Showing 12001 words to 15000 words out of 33116 words

Chapter 5 - DAFIN SO Document Complete By maji dadin kainuwa.txt

"Umma me yake faruwa?"


"haba rabu dashi Adnan duk iskancinshi na shirya masa yanzu, yaro yaki jin rarrashi, tona gaji da zaman aure zan masa kuma da Madina inyaso ya hadiye rai ya mutu ".


"Madinat fa kikace Umma, don Allah ki Aura masa kowa banda Madinat, ina rokon wannan alfarmar Umma"ya karashe maganar yana hade hannuwansa duka biyu alamar roko.


"yasan bazai iya ba ya fara?, shin ita ba mutum bace daya lalata mata rayuwa, hakan Kana ganin adalci ne abarta kawai "Umma ta fada.


"tabbas babu adalcin daya wuce wannan, kiwa Ashman aure amman bada karuwar data kasa tsayawa namiji daya ba, karshe ma yanzu haka gidan wani take zaune bada iyayenta ba, sannan duk abunda ya faru munafircinta ne ita ta lalata komai Umma, idan har akayi auran nan idan soyayyar Janna bata kashe Ashman ba to tabbas wata cutar zata kashe shi ta dalilin Madona, Umma don Allah kiyi tunani akai "ya kare maganar yana marairaice fuska.


"shikenan tashi kaje zanyi tunani akan wannan ".


Godiya yawa Umma sosai sannan yabar gida ba tare daya kuma kula Ashman ba.


Ashman kam takaici ya isheshi ya rasa wacce duniya yake dukya fasa kayan dakinsa sai huci yake a haka baccin wahala ya daukeshi.


************


"Momy me kikeyi anan bayan gida kuma? "Sulaiman ya tambaya tare da rike duka hannuwanta biyu yana kallonta "Momy badai tunani kikeyi ba, ki tausaya mana kodon lafiyarki Momy na "




"Sulaiman tunani ya zama dole gareni, ya kake tunanin zan iya daina tunani akan y'ata mace kwara daya tak da kaddara ta fadawa, ace na bude ido babu Maryama a gabana, yanzu wayasan inda take, Allah baxai taba yafe duk wani hakkinta akanmu ba, bayan mune mukai mata gatan dahar ta koma haka,shin ku baku damu da yar uwarku bane ,wacce irin zuciya ce gareku? ".




"Umma yin shiru baya nufin mun manta da ita, duk abunda nakewa janna inayine don gudun lalacewar rayuwarta bawai don bana sonta ba, Momy aduk gidan nan babu wanda nakeso kamar yacce nakeson Jannat, nasan kowa yaji zaiyi mamaki, ina takura mata ne dukdon rayuwarta tayi kyau, saidai ina gini ana rushemun shiyasa na zare hannuna bawai don bana sonta ba, Momy ina son yar uwata kuma insha Allah zata dawo garemu ki daina damuwa".




Karo na farko aduk watannin da Abba ya kori Janna sai yau ya fara jin be kyauta ba da alamun nadama, tabbas shine wanda ya ruguza rayuwar y'arsa kuma mamadin yayi gyara saiya koreta, ji yayi zuciyarsa ba dadi kewar y'arsa ta dawo masa, kai tsaye parlo ya nufa anan ya samu su Inna tanata fafatawa da Sawam don shima yanzu yayi baki.




"kaji shegen yaro, kaima ka lalace ko, to wallahi kabi a hankali kafin nasa kaima kabar gidan "Inna ta fada.




"innabar gidan ke ki zauna tsaron duniya a ciki, ae komai yake faruwa dasa hannunki baku kuka lalata Janna dinba ba'a da ikon a mata gyara, toma meye na tada hankali bayan kawo maku abunda kuka aekata nema tayi, wallahi hakkin yarinyar nan baxai barki ba, tsohuwa Kin matso ga kabari amman Kin fitini mutane ".




kuka sosai ta rushe dashi tana tafa hannuwa "Sawam nika zaga, ni kake cewa na mutu, tsigagge marar tarbiya, Allah ya isarmun ME kama da tsohon jakki ".


Beko kula taba yabar mata parlon ya wuce Abba shima ko kallonsa beyi ba.


"yanzu a gabanka Abdullahi harka haifi yaran da zasuna wulakantani?"


da sauri ya matso gabanta "Innata don Allah kiyi hakuri zan masu magana, bazasu sake ba".


"yadai fi maka "mikewa tayi tabar dakin tana shartar majina da habar zani. Shima dakinshi ya wuce nadama fal aranshi, gidanshi mai cike da farin ciki da walwala shine yanzu ya koma kamar filin yaki kuma dukta silarshi, dole yasan abunyi kam.




*ADAMAWA*




zaune take akan Chair rigar Buba ce ta shadda Blue colour jikinta ta daura kallabi kamar gwargwaro tayi fari tayi kyau sosai ga y'ar kiba da tayi, cikinta yayi babba sosai ya fito dakyar take tafiya kimanin cikin wata Takwas (8),Amman yayi kamar wata tara, apple ne hannunta tanaci a hankali, lekenta yakeyi ta window komai Amira (sunan da suke kiranta dashi kenan, saboda Sunan Amma ne) tayi burgeshi yakeyi tun bayan rasuwar Minal be taba ganin matar dayake soba kamar Amira komai tayi sai yaga kamar Minal ce, amman cike yake da tsoro karya rasata itama wurin haihuwa shine abunda yake tashin hankalinsa kullun yana rokon Allah daya sauketa lafiya.


Da gudu Mahmoud ya fito yana kiran "Aunty ,Aunty "daram ya haye bisa cinyarta yana haki.


murmushi tayi ta shafa kanshi tace "wa kuma ka tsokana ".
Ibtihal ce ta fito, tana jefa masa harara, kafin tayi magana taji muryar Yaya Faruq yana cewa "haba Muhamud baka ganin ya Aunty take, ka daina zama akanta pls "




"yaya bafa komai zan iya har goyonshi mafa"Janna ta bashi amsa.


Murmushi ya subuce masa yace "yace oya tashi ki ruga mu gani ".


zaro ido tayi alamar tsoro, kokarin mikewa ta somayi ta kasa kwabe fuska tayi rau rau da ido.


dariya Ibtihal ta kwashe dashi tana mata gwalo.


Maji dad'i✍🏻




*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
*____________________________________*


*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*


πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*DAFIN SO*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


Story and writing by
*Maryam Ismail*


*MAJI DAD'IN KAINUWA CE* ✍🏻


facebook
Maryam ismail(maji dadi)
Inster
maryam maji dad'i


Page 85 to 86




Pillow din Chair ta dauka ta jefa mata ta kwabe fuska kamar ta saka ihu, tana harararta, matsowa Ibtihal tayi tana kokarin tashinta amman ta kasa, Ammi ce ta fito tana fadin "me kuma akewa wannan dariyar ".


"da y'arki Ammi, ta kasa tashi "Faruq ya fada yana danne dariyar data taso masa.


"shine kuka sakata gaba kuna mata dariya, rabu dasu, itama Ibtihal din aure zan mata ki rama dariyarki ".


Takowa takeyi cikin isa har zuwa cikin parlon tana taunar Gum sai kara yakeyi, da gangan tabi ta saitin Jannat ta take mata k'afa da Shoe dinta masu tsini.




Wani irin zugi taji ya ziyarci duka kwalwarta xuwa sassan jikinta, ihu takesonyi amman ganin Faruq Wurin yasa ta toshe bakinta tare da rumtse idanuwanta, hawaye na shirin fitowa,ta makara kam don ya dade da ganin abunda Ibtisam tayi, shima zama yayi, yayi crossing legs dinsa yana kare mata kallo.


Itakam kamar batayi komai ba ta zauna tana fiddo waya ta soma Chart, duka dakin tsaye sukayi suna kallonta, Ibtihal na jinjina mugunta irinta y'ar uwarta kasa shiru tayi tace "Haba Ibti bakya ganin irin takata da kikayi, amman kamar Kin taka icce ".


"dallah malama ki rufamun baki a wajen, uwar kalar dangi, ita bata da bakin magana saike uwar iyayi, to ki rama mat......"idasa hadiye maganarta tayi ganin Faruq zaune ya kura mata ido, ita koda ta fito bata lura dashi a parlon ba, zare ido ta somayi tana gyarma don tasan yau ta gama yawo zataji jibga ne.


Kawar da kai yayi sannan yace "you idiot come here ".


Tsoro karara ya bayyana a fuskarta baki na kyarma tace "ah....ah Yaya Allah ban kula ba, i'm sorry pls ".


"na tambayeki wani abu ba "ya fada kamar bashi yayi maganar ba.


Zuwa tayi gabansa ta duka, batayi aune ba saijin saukar mari tayi a fuskarta, hawaye ne suka gangaro mata ta dafe wurin, tanajin xafi na ratsa ta.


Yunkurawa Jannat tayi da taimakon Ammi ta mike, da kyar ta iya dukawa gabansa tace "Yaya pls kayi hakuri, bata gani ba, kuma ta ban hakuri ".


Da mamaki yake binta da kallo, kullun ita kokarinta ta kare Ibtisam, amman ita kuma kamar kara hura mata tsanarta akeyi arai.


Wani mugun kallo Ibtisam ta bita dashi babu abunda zaka hango sai tsantsar tsana da kiyayyah a fili, mikes tayi da gudu ta nufi fakinsu.


Ammi murmushi tayi don harga Allah tana matukar son Jannat kodon halayyarta masu kyau, dakinta ta wuce tana jin kaunar yarinyar har cikin ranta.


Kallonsu suka maida ga TV din dakin da zazzak'ar wak'ar ke tashi ta secret Super Star, batunsu d'aya shine ina ta shige, alumma kowa ta ita sukeyi, bata ida tantance cewa tana da masoya ba saida aka soma karanto sakonni kowa akanta yake magana, take rayuwarta ta baya ta soma dawo mata cikin kai hawaye ne suka soma zubo mata kokarin tashi tayi ta kasa, kamata yayi ta mike tsaye ya rike hannunta tana jan kafarta datayi jajir, a hankali ya bita harta haye benen ta shiga dakinta, a bed ya zaunar da ita, idanu ya zura mata yana kwab'e fuska, zabura tayi tana maida numfashi.


hakan yayi daidai da fashewar glass cup din dake hannun Ahmad jini ya soma zuba, bakinsa ya soma kyarma.


"yadai, ki nutsu mana, meye matsalar ".


"Yaya Ahmad "abunda bakinta ya iya furtawa kenan.


"kinga ki daina kuka To, yana lafiya kinji, kinga lokacin haihuwarki ya taho ba'son kina damuwa ki daure kinji,bana son kukanki pls".


gyada kai tayi tana share hawayenta, tana kakaro murmushi.




"Umma, ban fahimci me kike fada mun ba "Ahmad ya fada fuska cike da damuwa.


"cewa nayi ya kamata kayi aure nanda wata biyu, kuma Hanan ce matar da zaka Aura, ina fatan yanzu Kaji mena fad'a ba "


dukawa yayi akan kafafunshi ya kasa magana yana fadin "U..m.. m..a "muryarsa ta shake dakyar ya fizgo maganar yace "pls Umma don Allah kada ku ida rusamun rayuwa, bazan iya son kowa ba sai ita, itace farin ciki na, idan kika tilasta nayi aure yanxu zan cuci Hanan don bazan taba iya kula da ita ba".


hannu ta daga masa alamar ya isa "bana son zancen banza Ahmad har yanzu baka manta da wannan asararriyar karuwar yarinyar nan ba, to bari Kaji ko mutuwa zakayi saidai ka mutu aure anyi an gama ".


"karuwa, karuwa, shi kowa ke fada kuma bancin babu wanda yasan komai akai, So d'aya (na maryam Ismail) ne kuma na bada shi ga Janna zan mutu da sonta araina, Umma ki taimaka mun na nemi yafiyar laifin dana aekata, ki ceci rayuwa ta ".


"mtswww aekin banza "ta mike tabar wurin.


glass Jug din dake gabansa ya dauka yayi jifa dashi ya tarwatse akan glass table din dake wurin, jifa ya somayi da duk wani abu dake gabansa yayinda zuciyarsa ke zafi kamar ta fasa kirjinsa ya fito, ihu ya kurma ya fadi a wurin, dukya jiwa jikinsa ciwo, da gudu Hanan da Sadeeq wanda shigowarsa gidan kenan sukayo dakinsa, Granny ma ta tufa masu baya, kuka Hanan ta Saki tayi kansa da gudu ta rike hannunsa da yake kokarin daurawa a kwalba, d'an kwalinta ta cire tana daure masa hannun, mugun kallo yake jefa mata tureta yayi yana dafe zuciya, lumfashinsa ya soma Sama sama, Sadeeq ya rungumesa ya sume a hannunsa. Kuka Granny ta Saki tana kiran sunanshi.
Maji d'adi ✍🏻




*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
*____________________________________*


*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*


πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*DAFIN SO*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


Story and writing by
*Maryam Ismail*


*MAJI DAD'IN KAINUWA CE* ✍🏻


facebook
Maryam ismail(maji dadi)
Inster
maryam maji dad'i


Page 87 to 88




Ko motsi beyi ba, girgizashi Sadeeq keyi amman shiru saman bed ya maidashi ya dauko kayan aeki yana basa taimakon gaggawa, dukya rude, Hanan kuka take kamar ranta zai fita, "pls kudan bani wuri"saida Granny ta kamata sannan suka fita, cikin ikon Allah Ahmad ya karbi numfashi da Sadeeq ke hura mashi, Jannat, Jannat shine abunda yake furtawa yana surutai, allurar bacci ya masa, anan bacci ya daukesa, ajiyar zuciya ya sauke yana mamakin irin son da Ahmad yakewa Jannat, wanda ko magana be cika yiba sai gashi son wacce besan ina take ba sonta na neman zautar dashi.


Rufeshi yayi da Duvet sannan ya tattara kayanshi ya fito, a parlo ya samesu kowa ya jefo masa tambayar ya yake amman banda Umma wanda abun ya dameta a rai saidai ba zata iya fifita soyayyar d'anta akan ta Hanan ba.


Zama yayi yana goge gumi yace "Alhmdllh, amman yanxu zuciyarsa takai matakin karshe yanzu, inhar aka takura shi, kuma be samu abunda yake so ba, to ko yaushe zamu iya rasashi, zuciyarsa tayi sanyi bata da karfin iya daukar ko wacce irin damuwa yanzu, saidai muyi masa addu'a kawai, anjima zan kawo masa Drugs "bece komai ba ya mike yabar gidan, hawaye ne ke zubowa a fuskar Hanan basa ko tsayawa, mikewa tayi kai tsaye dakinta ta shiga ta dauki laptop ta soma bincike, a ranta ta daura aniyar duk inda Jannat take zata kawowa Ahmad ita, zata sadaukar da Soyayyarta garesa, ranta fansa ne garesa.




After one month


Kayan lefe ne aketa dubawa gidan a cike, kaya ne har kaya sunyi matukar kyau akwati 8,"yanzu yaushe za'a Kai kayan lefen nan? ".Umma jamila ta tambaya kanwar Hajiya.


"gobe ne mana, munyi magana da Hajiya Karimar ae ".


Sallamar Ashman da Adnan ne ta katse masu maganar da sukeyi, "yauwa Angunan Sun iso kenan, kuzo ku duba kayan "Umma Jamila ta fad'a.


Ashman beko kalleta ba yace "komai kuka saka yayi "be jira ansarta ba yabar parlon yanajin tukukin bakin ciki na taso masa.


"waikam yaron nan be saluda da duniya, yanzu ina yasan inda wata Jannat take bayan shiya yaudareta ya lalata mata rayuwa sai yanzu kuma yazo yana neman wata damar a wurinta".


"rabu da iskancin yaran yanzu, auren shi dai da Mubaraka babu fashi wallahi(mubaraka yarinyar kawar Hajiya ce, lokacin da yaki amincewa da auran Madinat shine ta nema masa auran y'ar aminiyarta akayi sa'a kam itama ta dade da soyayyar Ashman a ranta ".Hajiya ta fada.


Key din mota ya dauko ya fito shida Adnan yanzu kam ko kallonsu beyiba yayi waje abunsa, Gidansa daya zame masa wurin hutawa nan suka nufa, a parlo nan suka samu Madinat zaune akan chair tana kurbar lemu hankali kwance ga TV tana kallo.


Ko Kadan Ashman beyi mamaki ba don yasan tana da Key din gidan, katse masa tunani tayi ta mike tana zagayesa tace "your welcome my Dear, naji dadin zuwanka akan lokaci, don tun dazu kai nake jira, ina da magana da kai ".


Hannu yasa ya fizgota "ki daina zagayeni, kiyi abunda ya kawoki kafin lokaci ya kure maki "ya kare maganar yana nunata da yatsa.


"meye na daukar zafin haka, naji ance zakayi aure, shine nazo maka da mafita da fada maka abunda ya dace kayi, Ashman ka kalleni indai ina da rai baka isa ka auri ko wacce y'a Mace ba, Kai baka isa ka yaudareni ba, yanzu nazo na sanar maka cewa ina dauke da cikinka na tsawon wata hudu kuma na tabbata naka ne, so mafita daya ce kazo muyi aure mu rike cikinmu mu tallafi abunda muka haifa ko kuma na tona maka asiri a gidan sirikanka ".


Rabon da Ashman yayi dariya harya manta ,amman yau yayi dariya harda rike ciki ya zauna a chair ya dora kafa daya kan daya yace "ke wacce irin jahilace bana da lvr, kin manta wanene Ashman ko, to inaso ki sani yacce kikabar cikin mahaifiyarki haka bazaki taba samunaba har abada, niba zan auri karuwa me zaman Kanta ba, nida kin taimaka mun kinje gidan surikan nawa wata kila su dauki maganarki kosa fasa auran da kinman babban taimako ".


wata irin zuciyace ta ciyota ta soma dura ashariya dan kaza kazanka wallahi baka isa ba "


Wasu kyawawan maruka guda biyu ya falla mata, saida ta gigice ta kurma uban ihu, kafin kace me ya zare belt ya soma jibgarta ta ko ina tana ihu, sai lokacin Adnan ya soma basa hakuri da kokarin rikesa amman ina saida yai mata jina jina ya taka mata ciki sannan Adnan yayi nasarar kwace ta, hawaye ne suka zubowa Ashman ya fada kan chair Yana fadin "Allah ya isa tsakanina dake, kekam shedaniyace muguwa azzaluma, Allah sai ya biwa baiwar Allah hakkinta, toke hakkin mutum nawa kika dauka ma, har yanzu bazaki saluda ba, na tsaneki Madinat, na tsaneki ki bacemun da gani kafin in lahantaki anan ".


kuka takeyi rurus hankalinta tashe ko ina jikinta ciwo yake mata dukta rude, ganin ya yunkura yasa ta baza da gudu tayi hanyar waje tana zabga Allah ya isa kai tsaye gidan Alhajinta ta nufa, shima a tsaye ta iskeshi ya tattaro mata kayanta watse a filin gidan yana haki, wata razananniyar tsawa ya saka mata yace "karki kuskura ki takO nan bana hanaki zuwa wajen wannan kwarton naki ba shine kika saci hanya kika fita, To duk inda zaki saka kafarki ina sani, to kije babu ni babu ke"watsa mata kaya waje yasa akayi, duk magiyar da take masa beji ya damki hannunta ya turata waje ya rufe gidansa, anan ta duka ta rushe da matsanancin kuka hankalinta a matukar tashe.


*tofa duniya ta soma juyawa, Madinat baya ko yaya zata kaya*
Maji Dad'i ✍🏻


*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
*____________________________________*


*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*


πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*DAFIN SO*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


Story and writing by
*Maryam Ismail*


*MAJI DAD'IN KAINUWA CE* ✍🏻


facebook
Maryam ismail(maji dadi)
Inster
maryam maji dad'i


Page 89 to 90


*ADAMAWA*


Tun safe data tashi takejin matsanancin ciwan mara hakanan take sauteed tana y'an hidimominta,dakyar taja kafarta zuwa toilet ta watsa ruwa gaban mirrow ta zauna tanajin ciwon na kara tsananta sai faman cije baki takeyi.


Sanye ya fito cikin uniform na kakin soji sosai kayan suka karbi jikinsa, ya kara fitowa cikakken namiji Faruq kenan d'a ga General din soji .a dining ya zauna yana shan coffe ganin kowa na harkarsa a gidan amman har yanzu bega Amira ba yasa ya kira Ibtihal "ina Amira?"


"na barta zatayi wanka ne? "ta bashi amsa, be kuma cewa komai ba ya mike ya kwashi Keys dinsa ya tafi office.


Sosai ta soma galabaita, don ko motsin kirki ta kasa, zufane ke faman tsiyayo mata, dafe take da mararta harta durkushe kasa ta soma zubar da hawaye, ji takeyi kamar ranta zai fita ne dan tsananin zugin da k'asanta ke mata.


"kinga Ibtisam ki dubamun Maryama d'aki ko lafiya dukyau bata fitoba ko breakfast banga ta fito ba "Ammi ta fad'a.


Kunbure

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login