Showing 15001 words to 18000 words out of 21013 words

Chapter 6 - FAHIMAH Book 2 End COMPLETE Writing by Sumayya Abdulkadir Takori kabara .txt

ga cewa duk ne yayi zafi akan soyayya wadda bata zama dole a rayuwa ba? Da ita, da babu, dan adam irin ta mai abun yi bazai kasa rayuwa ba.
Tana da tarin abubuwan yi masu yawa da muhimmanci a gaban ta, she's a goal-oriented, dama auren Uwais ya zame mata kamar alaqaqai ga 'goal' din ta, da take ta faman raba hankalin ta a kai, don ganin ta bada lokacin ta da energy din taga kowanne bangare (aure da karatu) wanda haduwar su waje guda abu ne mai wahala ga 'yan hutu irin Amrah.
Da wannan tunanin dama wasu hujjojin ta masu yawa da bata ambata ba, Amrah ta runtse ido tace.
"Uwais Shagari, na ji dukkan bayanan ka, sannan na fahimce su. Amma abu daya nake so ka gane it's too much for me to bear. And it's too late to cry.....when the head is cut off.
Ka riga ka dusasar da tauraruwar ka daga idanuna bazan iya kara yarda da kai ba.
Ka zo da bayanin gaskiya a lokacin da bakin alkalami ya riga ya bushe, wani nawa bazai iya sauraron ka ba, including Yaya Jabeer.
Don haka aimakon mu cigaba da zaman daukar hakkin juna da wahalar da zukatan juna, mu yi hakuri da juna shi ya fi, wanda aka yi a baya Allah ya bada ladansa.
Inada yaqinin cewa you've found your true and real love wanda ya zarta nawa........". Amrah ta fada, tareda fitowar wani guntun hawaye daga gefen idanun ta. Ba mutuwa ake wa kuka ba sabo ne. Ta daga kai ta dubi Uwais da murmushi a kyakkyawan bakinta.
"I'm wishing you and Fahhimah all the very best in life, so many kids as you are dreaming, masu kama da dukkan ku, don zasu fi yin kyau fiye da nawa da naka a dalilin mixed complexion".
Ta karasa cikin zolaya duk da cewa still da kananan hawaye cikin fararen idanun ta.
"Uwais, ina taya ka murnar mallakar mace daya da daya a cikin mata, na zauna da ita na san halin ta, na kuma fahimci qualities din ta. Allah ya baku zaman lafiya ya hada hankulan ku da ra'ayoyin ku wuri guda ba kamar ni ba...".
Da sauri Uwais ya rungume Amrah, yace cikin rawar murya.
"Amrah na yarda mu cigaba da auren mu yadda kuke so ke da iyayenki, i will never complain again, duk sanda kika samu dama sai ki ziyarce ni. Yanzu kam na amince da wannan tsarin since i have an alternative, mun wuce wannan wurin.
Sauran matsalolin duk da zasu biyo baya na tabbata zasu kasance kanana ne Amrah, wadanda zamu iya overcoming din su da karfin son da muke wa juna. Tunda zama waje guda shi ke kawo matsaloli zan yi kokari inga cewa kowacce tana muhallin ta daban nesa da na 'yar uwar ta, sai kun so zaku hadu da juna........". Amrah ta girgiza kai ta sanya yatsunta cikin na Uwais ta ce.
"Auren ne bana bukata kwata-kwata yanzu, i'm going for my life ambition, i'm done with it, i have to go for my goals. Ban sani ba dai ko a can gaba in bukaci auren? Allah shi ya barwa kansa sani".
Uwais ya fahimci ko me zai ce da Amrah ta riga ta yanke hukuncin da take ganin shine dai-dai da rayuwar ta. Zai zamo ihu ne bayan hari. Amrah no longer wants him in her life. Don haka shima ya ce.
"Na fahimce ki Amrah, and i will not force you ki yi abinda ba kya ra'ayi, tunda shi aure contract agreement ne na mutane biyu ba mutum daya ba. I wish you good luck in your all endeavours.
Kuma ina fatan as you actualize your goals, (bayan cikar burikan naki) zaki yi aure immediately, ko da ba da ni Uwais ba.
Ki sani Amrah duniya ba matabbata bace, lahira ita ya kamata a yiwa kyakkyawan tanadi irin wannnan ba zaman duniya mara tabbas ba, wanda mai karewa ne kamar kiftawar ido".
******
Wannan ita ce rabuwar masoyan ta karshe, wadda tazo ta dagula zukatan su a kwanakin da suka biyo baya. Kowannen su ya zama emotional. Bayan Uwais ya kaiwa Jabeer takardar sakin Amrah wadda ya sake rubutawa again. Ya zama saki biyu kenan bayan na farko da ya riga ya rubuta.
Fahimah data fahimci Uwais na cikin wani hali bayan dawowar shi daga Abuja sai ta janye jiki daga gare shi, ta daina shige masa, bata takura masa da tambayar me yake ciki shi da matar sa ba, don dai ta bashi dama yayi sulhu shi da zuciyar sa.
Ta dai fahimci ba'a yi nasara ba a komen Amrah amma da bakin sa bai ce mata komai ba. Illa iyaka walwalar sa ta ragu, amma hakan bai sa ya daina nuna mata kulawa da soyayya in a gentle way ba.
Kwana daya, biyu har uku bata ga Amrah ta dawo ba, abinda bata sani ba already su Wasila kamar jira suke sun zo sun kwashe kayanta kaf daga Sultan Road zuwa Abuja.
*****
Uwais yayi sallama a falon Ammi, dawowar ta kenan daga BUK, ta amsa da madaukakiyar far'a tana zolayar sa,
"ka ga angon Fahimah da Amrah, mai mata biyu wanda ba aminin gwauro ba".
Murmushi yayi kadan, sannan ya zauna a daidai kafafunta.
Suka sake gaisuwa, irin tasu ta Sudanese, Ammi ta tambayi Fahimah yace tana barci ya fito. Sannan ya sake tankwashe kafafunsa ya ce.
"Ammi mun rabu da Amrah fah, ina nufin auren ya kare".
Ammi ta ja wani dogon salati ta sanar da Ubangiji. "Garin yaya Uwais? Me ya kai ka aikata wannan danyen aiki?"
Uwais ya sunkuyar da kai sannan ya dago idanun sa da suka rine ya dubi Ammi.
"Because this is the best decision agare mu ni da ita. Fahimah ta isheni rayuwar duniya har da ta gidan aljannah mai zuwa anan gaba in Allah ya yarda. Amrah bata bukatata cikin rayuwar ta yanzu Ammi, na fahimci ma kamar dama jira take ta samu hanya ta kubucewa auren.
Tana da abubuwan da tasa a gaba da suka fi ni muhimmanci, na dade da sanin wannan ina karyatawa ne da gangan har zuwa yanzu da ta bayyana hakan da bakin ta".
Ya kwashe duk yadda suka yi da Alh Umar Dikko a waya ya gaya mata, yadda ya rubuta sakin tun kafin ya dawo, yadda aka yi Fahimah ta gani da takura mishi da ta yi ya maida auren, ya kuma yi tattaki zuwa Abuja don ya dawo da Amrah. Da kuma yadda ta kasance a tsakanin su.
Ammi Safeeyah is speechless, ta gamsu da hujjojin sa, yayi iya duk abinda zai iya don ya zauna da ita, ita kuma for now ta ga bazata iya ba, sabida principles din da aka riga aka dora ta akai.
Ammi bata ja zancen da nisa ba, dama auren Amrah ai zabin zuciyar sa ne, yaran yanzu ne abinda kake hango musu su ba shi suke hangowa ba, in suka so mallakar mace kamar Da ya so fitowa cikin uwar sa. A kullum kyal-kyal banza da kwadayin dukiyar iyayen yaran ke burge su. Duk da ta san Uwais kam bai kwadayin dukiyar gidan su Amrah amma yana kwadayin kyawun halittar ta.
Shi da kansa yanzu ya zo ya gane cewa kyawun halitta does not matters a lot in marriage, sabida shi aure ba abu ne da ake yi don nishadin zuciya kawai ba, a'ah ibada ce mai zaman kanta wadda a cikin ta akwai jarrabawar imani kala-kala ga kowanne dan adam.
Don haka ake so a gina shi bisa doro na gaskiya da amana, sannan kauna da soyayya su biyo baya.
"Idan wannan shine alkhairi a gare ku kaida ita, Allah ya hakurkurtar da zukatan ku, ya hada kowa da rabon sa na alkhairi".
Wannan sune kalaman Ammi a takaice, akan rabuwar Uwais da Amrah,
"Amin Ammi, insha Allah shine alkhairin da muke rokon Ubangiji dare da rana, akan kada ya bar mu da iyawar mu, ya zaba mana abinda zai fi zame mana alkhairi".
****




UWAIS&FAHHIMAH
(When Hatred turned to Extreme Love).
"FAH-HIMAH, kin gama ne mu wuce ko har yanzu kina nan kina lakai-lakai din kwalliyar taki sai jirgi ya tashi ya bar mu?"
Uwais ya fada daga bakin kofar shigowa bedroom din su, tana zaune gaban mudubi daga ita sai farin towel iya cinyoyin ta, ga cinyoyin nan sambala-sambala a fili suna sparkling suna zagin idon Uwaisu, wanda ya hade cikin shadda getzner deep green. A matsayin sa na farin mutum sharr mai sirkin jaja-jaja! Kada ki so ki ga yadda deep green colour ta amshi fatar jikin sa.
Yau din kuma yayi saisaye ya aske duka gashinnan na kansa, don haka bai saka hula ba yau, don ya san ko ya saka bazata zauna daidai ba.
Ta lakato lotion din ta (Makari) a tafin hannun ta, ta jefe shi da wani irin lallausar kallo kafin ta shigar da fararen kwayar idanun ta cikin nasa, ta juya su ta sake juya su cikin sigar jan hankalin maigida, ta ce.
"Jira na ke ka zo ka shafa min lotion".
Uwais yayi murmushi broadly yana karasowa gabanta hannayen sa duka biyu zube cikin aljihun sa kamar yadda yake a al'adar sa. Takun sa gonin kyau kamar yadda komai nasa yake mai kyau a fili da boye.
"In shafa miki lotion a nawa? Kin san ni komai nawa DEAL ne!".
Dariya ta yi da ta tuno da birnin Ikko, damben Ikko, kisses din Ikko, a lokacin har ya matso lotion din a tafukan hannun sa ya mutstsika ya soma shafa mata a cinyoyin da tun dazu suke zunguro idanun sa.
Amma da shafa mai yayi shafa mai, sai ta ji Uwais ya saki layi gabadaya. Ta san haka zata faru, itama kuma dama ta yi ne don ta tsokano shi. Nan suka shiririce cikin farantawa juna, da kyar in jirgin bai tashi ya bar su ba.
Sanda suka isa 'terminal' ma an kusa rufe jirgin, wanda zai tashi zuwa Geneva din Switzerland babbar hedkwatar bankin duniya (World Bank). Kusan sune karshen shiga jirgi, suna shiga ana rufe jurgin na Boeing 704.
*****


FAHIMAH DA UWAIS A GENEVA
Geneva, shine gari na biyu mafi girma da shahara a kasar Switzerland bayan Zurich wato (capital territory) din kasar. Ganeva, shine tabbataccen muhallin majalisar dinkin duniya 'United Nations' (bayan muhallin su na kasar Amurka dake New York). They speak German, Italian, French and Romansh. A shekarar 2017 population na Geneva ya nuna 198,979 (-United Nations). Sabida haka garin is not crowded at all. Birnin Geneva ya shahara akan guraren ziyara guda biyu; wadanda aka sani da 'Lake Geneva' wato kogin Geneva, da kuma 'Jet d’Eau' (Europe’s largest Alpine lake). Wanda sune manyan tourist attraction na garin Geneva.
Rayuwar Uwais da Fahimah a wannan birni mai sanya nutsuwa ga zukatan masoya, kwatankwacin rayuwar su ta birnin Ikko ce. Banbancin shine wannan cike take da soyayya, yarda da Amanna da juna. Waccan ta Ikko kuwa cike take da waswasi, rashin tabbas da rashin tsayuwar zukata wuri guda. Ba sa komai sai kula da juna, daga Uwais ya je aiki ya dawo, sai tayi girki su ci a kwana a hantse ana shan soyayya.
A wannan lokacin Fahimah da Uwais suka kara dinkewa da juna tamkar Lailah da Majnoon, soyayya suke zubawa kamar a birnin Hindi, Fahimah bata baro Geneva ba, sai da tsarabar yaron ciki dan sati biyu.
Shiru tayi da bakin ta bata gayawa Uwais ba alokacin da Pt stripdin ta ya nuna mata, musamman in ta tuno yadda ya kallafa rai akan cikin Amrah, amma a karshe Allah yayi bai rayu ba. Gara ta yi shiru kawai kada ta dugunzuma masa zuciya har sai ya gane don kansa.
Inda Allah ya taimake ta cikin mai hakuri ne bai da laulaye-laulaye, in dai zata ci ta koshi to kuwa lafiya-lafiya ita da dan tayin cikin ta. In bata ci abinci bane na kamar awanni biyu don gigicewa kamar ta zauce, kuma zata yi ta ci hannu baka hannu kwarya.
Satin su uku Uwais ya kammala course din da ya kai shi kasar Switzerland, dama kuma ba a masaukin su ya sauki Fahimah ba, wani karamin gida daga waje can ya kama musu, don ba'a basu accommodatin na iyali ba, suka tattaro suka dawo gida da sabon cigaba, wato takardar daukar aikin Uwais da World Bank Group. Reshen kasar Najeriya mai muhalli a birnin tarayyah.
Hedkwata din su na kasar Nigeria na nan a Yakubu Gowon Crescent. Don haka gidan da Uwais ya kama bai da nisa da ofishin su. Tunda suka dawo gida ba abinda suka sa a gaba sai shirin komawa Abuja, inda Uwais zai shiga sabon ofishin sa matsayin daya daga cikin jami'an World Bank na kasar Najeriya. Yayi sallama da GT kuma.
Sun tsara a junan su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login