Showing 9001 words to 12000 words out of 21013 words

Chapter 4 - FAHIMAH Book 2 End COMPLETE Writing by Sumayya Abdulkadir Takori kabara .txt

na rike Uwais a raina bayan duka wannan ni’imar da Allah ya yi min ta mallaka min shi matsayin mijina uban 'ya'ya na, na zama mara godiyar Ubangiji.
Besides, an ce so hana ganin laifi Ya Uwais, ni fa ban taba jin haushinka ba, karewa ma komai ka ke yi burge ni ka ke yi. Rana daya ce na ji haushinka a rayuwata, ranar nan a Sudan…”.
Da sauri shi ma ya toshe mata baki yana girgiza kai, "Kada ki tono abin da ya riga ya wuce, domin na tabbata alhakin wannan ranar ba nawa ba ne, naki ne. And i sincerely repented, so ni da ke duka masu laifi ne kuma tare za mu ke istigfari”.
Let’s go for another ......…” Ya rada mata sauran maganar cikin kunnuwanta.
“Umh…” Fahimah ta iya cewa domin dadin bakin Uwais in yana son abin da yake so yawa gare shi, ba ta da ikon musantawa don bai ba ta damar hakan ba ma.

Ammi ba ta gansu ba sai karfe sha daya na dare. Fahimah sai baya-baya ta ke yi daga bayan Uwais da ganin ta ka ga mara gaskiya. Shi ko Uwais ko a jikinsa, karasawa ya yi da sassarfa ya rungume Ammi ya sumbaci goshinta. Da wannan damar Fahimah ta yi amfani ta gudu dakinta, ta barsu suna tasu soyayyar ta da da mahaifi. Har wata ajiyar zuciya ce ta kwace mata da ta ganta a dakinta. Ba tare da ta karbi query daga Ammi ba.
Ammi kuwa ba ta bi ta kan wannan ba, farin cikin ganin Uwais ya ishe ta. Sun gaisa sun sake gaisawa har da musabaha irin ta larabawa. Ta ce, “Uwais kamar ba kai ba, Switzerland ta amshe ka, ina fatan an yi nasarar duk abin da aka je nema?”
Uwais ya ce, “Nasara kam an same ta Ammi alhamdu lillah, ga sabon albishir da nake son yi muku, World Bank da muka je yin course dasu sun ba ni aiki tare da su a yanzu haka, na bar GT idan na dawo. Yanzun ban karasa ba saura sati 3 mu gama gabadaya, na ga cewa ya zama dole in zo in saita al’amuran gidana”.
Ammi ta ce, “Ina yi maka ta’aziyya Uwais, Allah ya sanyaya, Allah ya ba mu rayayye. Sannan sai ka kai zuciya nesa ka yi hakuri da Amrah, don kuwa laifi kan laifi ka yi mata. Don haka ka jure duk abin da za ka gani ko za ka ji daga gare ta ko iyayenta, tunda kai ne mai laifi”.
Uwais ya yi murmushi kawai ya mike, bai gaya wa Ammi abin da Alhaji Umar Dikko ya ce ba, na cewa in bai sako masa Amrah ba zai kai shi kotun koli. Da kuma hukuncin da zuciya ta kwashe shi ya yanke tun a lokacin ta sakin Ammi, yanzu haka takardar tana cikin kayansa, jira yake zuwa jibi in ya kara hutawa ya runtse ido ya kai wa Jabeer.
Yana addu’ar Allah ya sa kada rabuwarshi da Amrah ta yanke kyakkyawar alakar da ke tsakaninshi da Jabeer Dikko.
Wanka ya sake yi sannan ya sa farar shirt (Hilfiger) da wandon jeans dark blue ya fito falon jaye da akwatuna guda biyu.
Ya samu Ammi tana marking takardun dalibanta da medical glass a idanunta. Ta daga kyawawan idanunta ta dube shi tana murmushi.
“Sai ina kuma? Na ganka ka dau wanka ka janyo akwatuna? Ko bikon za a tafi cikin daren nan?”
Murmushi Uwais ya yi ya zauna a gefenta yana bude akwatunan, ya ce,
“Ammi bikon lafiya? Laifin me na yi da zan je biko? Na dauka bayan Amrah da Fahimah ina da damar kara guda biyu ba tare da na yi wa Ubangijina laifi ba?”
Ammi ta ce, “Haka ne, amma a al’adance ka yi laifi ba a addinance ba. Ni dai ban yi wa kowa cikinku laifi ba daga kai har Amrah domin kuwa auren Fahimah na sa aka fara daurawa, ban kuma ce wani cikinku ya boye zancen ba, don haka can ta matse muku kai da Amrahn. Amma ina so ka yi hakuri ka dauki girma ka amsa laifinka, sannan ka bada hakuri ta dawo dakinta. Kowa ta zauna a gidanta, ban yarda da hada muhalli ba”.
Uwais bai ce komai ba, ya rika fidda tsala-tsalan atamfofi, shaddodi da lesuka yana tulewa a gaban Ammi, ya ce, “Ammi ga tsarabarku. Sai ki zaba wa Fahhimah wanda zai dace da ita, I don’t know her favourite colours yet, kuma ban yi azancin tambayarta ba”.
Ammi farin cikinta ya fi gaban misali, “Allah ya albarkaci rayuwa Uwais. Amma ni tsohuwa me zan yi da wadannan kayan gayun? Na bar wa Fahimah bakidaya tunda tarewa za ta yi, ta je ta yi ta yi maka kwalliya da su’.
Murmushi ya yi ta sake cewa, “Ina na Amrah?”
Kamar ya ce mata, “She’s no longer Mrs Shagari now”. Ya tuno halin Ammi na dattaku ba za ta bar shi ya bada takardar nan ba ko da za su kai shi kotun.
“Zan kai mata jibi in za ni, don gobe tun safe har dare in na fita ba zan dawo ba, zan maida hankali a kammala komai na gidan Fahhimah ta tare jibi, don tare za mu koma Switzerland tunda sun yi hutu, wata daya ne na gama gaba daya don a reshensu na Najeriya za'a ajiye mu. Kuma a garin Abuja ne, don haka zan nema wa Fahimah transfer zuwa (BAZE) tunda ta gama year 1”.
Ammi ta ce, “Hakan shi ne daidai, ni bana bayan miji na wani gari matarsa tana wani saboda kananan dalilai. Duk abin da zai zama dole ba a barshi a nemi alternative a zauna tare a nemi lahira. Tunda duk wani buri na duniya an gama samunshi, ilmi, career da aure na hakikah.
Yanzu sai shirin tarbar abokai da kawayen Ammi.
Sannan Uwais na aika takardar murabus daga aiki, idan kun dawo daga Switzerland kun nabba’a a permanent sabon muhallinku, ni kuma zan koma SUDAN gaba daya, a can zan karasa rayuwata. In kun haifa ku kai min Khartoum zan rike muku”.

A firgice Uwais ya ce, “Kada ki yi mana haka Ammi, Fahimah ba ta da kowa a kasar nan sai ke, ni ma ba ni da kowa sai ke Ammi, we need you behind us, burina shi ne in mun koma Abujan ki dawo gidanmu ki zauna tare da mu Ammi”.
Ammi ta shafo lallausar sumar kansa, ta ce,
“No Uwais, ku yi hakuri ba zan bi ku ba, I’m going back to Khartoum. Dukkanku kun kai munzalin da za ku tsaya da kafafunku ku tara iyali ku yi musu tarbiyya irin wadda ku ka samu. Ku yi hakuri ina Sudan ina Najeriya tunda kullum akwai jirage masu zuwa? Sannan ga waya, ko tari ku ka yi zan jiyo ku ta cikin waya”.
Ammi ba ta san yaushe Fahimah ta fito ba, ta kuma tsinkayi karshen maganganunta na komawa Sudan. Ai sai ta dora hannuwa biyu a ka ta saka kuka wiwi.
Ta fada jikin Ammi tana ta yi, Ammi na lallashinta tana fadin, “Ai da saran lokaci ba gobe ba zan tafi ba, na ce sai kun nabba’a a waje guda tukunna”.
Fahimah ta ce, “Ammi lallai sai na amsa sunan marainiyar da gaske? Idan ina ganinki kullum manta ko ni wace ce nake, idan ki ka tafi ki ka bar mu zan tabbata marainiya, rayuwata ba za ta taba zama cikakka kuma mai dadi ba kamar da”.
Ammi Safeeyyah na murmushi, ta ce, ‘Bayan ga ki ga Uwaisun naki? Uwaisu sarkin soyayya, baban soyayyah?”
Kunya sosai Fahimah ta ji, ta sunne kanta a jikin Ammi tana cewa, “Kai Ammi". Uwais waya yake amsawa don haka bai san me suke cewa ba”.
Ammi ta ce ta kwashe kayan nan duka ta tafi da su dakinta tsarabarta ne in ji Uwais. Fahimah ta ce, “Ammi ai ban ga naki ba”.
Ammi ta ce, “Na tsufa da lesussuka Fahimah, don haka na bar miki”.
Ta sanya hannu ta dauki atamfa Vlisco guda biyu ta aje a gefe, ta ce, “Ga shi na dau wannan Allah ya yi muku albarka”.
“Ammi zan je na kwanta. Na gaji sosai”.
Ammi ta ce, “Fahimah kin gyara misni dakin in ce ko?”
“Na gyara Ammi, har maganin sauro na fesa kada sauro ya ciji dan kasar sanyi daga dawowarsa”.
Dariya Uwais ya yi ya wuce yana kada kai, ya ce, “Kin ci bashi kuma za ki biya”.
Ammi ta ce, “Kayya da ba ki fesa ba, da kin barshi ya gane cewa ya dawo kasar haihuwarsa, kowa ya bar gida ai gida ya bar shi”.
Fahima tana dariya ta ce, “Kai Ammi”.
Ya wuce ya barsu suna ta barkwancinsu kamar jika da kaka.
Da wuri ya kwanta don da gaske yake ya gajin. Da asubah da ya dawo sallah daga masallacn kusa da su ya ce, bari ya tada Fahimah ta yi sallah. Don wasu lokutan tana da nauyin barci.
Ilai kuwa ya same ta ta yi dai-dai tana barci da wata ‘yar kyakkyawar nighty a jikinta wadda ita da babu duk daya. Uwais ya runtse ido a hankali amma sai ya ce bari ya mata mugunta tunda ta gota lokacin sallah.
Toilet ya je ya debo ruwa a kofi mai sanyi da shi ya zo ya yayyafa mata. Ai kuwa ba shiri ta mike a razane. Ganin shi ne ta shagwargwabe fuska, “Kai Yaya Uwais, wannan ai mugunta ce”.
Ya ce, “Yanzu wannan barcin da ki ka ware minshari kina yi kin yi sallah ne?”
Da sauri ta mike tana fadin, “Ya salam”. Ta yi toilet, shi kuma ya fita zuwa dakin Ammi.
Bisa sujjadah ya same ta tana lazimi, ta jima da idar da sallah. Ta ce, “Uwais har ka dawo masjid?”
Ya ce, “Na dwo Ammi sabahul khair”.
Suka yi gaisuwa cikin harshen larabci tana fadin, “Bari in je in tashi Fahimah ban ganta ta shigo ba”.
“Na tashe ta yanzu tana sallah. Ammi da na yi breakfast zan tafi can UDB (inda yake ginin Fahimah) in tsaya a kan ma’aikatan nan sai komai ya kammala. Sannan Ammi na tura kudi a wayarki da za a yi mata kayan daki, duk da ba zama za mu yi sosai ba a sayi komai ya dace a zuba, don duk sanda muka zo Kano a nan za mu zauna.
Sai maganar komawarki Sudan, don Allah Ammi ki barta”.
Ammi ta girgiza kai zuciyarta cike da jin dadin abin da ya yi kuma yake kan yi a kan Fahimah, mai nuna a karshe ya gama maraba da ita cikin rayuwarsa, ya ba ta matsayi mai girma kamar ko ma fiye da na Amrah. Don tun saukarsa ba ta ji sunan Amrah a bakinsa ba, Fahhimah… Fahhimah dai kamar shi ya rada mata sunan.
"Kada ku bata ranku a banza, kai ma ka san bana magana biyu, Sudan na koma ta na gama insha Allahu.
Fahimah na godiyar kayan daki daga Yayanta, wannan ya nuna min Uwais ko babu raina za ka rike min Fahimah da amana. Kuma da ma ko ba kai Fahimah ta aura ba hakkin kayan dakinta yana wuyanka. Sai ka yi amai ka lashe abinka”. Ta karasa cikin zolaya.
Cikin murmushi Uwais ya dukar da kai ya ce, “Ammi for the first time ina bada hakurin duk abin da na yi a baya cikin ajizanci irin na dan Adam. Ammi kin ce watarana zan zo in gode miki ba ki yi karya ba, yau ga ni gurfane a gabanki ina miko kwandon godiya ta. Kin ce da kaina zan zo in gaya miki wace ce Fahimah, kuwa ba ki yi karya ba.
She’s a darling (ita din abar so ce, kuma sai mai tsananin rabo zai yi sa’ar samunta a matsayin matar sa. Sai namijin da Allah ke so da rahma. Ammi na I remain loyal, grateful, and I remain regretful’.
Ammi ba ta san lokacin da ta kama tausasan hannuwan Uwais ta rike cikin nata ba, tana murmushi ta ce.
“Ban rike ka da komai ba Uwais sai tarin fatan alkhairi, ko babu komai ka yi gaggawar gane gaskiya kafin lokaci ya kure maka, ka zo ka yi nadamar da ba ta da amfani. Yanzu kuwa repentence dinka bai makara ba, ka yi shi a lokacin da ya dace.
Nasiha ta da kai Uwais ita ce, in za ka so abu ka so shi sawwa-sawwa, haka in za ka ki shi, kada ka zurfafa kiyayyar. Domin Allah shi ne kadai masnain gobe da abin da ya boye cikin rayuwarmu”.
Uwais ajiyar zuciya ya sauke yana mai AMANNA da kowacce kalma da ke fita daga bakin Ammi.
Fatansa Allah ya bar masa Ammi. Ya tsawaita rayuwarta, Ya inganta lafiyarta har sai ta yi wa ‘ya’yansa da Fahimah aure.
Wayewar gari ke da wuya ya nufi gidansa na UDB Road, a wannan tafiyar Uwais ba kananan kudi ya samu ba, don haka akalar ginin ta sauya gabadaya, gini ake sosai na gani a fada. Kafin ya dawo dama sun kammala komai, yau ya zo ya tsaya ne don a karasa kananan abubuwan da ba a karasa ba.
Ammi da Fahimah kuma suka tafi zaben kayan daki. Ba yadda Ammi ba ta yi ba Fahimah ta zabi abin da ta ke so ta ki, ta ce, “Ammi, duk abin da ya yi miki ni ma ya yi min. kin sani kullum ra’ayinmu yana zuwa daya, don haka ko me ki ka dauka zan so shi”.
(Me ya fi danka ya auri matar da ta san mutuncinka ta ke girmamaka fiye da mijin kansa?) Ammi Safeeyah ta fada a zuciyarta.
Don haka ita kuma ta zage ta yi wa Fahimah kayan daki na gani na fada, wadanda sai ‘ya’yan gata kadai ke samunsa. Bayan kudin da Uwais ya bayar, Ammi ta zuba nata har ba adadi.
In ka ga gidan Uwais da Fahimah komai ya yi acan-acan na masu ilmi da iya tsari, babu almubazzaranci ko kadan, komai da ke dakin Fahimah da kicin dinta mai amfani ne.
Inda Uwais ya sa aka yi mata english kitchen duk wata na’urar saukaka girki ta zamani Ammi ta saka wa Fahimah.

Don haka a washegari ma bai samu zuwa Abuja ba, kuma ba su samu komawa a ranar da aka gama komai ba sai washegarin ranar.
Washegarin kuma da asubah Ammi ta ce su tafi, don an fi so a shiga sabon gida da asubahi.

Da daren ranar Fahimah na gaban Ammi kuka kawai ta ke yi, Ammi na hada mata sitturunta da ke dakin da duk wani abin amfaninta, ita ma dauriya kawai ta ke yi, amma ta gama karaya. Shekaru kusan goma sha tara ban da zuwansu Lagos da Sudan ita da Fahima ba su taba kwana ba gida daya ba.
Lallai aure ya ci sunansa yakin mata. Ban da shi din, wa ya isa ya raba ta da Fahimarta?
To amma me? Uwais ne mijin. Uwais dinta kwalli daya, don haka Fahimah sauyin muhalli kawai ta samu, amma tana nan cikin gidanta.
Wannan tunanin ya sa Ammi Safeeyyah ta rage wa kanta damuwa, ta koma tsokanar Fahimah wai ai yanzu 'yammata sun daina kukan aure. Ita mai auren gata ma auren gida, auren cikin daki, auren da babu mai raba ta da Amminta.
Washegarin ranar da karfe 5:30am Ammi da Talatu suka raka Fahima har motar Uwais. Tunda ya dawo masallaci bai koma gidan ba ya yi zamansa cikin mota don ba ya son ganin rabuwar Ammi da Fahimah. Ko shi da yake namiji ya ji barin gidan a ransa kamar wannan ne karo na farko da ya fara yin aure.
Yanzu ne yake jin barin gidan sosai a ransa, ko don Ammi ta dage ita ma barin gidan za ta yi oho! Gida ne da ya kunshi tarihin duk wata dabdala ta kuruciyarsu. Ya sabbaba aure mai dimbin tarihi tsakaninsa da Fah-himah, Fah-himar da ta juya duniyarsa da tunanin sa baki daya.
Talatu ce ta rufe mata kofa don Ammi ba ta iya tsayawa ganin tashinsu ba. Kukan Fahimah ya karya zuciyarta sosai. Ta koma cikin gida cike da kewar Fahimah amma tana mai hamdala a zuciyarta. Yau ta sauke babban nauyin da burin kowacce UWA ta sauke shi, sai ta koma binsu da addua kala-kala.
Uwais ya kashe motar a harabar flat dinsu, wanda aka yi wa rufi da dark blue roofings. Bai cika girma sosai ba, amma ya tsaru iyakar tsaruwa daidai bukatar kowanne mai rufin asiri. Duk abin da Uwais ya samo a course dinsa na World Bank a gidan Fahimah ya kare.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login