Showing 6001 words to 9000 words out of 33116 words
Chapter 3 - DAFIN SO Document Complete By maji dadin kainuwa.txt
zafi da zugi suka ziyarci kuncinta tuni shatin hannunsa suka fito a kumatunta,hawayene sukaci faba da zarya akan kyakyawar fuskarta data kade tayi jajir.
"Ke yanzu Jannat wannan rayuwa?,kina zubar mana da mutunci yanzu wani ya ganki a hanya miye banbancinki da masu tafita Church, baki da aeki sai shigar kafurai har ki zagaye garinnan bakijin komai,anya kuwa kina da cikakken hankali" ya karashe maganar yana zare belt din wandonsa.
"Lafiyanta qlau Sulaiman,iskanci ne,nayi nayi tabarsa kayannan tak'i,amma laifin Abbanku ne tunda ko jiya saida ya siya mata wasu wallahi duk abunda Janna ta zama laifinsa ne ,so aeba hauka vane" Momy ta karashe maganar tana zabga mata uwar harara.
A bazata saidai jin saukar Belt rayi kota ko ina tuni ta rude ta rasa wurin sosai ihu kawai take saki tare da neman agaji,a guje Sawam ya fito "Yaya don Allah kayi mata hakuri".
" barnan kona had'a dakai wallahi"ya vashi amsa a hassale
"Wayyo Allah na ni Maryama na shiga ukku na lalace,Sule mai kake shirin yiwa takwarar tawa ,mugu azzalumi ka bigi Aysha gata nan tana kallonka karka kuma bugunta mugu mai kama da kumurci" Inna take fad'a da kuka wewewe.
A rude Momy ta nufota"inna don Allah kiyi hakuri ".
Tsaida kukan tayi cak tana bin Momy da mugun kallo" yau kaji munahinci Anya Aysha kinason ganin annabi kuwa,yarinya Ku daura mata karan tsana komai tayi ba daidai ba,ki zuba ido wannan gardin banzan yaita zabgarta,wallahi bari Audun ya dawo zaki Sani"
"Nifa kada ki kara cemin gardi wallahi"
"Sule nace ubanka ,yo kai menene inba gardin ba mai lasisi kuwa,ko nima dukana zakayi hatsabibin marar kunya,mai bak'ar zuciya"
Bude baki yayi zaiyi magana Hannu Momy ta d'aga masa,a dole ya hadiye maganarshi tare dajan tsuka yana jefawa Inna harara.
"Kai Sawa (Sawam),maza kama ta mu tafi".
Jannat kam kuka kawai take ruzga haka sawam ya kamata suka tafi d'akin Inna ,ta had'a mata ruwan wanka tanata sababi da masifa.
***********
Kallon idon yarinyar yakeyi kuri dason tuno tabbasa ya tab'a ganin mai wannan idon da irin kallonnan tuni ya Lula duniyar tunani.
" aekin kenan kallon wad'annan mararsa aekinyin maza sauyamun tasha bazan iya jurar ganin wannan rashin tarbiyarba yarinya Karama ta bata rayuwarta ae banga amfanin boye kanta da takeyi ba gara ta fito ta ida saida kyawunta ga mazan waje"Umma ta karashe maganar Rana zama
"Um um humm ae da yake ke Uwar data haifesace ya canza,Niko ae ko kallo ban isheshiba saidai ya tareni da wancan mugun kallon nasa yana tsotsar baki irin na y'an iska" Granny ta fad'a tana bankawa Ahmad harara.
Shima hararar ya bita dashi ya kuma tsareta da idanuwansa.
*Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe*
*ALKALAMIN MARYAMA* βπ»
Pls
Vote
Comments
And share
ππππππππππππΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉπΉ
ππΉππΉππΉπ
ππΉππΉππΉ
ππΉππΉπ
ππΉππΉππΉππΉ
*DAFIN SO*
Story and written by
MARYAM ISMA'IL
*MAJI DA'DIN KAINUWA CE* βπ»
*FITATTU SHA BIYAR (15) 2020*
*LITTAFAN MARUBUCIYAR*
SANADIN GATA
YAUDARA KO BUTULCI
HANAN
DALILIN SO
ASALI NA
TABON 'DA NAMIJI
ADDINI NA
SO 'DAYA
AND NOW
*DAFIN SO*
ππΉππΉππΉππΉ
*Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
*
___________________________________
*πKAINUWA WRITERSβπΌ ASSOCIATION*π€π»
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
Page 21 to 25
"Kaini masha Allah, kurwata kur wallahi ,ka wani tsareni da mayun idanuwan nan naka mararsa fasali da Kyan gani" Granny ta karashe maganan tana bankawa Ahmad harara
Remote ya dauka tare da sauyawa Umma tashan ,sannan ya juyo da kallonsa ga Granny "waike ina ruwanki da harkana,mata kin matso ga kabari amma bala'in sa'ido bazai barki ki zauna lafiya ba,you're disturbing me fa Granny".
" kwal ubanka Madu ,ni kake cewa tabin(disturbing), yaro ka zauna ka zageni tsab to wallahi baka isaba ,muna fiki kawai ki ganshi sululu amma ya dage da zagin wacce ta haifi ubanshi kuma kana kirana wani Grandi can don mugunta,to ba yafewa zanyi ba".
Harga Allah maganan da yayi da farko tasa ya gaji sosai donshi ba dabi'arshi bace dogon magana ba,saidai Granny na damunshi tana zame masa ciwan kai ga gulmar tsiya"kada ma ki yafe d'in"ya bata amsa.
Sallamar Alhaji Aliyu shiya bata damar bata ansa kafin ta ansa sallama saida ta nunashi da yatsa"wannan ko Madu gashi nan ya shigo toda Ali kake tsohwan marar kunya".
Shikam Alh Aliyu dariyace keson kwace mashi don tabbas yasan halin nasu ne suke bugawa,cikin sauri Ahmad ya karbi jikar Baban basa yana fadin"you're welcome Abee".
"Thanks my Son".
" welcome back Abee"Umma ma ta fad'a tana d'an risinawa.
Saida ya zauna k'asa kusa da Granny sannan ya amsa mata ,kafin ya juya kallonsa ga Granny "Mama sannu da gida".
" nikam ina ganin masifa gidannan,yo bakuso inji kuna zageni ko to da kuka kai k'arata ga Alin dukana zaiyi ko Yaya,kuita wani shegen yaraye da babu dalili ,kawai kuyi mashi haye gaskiya bakuji dadi ba,kai Amadu kalli Ubanka a k'asa koshi biyayya yake min ballantana kai na baya dana rena, wannan yaro anya bak'in halinka zai bari ka samu mai sanka ko".ta karashe maganan tana rike haba.
A rayuwa babu abunda Ahmad ya tsana sama da surutu sosai yake takura nashi, kanshi ne ya soma alamar ciwo mikewa yayi tare da nufan part dinshi kad'an ya juyo yace"wannan d'in haihuwarshi kikayi ae"ya karashe shigewa part dinsa yana saluting dinta.
"Ka k'amewa Hauwa ,d'an banza nasan maganinka gidannan,badai baka da kunya ba".
Umma da Abee kyau dariya ke cinsu ba halinyi,yanzu Abu ya dawo kansu,dole suka gumtse.
" yauwa Aliyu sai yanzu na samu damar ansa gaisuwarka,sannu da dawowa,maza tashi kuje kaci abinci ko ka huta,Hauwa tashi ki kula da mijinki nima bacci zanje nad'anyi kafin na shiryawa Mishkili tsiya sai yasan yayi dani".
Da"to "suka amsa tare da mikewa sukayi part dinsu itama wurinta ta wuce tare da kushin kid'awa tana lumshe ido.
Tsaye yake cikin toilet yayinda ruwan shower ke zuba bisa jikinsa,gashin kanshi yayi luf gwanin burgewa,kyawawan idanuwansa a lumshe ga zarazaran eyelashes da suka kara k'awa fuskar tashi,towel ya dauro ya kuma rike d'aya yana tsane ruwan dake kanshi,kwata kwata ya rasa meke damunsa motsi kad'an ita yake gani duk Inda ya juya ta kasa v'acewa tunaninsa,kyakyawan murmushinta kawai yake gani,tuni zuciyarsa ta soma azalzalarsa akan son sanin wacece wannan yarinyar kuma mai yasa ya damu da ita,So ne zuciyarsa ta vasa amsa," kai no,bashi baneba"yaba kansa Amsa da sauri,yanke shawarar ya kira Sadeeq ya tambayesa ya So yake,wayarsa ya dauka tare da dannawa Sadeeq kira.
Bugu d'aya ya dauka tare da fad'in"Angon Granny sha mamaki".
"Mtswww banfa son iskanci ,mu had'u Royal nan da 1hrs".
Murmushi Sadeeq yayi shi wannan iko na Ahmad na bashi mamaki " ina wani abu kad'an".
B'ata fuska ya kumayi"to ka kwana kanayi,kasan bans son jira"yana fad'in haka ya kashe wayarshi tare da cillar da phone din a bed.
Murmushi kawai Sadeeq yayi ya mike tare da fara shiri.
Zaune yake cikin hadadden wurin hutawar yana duban tsadaddiyar Rolex din agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa ,yayi kusan 5mins kenan tsaki ya kuma saki lokaci na barkatai donharya kufulu.
"Am very sorry friend, but am here" Sadeeq ya karashe maganan yana zama a chair din dake fuskantar ta Ahmad.
Murya can cikin makoshi yace"yazan gane inason wani".
Wani shu'umin murmushi Sadeeq ya saki yana kuma bin Ahmad da kallo sannan yace"As how".
Tamke fuska Ahmad ya kuma yi yace"will u answer me or I shall go,ina da abunyi".
"Kullun bazaka canzaba uban y'an zuciya,alamomin so suna farawa ne ta hanyar tausayi,nuna kulawarka akan Wanda kakeso kullun kana son kasancewa tare da shi,wannan ma ya isheka ka gane halin da kake ciki Ahmad".
D'an zaro dara daran kyawawan idanuwansa yayi tare da fad'in" u mean am in luv with her,kai it can't be possible Friend "ya fad'a yana mai dora yatsun hannunsa akan goshinsa tare da cije cute pink lips dinsa kamar zai huda.
" Allah na gode maka yau Granny ta zub ruwa k'asa Tasha ,Allah yasa Hanan ka fara so yarinyarnan na sonka amma kaita ja mata aji,shegen kaya.
Wata Uwar harara ya shiga jefawa Sadeeq din "karka kuma wannan kuskuren na had'ani da that stupid girl guy", mikewa yayi ko sallma basuyi ba ya shige motarshi ,had'a kanshi yayi da sitiyarin mota yanajin bugun zuciyarshi na k'aruwa ,shi kanshi yasan zuciyarshi nada rauni bata da karfin daukar abu,ba komai take iya jurewa ba sakamakon tunda aka haifeshi yake tare da matsanancin ciwan zuciya,ji yayi koda so d'aya tak yana kuma son ganin wannan yarinyar data hargitsa dukkan wani tunaninsa tabbas indai haka so yake to yanayiwa yarinyar so mai tsanani Wanda yakejin bazai iya rayuwa babu itaba,ganin Sadeeq ya nufo motar yasa ya tada mota yana d'aga masa hannu.
" Allah ya shiryamun kai Ahmad u will never change kullun iskancinka k'ara gaba yakeyi"shima motarsa ya Shiga ya tada ya nufi harkokin gabansa.
*************
"Audu ae gwara aka dawo,dama zaman jiran ka dawo daga tafiya nike wallai"Inna ta fad'a fuska daure ita a dole ranta bace yake.
" meya farune innata?"Daddy ya tambaya.
"Meye ma be faruba,shin dama daka haifi Maryam ka d'anka tarbiyarta ga Sule ne koko,k'aton banza dashi ya damki y'ar ficiciyar yarinya ya dunga jibga ".
" wai Inna me kike nufi ne,kina ganin ae yarce ta fita da irin dadewar da tayi shin cikunku wani ya damu da ina take zuwa ko me take aekatawa y'a mace face haba Inna karki rika kasa fahimtar me nake fad'a"Sulaiman ya karashe magana a tsawace.
"Dakata Sulaiman ,Nina Haifi Jannat kuma nasan tarbiyar y'ata nasan me zatayi da kuma abunda bazatayi ba na tabbata bazatayi wani abu marar kyauba ,don Allah ka tausashi zuciyarka akan y'ar uwarka ka daina mata mugun duka" Daddy ya fad'a.
A fusace Sulaiman ya mike yana harara Inna yace"gaki gata nan ina jiye maku lokacin da zaku gane cewa wannan ba gata kuke nuna mata ba lokacin da nadama bata da amfani gareku ,ninan Sulaiman na cire hannuna akan lamarin Jannat komai taga dama tayi wallahi na gama bi ta kanku".
"Eh kuma a fito da matar Aure nanda sati d'aya gwauran banza dakai" Inna ke fad'a.
"Aure kam zanyi kodon na nisanta da ganin abunda kukeyi,ki zuba ruwa k'asa kisha gobe za'a saka bikina,kuma ki fita harkata salan na kawo matata kice zakimin iyayi " yana zuwa nan ya fice a zuciye,Sagir na kiranshi amma ko waigowa beyiba yabar gidan.
Haka suka watse daga parlon kowa da abunda yake sakawa aranshi,Momy kam tasan halin Sulaiman da bakar zuciya tasan ko za'a mutu ya fita daga sabgar Jannat kenan ko me zatayi bazai tsawatar dinba,kuma tasan yanzu tarbiyar Jannat nadab da rushewa saboda illar gatan data samu.
Har sunyi shirin kwanciya amma bacci Sam ya kauracewa idonta Batayi niyar shiga maganar ba amma yanzu kam ta kasa hakura balle data biyo ta d'akin Jannat taji babu abunda takeyi illah waya da saurayi.
"Wai meke damunki kin kasa sukuni ko barci ya gagareki Momy" Daddy ya fada yana zama kusa da ita.
Murmushi takaici tayi tace"Daddy yanzu kana nufin kace bakasan meke damuna ba,be kamata ace kayi abunda zai raba kan yaranka ba ka nuna fifiko da soyayyar Jannat karara a fili,Daddy gaba ake dubawa,ko da fad'a zakayiwa Sulaiman be daceba ace kayishi akan Idon Jannat ba".
"An tab'a d'an so ko Momyn Sulaiman,nasan kina matukar son Sulaiman saidai ni kuma bazan zuba ido ya nemi kashemin tawa y'ar son ba,komai Maryam tayi a sanar dani zanyi hukunci da kaina,amma Ku barta tayi abunda takeso ,da kuke maganar shigar da takeyi duka shekarunta nawa, meye abun sha'awa a jikinta ga wani ,please mubar wannan maganan Ku daina takurawa Mamata".
Hawayen takaici ne suka zubowa Momy tasa hannu ta share tace" eh inason Sulaiman saidai ban nuna banvanci a tsakanin yara na ba,kuma ban hanashi tarbiyyah me kyau ba,wallahi Daddy ina guje maka ranar dana sani ranar nadamarku".
Mikewa Daddy yayi yana sababi kada tayiwa y'arsa mugun vaki,gashi zata fara weac wai addu'a take buk'ata gaba d'aya dakinma ya bar mata.
Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karashe
*ALK'ALAMIN MARYAMA* βπ»
Please
Vote
Comments
And share
ππΉππΉππΉπ
ππΉππΉππΉ
ππΉππΉπ
ππΉππΉππΉππΉ
*DAFIN SO*
Story and written by
MARYAM ISMA'IL
*MAJI DA'DIN KAINUWA CE* βπ»
*FITATTU SHA BIYAR (15) 2020*
*LITTAFAN MARUBUCIYAR*
SANADIN GATA
YAUDARA KO BUTULCI
HANAN
DALILIN SO
ASALI NA
TABON 'DA NAMIJI
ADDINI NA
SO 'DAYA
AND NOW
*DAFIN SO*
ππΉππΉππΉππΉ
*Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
*
___________________________________
*πKAINUWA WRITERSβπΌ ASSOCIATION*π€π»
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
Page 26 to 30
Rushewa da kukan bak'in ciki Momy ta kumayi ta rasa wannan wanne irin gata ne,fatan ta dai Allah ya shirya mata Jannat ,in ta samu akasin hakan batasan ya zatayi ba kuma.
Washe gari tun safe suka shiga hidiman had'a kayan bikin Sulaiman komai a ranar suka kaishi har akwati sannan aka tsaida ranar aure nanda sati biyu.
(π€£π€£sulen inna za'a angwance sai murna nake,dikda yayiwa gidan yaji).
Zaune suke a main parlo fira kwai sukeyi yayinda Sagir keta fama da Imam yaronsa ya hanashi sakat gashi so yake ya fita.
Cikin natsuwa ta soma safkowa daga stairs din gidan zuwa parlor kowa da kallo ya bita ,sai lokacin nima na soma kallonta,sanye take da black jeans sai pink top mai irin budaden wuyan nan ,gashin kanta tubke tsakiyar kanta sai wata hadaddiyar hula black colour, hills ne sosai kafanta bakake sai zaran dauresu pink shima yayinda fuskarta ke dauke da lite makeup ba kad'anba tayi kyau sai wata jakar goyon bak'a data Goya ,har gabansu ta safko tace"Momy zanje na dawo yanzu kinji".
"Yanzu Janna haka zaki fita,kalli shape din jikinki,wai meke damunki ne,kuma gidan ubanwa ma zakine" Momy ta fad'a.
Turo d'an karamun bakin ta tayi tana bin Momy da kallo murya cunkushe tace"bakinsan mun fara lesson a scul ba".
"Yanzu kuma mai shigar nan tayi ,ga wannan yarinyar cikin kayan dana bata jiyane meye aibunsu ae sun rude ko ina kuma a mota za'a kaita ko,jeki Mamana" Abba ya fad'a.
Rungumar Abban tayi"I love u Daddy so much".
"Love u too,Allah ya tsare hanya" ya fad'a yana shafa kanta
Hanyar fita ta nufa sora kad'an ta fad'awa Sulaiman dake shigiwa gidan,a matuk'ar tsorace taja baya tana hak'i murya na rawa take fadin"Yaya am sorry pls"
"Mtswwwww" yabi ta gefanta ya wuce .aeki da gudu ta sheka waje, driver yaja motar suka wuce School,don Sawam ya fita.
Momy kam dakewa tayi bata kuma kallon Daddy ba don bak'in cikin yayi mata yawa.
Cike da ladabi Sulaiman ya gaeshesu suka amsa,yayinda Sadiya matar Sagir ta gaeshesa,ya amsa cike da fara'a,yasa hannu ya dauki Imam yana fadin"oh my sweet boy".
"Eh aefa yaranka sun bani da yarayen banza na yahudawa dolema su koya ,kai ammafa ka burgeni da zakayi auran nan ko kaima kaga kwanka a duniya my tab'a Musa albarka".
Waro ido yayi" ki tab'a yatonwa ki koya masa sa ido,wallahi badai d'ana ba kyaji dashi dai,aeki ganinsa ma bakyayi kinma ji"ya Kare maganar yana mikewa.
Kallon baka da hankali Inna ta masa tare da sakin baki tana tunanin iya ina rashin kunyar Sulaiman ta tsaya,takin Momy ya wuce a ciki ya sameta da sallama ya karasa gabanta ya duka tare da dora duka hannayensa biyu saman cinyarta muryarshi na rawa yace"Momy na meye damuwanki duk kika canza haka".
Murya na cracking ga hawaye cike idonta tace"Sulaiman,Jannat"sai kuam tayi shiru.
"Na rokeki Momy na kada kiyi mata kuka,kiyi mata addu'a ki jure,komai Jannat zatayi kinsan dasa hannun Daddy,amma don Allah kada kiyi mata kuka Momy,shiriyarta muke buk'ata" ya fad'a yana goge wa Momy idonta.
Murmushi tayi tana k'arajin soyayyar d'an nata a ranta"Allah yayi maka albarka ,kayi ma y'ar uwarka addu'a kaji".
"To Momy ni damuwarkice bana so,kuma ba fushi nike da itaba kawaidai harkarta ne bazan kuma shigaba" ya k'arashe maganan yana had'e ido kamar tana gabansa.
*******
Kwance yake rubda ciki akan makeken Bed dinsa,da kingansa zakisan cewa tunani kawai yakeyi yayinda zara zaran lashes dinsa suka kara kawata fuskarsa kasancewar idanuwanshi suna a lumshe,kamar an muntsinesa ya tashi da sauri tare da safko legs dinsa kasan bed din hannuwansu duk biyu yasa tare da dafe kansa yanajin zuciyarsa na masa zafi,ji yakeyi yau in be ganta ba besan yazai kasance bama.
Turo kofar dakin Ummu tayi ta shigo da sallama bakinta,zuba masa ido tayi ganin bemasa ta shigo ba,ajiye plate din hannunta tayi akan k'aramun table din dake kusa da ita isa wurinsa tare da zama tace"Son what's ur problem at all ka canza bansan meke damunka ba kuma,ni mahaifiyarka Ce kana da wacce ta fini da zaka fad'awa damuwarka".
Sai lokacin ya d'ago idanuwansa dahar sun fara canza launi ya kurawa Ummu Ido murya sanyaye yace"just pray for me Ummu".
Ji tayi itakam wannan hali na Ahmad ya fara isarta duk ya ida juyewa dama can gashi da murd'ad'an hali ballantana yanzu kuma,plate din abincin ta jayo tana bud'ewa,white rice Ce sai stew da namu a ciki,saurin kauda kanshi yayi yana yatsine fuska.
"Oya look at me Ahmad Kasan Allah u must eat today,kai kullun babu abunda ke baka wahala sama da cin abinci ,tona fara gajiya" Ummu ta fad'a tana mika masa plate din ta hade rai.
Badon yasoba ya k'arba'a ya fara jujuya Spoon cikin abinci da hankali yake sakashi bakinshi yana taunawa kamar me cin magani,da kyar yaci spoon 5 ya shagwabe fuska yace "Ummu na Please".ruwa ta mika masa a glass cup yad'an kurb'a kadan yana kallon agogon dake manne cikin d'akin zunbur ya mike yace" I have to go Ummu,let me fresh up".
Batace mishi komaiba ta dauki plate din abincin tabar dakin,shikam wanka yayai ba'a dauki lokaci ba ya ahirya ciki. K'ananun kaya yayi maaifar kyau sai zuba kamshi yake,inka Kalli Ahmad bashi da maraba da larabawa inhar ba magana yayi ba,key din mota ya dauka ya fito waje yana duba Mobile phone nashi,tsaye yayi cak ganin Granny gabanshi ta zuba mashi ido,zaro daradaran idanuwansa yayi tare da dafe kai da hannunsa yace"chaii another problem woo".
"Au iyar shegen yakai nan Amadu ni kake kira hirablam(problem), babu abubda ka iya daga wanka sai a canza kaya abi wannan inuwa ta kare a dawo gidan uwa,k'aton banza ba aure".
Hade fuska yayi lokaci d'aya yana hararta yace" fitarmun a hanya,baza'ayi auranba"yana zuwa nan ya rab'a ta gefanta ya wuce.aekam da Sauri ta juyo tana fadin"kawa hauwa rashin kunya,fitsararre kawai zaka dawo ka sameni nasan maganinka ae"tana zuwa nan ta wuce tana sababi.
Shikam motarsa ya Shiva