Showing 18001 words to 21000 words out of 33116 words

Chapter 7 - DAFIN SO Document Complete By maji dadin kainuwa.txt

sosai ta Karbi jikinta tayi masifar kyau, be dawo gidanba sai wurin 10 kai tsaye dakinsa ya shiga yayi wanka, ya fito yana goge kai da karamin towel, knocking yakeji "come in"ya fada yana murza mai a jikinsa.


Tun kafin ta shigo kamshin turarenta ya bide dakin, taku takeyi cikin nutsuwa harta iso kusa dashi ta duka har k'asa tace "ina kwana ",gabanta na dukan ukku ukku tana Tsoron amsar da zata samu dauriya kawai tayi ta shigo,ba kamar data ganshi da towel.


Tsab ya gama karantar yanayin da take ciki, kawar dakai gefe yayi yace "lafiya".


Murya na rawa ta kuma cewa "your break fast is ready Sir".


"nace kiyi girki da ni ne?, ko kuwa nace zan rika cin jagwalwalonki? ".


Tuni idonta ya kawo ruwa tace"kayi hakuri, gani nayi ya dace nayi, tunda zamanka nakeyi ".


"Owk kije ina zuwa naga ko zan iya daurewa naci ".


Murmushi tayi k'asa k'asa don harga Allah taji dadin amsawar da yayi, don ba haka tayi tsammani ba,mikewa tayi tana tafiya, da kallo ya bita ko ina na jikinta rawa yakeyi, donko mubaraka itama ba baya ba wurin kyau.


A gaggauce ya shirya cikin k'ananun kaya don fita zaiyi, sai zuba k'amshi yakeyi ya fito, zaune take a parlo da sauri ta mike ta karbi wayoyinsa da Key din motarsa ta bisa baya zuwa dinning, tunda ta bude girkin, kamshinsa ya bide wurin chips ne da farfesun y'an ciki sai ruwan lipton da yaji kayan kamshi, yana yatsine fuska yake cin abincin kamar yana tauna magani(🀣🀣anji dadi anata fuskewa kafin mubaraka ta halbo jirgin mutum).be wani ci sosai ba ya mike ya karbi kayansa tana masa Allah ya tsare bece komai ba ya fice abunsa. Tashi tayi ta soma tattare wurin.Haka rayuwa ta ci gaba da tafiyar masu, tun yana d'an shareta harya fara kulata wani lokacin har fira suke d'anyi, don mubaraka ba daga baya ba.


**********


"me kake tunani Abban Sulaiman "Momy ta fada.


murmushi yayi yace "ina tunanin rayuwa ne, Momyn Jannat ".


da sauri Momy ta dago tana kallon Abba wanda rabon da taji ya Kira sunan Jannat tun ranar daya koreta, wani sanyin dad'i taji a ranta ganin koya sauko ne.


janyota yayi zuwa jikinsa yace "kina mamaki ne Umman Jannat? "


gyad'a kai kawai tayi tana murmushin itama.
"ba abun mamaki bane, dama can sharrin zuciya ne, yanzu kam ina rokon Allah ya nuna mani y'ata kodon na gyara kuskuren dana aekata".


Hawayen dad'i ne suka zubowa Momy ta d'aga hannu tana godewa Allah daya nuna mata wannan rana, sosai suka sha soyayyah ranar ran Momy Fes.


"uban me kuma kake leke, shege me siffar aljannu "Inna ta fada tana fitowa daga part dinta.


"karki kuma cemun shege tunda kinsan Ubana, part dinki na lek'ane ne, wallahi zamu koma da"Sulaiman ya bata amsa.


Harara Inna ta watsa masa tace "wallahi Sulaimanu ina raga maka ne saboda wancan matar daka dake dauke da tsohon ciki da tuni nasa anyi waje da kai kaima ".


"aeko ke da kinga inda zaki, donni kinsan ba'a wannan dani, tsohuwa kin kusa mutuwa amman ki hayyaci kowa wallahi nayi maganinki"barin wurin yayi yanajin in yana wurin ba hakuri zaiyi ba.


"kuma nace Shege, munahiki Allah wannan yaron indai yana gidannan wataran kasheni zaiyi "tanayi tana matse kwallah.




dariya Sawam ya fashe dashi yace "dama shine maganinki ae, inkin raina kowa shi Zai saita maki sahu ae, kema saiki tab'o wanda ya fiki ".


"kaini naga jaraba, shegun yara duk Sun gado bak'in hali irinna Uwarku, nidai banga ranarku ba, Duka zansa ya koremun ku daga gidan ".


"kanki akeji dai, kinga tafiyata "nan ya barta tana sababi.


bari mu leka Adamawa


Majidad'i✍🏻




*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
*____________________________________*


*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*


πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*DAFIN SO*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


Story and writing by
*Maryam Ismail*


*MAJI DAD'IN KAINUWA CE* ✍🏻


facebook
Maryam ismail(maji dadi)
Inster
maryam maji dad'i


Page 97 to 98


"kinsan Allah zan Kira Yaya Faruq, ki tashi ki kama yara sai zuba kuka sukeyi, kin tsaya kallonsu ".




"ni bansan me suke soba, nidai na gaji wallahi abada su "Jannat ta kare magabar tana raurau da ido hawaye ya cika taf a idonta.


"mtswww aekin banza, ubanwa ya haifesu da za'a badasu, kin wani damu mutane, to ki daukesu ku tafi gidan ubansu idan akwaishi "Ibtisam ta fad'a.




Uwar harare Ibtihal ta jefa mata tace "ke baki daina shiga abunda babu ruwanki ko?, wai harsai yaushe zakiyi hankali ".


"dallah malama rufemun baki, ko ciwan kanki baki sani ba kawai kin zama y'ar raino ,to karya nayi inda uban a tafi wurinsa mana, kuma wallahi idan kika kara cemun bana da hankali sai munyi bala'i dake ",zura shoe dinta tayi tabar dakin tana sababi.


Itakam Jannat hawaye yaki k'afewa daga fuskarta, ashe bata huta da wahala ba, ashe gori bazai kare mata ba, lallai Uba daraja ne ga yaransa sai yanzu take kara jin ciwan abunda Ashman da Madinat suka mata, bata tabbatar Sun gama tarwatsa mata rayuwa ba sai yanzu,dafa kan yaranta tayi hawayenta suka zuba akan fuskarsu tace "mahaifinku na sanku, yana kuma kaunarku kaddara ce ta rabaku kuma ina fatan ko bayan raina ta sake had'aku ".


Zuru yaran sukayi mata, wanda sunyi wayau sosai gasu bulbul abunsu kwanin sha'awa, sai halba kafafu suke suna gwaranci, jin tausayin yara na ratsata tayi, dafa kafad'arta Ibtihal tayi tace "Aunty Amira don Allah kiyi hakuri, kinsan halin Ibtisam ba wani abu sabo, insha Allah zata daina ".


Murmushin takaici Jannat tayi tace "karki damu, tana da gaskiya da gidan Ubansu suke wazai goranta masu, gara ta rika tunasarmun da inda nake kona san abunyi, ni ban riketa a raiba".


Da gudu Mahmoud ya shigo dakin ya fada a bayan Amira ya rungumeta "Aunty Momy na dawo"abunda ya fada kenan.


Share hawayenta tayi kafin ta juyo don tasan halin Mahmoud da shegen wayau ga surutu, "Oyoyo yaron Aunty sannu da zuwa, ya School din? ".


Hannuwansa duk biyu yasa ya tallafi fuskarta "Aunty waya Saki kuka na halbeshi da bindigar Daddy ?".kamar daga sama taji tambayar tasa.


"Habibi Idona yakemun ciwo nefa"ta basa amsa.


Da gudu ya fita a dakin, part din Faruq ya shiga yana hak'i baya parlo Kai tsaye Bedroom ya fada yana maida numfashi.


Juyowa Faruq yayi ya jingina da mirrow yana kallon Mahmoud yace "ba sallah yaron Aunty? ".


"Oh am sorry Abban twins, Aunty na tana ciwan idone fa, sai ruwa yakeyi ".Mahmoud ya basa amsa ,be jira me Faruq zece ba ya Kama hannunsa suka fito, har dakin Jannat ya kaisa lokacin Iftihal ta fita, zaunar dashi yayi a bed yace "Daddy ka tambayeta ka bata magani, bara naje na canza kaya kafin Ammi na ta fito da gudu yabar masu dakin.


"me yake damun ki ne ?".
Kamar daga Sama taji tambayar tasa.


Basarwa tayi tace "ba wannan yaran bane sai wahala suke bani ba "ta kare maganar yata kwabe fuska.


murmushi kawai yayi don tsab ya gane ba abunda yasa ta kuka kenan ba, sharewa kawai yayi yace "to Maman biyu ae sai hakuri,kuma kinga Anif ae baya da rigima, rigima saidai takwara na ".


Murmushin ta mai kyau tayi har hakoranta suka bayyana "kilama gado yayi, kaima kawa Ammi rigima ".
Sosai ta birgesa da irin farin cikin da yaga tana yi, yunkurawa yayi zai mata dundu.


"Allah Yaya na daina fad'a, bakayi rigima ba "ta kare maganar tare da rumtse idanuwanta sosai ta soma kyarma.


"matsoraciya "ya fada ya kwashe yaran yabar mata dakin.


*********


Shirin biki ya kankama babu abunda Ummu da Mama (Maman Hanan) basu gama ba, amarya sai shan gyara takeyi, har wani Shek'i takeyi,lefe na gani na fad'a Umma ta hadawa y'ar tata akwati goma.


B'angaren Ango suma babu abunda basayi harta kayan sakawa komai iri d'aya Sadeeq da Ahmad sukayi, saidai a bikin ya hana hidimar komai daurin aure kawai za'ayi sai walima, Umma ce ta had'a walima daren aure,yaune ya kama ranar walima, an shirya komai tsab, Manya manyan Malamai Umma ta gayyata, amarya tasha kyau cikin purple lifaya da wani d'anyan leshi shima purple ga zanan lalle ansha ga kitso tayi matukar kyau sosai, Wa'azi sosai Malamai sukayi akan aure da biyayyah ga miji, Amarya tasha kuka sosai Wa'azi ya ratsata, tasha kyaututuka daga y'an uwa.


Ranar daurin aure


yaune ya kama ranar daure, kofar gidan Alhaji Aliyu ya cika d'an kam da d'an Adam abokai na kusa dana nesa, sai kayi da gaske kake gane wanda kake nema, maroka sai aekinsu sukeyi.
Can kusa da liman na hango taurarun wato Ahmad da Sadeeq komai nasu iri daya harta agogo sunsha kwalliya cikin wata d'anyar shadda Ash colour sai Hula da takalma bakake sai fitar da wani sihirtaccen kamshi sukeyi suna kyalli.


shelar dana jiyo ne ta tashi hankali, yasa na kara kutsawa don tabbatar da abunda kunne na yaji mun, tabbas haka ne An daura auran Zainab Kabir (Hanan) da Sadeeq Nasir akan sadaki naira dubu d'ari.
mikewa sukayi fara'a fal fuskar su, suna gaisawa da jama'a,ana masu murna, bani kadai na shiga rudani ba har mutane da yawa a wurin.


Tofa Reader's kunji wata sabuwa.
Majidad'i✍🏻




*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
*____________________________________*


*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*


πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*DAFIN SO*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


Story and writing by
*Maryam Ismail*


*MAJI DAD'IN KAINUWA CE* ✍🏻


facebook
Maryam ismail(maji dadi)
Inster
maryam maji dad'i


Page 99 to 100


Radau haka taji shelar daurin auran ta, a kunnen ta, wasu hawaye suka wanke Fuskar ta, ta rasa gane shin na farin ciki ne ko kuwa aka sin haka?, tabbas tasan tayi rashin wanda take so har abada, amman tasan Sadeeq ma ba daga baya ba, tashin hankalin ta shine idan Umma taji ya zata dauki abun, sai dai kuma tana farin ciki donta auri wanda yake matuk'ar son ta.


Umma kam mutuwar tsaye tayi, ko dai Kunnen ta ne beji mata daidai ba?, Auran Ahmad akeyi yau ba na Sadeeq ba, rud'ani ta shiga sosai, waya ta dauko ta soma kiran layin Daddy, baya amsawa ,haushi taji ta yi jifa da wayan,safa da marwa kawai takeyi duk ta rasa meke mata dad'i.


Bayan lafawar mutane, Daddy suka tara meeting din gaggawa wanda kowa ya halar ta, tun daga y'an gidan su Ahmad, Sadeeq kai harda na su Hanan.


Cikin nutsuwa take shigo wa, babbar lufaya ta yafa sai zuba kamshi take yi,gefan Umma ta zauna kanta na kallon k'asa ta gaishe su, amsa sukayi tare da saka mata albarka.




Sai lokacin Daddy yayi gyaran murya, aka bud'e taro da addu'a sannan yace "Nasan da yawa cikin ku, kuna dauke da tarin tambayoyi akan sabon Al'amarin da kuke ji yanzu, amman idan kuma kuka tuna komai Allah yana iyawa, to ba zai zama abun mamaki ba, kamar yacce kowa ya sani ansa aure da niyar Ahmad amman kuma Allah da ikon sa sai ya koma akan Sadeeq, ina so ku sani dama Allah ya nufa Hanan matar Sadeeq ce ba Ahmad ba, hakan ya faru ne ta dalilai, da azo a samu matsala gara kar a fara".
Nan Daddy ya fad'a masu komai ya faru da yacce akai auran ya koma kan Sadeeq, Alhmdllh kowa ya gamsu da baya nan sa.


"Ae ba wata matsala indai Hanan ta amince, don ni ita nafi ji, duka da Ahmad da Sadeeq duk yara na ne ,fata na Allah ya basu zaman lafiya "Umma ta fad'a.


Sosai Hajiya taji dad'in karar da Umma tawa yaron ta, wanda bata yi tunani ba, albarka tasa masu tare da yiwa Umma godiya.


"To Alhmdllh tun da kun fahimta, sai dai ina rokon ka Ahmad daka fitar da Mata, zaman ka haka nan bazai yiwu ba, karka bani kunya "Abbu ya fad'a (baban Sadeeq).


Sosai sukayi godiya, sannan aka tashi taron cike da so da kaunar juna, kamar Family d'aya, da yamma aka kai amarya dakin ta, washe gari akayi walima, Ahmad yasa Umma zata masa magana amman sai ta share shi,shima haka yaci gaba da rayuwarsa cikin jin dad'i .


B'angaren Amarya da Ango kuwa hankali kwance suke zaman lafiya, Sun fahimci juna, suna rayuwa cike da girmama juna.


A gurguje pls


After 6 year's




Yara ne maza masu matuk'ar kama da juna, ga shegen wayau, kamar yaran larabawa, komai nasu iri d'aya, ball suke halbawa a cikin makeken Gate din gidan, karar motar da suka ji ne yasa sukayi wurin motar da gudu suna "Appie oyoyo ",cikin sauri Faruq ya fita a motar ya rungumi yaran tare da d'agasu Sama yace "Oyoyo my twin's "kallonsu yayi sosai sannan yace "Anif waya saka ball?"


Kyakyawan yaron da aka Kira Anif wanda daka gansa kasan be cika hayaniya ba yace "Just ina gwadawa ne ".


Jansu yayi zuwa cikin gida, anan suka samu Mahmoud yana ta aekin game a system yanzu ya zama saurayi yana JS 2.


da gaggawa ta safko daga stairs tace "Mahmoud maza dakko mun Anif, Ball fa yake yi, yasan baya da lafiya kuma "


Sai lokacin ta lura da Faruq dake dauke da yaran, murmushi tayi tace "Appie sannu da zuwa, harka dawo? ".


kallonta kawai yake yi, tayi masa matuk'ar kyau, sanye take cikin dogon riga na material Pink colour Sosai kayan suka Karb'i jikinta ga daurin zara buhari datayi, sosai ta kara fari da kyau tayi d'as abun ta ga kibarta daidai kwanin sha'awa.


Sauke yaran yayi yace "eh Aunty na dawo ".


kama kunnen Anif tayi "Ahmad bana Hana ka Ball ba? "


"aushhh Aunty kad'an nayi, banyi gudu ba, am sorry to "Anif ya fad'a.


Janye yaron yayi yace "Amira aeko mutuwa tana kunyar idon mahaifi, karki cirewa yaro na kunne ".


Dariya Mahmud yayi yace "Aunty muyi tafiyar mu, idan Appie yaga twin's ko kulamu baya sonyi".


Haka dai suke ta fira gwanin burgewa, kafin kowa ya kama gabansa.


******


da gudu ya fad'o masa ya fige tab din dake hannunsa, shiru yayi idonsa k'asa can kuma yace "Stop disturbing me pls, i hate that nonsense "


Zaro ido Arif yayi a fusa ce yace "u call me nonsense,am not i think u are "


wani uban naushi Anif yawa Arif a baya,yana d'agowa ya rama shima, jin hayaniyarsu yasa Jannat shigowa d'akin ,da sauri ta rike hannun Anif tace "what's that, bana hanaka dukan sa ba "


"Aunty he call me nonsense "Arif ya fad'a.


Cikin tsawa Anif yace "u did First, who ask u to come here"


"stop that, bana son wannan fad'an ranku zai b'aci yanzu kam ".


naushi Anif ya kaiwa chair din dake gabansa sai hawaye shar shar, bakin ciki ya dame sa an hanashi ya rama, barin d'akin kawai yayi don tsabar takaici.


ji tayi har cikin ranta bata ji dad'i ba, don gaskiya tana matukar son Anif kuma tasan baya da rigima zaku iya wuni a wuri be tanka kaba tasan Arif ya tsoka nesa, to amman bata da yarda zata yi.


"Arif ka daina tsoka nan sa, bana son kuna rigima ".


Bude baki yayi zaiyi magana da tsawa tace "keep quite boy".


Ta fita tabar masa dakin.


Majidad'i✍🏻
stylish Star ✨




*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
*____________________________________*


*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*


πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*DAFIN SO*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


Story and writing by
*Maryam Ismail*


*MAJI DAD'IN KAINUWA CE* ✍🏻


facebook
Maryam ismail(maji dadi)
Inster
maryam maji dad'i


Page 101 to 102




Tun da ya dawo gidan bega Anif ba, tun daga dakinsu yake kwallah masa Kira "Anif, Anif, my Son Why are you "shiru beji motsin kowa ba, da Jannat yaci karo, "ina Anif? "tambayar daya jefa mata kenan, kauda idonta tayi "bansan ina yake ba "ta bashi amsa a takaice, wani wawan kallo ya jefa mata "amman ae kinsan ba lafiya ne dashi ba, kuma kika barsa, bazaki iya neman sa ba "kwafa yayi, ya wuce bayan gidan, enterance na lambun gidan ya shiga, can ya hangosa mak'ale bayan flowers sai gyarman sanyi yake numfashinsa na fita a sassarke, da gudu ya isa Wurin sa yana jijigasa, idanuwansa harsun canza kala, daukarsa yayi da sauri ya fito zuwa compound na gidan driver din Ammi yake kwallahwa Kira, har riga rigan fitowa Ammi da Jannat, "lafiya Kake kwallah wannan kiran haka? ",turus tayi ganin Anif a Hannun sa "subuhanallah meya samu Ahmad din ","ki tambaye ta Ammi "ya kare maganar yana jefar Jannat da harare, Key ya fizge daga hannun Bala ya fad'a motar ya fizgeta da uban gudu, cikin gaggawa Gate man ya bude masa, shikam yayi gaba, "wai me yake faruwa ne Maryama?, meya samu yaron ne? "
Shiru tayi tana raba ido, "Ammi nima ban gansa tun dazu bafa "ta bata amsa.
"maza dauko mayafin ki da Key din mota ,mu bisa ",da gudu tayi daki ta dauko hijab, dakin Ammi ta shiga, Ibtisam ce kawai a dakin bata kulata dame take fad'a ba ta zari Key tayo waje, ita ke driving din kai tsaye asibitin su Dr Salim suka nufa, mintuna kad'an suka kaisu, a reception sukayi tambaya, aka basu amsa yana Emergency, tun daga nesa suka hango Faruq yana ta safa da marwa da sassarfa suka isa, "ya jikin sa? "Ammi ta tambaya, goge zufar kansa yayi "abunda nake jira kenan "ya bata amsa.
Ta glass din wurin Jannat ta hango yaron ta likitoci a kansa harda abun tai makon numfashi ,tuni hawaye suka wanke mata fuska yaron da take masifar so kamar ranta, shine yake wahala haka saboda saka cin ta, tuni ta rude tana karanto ko wacce irin addu'a tazo mata, ganin ya yunkuro kamar zai dai na numfashi, bata san ta Saki kara ba, tana bubbuga Glass din kofar shiga take nema, da sauri Faruq ya rike ta "oya keep quite, bana son shirme anan ","Appie kaga yana wahala fa, mutuwa zaiyi ya barni, idan ya mutu zan bisa Allah, kace ya tsaya don Allah karya barni bazan kuma bari a b'ata masa rai ba ".
"shhhhhii nace kiyi shiru

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login