Showing 30001 words to 33000 words out of 33116 words

Chapter 11 - DAFIN SO Document Complete By maji dadin kainuwa.txt

الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*DAFIN SO*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


Story and writing by
*Maryam Ismail*


*MAJI DAD'IN KAINUWA CE* ✍🏻


facebook
Maryam ismail(maji dadi)
Inster
maryam maji dad'i


Last page
🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚


Inna harare kawai takeyi,ta rasa meke mata dadi dan tsabar haushi da "ni dai ba ruwa na, gara ma ki sakar masu d'iya, kije ki jajubowa kanki masifa da wannan shegen ciwan sai tsami sukeyi, Allah dai ya saka wa jika ta ni dai, dan dai ba yafewa mukayi ba ".


Abba kallon Inna kawai yakeyi shi yama rasa me zaiyi, kullun abunta kara gaba yakeyi.


Sallama tayi masu zasu tafi, kallon ta Jannat tayi tace "ki bar Lamrat anan ,ta kwana biyu "


"inna yarda shegiya nake, y'ar kwararon ita zaki jajibar mana Allah dai ya tsine halinki y'ar nan, yanzu duk wannan mugun abun da aka maki saikin makale mata, wallahi na rabaku marar zuciya kawai, kai Ummaru daukar ta ku koma can tunda bata barin halin yardar data saba "
Murmushi kawai Faruq yayi, bece komai ba, Inna dai na sababi haka aka tafi aka bar Lamrat yarinya kyakyawa da ita.


Sawam ne ya shigo rike da hannun yaran yace "mukam zamu je siyan ice cream "


"shegen shan sanyin irin na uwarsu zaka koya masu "Inna ta fada
Beko kulata ba yaja hannun yaran ya fice, a mota ya saka yaran suka bar gidan, wurin Humaira Jannat takai Lamrat.




*******


Da sauri ya fito dakin da Key din Motarsa a hannunsa, "kaga ka siwo wa Imaan ice cream tun dare take damu na da fiti na "


Yarinyar da aka Kira da Imaan ta fito da gudu tana kiran Uncle ,yarinyar kallo daya zaka mata ka gano tsantsar kamannun ta da mahaifin ta wato Sadeeq, rungume kafafun sa tayi tana murmushi, jan hancin ta yayi yace "kinci sa'a ba office zanje ba, oya muje "
Kama hannun ta yayi suka ida safkowa daidai fita kofa yaci karo da Madinat zata shigo, daga idon sa yayi yana kallon ta, kamar ya tuna wani abun ya basar ya wuce ta, ita kam ta bisa da kallo har ya bacewa ganin ta, sannan ta shiga gidan da sallama dauke bakin ta, Granny dake fitowa parlo ta amsa sallamar tace "Sannu baiwar Allah, shigo "


Idasa shiga tayi, tana shiga ta duka akan gwaiwowin ta ta gaishe da Granny, amsawa tayi tana Kare mata kallo, Umma ce ta safko daga Stairs kallo daya ta mata ta gane ta, ta tsaya tana kallon ta,tana kuma cike da tsananin mamakin irin ciwan daya same ta, me kuma tazo yi?,Madina na daga kai ta kalle ta tace "Hajiya don Allah ki yafe mun, wallahi sharrin shai dan ne da son abun duniya, amman nayi nadama gashi komai kaina yake kare mun, ki yafe mun ko na samu rahamar ubangiji na "


zama Umma tayi a chair tace "baiwar Allah lafiya?, me kika yimun? ".
"ah to kema kin kara gani, ni Grandy ko ni dai ban gane me take nufi ba ".


Sallamar Hanan ta kuma katsesu, isowa tayi cikin parlon ganin duk yanayinsu ba daidai ba yasa tace "Umma me yake faruwa ne? "
Kallon ta Madina tayi tace "kece kice ta yafe mun dukda nasan ban cancanci yafiya a gare ku ba, nice wacce nazo na gaya maki tsakanin Ahmad da Jannat wanda duka ni na shirya komai saboda tsananin hassada "nan ta kwashe labarin ta fada masu komai.


"Kai duniya munafuki beji dadi ba, Allah yabiwa Amadu hakkin sa, nan kika hadasa da uwarsa kika raba kauna, kika canzamun zaman gida, yo ae koni kinci da hakki na wallahi, yo eh mana meye hakki nan kika sa Amadu yaita ciwo ke har yanzu be warke da wannan ciwan ba "cewar Granny


"yanzu ina Jannat da abun da ke cikin ta? "Hanan ta tambaya.


"wacce irin tambaya ce wannan ?,kiyi uban me da abunda ta haifa da ita kuma "Umma ta fada a fusace sannan ta maida kallon ta ga Madinat tace "aeke banda abun da zan fada maki, kika saka yaro na yayi zina, da wannan yar iskar yarinyar amman keda Allah tun yanzu kinga karshen ki, bazan ce maki komai ba, amman kin cutar da ni wallahi "


girgiza kai Hanan tayi tace "Umma wannan ba mafita bace, komai dai ya riga ya faru, zaifi sauki ki yafe mata, Allah ma muna masa laifi ya yafe mana ballan tana bayin sa,yanzu Madina ina Jannat? "


"ta nan gidansu ta dawo da yaran Ahmad y'an biyu duka maza "


wata uwar ashar Umma ta lalubo ta afkawa Madina tace "kaji mun uwar jan alkaba'i ,wannan yaran kuyi gaggawar nemo ubansu wallahi badai Ahmad ba,ni bana ma so yasan ta dawo ballan tawa shegun da take son lika masa "


"ke yanzu abunda kikeyi shiya kama ta?, girma ne wannan? Karna kuma jin bakinki ga abunda baki da tabbas "Daddy ya fada yana zama a chair yaci gaba da cewa "duk naji me kuke fada "aniyar gyara zamu dauka, ya kamata tunda tayi laifi kuma ta gane tayi laifi har tazo neman gafara toku yafe mata, fushinku akan ta baya da wani amfani, yara kuma dole idan na Ahmad ne ya karbesu tunda sheda ta nuna shiya mata cikin,bana son na sake jin bakinki anan ciki, idan kin yafe mata ruwanki sai dai inaso ki tuna kema kina da laifi wurin Allah kuma kina bidar ya yafe maki "
"ke kuma Allah yayi maki albarka, Allah ya yafe mana baki daya "


"na yarda na yafe mata, amman bazan karbi yaran nan ba kuma bazan yarda Ahmad ya maido da alakarsa da wannan yarinyar ba ".


"to ae inaga kece Allah, Kaji bakin hali ace an haifi yara har biyu kice bana danki bane, ae saiki jira a gwada, kuma jika na bazai zauna a gwauro ba, dole ya auri abunda yake so, gashi harya tsufa ba aure "


sallama madina tayi tabar gidan, cikin sanda Hanan tabi bayan ta da gudu, taje ta samu address din gidan su Jannat ta taka mota sai gidan.


Umma kam tsabar takaici kasa fadan komai tayi kawai tabar parlon.


*********


Ice cream suka siya harda na Humaira da Lamrat, Arid sai zuba surutu yake yi duk wanda ke wurin su ake kallo, baya yayi ya bige Ahmad, zaro ido yayi yace "am very sorry Uncle ban gani bafa, kada Aunty taji zata dake ni ne ".


Muta nan dake wurin cikin su wani yace "ikon Allah ni dai naga kamar tayi yawa, sai ka Kama yaran ka ku tafi gida, ka fadawa Aunty ta masa bulala tunda ya bige Abban ".


"kai baka san Aunty da fada ba, wallahi bazan kuma ba".


Sai lokacin Anif yayi murmushi yace "kamar kayi a kunnen ta kuwa ".


"u idiot waya saka da kai ".
wani mugun kallo Anif yabi Arif dashi yace "ni kake fadawa idiot"ya nufo sa rai a matukar bace, da sauri Sawam da sai lokacin hankalin sa yakai ga abunda ke faruwa ya tare sa, tsabar takaici da haushi yasa ya soma tari tuni idonsa ya sauya yayi hanyar waje da gudu ga numfashinsa na Sama sama, waya Sawam ya ciro ya Kira Sulaiman yana fada masa a lokacin yaron ya suma a hannun Ahmad, yama kasa gane me zaiwa yaron gani yayi ya koma kamar ba likita ba, Sulaiman na sauke waya ya fadawa Faruq sai cikin kunnen Jannat kuka ta saka ta bisu baya da gudu, duk jarabar Suleiman sai da ya hakura aka tafi da ita,tun a mota babu abunda takeyi sai kuka har suka isa, tun kafin Mota ta tsaya ta balle murfin mota, Faruq na kiran ta bata saurare saba ta shiga wurin da gudu inda ta ga muta ta fada da gudu, shikam duke yake yana hura masa iska a bakinsa rike yaron da tayi ne yasa ya dago yana kallon ta da mugun mamaki, kara murza idonsa yayi yace "Maryama"sai lokaci ta daga tana kallon wanda taji muryarsa ta daki dodon kunnen ta, cak komai nata ya tsaya da taga Ahmad lokacin da suka kalli juna ido cikin ido murya na kyarma tace "wallahi duk abunda ya samu yaro na bazan yarda ba, sai yanzu na gane da gangan kayi masa wani abu, wallahi bazan barka ba, kaima Umman ka tasa kazo ka kashe mun yaro wallahi d'ana ya mutu bazan barku ba ".ta kare maganar cikin kuka.
Da mugun mamaki yake kallon ta ,ganin ta rude yasa ranshi matukar baci ya ture ta ya dauke yaron ya fizge hannun Arif daga na sawam ya sakasu mota ya fice a guje daga wurin ,wani kukan ta rushe dashi a daidai lokacin ne kuma Sulaiman da Faruq suka iso wurin, da sauri Faruq ya rike ta kafin yace komai tace "Appie ya dauke mun yara na, ya gudu wallahi mutuwa zanyi idan be dawomun dasu ba, nasan halin sa zai rabani dasu ne "


"waye ya dauke maki yara? "Sulaiman ya jefa mata tambaya cikin kuka tace "Ahmad ne "


Murmushi Sulaiman yayi yace "ya gane yaran sa kenan, ku tashi muje gida sai muga ya za'ayi"
Da kyar Faruq ya lallabata Suka wuce gida ganin bata ji bata gani yasa ya kira Ammi ya mata kwatancen gidan tace gata nan zuwa ita da Ibtihal yanzu, bata tsaya shiri ba hijab kawai ta saka suka fita ita da Ibtihal.


********


Ahmad kam Kai tsaye gida ya nufa, yayiwa Sadeeq waya su hadu gida, cikin kankanin lokaci suka isa gida, rungume yaron yayi Imaan da Arif suka bisa baya da ido Arif yake bin gidan yace "Uncle pls take us home, Aunty nacan tana kuka, kuma Ammi zata neme mu ".
"ae baku da gidan da yafi nan, so u better come inside Boy,i will take u later ".


tun daga parlo Umma tace "ina ka samu yara? "ganin tsantsar kamarsa da yaron dake binsa baya, sai kuma wanda ya kwantar a chair yasa gabanta mugun faduwa dan gani takeyi kamar Ahmad ne aka maido mata yana jariri ta kuma cewa "da kai nake malam ".


Granny ta fito da sauri tace "la ba shakka da gani wadannan sune jikoki na wallahi ,yaran Janna ne "


Hararan kasan ido Umma tabi kaka dashi, da sauri Dr Sadeeq ya shigo da gaggawa ya soma duba yaran cikin ikon Allah ya karbi numfashi gwaje gwaje yaci gaba dayi masa bayan ya gama duba results yace "My God, duka case dinku iri daya he is Asthmatic fa ga ciwan zuciya "


Zaro ido Ahmad yayi yace "subuhanallah, Allah mai juya Al'amari yacce yaso"
Kallon Umma yayi yace "ga yara na nan, ko wannan kadai ya isa ki gane jini nane su "
Sadeeq ya kama Arif yace "Boy what's ur name "
"am Faruq (Arif), and my twin is Ahmad (Anif).
"Umma na karbo yara na, kuma bazan mayar dasu ba, lokaci yayi da zasu zauna gidan Ubansu suma "yana fadin haka ya janye yaran ya wuce dakin sa.


********


A gate suka hadu da motar su Ammi Sun iso da yake babu nisa tsaka ninsu


da gudu Jannat ta rungume Ammi tana kuka kamar zata sike tace "Ammi ya rabani dasu Allah zai iya barin garin dasu, nikam bazan bar masa ba ".


"shine kikewa kuka haka?, babu abunda zai sami yaranki, kiyi shiru kada ki tadawa Momy hankali kinji, zamu karbar maki yaran ki "gyada kai tayi tana sharar hawaye kafin suka shiga cikin gidan a parlo suka samesu harda Hanan dake zaman jiransu. Tun kafin su iso Sawam ya kira Daddy ya fada masa me yake faruwa.
Sosai Hanan taji tausayin Jannat ganin lokaci daya har rama tayi saboda tashin hankali tace "dan Allah kiyi hakuri, wallahi Yaya na yana sonki yana kuma son yaran sa kullun kune a mafarkinsa dukda besan me kika haifa ba, nasan bazai taba cutar dasu ba ,nice shaidar haka saboda ke yasa yake har yanzu beyi aure ba yana zaman jiranki, a ta dalilinki yasa na fasa auransa ,dalilin fasa auran kuwa shine tun lokacin da kuka rabu ya kasa kwanciyar hankali kullun cikin ciwo yake da akace ya aure ni mamadinki a lokacin sai ciwansa ya kara tsanan ta, abokinsa ya sadaukar da komai nasa don ceto rayuwar sa yaje ya samu Granny yace ta dubi girman Allah ta yarda ranar auran mu da Ahmad a daura dashi saboda tabbas idan aka aurawa Ahmad ni rayuwarsa zata kara tabarbarewa kuma zamu iya rasa shi, ita kaka tace su bari zata fara yin shawara dani lokacin data Kira ni na karbi auran Sadeeq ne bawai don bana son Ahmad ba a'a nayi ne don ceton rayuwar sa, saboda tsananin son da nake masa yasa na sadaukar da komai nawa dan nema masa farin cikin sa a ko ina, nayi kuka hankali na ya tashi amman na daure na karbi auran Sadeeq wanda yanzu muke da y'a daya, na tabbata har gobe yana sonki kuma dan Allah ki yarda da auren yaya na ku rike yaranku, acan yaranki zafi samun y'anci "
[7/1, 1:38 PM] Maryam Maji Dad'i: "Kira mun shi, ya zai raba uwa da yaran ta banda sakarci "Daddy ya fada.


Mikewa Umma tayi ta shiga dakin Ahmad ganinsa rike da yaran yasa ta jefa masa mugun kallo tace "inka ga dama ana jiran ka parlo "ta juya tabar dakin parlon ta dawo inda ta samu Granny a wurin bataji dadin ganin ta ba dan tasan dole ta tayar da wani rigiman, Ahmad ya fito kanshi kasa ya duba gaban Daddy in a cool voice yace "gani Daddy "
"waikai meke damunka?, za zaka dauke mata yara?,bayan kasan dole sai an nemi sulhu, Inna ta yanke hukunci kaje ka dauko yaran Yanzu zamuje gidan"Daddy ya fada.
Bata rai Umma tayi daukar ta fada zasuyi masa sai taji wani sabon zancen tace "yo muje kuma mu dauko me?, ni dai dana bazai auri mawakiya ba gaskiya "
"Allah dai ya tsine halinki Hadiza to ina ruwanki?, wallahi y'ay'a na bazasuyi zaman agolanci ba in bakyaso ta shigo ke saiki fita, ke yau harda sadaki zamu fita, ni dai ba ruwa na, mata sai bakin hali, ku tashi muje ni "yaran Ahmad ya dauko suka shiga mota shike driving daya hada ido da Umma ta mirrow saita maka masa harara har Suka isa gidan, iso sukasa akayi masu, har babban parlon Alhaji Abdullahi aka shiga dasu, sosai Suka samu karbuwa kafin ya fito tare da su Inna ya fito turus suka tsaya suna kallan kallo, Inna tace "na shiga Ukku ni maryama Binta dama kina da rai "sai ta fara matsar kwallah, Granny ta matsa kusa da ita tace "maryama muna gari daya bamu haduba tsawon shekaru wayyo ni, ashe ina da rabon kara ganin y'ar uwa ta "
Sake da baki duk mutan parlon ke kallonsu.
Tsaki Inna taja tace "Allah dai ya tsinewa y'an sa ido, to binta dai kawar wasa tace zumunci na kusa balle a rabamu, mutum sai yaci kansa wallahi ".
"ke rabu dasu, aeni na dawo daga rakiyar su wallahi, kilama da gangan suka ki hadamu, saboda munahincin su ni dai ba ruwa na kuma gashi dai mun hadu ae "
Hannu Abba yaba Daddy yace "barka da zuwa Alhaji Aliyu, ashe abunma dukna gida ne "
"barka kadai Alhaji Abdullahi "ashe Daddy da Abba abokai ne sosai aeki ne ya raba su.
Zama sukayi kafin ya aeka aka kira Jannat, hijab ne har kasa jikin ta daka kalli fuskarta zaka san Tasha kuka harta gaji, yaran ta na ganinta suka ruga zuwa gare ta, rungume su tayi itama tana sakin murmushi kafin Suka karaso ta zauna, sai kallon ta Ahmad yake yi, suna hada ido ta murguda masa baki.


"ni dai ba wani dogon surutu bani so yara na suyi agolanci, Maryama nazo karbar auran wancan yarinyar ne ga jika na Amadu gashi nan "
"to duka ae naki ne, bar gantalallah a daura kawai ku tafi kafin ta sake daukar magana "
Turo baki Jannat tayi tana hararen Inna.
Kallonsu Sulaiman yayi cike da takaici yace" but Faruq wants marry Jannat since ".
"ka dai zagi uwarka gata nan "Granny ta fada.
D'an taboshi Faruq yayi yace "what's that pls, ka barsu inaga hakan shine masalaha kuma indai shine harga Allah na hakura zuciya daya kuma na tabbatar Jannat na sonsa sosai, fushi kawai take dashi dan haka ita ta amince, sake da baki Jannat ta bishi da kallo be yarda Sun hada ido ba.
"Au bintu na gane me suke nufi yanzu, yaro Ummaru dan girman Allah kayi hakuri ka barwa jikana Ahmadu shine rufin asirin yaran baki daya "
"Inna babu komai na bar masa zuciya daya "
Albarka suka dinga saka masa.
Nan aka tsaida ranar aure, nanma Sawam yaga Ibtihal yace yana so ba ja ta amince aka saka tare, Ibtisam tasha mamaki da taga asalin Jannat sosai ta bata hakuri ta yafe mata, itama ta yafe mata,wanda ke santa ma ya fito,gidan Daddynsu daya na abuja Suka zauna basu koma adamawa ba.
****************
"Haba Janna yanzu duk rokon da binki yakeyi bazaki yafe masa ba, yayi nadama dan Allah ki yafe masa "Mubaraka ta fada tana goge hawayen idonta


"sai dai na yafe dan darajar ki, badan shi ba, na yafe masa duniya wa lahira "ta kare maganar tana duban Ashman daya kure ta da ido duk yayi kalar tausayi. Sosai ya mata godiya kafin suka wuce gida, a kuma satin ne Goggo ta tasu sunyi jimami sosai da taya Madinat bakin ciki,sosai aka shirya gaggarumin biki na gani na fada, ranar Friday dubban alumma suka shaida daurin auran yaran Ukku akan sadaki dubu dari ko waccensu, da yamma ko wacce amarya ta tare gidan ta, anan kuma Faruq ya hadu da Jamila kanwar mijin Asma'u da sukaxo biki yarinya natsatsiya da kirki aka sha biki suma.
Wayan dake hannun ta ta Saki ta kwala ihu da gudu Ahmad ya fito yana tambayar lafiya "Madina" kawai take fada
Wayar ya dauka ya kara a kunne yaji Allah yayiwa Madina rasuwa sosai mutuwar ta taba mutane musamman Jannat da tafi kowa shiga tashin hankali ta kama Lamrat ta rike tace bazata bawa kowa ba tun a sadakar Ukku ta dauke ta, ta zame mata uwa ta zame mata uba.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login