
*Story and written by*
*
*Nanameera*
_Tauraruwar royal star_
🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_
*Alk'alaminmu 'yancinmu*
```Haɗaka palace```
_Page19&20_
________Ta ce " gaskiya Abu Azaad kana shagwaɓaata da yawa jifa wani rashin mutunci ana bata tana wani yatsine fuska" harararta Samha ta yi ta ce" kedai ki daina munafurci wlh banza kawai" ɗaga kafaɗa ta yi ta ce" ina ruwana" tashi ya yi ya ce" nikam saida safe dan gobe inada abubuwa dayawa" murmushi Saima ta yi ta ce" amma ai baka kusa tafiya ba ko?" ya ce" no nakusa In sha Allah next week nakeso na koma" buɗe baki tayi ta ce" haba Abu Azaad gaskiya kabari sai nanda two weeks sannan" murmushi ya yi ya ce" su kuma patient ɗina nayi yaya dasu?" turo baki tayi ta ce" sai suje wani asibitin " dariya ya yi ya ce"kin fiye rigima saida safe" ok ta ce sannan ya shige ɗakinsa.......
Yana shiga ta kalli Samha ta ce" twinny kinsan me?" girgiza kai ta yi ta ce"wlh mutumin nan fa classy ne na rantse ga kyau ga kuɗi abun ba'a cewa komai " tsaki Samha ta yi ta ce" ke bakida hankali ko?, ki dinga da kinga mutum kice classy ne zakiga classy ganin idonki wlh" ta ce "tab wlh saina faɗa kinsan ni inaso naga namiji haɗadɗe sosai yafi birgeni wlh" tashi ta yi ta ce" ai kuwa kina tareda wahala" daga hakka ta shige cikin ɗakin da ta duba me su Azaad keyi.......
Washe gari suka shirya suka tafi makaranta as usual amma saida ta fara biyawa gidansu Zahra ta kaimata Amrah sannan ta wuce ta kai little Azaad makaranta.....
Tunda taje makaranta ta zauna tayi shuru ba kamar ko yausheba da take cikin nishaɗi da kula mutane, bayan sun fito daga lecture ne Aleeya ta ce" wai yau Saima.lafiyarki klao?" harararta ta yi ta ce" bansani ba, please Aleeya ki rabu dani saboda rai na aɓace yake karki tunzurani please ki rabu dani" da mamaki Aleeya ta ce"Saima yau ni kike na rabu dake?, ni Aleeya!?"afusace ta ce " and so what?, ko ana dolene nace ki rabu dani" bata tsaya saurarenta ba tayi gaba ta barta agurin. Kai tsaya department ɗin su Samha ta tafi, tana zuwa kuwa tayi sa'a suna zaune itada Aysha suna karatu, zama tayi gefenta ta yi shuru hakan yasa Samha ta ce" what's wrong?" kallonta ta yi ta ce"nothing' kawai dai nazo wajenki ne" sosai Samha tayi mamaki dan rabonda Saima.tazo wajenta haka kawai har ta manta amma sai ta basar ta cigaba da karatun ta........
Bayan sun tashi daga makaranta sun fito taga Saima tsaye kusada mota ta ƙarasa wajnta dan tayi mamaki da ta ganta a tsaye, tana zuwa ta ce" Saima lafiya baki tafi gidaba?" murmushi ta yi ta ce" i'm waiting For you shiyasa" sosai taji daɗi aranta ta ce" ok zo mutafi" toh ta .ce sannan suka jera suka tafi abin sha'awa kamar da.....
Suna shigowa gida Azaad ya fito daga mota da gudu ya yi cikin gidan saboda motar Abbunsa daya gani........
Suna shiga suka tararda Daddy, Mommy, Abu Azaad sai kuma Azaad da mamaki Samha ta ce" lafiya dai?" kallonsu Daddy ya yi ya ce" Wlh Zaheera ce batajin daɗi shine aka faɗa masa zai tafi" Saima ce ta ce" inna-lil lahi wa inna-ilaihi raji'un yaushe?" Mommy ta ce"wai kusan one week tana ciwon a tsaitsaye to yanzu kuma shine abin yayi worth" Samha ta ce" Allah sarki Allah ya bata lafiya" sai a sannan ya ce" Ameen" ta kalli Azaad ta ce" Azaad zaka bi Abbunka ne?" da sauri ya ɗaga mata kai ya ce". Aunty Samha zani naga Ummina" batasoba amma bazata hanashi zuwa ganin mahaifiyarsaba ta ce" tom zona sanja maka.kaya" girgiza kai ya yi ya ce" no ni kibarni haka" ta fuskanci yaron ya tsorata so yake yaga babarshi yasa ta rabu dashi kawai Daddy ya ce" yanzu zaka tafi?" ya ce" Eh nasa an yimin booking ɗɗin jirgi to wank kawai zanyi na tafi, Azaad muje kayi wanka kaji sai mutafi" bai masa musu ba ya kama hannunsa suka shiga ɗakinsa Mommy ta ce" Samha ki ɗauko masa kaya kafin yayi masa wanka" to ta ce sannan suka shiga ciki jiki a mace.......
Tana shiga ɗakin ta tararda ya gama shiryawa yana shafawa Azaad mai, ahankali ta ƙaraso ta zauna gefen gadon tana shaƙar daddaɗan ƙamshin turarensa wanda duk inda ya zauna sai turaren ya riƙe saida ya gama shafa masa sannan ta jawoshi ta saka masa kayan tana gama saka masa Aliyu ya ce" jeka yiwa su Daddy bye bye" da gudu ya fita ta bishi da kallo. Sai da ya fita sannan ya zauna gefenta yana kallonta ganin yanda yake kallonta yasa ta sunkuyar da kanta tana goge hawayen fuskarta, tattausan hannunsa yasa ya ɗago fuskarta kamar wanda ya zuga ta ta fashe da kuka, rungumeta ya yi yana patting bayanta kusan 5mins suna haka kafin ta fara sauke ajiyar zuciya saida yaga hankalinta ya nutsu sannan ya ce" mene na kukan?, ai zaki biyo mu ko?" sake rushewa tayi da kukan ta ce" Abu Azaad plx karku tafi kaji" tattausan murmushi ya yi yana goge mata hawayen ya ce" kinaso ki bimu?" ɗaga masa kai ta yi ya yi murmushi ya ce" shikenan ki tambayi Daddy" kwaɓe fuska ta yi ta ce"he won't let me" ya ce" to kinga ni yanzu dole na koma saboda bazai yiwu ba ace Zaheera na asibiti ni kuma ina nan, amma ki bari In sha Allah soon zan dawo" haɗe rai ta yi tana tureshi ta ce" ni kadai naimin maganarta, kuma kuyi tafiyarku ko kadawoma bazan bikaba" dariya ya yi yana jawota ya ce" shikenan sorry kinji yanzu kizo muje ki rakani" tashi tayi ta fita sannan shima ya fito.....
Zaune suka tadda su kowa ya shirya hakan yasa sukai waje kai tsaye kuma filin jirgin malam Aminu kano suka nufa..........
Wajen 5mins a fara alerting tashin jirgi suka miƙe little Azaad yana kallon Samha ya ce" Aunty Samha i'm going to miss you" batasan sanda ta fashe da kukaba ta rungumeshi shima yana kuka da kyar aka samu sukai shuru sannan suka tafi yana ɗago mata hannu nikam nace Allah ya tsare hanya ya kuma kai ku lafiya Abu Azaad nd little Azaad.....
Tunda suka dawo sukaji gidan so lonely sabo tirken wasa haka suka ƙarasa ranar gidan babu wani daɗi........
*Ethopia*
Tunda yaje asibitin jikinsa ya yi sanyi domin bai ɗauka jikin nata yake hakaba shikuwa Azaad sai ɗauke shi su Ayaan sukayi saboda yanda yake kuka shi sai Umminsa ta tashi Hajia Mamama tayi shuru babu wannan kara gaɗin, da safe suna zaune a parlourn yashigo ya zauna suka gaisa sannan Mami ta ce"ya jikin nata?" ya ce" da sauƙi alhamdulillah" ta ce "Allah ya ƙara sauƙi" ya ce" Ameen", Azaad ne ya taso daga wajen Zaitoon ya dawo gabanshi ya tsaya ya ce" Abbu yaushe Ummi zata dawo?" cikin tausayin ɗan ƙaramin yaron ya ɗorashi kan cinyarsa ya ce" in sha Allah ta kusa dawowa kaji Azaad"kwanciya ya yi aƙirjinsa ya yi shuru kusan wasu mintuna bacci ya ɗaukeshi. Mama ta kalleshi tayi tagumi ta ce" Allah sarki Allah ya bawa wannan yarinya lafiya ji yanda ɗanta ya zama kamar maraya" murmushin ƙarfin hali Aliyu ya yi ya ce" Ameen Mama"..........
Da daddare bayan an dubata suna zaune kusada gadon shida Azaad banda computer da take ƙara bazakace tanada rai ba deep down yake mamakin abunda ya haɗa Zaheera da cancer, amma idan ya tuna babu irin cutar da Allah baya ɗorawa bawansa a matsayin jarraba kuma anyi tafi haka sai yaji daɗi aransa............
~Nigeria~
Kusan two weeks kenan da tafiyar su Azaad inda kullum Saima ta ke kasancewa a ɗaki saɓanin da da Samha ce me wannan ɗabi'ar yauma kamar kullum tana kwance a ɗakinta tayi shuru tana tunani kamar wacce aka tsikara ta tashi dukda yanda take jin babu daɗi jikinta ta fito ta shiga ɗakin Samha. Zaune ta tadda ita tana chatting a wayarta ta zauna gefenta Samha ta kalleta ganin yanda ta rame ta ce" wai Saima har yanzu jikin ne?" shuru ta mata tana kallonta Samha ta ce" i'm talking to you Saima" hawaye ne ya fara zirarowa daga idanunta ta riƙe hannun Samha cikin sanyin murya ta ce" twinny dan Allah na tambayeki wani abu?" da mamaki ta ce" why not?" ajiyar zuciya ta sauke ta ce" please twinny ki faɗamin meyasa bakiso na auri Yazeed kuma mene ne haɗinki dashi please Samha karki ce A'a" ji tayi gabanta yayi wani irin faɗuwa ta kalli biyunin tata ganin yanda take kuka yasa ta ce" zan baki labarin yanda nasan Yazeed da kuma abunda yasa banaso ki aureshi wanda hakan ya kasance alƙawarine amma ayau zan karya shi" sosai tabada attension ɗinta ta ce" ina jinki" ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce"
*Two years ago*
```Written by```
*Nanameera*
_Tauraruwar royal star ce✍️_
~Love's yhu oll~
🥰🥰🥰🥰🥰🥰
[2/9, 23:18] Nanameera writer: 🌹*TSAKANINMU*🌹
*Story and written by*
*
*Nanameera*
_Tauraruwar royal star_
🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_
*Alk'alaminmu 'yancinmu*
_Haɗaka palace_
_Page 21&22_
__________Fitowarsu kenan daga class a lokacin an fito break su hudu abunsu Fatima Mukhtar(Zahra), Zainab Sufyan(Zee)Lubna Kabir sai Fateema Ahmad Azaad(Samha). Tafiya suke suna hira kana ganinsu kasan ƴaƴan manyane dan duk a cikinsu babu ƴar me ƙaramin ƙarfi, suna shiga hostel ɗinsu kowacce ta zauna dan sosai suka gaji. Zee ce ta ɗauko goran ruwa ta buɗe ta sha sannan ta ce" gaskiya yau nagaji barin wancan malamin physics ɗin ɗan jaraba bazan taɓa barinka ka huta ba" dariya Lubna ta yi ta ce" ki ka gaji ko nagaji?, ai wlh idan na koma gida zan faɗawa Daddy a SS two zanyi graduation na huta dan banajin zan kai next year a makarantarnan" harararta Zahra ta yi ta ce "amma ke bakida hankali, banda hauka mene ne tazarar ss two ɗin da three naga idan kinyi haƙuri ƙammar yau ne zamuyi graduation ɗin kowa ya kama gabansa kodai Anas ne yake zugaki kiyi sauri ki gama kuyi aure?" dariya suka hau yi dukkansu banda Lubna wacce ta haɗe rai tana aika mata da wani mugun kallo ta ce" A'a uwar Anas ne ya sani agaba, na rantse Zahra idan kika cigaba da yimin haka zan yi miki rashin mutunci banza kawai ƴar iska budurwar malami" waro ido Zahra ta yi ta ce" kan ubancan! ni zaki zaga haka?, mikewa tayi tana riƙe ƙugu ta ce" to ai bani kaɗai nake kula malamiba kuma naga ai ba haramun na aikata ba" tsaki Samha ta yi tana kamo hannun Zahra ta zaunar ta ce" wai meyasa kuke yiwa mutane irin wannan halinne?, babu yanda za'ayi ku zauna bakuyi faɗaba, yanzu idan tayi candy wannan shekarar bafa zaku sake haɗuwa ba sai ikon Allah amma kullum cikin faɗa kuke kanar wani na ganin hanjin wani" murmushi Zee ta yi ta ce" gwara dai ki faɗa musu Samha wannan ai yawa ne wlh" tashi tayi ta ce" dan Allah kuzo muje mu ci abinci" tashi sukai suka fito dan zuwa inda suke cin abinci kamar yanda suka saba......
Sanye yake da wata dakkarkiyar shadda ash colour ya sanya hula da takalmi baƙi ya yi kyau sosai abunsa, zuba masa ido tayi sai kuma ta taɓo Zahra ta ce" Zahra!!Zahra kinga wani kyakkyawan guy" murmushi Zahra ta yi ta ce" wlh kuwa tubarkalla masha Allah yayi kyau" juyowa ta yi tana kallonsu jin suna magana ƙasa-ƙasa da mamaki ta ce" A'a lafiyarku klao?" dariya Zahra tayi ta na nuna mata hanyar dayake tafiya da ido ta ce"wlh wancan guy ɗin muke kallo" tsaki ta yi ta girgiza kai ta ce" Allah ya yaye muku wlh idan kuna haka bazaku samu kalar mazan da kuke soba saidai kullum kuyita gane-gane" Lubna ta ce"wlh ki gani akanki" suka cigaba da tafiya........
Yana zuwa gabansu suka durƙusa da girmamawa suka ce" good morning sir?" banda Samha wacce tayi kamar bata gansaba, babu yabo babu fallasa ya ce"morning how are you?" suka ce"fine" "good" kallon Samha ya yi sai kuma ya yi gaba bai ce komai ba....
Da mamaki Zahra ta ce" wai Samha lafiyarki klao kina ganin Sir Yazeed kuma kinsan abokin director'n makarantar nan ne amma baki gaisheba" harararta ta yi ta ce"to dayake abokin director ubana ne dazan gaishesa?, ni ko ƴan uwana sai naga dama nake gaishesu bare kuma wani can banyi niyya ba" tafa hannu Zee ta yi ta ce" correct, tawajena wlh shiyasa nake sonki nima kawai sabida ya burge ni yasa na gaishe sa wlh" dariya tayi Zahra ta ce" Ashe bamu kaɗai ya burgeba Lubna, itama Samhan da ta ciki na cikine" taɓe baki ta yi ta ce" wlh kuwa ƙarya kike kawai ni banga abun burgewa ajikinsa ba saboda nasaba ganin waɗanda suka nunkashi kyau da aji da kuɗi a family ɗinmu" haɗa baki sukai suka ce"Awwwnn " Lubna ta ce"please Samha dawa zaki haɗani wlh burina na auri handsome guy" dariya Samha ta yi ta ce" ai duk sunfi ƙarfinki bamu aurawa ƴan nigeria" riƙe haɓa ta yi ta ce"eyyeee harda faɗar magana?,to Allah ya baki haƙuri muma zamu sami daidai damu ƴan nigeria" ɗaga kafaɗa ta yi ta ce" da yafi sauƙi" daga haka babu wacce ta sake magana har suka isa.........
Bayan sun gaisa da abokin nasa Kabeer mai Fata wanda shine director'n makarantar ya kallesa bayan ya ajiye ruwan hannunsa ya ce" abokina wata nagani a school ɗin nan kuma wlh ina sonta yarinyar ta haɗu" dariya Kabeer ya yi ya ce" kai kam wlh bakada dama, a ina ka ganta?" ya ce" wlh ina shigowa nagansu da wasu ƴan team ɗinta zaka ganta wata fara kamar dai half-caste ce " shuru ya yi can kuma ya ce" okeeee na ganeta Fateema right?" ya ce" i don't know her name but daga gani ƴar SS two ce saboda uniform ɗin ƴan SS two ne ajikinsu" ya ce" exactly Samha ce amma bari nasa akirawota ka ganta" murmushi yayi ya ce"thanks friend" ya kashe masa ido ya ce" never mind" daga haka ya hau kiran numbern messenger dan ya kirawota.......
Suna komawa aji bayan an koma break headgirl tazo ajin suna zaune suna hira ta ce" who is Fateema Ahmad?" tashi Samha ta yi ta ce" I" headgirl ɗin ta ce" ok kije office ɗin director ana kiranki" ta juya ta fita, batayi mamaki ba dan azatonta Daddynta ne yazo ta kama hanyar office ɗin director n.......
Da sallama tashiga office ɗin, ya amsa mata ransa asake ya ce" have a sit mana Fateema" ok ta ce sannan taje tasamu kujera ta zauna batareda ta kalli Yazeed ba wanda tun shigowarta yake kallonta. Kallonta Kabeer ya yi da murmushi a fuskarsa ya ce" Fateema kinsan meyasa na kiraki?" ta girgiza kai a hankali ya ce" toh daman ba wani abu bane friend ɗina ne ya ganki ya ce yanaso shine nasaka a kiraki saboda na sanar dake halin da ake ciki, idan yaso sai kije kiyi shawara zan nemeki" tunda ya fara maganar take kallonsa with mouth agape har ya idar sannan ta masa wani kallo ta ce" yanzu Sir dakai za'a haɗa baki wai wani ya kula ɗalibar makarantarka, wanda kamata ya yi ace kaine zaka hana faruwar hakan?". murmushi ya yi ya ce" Samha kenan ai wannan da kika sani amma yanzu zamani ya sauya kuma ni nasan halin abokina bazai miki wasaba sabida haka kamar yanda na faɗa kije kiyi shawara in sha Allah zuwa gobe zan nemeki" zatayi magana ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu ya ce" tashi kije" babu musu ta miƙe ta yi hanyar waje tana tafe tana waiwayen su cikeda mamaki.......
Tana fitowa ta koma aji amma har suka tashi bata daina tunanin irin maganganun da ya faɗa mata ba kuma ta rasa wazata faɗawa dan tasan duk ba hankali suka cika ba. Da daddare bayan sun gama night prep sun kwanta kasancewar gadonta na kallon na Zahra yasa suke taɓa hira kafin suyi bacci, ganin tayi shuru yasa Zahra ta ce" balarabiya lafiya?" ajiyar zuciya ta sauke ta ce" wlh wani abune yake damuna tun ɗazu" waro idanu ta yi ta ce" meya faru?" a nutse ta fara bata labarin duk abunda ya faru tun daga farko har ƙarshe............
Shuru Zahra ta yi na wasu mintuna sai kuma ta ce" shikenan kice masa kin amince saboda ina ganin hakane kawai mafita saboda idan baki faɗaba bazai rabu dakeba amma idan kince kin yarda zaki iya dinga ƙin kulashi a haka har ya haƙura, a shawarata" murmushi Samha ta yi ta ce" wlh hakama za'a yi kinga a hankali saina janye jikina na rabu dashi batareda sunga nayi musu rashin mutunci ba" da haka sukayi addu'a kowa ya kwanta.......nima naje nayi kwanciyata sabida naga dare ya yi, kuma lover's kuje ku kwanta......
Attention!! Attention!! Attention!!
*Na kusa gama book one na TSAKANINMU kuma book two ɗinsa isn't free it's 400# amma mutum ashirin ɗin farko zasuyi paying 300#only via 9086030007 Hauwa lawan Opay digital, you can start making your payment send evidence via 09086030007 whatsapp only*
_Written by_
*Nanameera*
_Tauraruwar royal star ce✍️_[2/12, 22:52] Nanameera writer: https://chat.whatsapp.com/BRBJgmCve2uEO7OzFYz8Sj
🌹*TSAKANINMU*🌹
*Story and written by*
*
*Nanameera*
_Tauraruwar royal star_
🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_
*Alk'alaminmu 'yancinmu*
_Haɗaka palace_
_Page 23&24_
__________Da safe bayan sun gama shiryawa suka fito dan tafiya aji a hanya suka haɗu da Yazeed saboda daman kullum ne sai yazo makarantar kamar ibada, gaisheshi sukai kamar kullum sannan