Showing 12001 words to 15000 words out of 21013 words
Chapter 5 - FAHIMAH Book 2 End COMPLETE Writing by Sumayya Abdulkadir Takori kabara .txt
Amma ji yake inda yana da abin da ya fi hakan zai yi, don Fahimah da yayanta masu zuwa a gaba.
Ya kashe motar a inda aka tanada don adanata, sannan ya mika wa Fahimah kamsassan hanky dinsa,
If you are done with the cry sai ki goge hawayen mu shiga da kafafun dama, Im sleepy.
Farin cikin yau zan mallaki Fah-himah by my side a matsayin uwargida a duniya da lahira, bai barni na runtsa jiya ba.
Burina da fatana kawai gari ya waye in shaida wannan rana mai nisan zuwa kamar eternity.
Ki shigo gidanki cikin aminci, so da kauna da yardar mijinki. Na yarda da ke Fahimah na amince da ke matsayin uwar yayana.
Ki yi hakuri da ni a inda na kuskure don yanzu ne rayuwarmu ta hakika za ta fara. Rayuwar da duk son da ake wa juna sai an yi hakuri da 'flaws' din juna.
Sabida yanzu ne zan koma Uwaisu ki koma Fah-himatu, not Uwais and Fahimah sarauyi da budurwa".
Maganarsa ta karshe ta ba ta dariya duk da hawayen da ke fuskarta sai da ta murmusa tana share su da hanky din da ya ba ta, Uwais ya bude suka fita, sai ya zagayo ya sakalo hannunsa a kugunta, a haka suka shiga falon farko na gidan.
Fahimah ta ga cewa in ta tsaya kallon gidanta wanda ko a mafarki ba ta taba yin na mallakar kwatankwacinsa ba, to kuwa Uwais zai ce 'yar kauye futuk ya aura. Gara ta adana kallon zuwa sanda ba sa tare.
Soyayyar yau daban ta ke, domin ta zarce ta birnin Ikko wannan ta nutsuwar zukata ce. Mai licence, sannan ba hobbasar Uwais shi kadai ba, Fahimah ta agaza ta taimaka fiye da zatonsa. Shi da kansa ya yi mamaki domin ta sakar masa komai fiye da koyaushe. Ya ce,
"My wife today deserves an accolade!"
Kwana uku kenan suna barzar amarci kamar ba za su gaji ba. Takardar sakin ma bai san inda ya jefa ta ba. Tsabar yadda Fahimah ta tafi da dukkan nutsuwarsa, ta zamo silar wani irin 'life contentment' ga rayuwar Uwais. Gabadaya ya mance da Amrah.
Da yammacin yau yana daga can bayan gidan inda shuke-shuke suke yana motsa jiki kamar yadda yake yi a kowanne yammacin Allah iya dawo gida da kowacce safiya. Fahimah ta karaso inda yake da kofi mai zurfi (jug) a hannunta mai dauke da sassanyan kunun aya da kwakwa da ta matse da kanta. Ta zauna bisa fararen kujerun roba da ke gefe da tebiri a tsakiyarsu ta ajiye a kan tebir din ta tsiyaya a tambulan tana sha. Uwais ya dakata da excercise din yana yarfe gumi daga goshinsa ya ce.
"Abun naki ba ta yi? You know i'm thirsty".
Fahimah ta ce ba tare da ta dube shi ba, "Bari in dauko maka naka (power Horse) wannan na mata ne".
Uwais ya karaso wajen ya dauke jug din gaba daya ya kafa kai ya shanye duka.
Ya ce, "Ki hada kayanmu yau na kwana biyu, gobe za mu je Abuja a yi miki visa".
Ambatar Abuja da ya yi ya sa Amrah ta fado mata a rai,
"Ya Subhanallah Ya Uwais, yaushe za ka je ka taho da Aunty Amrah?"
Ya dan bude ido yana kallonta bai ce komai ba sai da ta sake maimaitawa.
"In muka je goben zan biya". Ya ki yarda su hada ido kada ga gane rashin gaskiyarsa.
A cikin kayan da ya dawo da su ta ke cire masa wadanda zai tafi da su. Cikin haka takardunsa suka zubo, wata 'yar farar ambulan ta fado da sunan 'Amrah' a jiki.
Ba ta yi niyyar budewa ba amma ta ji gabanta ya fadi, sabida rubutun na Uwais ne. An ce ba abin da ya fi dagawa mace hankali irin miji ya ba ta wasika ba tare da ta san me ta kunsa na, kuma an saka sunan Amrah baro-baro.
"Ya Ubangiji in na yi ba daidai ba ka yafe mini, but I must quench my curiosity".
******
Uwais na dakinsa yana fama da aiki cikin macbook sai ganin Fahimah ya yi tsaye a kansa rike da takarda tana hawaye.
"Yaya Uwais!".
Ta fada cikin rauni. Ya dago lumsassun idanunsa yana dubanta ba tare da ya ce uffan ba. Hawaye suka sake shimfidowa Fahimah, da kyar ta iya cewa, "Me Aunty Amrah ta yi maka ka sake ta? Mene ne hujjar hakan? Yaya Uwais ko don mun daidaita ni da kai ne? Ta ya ya ni ma ba zan yi tunanin in ta uku ta zo, ba za'a sake ni ba?
Wannan shi ne ga mari ga tsinka jaka. A yi mata laifi kuma a sake ta Ya Uwais, don Allah na roke ka don darajar Ammi ka janye sakin nan kada ka kai shi don Allah ya Uwais..."
Kukan da ta saki har cikin kwakwalwar Uwais, domin ta sanya gwiwarsa ta yi sanyi, jikin sa ya mutu, ya ce.
"Fah-himah ba laifina bane, kuma ban daina son Amrah ba. Babanta ne ya ce na sake ta ko ya kai ni kotu".
Fahimah ta ce, "Sai ka zage ka lallashe su dukkan su, bacin rai ne yasa shi fadar hakan, i don't think he mean it, amma fushin fari ba naka ba ne Ya Uwais. Amrah ba ta da laifi ko me za ta yi, laifi ne ka yi mata, sai ka karba a wuce wurin kawai".
Uwais ya yi shiru bai sake ce mata uffan ba, amma a cikin ransa ya janye sakin da ya yi wa Amrah.
Sun kwana da niyyar washegari Uwais zai tafi Abuja bikon Amrah.
Don haka Fahimah da wuri ta tashi ta sallame shi da dukkan abin da zai bukata. Karfe takwas na safe Uwais ya kama hanyar Abuja cikin motarsa Elantra.
A hanya ne ya kira Jabeer, yana dagawa kafin Jabeer ya ce komai ya ce,
"Friend, I'm on my way for biko".
Jabeer ya yi ajiyar zuciya, don ya san mawuyaci ne Daddy ya sake sauraron Uwais a kan batun Amrah. Amma bai fada masa hakan ba, don ya sani kullum Uwais mutum ne mai sa'a. Auren Amrah ma da ya yi ba karamar sa'a ya taka ba, don haka yanzun ma ba shi da tabbacin ko Alhajin nasu zai sauko daga fushinsa tunda ya yi tattaki ya zo don ya amsa laifinsa.
Ya isa Abuja wajejen azhar sannan ya karkata kan motar sa zuwa Apo.
Daga Amrah sai Mama a gidan yau Aunty Wasila ba ta zo ba. Maigadi ne ya shigo ya fadi cewa Uwais mijin Amrah ya zo yana waje.
Mama ta dubi Amrah don ganin reaction dinta sai ta ga fuskarta kamar an mata bushara da zuwan mala'ikan daukar ranta. Sosai Mama taji dadin hakan, wannan ya nuna Amrah ta dauki zugar da suke kwana da yini yi mata.
Dare da rana ba abinda familyn Amrah ke yi sai zugata akan rabuwa da Uwais, in har tana so rayuwar ta ta gyaru. Yau da gobe aka ce 'zuga' abu ce mai matukar illah, in bata dau wata ba tana daukar wata.
Don haka auren Uwais ya fucewa Amrah a ka, tana ganin gara ta hakura ta huta akan taje ta yi zaman kishi da Fahimar da bata san Yaya tsakanin ta da Uwais yake ba har yau, tunda su munafukai ne.
Da farko ma cewa tayi da maigadin ya je ya ce bazata zo ba. Mama tace.
"Ba za'ayi haka ba Amrah, gara kije ki san matsayin ki, in yin-yin in barin-barin". Sannan ta yi kwafa tace.
"Wannan Uwaisun, ya gama rainawa mutane hankali. Har yana da 'guts' din kwaso doguwar kafarsa ya sake kawo mana nan?"
A fusace Amrah ta zari mayafi ta fita, a dakin da suka saba zama lokacin da yake zuwa zance acan ta sameshi.
Uwais na tsaye har lokacin bai zauna ba, da hannuwa zube cikin aljihu, yana zuba idon ganin ta inda Amrah zata bullo, zuciyar sa cike da waswasi. Ba jimawa Amrah ta bayyana a gaban sa cikin wata fuska da wani yanayi irin na kamar dadai duniya bata taba sanin sa ba.
Daga bakin kofa ta tokare ta tsaya, Uwais ba ya son tuna yanayin da ya ga idanun Amrah a wannan lokacin; babu komai cikin su sai tsananin tsanar sa zallah.
A hankali yayi tattaki zuwa gaban ta, yana nan har yanzu a Uwaisun sa data sani mai kayatar da zuciyar ta, but he lose his magical appearance of love and trust. Dan burbushin son da ya rage a cikin zuciyar ta yanzu ba zai hana ta komai a rayuwa ba.,
Suka tsaya cirko cirko suna kallon juna kamar zakaru, kowanne striving yake da zuciyar sa don son gane cewa soyayyar tana nan ko ta ragu? Ko kuwa gabadaya ta kama gaban ta? Ta Uwais tana nan, amma ta ragu 50%. Ta Amrah na nan, amma bacin rai, kishi tsana da tunanin betrayance din da Uwais yayi mata ya kashe shi da 70%.
Sauran kashi talatin din da ya rage, Amrah ta sabya shi matsayin sabo da juna, kuma na tunani; zata iya overcoming dinsa da zarar ta koma Malaysia.
"Ina fatan ka taho min da takarda ta UWAIS SHAGARI?"
Amrah ta fada kai tsaye, da sunan da bata taba kiran sa da shi ba.
Murmushi yayi, wanda da gani iyakar sa fatar bakinsa, sannan cikin karfin hali irin na maza gogaggu da suka yarda da kan su, yace.
"Amrah ko gaisuwa babu? Na dauka tsakanin mu ya wuce haka?"
Wani irin kallo Amrah ta yi masa, tana mai tariyo kalaman data ji yana fadawa wata mace ba ita ba a waya, watan ma da ya ce 'yar aikin gidan su ce. Kalamai masu tsauri da matar ka ta sunnah kadai ya kamata ka iya gayawa.
Kuma in a gaban idon ta ne ya nuna ko son zanen yarinyar baya yi. Wanda ke iya fadar wadannan tsauraran kalaman a waya, a fili wace irin soyayya yake aikatawa a gareta? Allah kadai ya sani.
"Ban fito nan don kayi min dadin baki ba, na fito ne in karbi takarda ta, domin na yanke shawarar dana ke ganin tafi amfani a gare ni. Itace rabuwar auren mu".
Da kyar Uwais ya zuki numfashi ya fesar.
"Ko rabuwar kika zaba Amrah, yana da kyau ki saurari kalaman baki ba, kafin ki yanke kowanne irin hukunci, ban ce lallsi ki yarda dasu ba, amma inada hujjojina, tunda dai soyayya ce da yarda suka hada mu ba akasin su ba".
Amrah tayi wata irin dariya tace "soyayyah........ Uwais? Really? Does it really exist a duniyar nan kuma a zamanin nan?"
Uwais ya shafo lallausar sumar kansa cikin damuwa yace "It really does, and i still love you Amrah. Kamar yadda nake son Fah-himah itama. Amma ki yarda cewa aure na da Fah-himah wata rubutacciyar kaddara ce daga Allah wadda tafi karfin na tsallake ta....".
Tiryan-tiryan ya soma bata labarin Fahimah, tun daga lokacin da Ammi ta dauko ta daga 'orphanage', kuruciyar su, yadda ya rayu yana uzzura mata, da goranta mata halitta, zuwa haduwar shi da ita Amrah a gidan Jabeer.
Yadda Ammi ta kafe in bazai auri Fahimah ba itama Amrah ba zai aura ba. Artabun da Ammi ta sha da shi akan Fahimah, kafin ya yarda su tafi Ikko tare.
Ya takataita zancen sa da cewa. "A wannan tafiya da nayi tare da Fah-himah, a dalilin rashin zaman ki wuri guda, al'amura suka sauya beyond my capability to escape. Kada ki manta ni namiji ne kuma mai cikakkiyar lafiya kamar kowanne dan adam, wanda Allah ya baiwa damar auren abinda yayi masa dadi daga daya-daya, biyu-biyu, uku-uku ko hurhudu.
Ko Ammi bata aura min Fahimah ba, a irin rayuwar da kika zaba mana, dole in kara aure. Don haka Amrah bai kamata ki ga laifi naba don na so Fah-himah at this expense tunda aure ne na sunnah a tsakanin mu, kamar yadda yake tsakanina da ke.
Laifi daya na san na yi muku Amrah, na rashin gaya muku tun farko, sai na gina neman aure ne a lullube, abinda ya kamata in yi a wancan lokacin shine tun farko in fada, cewa ku biyu za'a aura mini a lokaci guda, da ke zabin rai na da zabin mahaifiyata, in ya so in kin ga zaki iya aure na a haka ayi, in kin ga bazaki iya ba na hakura.
To amma Amrah idanuna sun rufe, na kurumce na makance a dalilin son ki, burina kawai na mallake ki. Ina tsoron duk wani abu da zai shiga tsakanina da wannan burin nawa. Na san kuma muddin na fada a wancan lokacin to na rasa ki kenan Amrah...... and i cannot affort to lose you.
In kuma nace miki a halin yanzu bana son Fah-himah Amrah na yi miki karya na yaudare ki, wanda hakan zai yi sanadin sake gina rayuwar auren mu akan rashin gaskiya a karo na biyu.
Ni dai na san zan kasance jajirtaccen miji mai adalci a gare ku, in kin bani dama kin dawo dakin ki Amrah".
Ko kadan maganganun Uwais cikin lallashi da karbar laifi (submissiveness), kwantar dakai da tsage gaskiya da hakikanin asalin Fahimah da ta ji a yau bai wanke zuciyar Amrah ba, daga cin amanar da take ganin Uwais yayi mata.
Karewa ma, labarin da ya bata sai ya ninninka mata kishin Fahimah..... the way Uwais yake kiran sunanta kadai cikin shauki zaka fahimci tana da kima da matsayi mai girma a zuciyar sa....
Tunanin Amrah a a wannan lokacin shine; ko ta koma gidan Uwais bazata taba ganin farin sa ba, komai adalcin sa da yake ikirari, ya riga ya munana a idanun ta, zuciyarta ta riga ta gama sallama shi. Sannan ta gama tsanar Fahimah a rayuwar ta.
Ba don kuma wai ta daina son sa bane a'ah, sai don hakan take ganin ya fiye mata maslaha.
Akan dai ta je ta zauna tsakanin wadanan 'yan gida daya, da suka ruwa a kofi guda, suka rayu gida daya karkashin tarbiyya da soyayyar uwa guda, suka kuma yi aure mai dimbin sarkakiya wanda a karshe ya koma musu auren soyayyah.
Daga Baban ta har mamanta da yayyenta babu mai son auren ta da Uwais, ita kadai take son kayan ta, sai ko Yaya Jabeer. Shima yanzu ya ce ya cire hannun sa. Hukuncin komawa gidan Uwais ko akasinsa nata ne babu ruwan kowa.
Amrah ta