Showing 18001 words to 21000 words out of 21013 words
Chapter 7 - FAHIMAH Book 2 End COMPLETE Writing by Sumayya Abdulkadir Takori kabara .txt
su biyu shi da Fahimah, tare da Ammi zasu tafi Abuja su yi ta hilatar ta suna mantar da ita komawa Sudan.
Ammi kamar ta sam me Uwais da Fahimah suke shirya mata, da suka zo suna fada mata cewa tare da ita zasu koma Abuja in ya so daga can ta wuce Sudan. Dariya ta yi musu tace "ni din ai ba ta yau bace Fahimah&Uwais. Ku bar ganin babu furfura a kai na amma na kwana biyu bazaku yi min wayo ba. Na gaji da kasar Najeriya cikin dangina zan koma, kuyi hakuri bazan biku gidan ku in zauna ba.
Amma na amince idan kin haihu zan zo in zauna in yi miki jego na kwanaki arba'in. Na yi wannan alkawarin. Daga nan har ki haihu ai amarci bai kare ba Fahimah, kin ga dacewar Uwa ta zauna a tsakanin ku?".
Ba Fahimah kadai ba har Uwais ya ji kunya. Ana i gobe Ammi zata tashi zuwa Khartoum Fahimah da Uwais a gidan suka kwana manne da Ammi, sun kasa matsawa ko nan da can daga jikin Ammi. A wannan ranar Fahimah ta yi kuka har ta gode Allah. Shi kansa Uwais daurewa yake yi a matsayin sa na namiji, kada Fahimah ta ga karayar sa ta kara sarewa.
Da asussuba suka kai Ammi da himilin kayan ta filin jirgi, Baba Talatu ta fi bada tausayi da tafiyar Ammi kasancewar tunda sauran kuruciya suke tare. Ammi ta yi mata ihsanin da zata dade bata nemi komai a rayuwarta ba. Kuma ta ce in tana so ta bi Uwais da Fahimah Abuja su zauna tare.
Baba Talatu ta ce kwarai zata so hakan amma itama 'ya'yan ta sun matsanta kan ta koma Jahun sabida tsufa ya riga ya cimmata, amma ta yi alkawarin kai musu ziyara lokaci-lokaci. Ammi ma ta yi alkawarin duk sanda ta sake zuwa Nigeria zata kawo mata ziyara har Jahun.
A lokacin da jirgin su Ammi 'Air Sudan' ya karci kasa ya daga ya bar Kano, yayi dai-dai da lokacin da Fahimah ta saki wani kakkarfan kuka ta kankame Uwais a bainar jama'a. Ji ta yi kamar ance rayuwar gata da parentship ta yi mata adabo. Ji ta yi kamar su biyu suka rage a fadin duniya daga ita sai Uwais.
A wannan lokacin Uwais ya rungume Fahimah cikin lallashi, his words are all supportive, loving and ecouraging cikin daukar mata alkawura da dama, alkawuran cewa zai tsayawa rayuwar ta tamkar Ammi in every aspect.
Yayi alkawarin zama mijin marainiya, namiji dan goyo har da daurewa da majanyi koda har su koma ga Mahaliccin su bata ga kowa nata ba. Wanda zai taka rawar IYAYE, MIJI, 'DAN UWA, ABOKI KUMA MASOYI ga matar sa duka a lokaci guda (all at once). Zai zame mata uban 'ya'ya nagari ta yadda bazata taba dana sanin zuwan ta duniya a yadda ta zo ba!!!
Alkawuran da Uwais ya daukarwa Fahhimah a yau, har ba su da adadi, wadanda yake fatan Allah ya bashi lafiya, tsawon rai da ikon cika su.
*****
Amma har bayan kwanaki uku da tafiyar Ammi Fahimah bata koma daidai ba, she became moody and depressed, haka bai kara ganin fararen hakoranta a waje ba balle a yi zancen kulawa a shimfida. Duk kulawar da yake samu ta zama a gefe she's internally suffering a zuciyar ta..... ya yarda Ammi itace gatan Fahimah amma kuma ai Allah shine gatan bawa. Sannan ko kai kadai Allah ya yi nufin zaka rayu a doron kasa to fa zaka rayu cikin hikima, iko da yardar sa. Yau in aka ce Ammi mutuwa ta yi, shin bazata yi tawakkali ba???
Abinda Uwais yayi ta kokarin nusar da Fahimah kenan a kwanakinnan, yace ko Ammi ta zauna a Nigeria tunda tace bazata bi su Abuja ba to fa duk daya ne da zamanta Sudan cikin 'yan uwanta. Gara mata zama a can din. Yana da yakinin zata fi samun farin ciki da kulawa acan fiye da ta zauna a gidan ita kadai babu Fahimah, tunda shi dama namiji ne, neman abinci bai bari ya tsugunna waje guda.
Fahimah dai har kwanaki bakwai she's still moody, don haka a hakan ta Uwais ya tattara ta suka kama hanyar Abuja.
Suna tafe a mota ma lallashin ta yake ta yi babu gazawa, har suka zo birnin tarayyar Najeriya da yammaci lis.
Gidan nasu yana kan titin Yakubu Gowon Crescent. Uwais ya sa mukulli ya bude suka shiya kayataccen falon. Ya juyo yana riko hannayen Fahhimah a cikin nasa...
"This is your humble abode!"
Uwais ya fada yana zaunar da Fahimah akan kujerun falon su, wadanda Fahimah bata taba hawa kujera mai laushi da taushin su ba. Su ba fata ba su ba roba ba su ba leather ba. A gidan duniya dai gidannan da bai cika girma ba kuma bai cika kyale-kyale ba ya ishe ta rayuwar duniya.
Uwais ya sunkuya yana fadin "lemme give you a welcome kiss Fah-himah my life, my wife, mother of my children, the one i love most (after Ammi). May we live together in prosperity and blessings, die together in love and affection, blessings upon blessings....... May Allah's Rahmah cover us forever......".
He then start to kiss her....... tun daga kololuwar zuciyar sa sautin sumbar yake fita tsut-tsut. Daga wannan ranar, wani sabon shafin rayuwa na gangariyar soyayya ya fara........
*****
Sai da cikin Fahimah ya shiga watanni hudu sannan Uwais ya farga. A ranar Uwais sai da ya kusa kuka don farin cikin yafi gaban ya yi masa dariya. Ya goya Fahhimah a gadon bayan sa, yana zagaye makeken falon su da ita a hankali, sannan ya dire ta cautiously akan gadon su.
Ya tashi da azumi a washe gari, ya kuma yi sadaqah a gidan marayu na garin Abuja, yana rokon Allah ya sauki Fahhimah lafiya, ya kuma raya duk abinda zata haifa, walau mace walau namiji shi bashi da zabi, kowanne Allah ya bashi yana so kuma ya gode, zai cigaba da godewa da basu ingantacciyar tarbiya har sai gashin kansa ya kode ya zana fari tas, yana rokon Sa yasa Fahimah ta haifi abinda ke cikin ta lafiya cikin tarbiyyyar Islam da koshin lafiya.
*****
MURFI
Kowanne dan adam yana da burin sa da kalar tunanin sa, wato dai kowanne dan adam da irin perception dinsa. Da irin aqidar sa wadda a ganin sa itace dai-dai da tsarin rayuwar sa.
Saidai daga sanda aka bar fadar Allah Ubangiji SWA aka kama ta malam bature zallah, (wanda shi bai san Allah ba, bai yarda da dokokin sa ba, bai san rayuwar duniya aikin banza bace) to baza'a ga yadda ake so ba, wato baza'a ga daidai ba.
Ina wannan sharar fagen ne akan Amrah Umar Dikko da ire-iren ta. Bayan wucewar shekaru bakwai, Amrah tayi nasarar zama cikakkar likitar fida (surgeon) ta fito da kwali mai daraja ta biyu, a wannan lokacin ne ta ga ya dace ta komawa masoyin asali; UWAIS SHAGARI, don yanzu ne take da lokacin sa 100%. Kuma yanzu ne ta shirya haifar 'ya'ya don tuni ta samu aiki a National Hospital.
A daidai wannan lokacin Uwais Da Fahimah yaran su uku; Abdulkarim, Safiyyah da Little Fahhimah wadda Uwais ya sanyawa sunan Fahimah don ya nuna mata matsayin da take dashi a rayuwar sa. A wannan lokacin promotion na aiki ya maida su kasar Switzerland gabadaya, a babban reshen World Bank, suna zaune a Geneva, inda acan ne Fahima ta haifi Safiyyah (Mami) da (Little Fah) yadda suke kiran ta. Abdulkarim kadai ta haifa a gida sanda suke Abuja.
Ammi Safeeyah duk bayan watanni uku take zuwa Geneva daga Sudan, tayi wata daya tare dasu ta koma Khartoum. Lokacin da Abdulkarim da suke kira Baba Shagari ya cika shekaru bakwai a duniya sai Ammi ta dauke shi daga Geneva zuwa Sudan, acan aka kaishi makarantar haddar Al'qurani mai hade da kimiyyah a Oumdurman ta kasar Sudan, Safiyyah (Mami) da Fahima (Little) su suka cigaba da karatun firamare a (La Decouvertè School) Geneva.
Karkashin kulawar jajirtacciyar uwa (the great Economist) Fahimah Shagari da uban da babu kamar sa wajen kulawa da nunawa iyali soyayya: Uwais Abdulkarim Shagari. A wannan shekarar Fahimah zata fiddo kwalin P.hD (Dr. Of Philosophy) akan Economics daga University of Geneva.
Amrah na can tana neman inda zata hadu da Uwais Shagari helter-skelter. Ta san har gobe Uwais bazai guje ta ba idan sauran mazan dake tare da ita suna bata mata lokaci babu zancen aure sai na holewa sun guje ta. Amma neman duniya Amrah ta yi bata samu Uwais ba a Kano, Abuja da Lagos. Layukan wayar sa data sani tuni ya daina amfani dasu.
Har tattaki ta yi zuwa 'Yankaba hopefully ko bata same shi ba za ta samu Ammi, inda ta tadda 'yan haya ne a gidan, suka kuma tabbatar mata masu gidan basa kasar Nigeria dukkansu.
Amrah kamar tayi dan karamin hauka, ga Jabeer ma yace shi rabon sa da Uwais tun samun aiki da yayi da World Bank, a karshe Amrah ta yanke shawarar ta nemi Uwais a social media platforms.
Tashin farko da ta nemeshi a facebook da IG da Twitter da sauran su bata sameshi ba. Amma cikin ikon Allah sai ta ganshi a LinkedIn tunda shi (professional network) ne, duk wasu manyan ma'aikata da kanana suna cikin sa.
Wani lafiyayyen hoton Uwais ya fito karkashin sunansa data rubuta. Inda ta ga cewa yana zaune a birnin Geneva, karkashin bankin World Bank. Gabadaya ya canza completely, girma da ya kara sai ya kara masa ilhama da cikar zati, yayi wani irin fresh kamar bai hada jini da hausawa ba ko kankani. Amrah ta kusa suma don dadi, a take ta rubuta masa personal messege ta tura.
A ciki ta bayyana masa dukkan success din ta, duka burika sun samu, shi kadai ya rage mata rayuwa ta koma cikakka. She's now a medical doctor amma bata da aure kuma bata da Da ko daya. Ya zo su koma da auren su, ta yarda ko mata uku gareshi zata zauna a ta hudu.
Uwais bai ga sakon Amrah ba sai a daren ranar da ya hau LinkedIn don duba sakonnin ofis. Da ya karanta sakon Amrah bai san sanda yayi murmushi ba, sannan ya saki wani mikkakken tsaki. This woman is sheer LUNATIC, me ta dauki soyayya ne?
Gare-gare abin wasan yara ko kuwa me? Shi tunda ya bar Nigeria bai kara tuna Amrah ba, yanada duk abinda yake so a matar sa. Ba Amrah kadai ba, duk wasu matan duniya ma basu kara burgeshi ba. Kowacce kallon wadda ta rako FAH-HIMAH duniya yake mata.
Da farko bai yi niyyar bata amsa ba, amma sai ya ga cewa in har akwai abokantaka ta gaskiya to har gobe Jabeer abokinsa ne. Ya rabu da Jabeer ne bai nemeshi ba tun zuwan sa Geneva don baya son wani abu ya kara hada shi da Amrah. A yanzu kuwa tunda duniya ta koya mata darasi ta waiwayi reality ya kamata ya bata amsa wadda zata sa ta kara sanin rayuwa ta kuma san baya bukatar ta arayuwar sa yanzu.
Hoton shi da matar shi da kyawawan 'ya'yan su guda uku masu kama da ruwa biyu (halfcaste) shi ya fara saka mata, sannan a kasa yayi rubutu kamar haka;
"A ganin ki wannan perfect and loving family suna bukatar wata mace daban a cikin su bayan MAHAIFIYAR SU?
Amrah kinyi kuskure da kika dauki soyayya tamkar gare-gare abin wasan yara! Da zaki iya gara tayoyin ta duk sanda kike so, gaba ko baya.
Ni a wajena soyayya shuka ce mai rai dake bukatar ban ruwa da taki domin ta cigaba da yin yado. Daga sanda aka bar wannan shuka babu ban ruwa babu taki, to grass-root dinta yake mutuwa tun daga karkashi har zuwa ganyayen ta, su bushe su mutu su zube a kasa.....
Wannan typical example ne na baki akan Uwais da Amrah. I already found true love, and all what a man dreamt of in my current WIFE. So i wish you all the best in life. Ina fata wannan ya zama sako na karshe da zaki turomun please and please, don in mata ta ta gani zata rufe min kofa.
-Uwais Shagari.
Ai kuwa yana gama tura sakon tana fitowa daga toilet kanta yana yararin ruwa, yanzu kam tana dan retouching dinsa ba kamar da ba, don haka kakkarfan gashin ya russuna sosai ya kwanta, wanka ta yi, domin kwanciya barci kuma rigar wanka ta tawul ce kawai a jikin ta.
Alamun rashin gaskiya ta gani a tare da shi ta kankance ido "Baban Fah, kai da wa kake waya?"
Sosa kai yayi, "ba fa waya nake yi ba, LinkedIn ne. Ko kinji ina magana ne?"
"Ban ji kana magana ba, amma ga ka da waya a hannu, lokacin da ya kamata ace already ka kashe, tunda kuwa lokaci na ne yanzu. Wannan lokacin na chatting din dare da 'yammata, ai in ina ganin ka da waya da daddare jini na zai hau ne, inta kissime-kissime koda ba chatting din kake yi ba".
Dariya sosai Uwais yayi, ya mike ya isa gareta ya tsaya a gabanta, ya sanya hannu ya rungumota gabadaya yana sumbatar ta ko ta'ina yana fadin; tsofai-tsofai dani at 40 zan tsaya chatting da 'yammata Fahimah? Inada wannan hadaddiyar Babyn a gida? Luscious, succulent and....." sauran maganar makalewa tayi a bakin Uwais sabida yadda Fahimah ta kwace linzamin ragamar rayuwar sa gabadaya.
****
NB
A karshe Amrah ta auri wani tsohon consultant dinta, yana da mata biyu ita ta uku. Kuma ra'ayi da akida ya zo daya, don haka lafiya suke zaune. Don bai hada ta da matan sa ba.