Showing 6001 words to 9000 words out of 21013 words
Chapter 3 - FAHIMAH Book 2 End COMPLETE Writing by Sumayya Abdulkadir Takori kabara .txt
na so ne, shiyasa na hakura aka yi. Amma ya yi da Umar Dikko dan Adamawa”.
Ya fiddo wayarsa a take ya kira Uwais amma ba ta shiga, ya yi ya yi ya kasa samunsa. Sai ya juya ga Jabeer,
“Ba ni shi almuri a lambar da ku ke magana”.
Jabeer ya soma bada hakuri, wata tsawa da ya daka masa ba shiri ya latso Uwais ya mika masa.
Uwais ya dauka Jabeer ne, don haka with much respect irin na wanda ya san ya yi laifi ya amsa. Sai muryar Babansu ya ji yana magana a matukar hasale.
“Kana magana da Umar Dikko Baban Amrah. Ina mai gargadinka da kada ka sake ka tako min gida, ka rubuta takardar sakin ‘yata ka ba wa Jabeer ya kawo min, ka ji na gaya maka. In ba haka ba kuwa kotu ce za ta raba ni da kai, na rantse daga nan har kotun kolin Najeriya”.
Ya kashe wayarsa ba tare da ya saurari Uwais ba, shima da ma bai da abin cewa, amma a fili ya sauke wayar sa, ya ce,
“Me ya yi zafi???”
Don so yana son Amrah har gobe, don she’s his first love. Wadda ya fara mallaka wa ragamar zuciyarsa ya ba ta dukkan so da kauna. Amma duk abun mutuncin da zai hada da cin zarafi, to fa Uwais ba ya daukarsa.
Ya yanke shawarar rabuwa da Amrah cikin wani hali na kaka-ni-kayi. Kafin Alh. Dikko ya kai ga taba mutuncin sa. Ya gama gane iyayen Amrah ba su son aurensu kaddara da rabo ne kawai ya kaddara auren. Ita ma Amran fama yake da ita a kan karan-kanta don ba ta dauke shi a bakin komai ba. Hakkokinsa na aure kuwa a gantale suke yawo.
Ammi ta yi gaskiya da ta ce, kyal-kyal banza ya daina dibanka. Halin mutum shi ne yake sa wa a so shi ba nasaba ko zubin halitta ba. Amrah ga nasaba ga zubin halitta, amma ta rasa iyaye masu dattaku, nasaba da asali ba ta yi amfani ba anan.
‘FAH-HIMAH!’.
Sunanta ya fado a ransa yana daga kwance. Ya wani irin lumshe idanunsa.
“Ita ko kara ya saka ya ce kada ta tsallaka ba za ta ko doshi hanyar ba. Ga iya soyayya in stylish. Komai cikin class da sanyin rai hadi da girmamawa. Ba ta da wayewa kamar Amrah, amma ta fi daidai da rayuwarsa. Tunda kuwa idan ya yi umarni za a bi shi, idan ya yi hukunci shi ne abin bi.
Me kuma yake nema a diya mace wanda bai samu a Fah-himah ba? Ya yarda Fahimah kyautar mahaifiya ce, kuma kyautar Allah a gare shi. Amrah kuma iznah ce kuma jarrabi a gare shi, duk son da yake mata da ita ma wanda ta ke masa rabuwarsu ita ce mafi alkhairi, domin zukata sun riga sun baci, ko an koma za a yi ta ganin juna da tsohon tabo ne.
Sannan upbringing na gidan su Amrah bai yi daidai da wanda yake fata wa ‘ya’yansa ba. Fahimah ita ce daidai da shi, daidai da komai nasa.
Sun samu tarbiyyah iri daya, raino da upbringing iri daya, wanda yake fatan ‘ya’yansa ma su taso a cikinsa…...
A bisa wadannan dalilan da ma wasu da dama, Uwais ya yanke shawarar rubuta wa Amrah saki ba tare da ya yi shawara da kowa ba, daga Ammi har Fahimah don ya san cikinsu babu wadda za ta goyi bayan haka.
Bai baro Switzerland ba sai da rubutacciyar takardar sakin Amrah a cikin takardunsa.
****
Yau Uwais zai sauka a Kanon Dabo, don haka Ammi, Fahimah da Talatu kowacce tana tsaye a kan kafafunta tun safe. Yau kwanaki uku ke nan Ammi ba ta komai sai gyaran Fahimah da kayan mata masu inganci wanda a baya ba ta samu damar hakan ba.
Musamman ta yi wa Hajiya Asabe waya, ta ce ta kawo gudunmawa, gobe ‘yarta za ta tare. Hajiya Asabe a ranar ta zo da babban shirinta har da dafaffiyar kazarta cikin romon maganinsu na Sokotawan usli.
Tun jiya Ammi ke ciyar da Fahimah nau’i-nau’in abin da zai kara ni’imtata, ya bambanta da sauran mata a wurin Uwais ko ya daina yo mata kwashe-kwashen ‘ya’yan masu kudi (ta bakinta), wadanda ba su san mutunci ba.
Fahimah ba ta san amfanin abubuwan da Ammi ke ta dirka mata ba, amma tunda dadi gare su a baki ba ta da matsala da su. Sai a daren ranar ana i gobe zai dawo ne da ta shiga toilet don yin wanka kafin ta kwanta, ta ji jikinta gaba daya ya sauya, tafi-tafi ta ji ba wanda ta ke son bude ido ta gani sai Uwais domin gaba daya Ammi da Hajiya Asabe sun rikita hormones dinta.
Don haka tana fitowa daga wanka yau tun kafin lokacin hirarsu ya yi ita ta kira shi da kanta, Uwais na dauka ya ce,
“Anything special for Uwais?”
Ta yi ajiyar zuciya mai nauyi, ta ce, “Ya Uwais, yaushe za ka dawo ne?”
“Gaya min tukunna, mene ne damuwar?”
Nan Fahimah ta hau kame-kame, “Ba wani abu fa Uwaisu- Uwaisunmu ni da yayata Amrah… I just want to see you, it is almost 70days ban sanya ka a idanuna”.
Uwais ya ce, “Kin ma fadi gaskiya za ki yi bayani dalla-dallah in na iso domin Fahimah na tara da yawa.... only Fahimah can treat my unnamed illness”.
Fahimah ta kai tafukanta ta rufe fuska tamkar Uwais yana ganinta. Da sauri ta kashe wayarta bayan ta ce, “Ya Uwais I’m not a doctor”. Ba ta karasa jin me yake cewa ba ta kashe sabida yadda muryarsa ta saukar mata da wata irin kasala.
Sallamarsu ta daren jiya ke nan.
Kafin su gama aikin abinci ita da Talatu, Ammi ta yi kiranta. Tana zuwa dakinta ta ce, “Bar aikin nan wa Talatu, ki zo ki yi wanka da ruwan turaren nan, in kin fito ki zo ki yi tsugunno a kan wannan turaren, sannan ki saka kayanki”.
Fahimah ta bi umarnin Ammi. Da ta gama ita da kanta sunsuna kanta ta hau yi sabida dadin kamshin da jikinta ke mata. Ta rasa ina Ammi ta samo wadannan mayatattun traditional turarukan.
Fahimah ta shirya cikin wani pink voyel wanda aka yi wa aikin dutse mai matukar kyau da tsari, babbar riga ce Senegales, Ammi ta ce ita za ta je ta dauko Uwais daga airport anjima, ita ba ta jin dadi, ba za ta iya tuki ba.
Duk da hannunta ba wai ya fada da tukin ba ne, wani zubin Ammi tana ba ta sai ta makala mata learner.
A shagwabe Fahimah ta ce, “Ammi gaskiya ni ba zan iya zuwa dauko Yaya Uwais ba, wallahi Ammi kunya nake ji”.
Ammi ta yi banza da ita ta ci gaba da shan shayinta, daga bisani ta ce, “To a barshi a can, kada a dauko shin, asarar wa? In don ta Safeeyyah-Basudaniyyah ne tana da ‘yarta, wata ce za ta yi asarar miji”.
Dariya fahimah ta yi don in Ammi ta so raha kamar kakarta ta ke komawa.
Ta dade a gaban madubi (dressing mirrow) tana kalmasa daurin kallabi, ta yi ta kwance ta sake daurawa, ta rasa wanne za ta bar wa Ya Uwais ya gani ya san cewa kwalliyar yau musamman don shi aka yi. Sai da Ammi ta kwala mata kira cewa lokaci ya kure, sannan ta hakura ta fita, bayan ta feshe jikinta da turaren oud midnight ta cakuda da (cerruti) ta yafa yalwataccen gyalen da ya shiga lightly da kayan jikinta, sannan ta fito.
“Na fito Ammi sai mun dawo”.
“Sai ki hanzarta, it’s almost past 8 now”.
Fahimah tuki ta ke a hankali ba ta gudu, sannan ba ta hawa tsakiyar titi da gani dai za ka san ‘yar koyo ce.
Tun daga ‘Yankaba har airport sabida lattin da ta yi tuni jirgin su Uwais ya yi landing suna can suna kokarin fitar da kayayyakinsu.
Ta tsaya daga can gefe, idanunta a kan kofar fitowarsu, yadda duk mai fitowa sai ta ga fuskarsa. Ba ta yi tsayuwar mintuna ashirin ba ta hango shi yana tahowa sabe da jakarsa. Ya maka bakin glass (GUCCI) a idanunsa.
Ba don ta yi masa farin sani ba, sama da shekaru sha takwas da ko kusa ba za ta gane shi ba. Domin kyawun da ilhamar sun ninka na baya, kasar Switzerland ga dukkan alamu ta gama karbarsa. Farar fatar nan ta yi luf! Sassalkar gashi ya kwanta a gefe da gefen fuskar wanda a baya ba ya barinsa bai aske ba. Sai ya koma Balarabensa sak da sirkin rayuwar kasar sanyi.
Ta gabanta ya gifta ba tare da ya gane ta ba. Sai kawai ta bi shi a baya. Har suka fita daga reception. Ya duba agogon (swatch - blustery) da ke daure a damtsen hannunsa yana kallon hanyar da jama’a ke bi. Kamar daga sama ya ji muryar Fahimah a bayansa.
“Maraba, lale, Ya Uwais!
Na kara baki ko akan nawa, shi ya sa ba ka gane ni ba?”
Da sauri ya juyo cikin wani irin yanayi, “Fah-himah, ke ce da kanki ki ka zo daukana? Wow! Lucky me’. Ya sa hanun damansa ya janyo ta barin damansa, daya hannun rike da bakar jakarsa. Kunya ta kama Fahimah, ta soma kokarin zamewa don ga mutane nan birjik suna wucewa, wasu suna shigowa. Ya ki ba ta damar hakan, domin kuwa ya rike ta gam-gam, suka zama kamar madara da bombita (black & white) suna taku tamkar ba su so, zuwa inda ta ajiye motar Ammi.
Ya bude booth ya sanya jakar hannunsa, sannan ya ce, “Ba ni makullin, ban shirya mutuwa yanzu ba da zan hau tukin ki. Ban dauki bakaken ‘ya’yana ba masu yi min addu’a? Ammi wane ganganci ya sa ta ba ki mota? Anyway, ni ta taimake ni cikin dimbin alfarmominta da ba sa karewa a gare ni”.
Ya karbi mukullin daga hannun Fahimah, ya bude mata gidan gaba ta fara shiga, sannan ya zagaya ya shiga ya zauna. Yadda yake treating dinta like a queen wajen shiga motar kadai abun ka tsaya ka kalla ne.
Maimakon ta ga sun dauki hanyar ‘Yankaba sai ta ga Uwais ya karkata kan motar ya dauki hanyar Sultan Road. Suna tafe a motar yana satar kallonta yana fadin, “Fah-himah kin kara yin baki, amma kin kara yin fresh, in ji dai ba aikin wahala ki ke yi ba? Kodayake ko zirga-zirgar makaranta cikin ranar kasar Nigeria ya isa ya sa dalibi duhu”.
Fahimah ta ce, “Umh, ina muka nufa ne Ya Uwais?”
Ya ce, “Inda ya kamata masoya kuma ma’aurata su samu privacy, kafin mu je ana kulle min mata ana saka min ka’idodi”.
Fahimah ta gintse fuska ta ce, “Da wa ka ke kenan? Ammin?”
Ya ce, “Akwai mai rike min mata ne bayan ita da zan kyale shi yana abin da ya ga dama idan ba ita ba?”
Fahimah ta marairaice fuska tace, “Ni dai babu ruwana Ya Uwais, mu wuce gida don Allah. Ammi na can na jira, ta tanadar maka abinci, in ta ga mun dade me za mu ce mata?”
Uwais ya wani irin juyo ya dube ta yana shigar da sexy eyes dinsa can ciki, ya ce, “Akwai abincin da ya kai black wife dina dadi ne? Ki bar ni in mori kuruciyata kafin furfura ta zo ‘ya’ya su cika gida su hana ni sakewa”.
Ya karasa fada ta hanyar sanya hannun damansa ya rungumo ta gaba daya, saura kadan sitiyarin motar ya kufce masa. Fahimah ta zaro ido tana fadin.
“Ya Uwais kada ka zubar da mu ba mu ajiye wa Ammi ‘ya’yan da ta ke buri ba”.
Maganar Fahimah ba karamin dadi ta yi wa Uwais ba. Ya kara kankame ta da hannu guda yana tuki da dayan cikin gwaninta har suka zo gidan sa.
Maigadi yana nan don Uwais ba ya wasa da hakkinsa da extra ihsani. Suna zuwa ya zo da gudu ya bude musu yana ta faman sannu da zuwa wa Uwais, Fahimah ta yi gingirin a cikin mota ta ki ko motsi bayan Uwais ya kashe motar ya bude mata kofa.
“Fito mana my sweet 16? Ko sai an ja min ajin ne yadda aka saba? Kiyi a hankali kada ya tsinke don na kusa hango ta uku”
Fahimah ta tsuke baki ta tattare gira ta ce, “Ya Uwais! Ba zan shigar wa Amrah gida don ba ta nan ba, Ammi ta ce kowa da gidanta, ta ya ya za ka kawo ni gidanta?”
Uwais ya kankance ido cikin mamaki.
“Gidanta ko gidana? Nawa muka hada ni da ita muka sayi gidan? Tun muna shaidar juna ki fito, ko ki ga abun mamaki a cikin motar nan”.
Amon muryarsa kadai Fahimah ta ji ta gane asalin Uwais dinta ne rigimamme, mara karbar uzuri kuma mara ragowa ta wannan bangaren. He will go far beyond abin da ya ce din in ta sake ta ki bin umarninsa, to kuwa maigadi zai sha kallo daga inda yake zaune. Motar Ammi farin gilashi kal gare ta.
Kafa a mace ta zuro ta kasa ta sauko tana turo baki tana kunkuni, “Haka kawai daga zuwanka sai rigima? Ba za ka bari mu gama gaisawa ba?”
Uwais ya sanya mukulli yana bude falon gidansa, ya ce.
“Akwai gaisuwar da ta fi wannan ma’ana ne?”
Ya karasa fadi ta hanyar janyo ta cikin falon da wata irin azama. Kamar yadda ta yi tsammani farkon love making din Uwais hot and deep kisses ne a kullum, amma na yau ya fi na kullum domin a urunce yake sumabatarta a ko’ina, kusfa-kusfa yana yi yana kiran sunanta. Abin har sai da ya koma ba ta tsoro, domin ba ta taba ganinsa a cikin kwatankwacin irin wannan bukatuwar ba.
Tamkar bai taba kusantarta ba sai yau… ya ba ta dukkan soyayyarsa, ya ba ta dukkan amanarsa da sirrikansa wanda daga ita sai Ubangijinta sai shi suka sani. Wani hidden side ne na Uwais da ko Amrah ba ta taba gani ba don ba ya jin tsananin urge din da yake ji akan Amrah kamar a kan Fahimah.... wadda ta zo cikin takaitaccen lokaci ta gigita duniyarsa, ta canza ta, ta fahimtar da shi a baya ba soyayya yake ba, sha’awa ce ta kyawun halitta.
Duk da haka har gobe yana son Amrah, amma yana ganin rabuwar tasu ita ce mafi alkhairi a gare su baki daya. He will miss Amrah, amma yana da yakinin yanzu zai iya rayuwa ko babu ita. Infatuation dinsa a kanta kullum kara raguwa yake yi, anya haka Ammi ta barshi? Wane irin sirri ne haka tattare da Fahimarta?
Uwais ya kasa shiru, a bisa doguwar kujerar falonshi suke yana kanannade jikin Fahimah domin ta yi rantsuwa ba za ta hau gadon Amrah ba, dakinsa ma ba za ta shiga ba tunda kuwa Ammi ta raba tuntuni, duk wani hali na Ammi na tsayuwa a kan magana daya ya lura Fahimah ta dauke shi tsaf. Don haka ne ya sa shi ma ya hakura ya kyale ta suka sha soyayyarsu anan falon shi kamar babu gobe… a karshe Uwais bai yi mamaki ba da ya ji damshi a idanunsa, ‘Hawaye yake yi ba tare da ya sani ba'. Fahimah ko a aljannah yana fatan a bar masa ita kadai a matsayin hurul eeninsa. Ya yafe 'yammatan aljannah.
“Ki yafe min Fahimah, hakika na yi kuskure a baya wanda yake hunting dina har gobe. Da zan iya da na maida bara-bana, na gyara all those inconveniences da na wanzar a tsakaninmu. Dana hadiye kalamai na na baya marasa dadi akan ki.
Watakila har in koma ga Ubangijina ba zan daina nadamar abin da na yi miki a baya ba. Ni dai na san a halin yanzu hukunta ni Ubangiji ke yi da hakkin ki, soyayyar ki nema ta ke ta kashe ni…”.
Fahimah ta kai tausasan yatsunta ta toshe masa bakitana girgiza kai, cikin wata irin tattausar murya ta ke magana.
“Tashi mu tafi wajen Ammi haka Ya Uwais, ko ta ganka ta ji dadi a ranta itama. Na ga Uwais after 70days, na kasance cikin alfarmar Uwais after 70days ....in a way and manner da na tabbata wata diya mace ‘yar uwata ba ta taba samu ba.
Idan