Showing 3001 words to 6000 words out of 21013 words

Chapter 2 - FAHIMAH Book 2 End COMPLETE Writing by Sumayya Abdulkadir Takori kabara .txt

most. Kada ka manta mahaifyarsa ce ta yi masa umarnin auren yarinyar nan, kuma ita ke rikonta sannan ta ce in bai aure ta ba, Amran ma ba zai aura ba. I’m sure dalilin shi na amincewa kenan. Wato tsoron rasa auren Amrah.
Kamar yadda ya ce din ne if you are in his shoe, ya za ka yi? Za ka yi zina ne tunda ita ta ki zama, ko ko za ka tafi ga ajiyayyen halalinka da ke gefe?”

Jabeer bai ce mata komai ba, amma yanayin fuskarsa ya nuna sassauci.

“Ki tashi mu je mu ga halin da ta ke ciki, ya ce tana asibitin standard”.
Murjanatu ta dauko mayafinta ta bi bayansa, domin tuni shi har ya kai waje. Babbar damuwarsa ya san laifin Uwais shi ma sai ya shafe shi a wurin Daddy, tunda dai komai ma shi ne sila.
Da tambayar sunan patient wadda aka kawo jiya, ta haihu dan ba rai Jabeer da Murjanatu suka dangana da dakin da su Fahimah suke.
Suna tsaye a kan Amrah ita da Ammi, Fahimah rike da kofin shayi mai kauri, Ammi rike da plate din kwai da dafaffiyar hanta da Talatu ta kawo suna ta aikin lallashinta a kan ta ci, Amrah ko idonta ta ki budewa balle ta dube su, abin da ya soma hassala Ammi don dai ita ba ta san laifin da suka yi mata ba, amma Fahimah ta fara shan jinin jikinta.

Sallamar Jabeer da matarsa a dakin ya sa Amrah ware dukkan idanunta. Sannan ta yunkura da karfi za ta tashi, Murjanatu ta yi gaggawar rike ta ta maida ta kwance tana fadin, “Oh no Amrah. Ki bari ki samu lafiya, ga ni na zo. Sannu kin ji? And we’re going to Abuja together”.
Amrah ta ji hankalinta ya kwanta, sai ajiyar zuciya ta ke yi, ta kuma daina kukan. Abin da ya daure wa Ammi kai, wato su ne ba ta son gani, to me suka yi mata ban da abun arziki? Ko tana zargin su suka kashe dan Uwais da hannun su?
Murjanatu ta juya tana gaida Ammi, kallo daya ta yi wa Fahimah ta gane ita ce matar Uwais. Class din yarinyar ya isa. And her black skin is expensive and radiant a cikin mata. Sai ta ji kwarai itama tana taya Amrah kishi da gaske.
Kishi da wannan zukekiyar black beauty ai sai jarumar mace mai karfin zuciya, wanda ta tabbata Amrah ba ta daga cikinsu.
Har dare Murjanatu na tare da su, ita ta sa Amrah ta karbi shayi ta sha. Abin da ya kara tayar wa Fahimah hankali shi ne, yadda tunda Amrah ta farka ta ki ko da duban inda ta ke.
Wannan ya tabbatar mata da kyar in wani bai lalata al’amarin ba (ya riga Uwais gaya wa Amrah) wanda shi ne sanadin nakudarta da wannan fushin da ta ke musu har Ammi.
Duk sai ta ji jikinta ya yi sanyi, don haka ta janye jiki daga inda Amrah ta ke. Daga baya ma ganin Murjanatu na nan ta ce da Ammi za ta koma gida ta yi wanka sai dare za ta dawo ta kwana. Ammi ta ce, Murjanatu ta tambayi Amrah me ta ke so a kawo mata da daddare?
Amrah ta tsuke baki ta ki cewa komai.
Ammi sai da ta kai zuciyarta nesa, amma da ita ma tafiya ta yi niyyar yi tare da Fahimah, amma ta taushi zuciyarta ta zauna. Ita kanta Murjanatu ba ta ji dadin wannan hali da Amrah ke nuna wa uwar mijinta ba. Amma Ammin tana wajen ba ta tashi ba, don haka ba dama ta yi mata fada.
Da Murjanatu ta tashi tafiya bayan magriba da Jabeer ya zo daukarta, Amrah tuburewa ta yi ba ta yarda Murjanatu ta tafi ba, sai dai ta kwana da sassafe su wuce Abuja ko Doctor bai sallame ta ba.
Kunya kamar ta kashe Murjanatu, don a gaban Ammi Amrah ta fadi maganarta kanta tsaye. Ita ma Ammin tun daga nan ta sha jinin jikinta cewa, abin da ta ke guje wa Uwais tuntuni ya faru. Wani munafikin ya yi masa riga malam masallaci.
Sai ba ta ga laifin Amrah ba, domin laifi guda har da rabi Uwais ya yi mata. To amma ita kam babu ruwanta, wanda ya ja ruwa shi ruwa kan doka. Ba yadda bata yi da shi ba akan ya fada mata tun farko ya ki.
Dole Murjanatu ta kwana, Fahimah kuma da ta koma gida ta dauki wayarta a inda Amrah ta yasar da ita, sai ta duba missed calls dinta. A nan ta ga received call na Uwais da sha biyun dare kamar lokacin da yake kiranta kullum don yin midnight call.
Ta tuna a inda ta bar wayar, da kuma barci da ya dauke ta da wuri. May be Uwais ya kira, Amrah ta dauka, shi kuma ya yi barambaramarsa da ya saba. Mutumin da in ya soma sakin romantic zance sai ta rasa inda za ta sanya kanta don kunya.
“Hasbunallahu wa ni’imal wakeel”.
Fahimah ta fada a fili, ta zauna gefen gado ta dafe kanta.
Wannan ne ya sa ta kasa komawa asibitin da daddare. Ta ma kashe wayar don kar Ammi ta kira ta ce me ya sa ba ta dawo ba. Shi ma Uwais yau ba ta so ya kira ta. Kowa ya je ya ji da damuwarsa shi kadai.
Ko barci ta kasa, sai kawai ta dasa nafilfili a tsayin daren baki dayansa. Takamaimai ba ta san me ta ke roka ba. Ko me ye bukatarta? Ban da Allah ya kawo daidaiton zukata cikin al’amarin, domin ba za ta so auren Amrah ya mutu a kan nata ba. Ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne, ko ita aka yi wa haka duk son da ta ke wa Uwais sai ta hukunta shi, balle Amrah da ta dauki dukkan yardar duniya ta ba shi.
Ita da ma a philosophy dinta babu sakankancewa a kan cewa namiji nata ne ita kadai. Ta sa a ranta bayan Amrah, Uwais na da damar da zai karo mata biyu, don haka ba ta taba yaudarar kanta ba kamar yadda Amrah ta dauka. To ina batun da ta ke yi mata a baya na cewa ta auri Uwais? Ashe dama duk a baki ne bai je har zuci ba zafin laulayi ne, lol? Ita kam tun daga wancan lokacin ne ta ji ta kara son Amrah, duk da hakan bai hana ta jin kishinta lokaci zuwa lokaci ba.

Washegari da safe bayan ta yi sallar asubah da wuri ta shige kitchen ta shirya abin da ta tabbatar Amrah za ta iya ci, da wanda su Ammi za su ci, sannan ta dauko basket din zuwa waje da zummar zuwa bakin titi ta hau adaidaita zuwa asibiti.
Tana fitowa harabar gidan motar Ammi na shigowa. Don haka ta ja tunga ta tsaya har Ammi ta yi parking a inda ta ke ajiye motar kullum. Fahimah ta karasa ta karbi hand bag din hannunta suka rankaya zuwa ciki. Tana fadin,
“Da ba ki wahalar da kanki ba sun tafi Abuja tun dazu, kuma kin kama kin kashe waya balle in gaya miki. Ni yau na ga abin da ya ishe ni, kishi hauka ne da za ki sabi hanyar Abuja da sabon CS a jikinki?”


“Hasashena ya tabbata!” Fahimah ta fada a ranta.
Jiki a sanyaye ta maida basket din kitchen ta koma daki. Ta kunna wayarta kenan kiran Uwais ya shigo, da sauri ta sake kashewa don ba ta da courage na cewa komai.
Amma sai ga Ammi ta biyo ta da tata wayar har dakin, “Fahimah, don me za ki ki amsa wayar mijinki saboda wata can ta yi fushi da ku? Maza karbi ki yi masa ta’aziyyar rashin da ya yi, ai shi ya ja wa kansa da ya bi maganata tun farko, da yanzu hankalinsa a kwance. Yana bukatar mai lallashin sa, maza karbi wayar nan kamin ki bata min rai”.
Fahimah ta karbi wayar. Ammi ta juya ta fita.

“Fah-himah, are you there?”
Muryar Yaya Uwais, ta karya zuciyar Fahimah ba ta taba jinsa ya yi magana a wanan yanayin ba.
A hankali ta ce, “Ya Uwais, I’m sorry… for all the inconveniences, ka zo ka dauke ni mu je mu yo bikon Aunty Amrah”.
Murmushi ya yi mai sauti, ya ce,
“Ba tafiyarta ce damuwata ba Fahhimah. Yadda na zama silar rasa baby dina. Fahimah I love babies, and I lost one. Ban san kuma yaushe Allah zai sake ba ni wani ba”.
“Soon insha Allah…”. In ji Faheemah, sannan ta sassauta murya ta ce, “Ina maka ta’aziyya Ya Uwais, Allah ya sa mai ceton mu ne”.
Ya lumshe ido ya ce, “Na gode Fah-himah, amma ya aka yi wayarki ta je hannun ta?”
“I don’t actually know. Kawai na farka na ganta a kaina cikin jini”.
Ta fada masa duk yadda aka yi suka ga Amrah ta zo ba zato ba tsammani da yadda ta kai ta dakinta don su kwana tare.
Uwais ya yi ajiyar zuciya, ya ce Allah ya riga ya tsara za a yi hakan, amma na yi niyyar gaya mata da zarar na dawo. Ya rage nata ta dawo ko ta yi hukuncin duk da ta ga dama”.
“A’ah Ya Uwais ba za a yi haka ba, kai ka yi laifi dole ka zage kwanji wajen bada hakuri har sai ta sauko. Ni ba bakuwar zafi ba ce ko guda uku ne ka karo…......".
Muryar Uwais wani iri ya ce, "Sabida ke ba kya kishina ko? Ko sabida ba ki sona Fah-himah?”
Dariya ta yi, ta ce, “In ka ji So, to daya kenan. So, so, so i love you so much. Ina son ka sau malala gashin tunkiya…...”.
Uwais ya ce, “Ina nan tafe jibi in gani practically, ban yarda da wannan malalar ba. Da Ammi za ta yarda ma tare za mu koma in karasa sauran satittikan da suka rage min, ko outside masaukin mu sai in kama gida, don cikin mu babu wanda ya zo da mata”.
Fahimah ta ce, “Sai ya Uwais?”
“Yeah, Uwais daban yake kamar yadda matarshi Fahhimah ta ke daban a cikin mata”.
Murmushi Fahimah ta ke from ear to ear duk wani tension ya barta. Ta dauka yana cikin mummunar damuwa MATAR SO ta daka borkono, sai ta ji sabanin hakan.
Sun dade suna hira kamar ba kudi Uwais ke narkarwa ba. Ya ce, akwai kyakkyawan albishir da zan muku ke da Ammi, amma sai na dawo. Now, kiss me a little ko na ji dan sanyi a zuciyata”.
Tafukan hannunta ta kai ta rufe fuskarta.
“Ya Uwais!”
Shi ma ya ce, “Yaya Fahhimah, I LOVE YOU”.

Fahimah kamar ta narke sabida yadda kalaman Uwais suka ratsa ta, suka tsirga har cikin ruhinta. Da yana kusa, kuma za ta iya, a wannan lokacin ba ta san wace irin runguma za ta yi masa ba.
“Zan ba ka babban kiss, amma sai ka dawo”.
Fahimah ta samu kanta da fada ba tare da ta shirya ba, tana mai mamakin kanta.
“Are you sure?”
“Very sure Ya Uwais, Allah ya kawo ka lafya”.
Zuciyar kowannensu wasai suka yi sallama.
****


ABUJA
A cikin mota a kan hanyarsu ta zuwa Abuja ba irin ban baki da lallashin da Aunty Murjanatu ba ta yi wa Amrah ba, amma Amrah ko sauraronta ba ta yi ba, ta yi rantsuwa ta gama auren Uwais ko da shi ne autan maza.
Sai karfe biyu suka isa gidan su Amrah a Apo, Mama sai ganinsu ta yi katsahan, Amrah babu katon ciki, sannan babu jariri. Itada ta kama hanya ta tafi ko kwana biyar ba'ayi ba. Mama ta ce, “Lafiya? Kin haihu ne? Ina dan?”
Amrah ta fada jikin Mama tana kuka. Wani irin kuka mai cin rai. Daidai lokacin da Aunty Wasila ta shigo da sallama don ita haka ta ke, kullum kafarta tana gidansu, ba ta zama gidan mijinta sam, da ta taso aiki sai ta zo ta rashe sai dare ta koma.
“A’ah Amrah kuma? Ke da ki ka tafi jiya ki ka ce ba za ki haihu wajenmu ba kada mu kashe miki da?”
Amrah ta kara sautin kukanta kamar za ta tsaga falon, ba ta ce komai ba. Sai Murjanatu ce ta yi wa Mama bayanin duk abin da ake ciki. Shi kuma Jabeer da ma tun shigowarsu falon Daddy ya wuce don ya same shi su tattauna.
Mama da Aunty Wasila kwafa suka yi, Aunty Wasila har da dariya, ji kake kyal-kyal-kyal. Suka ce, “Amrah Lailah matar Uwais Majnoon, how market?”
Amrah ta kara kuluwa fiye da wadda ta ke ciki, ta ce, “Duk da hakan dai na ji ina sonshi har gobe ya ya ranki? Ni boye min din da ya yi ne tun farko ya bata min rai. Amma yarinyar ba yau na santa ba, ba ta da matsala sam. I just cannot share my husband with anyone shi ya sa na yanke shawarar hakura da shi gaba daya”.
Mama ta ce, “Gantalalliya, a haka za ki kare cikin bacin ran namiji kuwa, wai har yanzu tana son kayanta. To don ubanki tashi ki koma inda ki ka fito, ba za ki kwana min a gida ba”.
Murjanatu ta ce, “A yi hakuri Mama, yanzu jego ne a gabanmu. Wanka za'ayi mata a gasa mata jiki don Allah a dama mata kunun kanwa a gasa mata nama da dan ruwa-ruwa”. Ta fada cikin lallashin surukarta.
Mama duk da haushin Amrah da ya kusa fasa mata zuciya, haka ta daure ta bi umarnin Murjanatu.

A can falon Daddy shi da Jabeer, kasancewar ranar lahadi ce yana gida, Daddy ya ce, “Lafiya na ganku haka hajaran-majaran da tsakar rana?”
Jabeer ya ce, “Mun kawo Amrah ne".
A fusace Alhaji Umar Dikko ya ce, “Uban me ta dawo ta yi mana? Ban ce kar ta sake ta dawo min gida ba? Ta je can wajen Uwaisun ta haihu, tunda ita ba ta san abin da ya kamata ba? Ana mata gata tana ganin ba a sonta".
Jabeer ya ce, “A yi hakuri Daddy, ta haihu yau kwana uku dan ya koma”.
Jikin Daddy sai kuma ya yi sanyi, don yana son Amrah sosai duk bacin ran da yake yi a kanta, ai don ya ginata ne. A sanyaye ya ce,
“Shi ne kuma ta dawo?”
Jabeer ya ce, “Akwai wata maganar bayan wannan’.
“Ina ji”. Ya fada a kagare.
“Eh to Daddy, Uwais ya yi wa Amrah laifi, wanda ya dace ku sani. Ashe tare aka daura auren Amrah da na wata ‘yar uwarsa a lokaci daya mu ba mu sani ba. Sai yanzu Amrah ta gane. And he confessed to me. But please Daddy take it easy na san Uwais is a brave husband zai iya zama dasu su duka kuma yana da halin da zai rike su, kuma daga yadda na fahimta mahaifiyarsa ce ta tursasa shi ya auri waccan din. Na tabbata zai kasance mai adalci a tsakaninsu".
Alhaji Umar Dikko bai san sanda ya kwada wa Jabeer ashariya ba, har yana zaburowa daga cikin kujerar sa, ya ce, “kun ci kaza-kazan ku kai da Uwaisun naka ku raba. Ya rike adalcinsa, ni ma in rike ‘ya ta. Ni za a raina wa hankali?
Nan wannan Balaraben kawun nasa kamar mutumin arziki da ya zo nema masa auren me ya sa bai gaya min gaskiya ba? Nawa Amrah ta ke da za a hada ta da kishiya ko ashirin fa ba ta kai ba, uwarta sai da ta shekara ashirin tare da ni na yi mata kishiya, balle a yi wa tawa ranar nata auren.
Da ma auren ba wai ya gamshe ni ba ne. Na ga amrah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login