Showing 1 words to 3000 words out of 21013 words

Chapter 1 - FAHIMAH Book 2 End COMPLETE Writing by Sumayya Abdulkadir Takori kabara .txt

 Da kyar ta iya mikewa ta soma dafa bango, tana mikewar jini na tsinke mata. Daga nan sai wani duhu ya mamayi ganinta, ganinta ya dauke gaba daya ji ka ke yif! Ta fada a kan Fahimah da ke jan minshari sabida dadin A.C.
A firgice ta farka, ta janye Amrah daga kan kafafunta tana salati. Ta mike jiki na rawa ta kunna kwan lantarki. Nan ta ga jini na fita a jikin Amrah, kuma ko motsi ba ta yi. Fahimah saboda gigicewa a guje ta fita dakin Ammi tana kwala mata kira tun daga falo.
Hatta Baba Talatu da ke baskwata sai da ta jiyo kiran Ammi da Fahimah ke yi. Babban tsoronta kada a ce ta kashe matar Uwais. Cikin barci Ammi ke jiyo ihun Fahimah yana doso dakinta, don haka a bakin kofa suka ci karo. Fahimah ta hada hannayenta waje guda kasan habarta kamar mai roko. Ta ce,
“Ki taimaka Ammi, Amrah za ta mutu a dakina, wallahi ban mata komai ba. Kawai tashi nayi na ganta a kaina jini na zuba. Na shiga uku Ammi…”.
Ammi ta ce, “Ke da Allah can shashasha, haihuwa ce”.
Ta ture ta ta wuce dakin nata. Daidai lokacin da Baba Talatu ma ta karaso. A tare suka shiga dakin suna ganin halin da Amrah ke ciki suka gane wannan haihuwa ta zo da tangarda.
Ammi ta ce da Talatu maza dauko min wayata da mukullin mota”.
Talatu da gudu ta juya ta dauko. Ammi da Talatu suka ciccibi Amrah suka yi waje. Ammi na cewa, Fahimah ta dauko jakar da Amrah ta zo da ita gaba daya ba za a rasa kayan jariri ba. Ta biyo su.

Asibitin Standard suka wuce don komai dare ba a rasa likita, suna zuwa aka karbe ta da gaggawa. Dubawa ta farko likita ta ce,
“Amrah ba za ta iya haihuwa da kanta ba an samu matsala mai girma, sannan babyn a breach yake, abu mai sauki shine CS kawai don su ceceta ko babyn, amma ita ko babyn dole a rasa guda.
Sabida tsananin rudewa Ammi kalmar shahada ta ke ja. Fahimah kuwa sai mazari ta ke daga tsaye. Likita ya ce maza mijinta ko mahaifinta su zo su sanya hannu don lokaci ya kure babu wani taimako da za su iya yi mata bayan CS.

Talatu ce mai karfin halin ce da Fahimah,
“Ba ni wayar Ammi da ke hannunki bayan kin latso min uban dakina”.
Haka Fahima ta yi, ita mantawa shaf ta yi da wayar Ammi na hannunta don a gida ta baro tata. Ta lalubo lambar Uwais hannunta na karkarwa ta bai wa Talatu.
Bugu daya Uwais ya dauka don yana can kamar mai nakudar shima, yana jiran abin da zai biyo baya, me ya kawo Amrah gidansu har dakin Fahimah cikin dare haka, kuma ina Fahimar ta ke da ta barta ta daukar mata waya tsakar dare? Ya tabbata sha’ani ya lalace kam, da ya ji shawarar mahaifiyarshi tun farko da haka ba ta faru ba.
Yanzu da wane yare zai yi wa Amrah bayanin da za ta fahimce shi? Kuma me za ta dauki Fahimah? Ba za ta kara yarda da ita ba duk son da ta ke mata yau zai koma kiyayyah.
Talatu na kira yana dagawa, a nitse ta gaya masa halin da ake ciki da bayanin da likita ya yi. Uwais ji ya yi kamar kwarankwatsa ta fado a kansa, ya ji kamar ya yi fiffike ya ganshi a Nijeriya. Babynsa! Gudan jininsa da ya kwallafa wa rai yau ga kuskurensa zai yi sanadinsa.
“Ba ni likitar”.
Kawai ya ce cikin tashin hankali.

Ya gaya mata ba ya kasar, sannan iyayenta ba sa gari, ya amince a yi mata CS din da duk wani taimako da ya dace. Ya kara da cewa,
“Likita ki taimake ni kada in rasa kowanne a cikin su. Don dukkansu ina so, and they mean a lot me. Kuma na yi mata laifi ina so in nemi gafarar ta… idan ta mutu a wannan halin bazan taba yafewa kaina ba.....".
Gaba daya muryarsa ta karye kamar ba Uwais ba. Bolded and courageous a komai. Likita bata tsaya doguwar magana dashi ba don ta lura ba'a hayyacin sa yake ba, suka shirya Amrah zuwa dakin tiyata.

******

"It’s a baby boy, amma bai zo da rai ba. The mother is still unconscious, za ta dawo hayyacinta in the next two hours in allurar barci (anaesthesia) ta sake ta, sai ku shiga ku ganta".

Siririyar nurse din ta fadawa Ammi, a lokaci guda ta mika mata jaririn nannade cikin farin shawul. Ammi hannu da jiki na rawa ta amshe shi ta bude fuskarsa su duka ukun suka zuba masa ido. Uwais sak! Fari sol bai debo komai a jikin Amrah ba. Hatta farcen yaron irin na Uwais ne.
Fahimah jin wata irin soyayyar jaririn ta yi, ko don kamanninsa da Uwais, ta kifa kai jikin Ammi tana kuka. Uwais na ta kira babu wadda ta iya amsa wayar sa. Ammi ta ce, Fahimah ta zauna ita da Talatu za su tafi da jaririn maigadi ya kira makwabta a yi masa sutura.
Ba su jima da tafiya ba aka gungura Amrah zuwa aminity. Da sauri Fahimah ta bi bayansu suka kwantar da Amraha kan gado suka yi mata duk abin da ya dace sanan suka fita.

Fahimah ta ja kujera daidai kan Amrah ta zauna. Tana karanta addu’a tana tofa mata. Ga karin jini ga na ruwa, tana da son haihuwa matuka, musamman da Uwais ya ce zai so ‘ya’yansu ne fiye da son da yake yi wa kansa.... Amma in haka haihuwar ta ke lala - lala ta hakura. Lallai wannan shi ne kafa daya a duniya, kafa daya a lahira.
Ta tuno uban jinin da ta ga Amrah na zubarwa, wani matsanancin tsoro ya kara kamata. Tunda dai Allah ya taimake ta ba ta yi cikin ba, to ba za ta kara yarda ta yi abin yin cikin ba. Ta barwa Amrah Uwais su yi ta haihuwa, tarewar ma ta fasa ba za ta yi ba. Zata cigaba da zama da Ammin ta.


Wajejen karfe goma na safe Amrah ta bude idonta a hankali. Kafin idanunta su washe a dakin su sauka a kan jinin da ake kara mata. A lokacin ne ta fahimci a kan gadon asibiti ta ke. To me ya kawo ta asibiti ita da ta kwanta a gadon Fahimah za ta yi barci?

“Masha Allah, kin tashi Aunty Amrah? Bari in kira likita”. Ta ji muryar Fahimah a gefenta.
Muryar da ta tado mata da ainahin dalilin zuwanta asibiti. Da sauri ta kai hannu kan cikinta ta ji wayam! Da azama ta yunkura za ta mike, daidai lokacin da likitan ya shigo, Fahima na biye da shi. Da sauri ya maida ita kwance, ya ce, “Be careful Madam, akwai aiki a jikinki”. Sannan ya tambaye ta,
“Are you alright?”
Kai kawai ta gyada masa. Ta runtse ido da Fahimah ta zagayo gefen fuskarta, tana tambayar likita ko za a iya ba ta tea ta sha? Doctor ya ce, ta bari sai an jima, Nurse za ta zo ta ba ta da magani.
Tunda Amrah ta rufe ido ba ta kara budewa ba. Don ba ta son ganin Fahimah, ba kuma barci ta ke yi ba. Har zuwa lokacin da su Ammi suka dawo.
Ammi bata san Amrah ta farka ba ta tsaya tana gaya wa Fahimah har an binne yaron. Allah ya ba su wani mai albarka, Ya bai wa iyayensa dangana. Shi ma Uwais din yana hanya gobe duk da bai gama abin da ya kai shi ba.
Wasu dumammun hawaye suka biyo ta gefen idanun Amrah, Dan ta ya koma, duk wannan wahalar da ta ci akan rainon cikin, duk a dalilin bakin cikin Fahimah da Uwais? Ko Uwaisu ne autan maza ta hakura da shi yau, in ba haka ba bakin cikinsa shi zai yi ajalin ta.
Ta soma tunanin hanyar da za ta bi ta tsere kafin Uwais ya zo ya tadda ita. To amma da wanne ido za ta koma wa iyayen ta???

Wannan tunanin ya sa Amrah fashewa kuka wiwi a fili. Su ba su san idonta biyu ba, kuma sun dauka kukan na rashin dan ta ne da ta yi. Su basu san abubuwan sun ma zuciyar ta yawa ba. Da wanne zata ji?
Ammi ta karasa ta kama hannunta tana ba ta baki. Ta ce, “Ki yi hakuri Amrah, insha Allahu mai ceton mu ne. Ba ki ganshi ba kamar Uwais ya yi khaki. Allah ya yi wa iyayen da suka rasa ‘ya’yansu suna kanana babban tanadi a ranar gobe. Kada ki yi bakin ciki, ki yi addu’ar Allah ya bada rayayye mai albarka, kin ji”.
Amrah ko kallon Ammi ba ta yi ba, ta ci gaba da gunza kukanta. A ranta ta ce, duk abin da Uwais da Fahimah ke yi da sanin Ammi tunda ai a gabanta suke, and she is educated enough da za su yi irin wannan danyen aikin ba da saninta ba.
Me kuma za ta ce mata yanzu? Ai ta bar mata danta ke nan har abada ta aura wa farkarsa, ko su ci gaba da watsewar su.
Gaba daya sun kasa gane kan Amrah, tunda ta farko ta ki ci ta ki sha, sai kuka, sannan ta ki karbar lallashin Ammi.
Har dare suna tsaye a kanta suna lallami, amma ko uffan ba ta ce musu ba. Sai da Ammi ta koma ta kira babban likita ta ce ya bincike ta ko da wani abu da ke damunta daban, kada jininta ya hau.

Likita ya shigo, ya ce duk su ba shi wuri zai yi magana da Amrah. Ya ja kujera a gabanta ya zauna, ya ce, “Madam, may I know your problem? Na dauka ke musulma ce, kin san mutuwa tana kan kowa babba da yaro? Na dauka za ki yi tawakkali ki yi masa addu’a, ki roki Allah ya sake ba ki wani cikin gaggawa?”
Amrah na kuka ta ce, “Doctor ni farin ciki nake da Dan ya koma. Ko bakomai zai dandani irin bakin cikin da ya kunsa min. Tunda gashi nan a dalilin cin amanar da yayi min shima ya rasa abinda ya kallafawa rai.
Damuwata yanzu kawai yadda zan je Abuja. Ka taimaka min ka sallame ni a yau, kuma ka ba ni aron wayarka in kira direbana ya zo ya dauke ni”.
Doctor ya ce, “Babbar magana. Ba zan iya sallamarki ba sai jibi, a ka’ida in aka yi wa mutum aiki sai bayan kwana uku ake iya sallamarsa shi ma in an tabbatar babu wata matsala da za ta biyo baya. Advisably ki bar ni in yi wa Mamanki bayani cewa kina son tafiya Abujan da zarar an sallame ki, na tabbata za ta fahimta ta kai ki da kanta…”.
Da sauri Amrah ta ce, “Doctor ba abin da ya hada ni da su, kuma in ba za ka taimaka min ba wallahi ko a kan iska sai na tafi".

Ta ci gaba da rusa kuka. Doctor ya rasa ya zai yi da ita, da ma kuma yana da lambar Uwais da suke magana wadda waccan likitar data karbi Amrah ta bashi da za su yi handing over, sai ya koma ofis ya kira shi, ya yi masa bayanin halin da matarsa ke ciki.

Uwais ya rasa inda zai tsoma ransa ya ji sanyi, ga booking dinsa ma an ce ba zai samu ba a goben sai bayan kwana uku, na goben bai yiwuwa saboda hazo. Da kyar ya iya ce da Doctor ya kula sosai kada ya barta ta fita, har zuwa kwana ukun, wato ranar sallamar ta, zai turo matar Yayanta ta tafi da ita, ya tabbata za ta yarda ta bi ta.
Daga nan ya kira Jabeer, a yadda Jabeer ya ji muryar Uwais ya tabbata ba lafiya ba. Ya ce, “Jabeer, I donno from where to start, don ko kai ba za ka yi min uzuri ba balle Amrah. Amma wallahi ka yarda da ni ina da niyyar gaya mata ne da zarar na dawo, don in samu ta haihu lafiya. Sai kaddara ta riga fata. Yau ga kuskurena da rashin jin shawarar mahaifiya sun jawo na yi asarar babyna”.
Jabeer ya ce, “Hasbunallahu wa ni’imal wakeel, me ya faru haka Uwais?”
Uwais ya share zufar da ke yankowa daga goshinsa, ya kwashe komai ya gaya wa Jabeer, ya kare zancensa da cewa, “I never take it serious, (auren sa da Fahimah), kuma tunda na mallaki Amrah ban kara waiwayar zancen Fahimah ba.
Na yi duk iya kokarina a kan Amrah ta fahimce ni ban iya rayuwa babu macen aure, ta dawo B.U.K mu ci gaba da rayuwarmu. Amrah ta ki fahimtata da gangan, ta sa kafa ta yi tafiyarta Malaysia ta bar ni. As a man like me na san za ka fahimci halin da na kasance kuma na san ina da wata matar.
Amma wallahi Jabeer ban taba tunanin auren zai je ko’ina ba shi ya sa na dauki lokaci ban gaya wa Amrah ba, sai kuma ga ciki ta samu mai matsaloli, sai na kara jinkirtawa da niyyar zuwa ta sauka.
Ban san ya aka yi Amrah ta zo gidanmu ba, har dakin Fahimah, har wayar Fahimah ta je hannunta. Daga nan komai ya lalace wanda I’m sure shi ne sanadin nakudarta.
I’m sorry Jabeer, wallahi ban yi da niyya ba, haka Allah ya nufa. Jabeer babyna da na kallafa wa rai ya zo ba rai, sannan Amrah na can ta tubure musu Abuja za ta koma. Bayan already na yi booking ina tafe in three days”.
Jabeer ma ransa ya baci sosai, amma sai ya yi hali na dattaku, ya ce, “Ka yi babban kuskure Uwais, kuma magabatanka ma sun yi kuskure tun a wajen neman auren Amrah ya kamata ku gabatar da wannan maganar, in ya so in yin yin, in barin-barin. Amma yanzu ka bata goma daya ba ta gyaru ba. Don ka san Daddy ba wai yana farin ciki da aurenku ba ne don dai ya ga Amrah na so ne ya hakura.
Don haka ni ban isa in rike Amrah a gidana ba tare da iyayen mu sun ji zancen nan ba, don Murjanatu ba ta taba haihuwa ba, ba ta san ya za ta yi da Amrah ba. Don haka in an sallame ta zan je in dauke ta a asibitin mu wuce Abuja”.
A sautin muryar jabeer Uwais ya tsinkayi bacin rai sosai, don dai yana kokarin dannewa ne. Babban bacin ran Jabeer wai a ce har shi bai gaya wa yana da wata matar bayan Amrah ba? Duk yadda suke da shi, ai zai iya gaya masa ma tun lokacin auren in ya so ya roke shi ya rufa asiri. Wannan itace abota ta hakika. Amma ina? A lokacin idon Uwais ya rufe da son mallakar Amrah anyhow.
Don haka yanzu kam yana bayan kowanne hukunci Amrah za ta yanke wa aurenta da Uwais don tana matukar sonsa, kuma ya yi betraying dinta a magana ta gaskiya.
Shi ya sa har kullum mota suke kuka da maza a kan rashin amanar soyayya, da gaske ne su maza ba su da tabbas in dai a kan mace ne. Amma why Uwais? Mutumin da ya ke yi wa kallon wanda ya fi kowa son Amrah? (in kina tunanin namiji na da tabbas a kanki to ki daina- Takori).
A yadda suka yi sallama da Jabeer a wayar ma duk da yana kokarin dannewa ya fahimci ransa ya baci sosai a matsayinsa na shakikin Amrah. To ina ga iyayenta da ita kanta?
Bai dora neman aurensa a bisa tafarki na gaskiya ba tun farko don haka he must try to be a man, ya yi dammarar facing every challenge da zai biyo baya kawai.

Duk maganganun da suke yi a kunnen Murjanatu wadda ke zaune a gefen sa. Bayan sun gama ta dubi mijinta sai huci yake yi. Murjanatu akwai ilmi, hankali da kyakkyawan tunani, don haka ta ce da mijinta Jabeer.
“Uwais abokinka ne na gaskiya wanda ya kamata a ce cikin kowanne hali ka tsaya tare da shi. Kada ka bi bayan kanwarka ka manta da darajar abokan taka. A halin yanzu he needs your support

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login