Showing 1 words to 3000 words out of 44948 words

Chapter 1 - UNGOZOMA Book Complete Original by Maman AFRAH F.txt

19 Oct 2024

5919

[8/19, 17:55] Mom mashkur & Afrah: *UNGOZOMA*
(Mai karɓar haihuwa)




NA






MAMAN AFRAH




GARGAƊI⚠️


Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ta kowace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowace kafa ba sai da izinina a kiyaye.





Page 1️⃣➡️2️⃣




Dare ya tsala, ko ina tsit kake ji babu abin da yake tashi sai kukan tsintsaye da karnuka. A can cikin ɗakin Gwaggo Ramma ita ce kwance a kan gadonta na kara irin na mutanan da ɗin nan tana shirgar bacci sai ƙaran munsharinta da ke tashi a ɗakin tamkar an shaƙewa zakara wuya. Mai Gari ma da yake can yashe a kan tabarmar kaba yana sharar nasa baccin ya ɗaga kan nan nashi sama baki a buɗe sai sakin munsharin yake a gefe ɗaya yana sakin tusa a kai -a kai saboda alalar da suka ci da rana sannan ita suka ƙara ci kafin su kwanta. Juyi Mai Gari ya yi a cikin baccinsa ya ji wani uban wari da ya durfafi hancinsa hannunsa ya kai ya buɗe mayafin da ya rufa da shi sabo da sanyin da ake zugawa, jim kaɗan cikinsa da ya kumbura ya shiga ƙara ƙulululuuuu bakam ya tashi a 360 ya yi jifa da abin rufar sai gashi a zaune hajaran majaran yana jefa idanu a cikin duhun ɗakin warin da ya haɗe ɗakin ya sanya shi sanya hannu biyu ya toshe hancinsa. Ƙaran tusar Gwaggo Ramma da ta saki guda biyu a jere su ne suka daki kunnuwansa a take cikin Mai Gari ya cigaba da hautsina wa.
"Kayyasa! Bar ganin ka tara ka kiyayi mai nema, taɓɗi sinasir wannan tusa da kike yi Ramma kamar an rufe mutum a ɗakin mushe duk kin haɗe ɗaki da wari" Cewar Mai Gari a fili yana ƙara danna hannayensa a hancinsa jin warin tusar tasu gabaɗaya ya haɗe ɗakin. Hannu ya kai ya sakarwa Gwaggo Ramma wani ɗaɗe a ƙwabrin ƙafarta a kiɗime ta tashi ta zaune mazaunanta sai kuwa ƙaran wata tusar ya fito darrrrrr.


"Subhanallahi! Ni Ramma a cikin masai (Toilet) Nake ko a ina? "Ta furta a fili jin warin ɗakin ya game ko ina.


"Babu wata masai a cikin ɗakin ki kike haba! Ina dalili duk kin kumbura mini ciki tun da na tashi da ƙaran fitar iskar mazaunanki na fara cin karo tamkar ana sace iskar tayar motar tifa duk kin hargitsa mini cikina... Kafin Mai Gari ya ƙarasa maganar da yake yi fitowar wata ƙatuwar tusa mai cike da mugun ƙara ta masa shamaki da sauran maganar da yake son faɗa, da kallo mai kamar harara da kuma ka raina mini hankali Gwaggo Ramma da ta kunna tocilan ta bi Mai Gari dan sai yanzu ta tabbatar da cewa ashe dai ba ita kaɗai ta cika ɗaki da wari ba har da shi. Kunya ce ta sanya Mai Gari ya ɗauke kai dan a halin da ake ciki ma yanzu wata tusar ce take son fito masa amma yana ta yaƙi da ita a kan kar ta suɓuce ta fito dan haka sai ya shiga murtsika mazaunansa a kan tabarmar kabar da yake zaune wacce ko arziƙin shimfiɗa bata samu ba. Amma cikin rashin sa'a duk ƙoƙarinsa na ganin ya danne tusar nan haka ta ringa ɓarin mahaukaciya da ƙoƙarin nasa har dai ta samu nasarar fitowa tare da bada wani sauti da ya sanya Gwaggo miƙewa tsayi ba tare da ta san hakan ko ta shiryawa hakan ba dan ita dama a tsorace take da gidan nan da suka tare a jiya, wanda taku kaɗan za ka yi daga gidan ka je katangar maƙabarta da yake ma katangar ba wani tsayi ne da ita ba idan kana daga tsaye kana iya hango kaburbura, wannan dalilin ne ya sanya ƙaran fitowar tusar Mai Gari hautsila ƴan hanjin cikin Gwaggo Ramma. A take cikin nata ya wani birkita sai ita ma ta saki tusar ɓet-ɓaɓet, lokaci guda ta ji wata gudawa ta matso ta.


"Na shiga uku ni Ramma, in banda abin majinyaci na mai magani ne, yanzu a cikin daren nan anya kuwa zan iya zuwa bayi, in sauke nauyin cikin nan nawa, gashi kuma gudawa bata da haƙuri ko misƙala zarratan idan ta taho dole ne sai mutum ya tsiyayar da ita sannan zai samu salama...
Kafin ta dire maganar da take yi a zuciyar ta Mai Gari ya zabura ya miƙe tsaye a can gefen tabarmar da ya kwanta ya hangi tashi tocilan ɗin dan haka bai yi ƙasa a gwiwa ba ya kai hannu ya ɗauka da sauri ya juya ba tare da ya bi ta kan Gwaggon ba ya nufi hanyar fita daga ɗakin dan shi a yadda yanzun nan gudawar ta matso shi ba ya jin ko minti biyu zai iya jurewa ba tare da ya yi kashi ba dan haka ya ɗaura aniyar ficewa ya riga matarsa shiga bayi sabo da ya san kaf gidan dai bayi ɗaya ne kuma ya san matsawar Gwaggo ta riga shi shiga bayin nan sai ta Allah dan ya san zai iya sakin kashin na a wando kuma abon kunya ne a ce shi Mai Garin GUMURZU ya yi kashi a wandonsa. Gwaggo kallon Mai Gari ya suri fitilarsa ya nufi ƙofar fita sai zuciyarta ta raya mata cewar shi ma kashin zai je, dan ta san a yadda yake da tsoro kamar farar kura babu abin da zai fitar da shi daga ɗakin a daren nan sai dai kashi, dan ta ji yana tusa kuma ta tabbatar bayi zai yi wa dirar mikiya, wanda hakan kuma tamkar yaƙi zai yi da rashin fitowar nata gudawar wani kallo ta yi wa bayan koɗaɗɗiyar rigar sanyin jikinsa kafin cikin azama ta yi taku biyu ta rafko ƙasan rigarsa, Mai Gari jin an riƙe masa rigarsa sai da ya ji tamkar ya saki ihu dan ya ji kashinsa daf yake da fitowa gashi Ramma za ta masa cikas ɗin fitowar kashin a kan lokaci.


"Wallahi in dai bayi za ka shiga sai dai ka jira har in shiga in fito dan kashina yana bakin boda daf yake da hantsilowa babu abin da ya fi kamata da kashin nawa sai dai ya ji shi a cikin duniyar masai(Toilet) " Cewar Gwaggo Ramma cikin sababi. Mai Gari ji ya yi bashi da ƙarfin yin magana dan yana buɗe bakinsa gani yake kashin ne zai zubo dan haka a hankali ya juyo ya fuskanci Gwaggo Ramma ya ɗaga hannu biyu ya fara mata maganar bebaye dan ba ya so ya buɗe bakinsa gudawar ta fito bai shirya ba.Wata uwar harara Gwaggon ta jefa masa ta ja rigarsa ta mayar da shi gefe guda dan bata jin tana da ishashshen lokacin da har za ta tsaya kallon zancen bebayansa bare har ta gane mai yake so ya faɗa mata.


"Kar ki mini haka Ramma" Cewar Mai Gari cikin raɗa-raɗa dan ba ya so ya buɗe baki sosai kashin ya zubo. Ai kuwa cikin rashin sa'a maganar da ya yi duk da ya yi ta ne cikin raɗa amma sai dai kashin nan ya yi masa barazanar fitowa, da sauri ya saki fitilar hannunsa ya kai hannu biyun ya dafe mazaunansa saitin mafitar kashin dan yana ganin hakan shi kaɗai ne salama a gare shi na hana fitowar kashin ba shiri.

Gwaggo kuwa ko ta kan Mai Gari bata bi ba, ta buɗe ƙofar bakam ta fice a sukwane tana fatan Allah sa dai ta kai har bayin ba tare da gudawar ta zubo ba bare har ta ɓata zaninta, takalmin ma ƙafa ɗaya ta saka ɗayar kuma bata samu damar sakawa ba tsabar yadda kashin ya matse ta a hannu ta ɗauki ƙafa ɗayar takalmin. Cikin gudu-gudu sauri-sauri ta tasamma hanyar da za ta sada ta da bayi da yake da ɗan tazara daga ɗaki zuwa bayi.

Salele da shi ma kumburin cikinsa ne ya tashe sa yadda lokaci guda ya ji gudawa tana neman hanyar fitowa bai yi wata-wata ba ya kunna fitilar wayarsa mai madannai ya buɗe ƙofa ya fito burinsa kawai ya gan shi a cikin bayi, yana fitowa ya saka takalmansa a baibai da gudu ya tafi sai da suka kusan cin karo da Gwaggo da ke nata saurin mai haɗe da gudu tana riƙe da ƙafar takalmi a hannu da kuma fitila, ganin ita ma ta doshi hanyar bayi mamaki ya rufe shi, kafin ya dawo daga mamakin ya hango Kakansa Mai Gari shi ma ya taho da gudu hannayensa dafe da mazaunansa shi ko arziƙin saka takalmin ma bai samu ba.


"Bala'i yau ake yinta wallahi sai dai ku hau layi bayana dan babu wanda zan ɗaga wa ƙafa ya shiga bayin nan sai na shiga" Cewar Salele a zuciyarsa yana ƙara ɗaga ƙafa ganin Gwaggo da gaske neman rigaye shi zuwa take yi. Gwaggo da har wani numfashin gajiya take saukewa sai dai ganin ta kusa ƙurewa hanyar bayin gudu sai kawai ta ɗan ji daɗi a ranta, amma kuma tana dab da ƙofar bayin kawai sai ganin Salele ta yi kamar wanda ya diro daga sama ya shiga gabanta zai shige cikin bayin.


Wani irin zaro idanu ta yi tare da buɗe baki ta shiga cewa.


"Salele ka yi uwarka da ubanka da muka kawo su duniya, kai kuma suka kawo ka duniya kar ka shiga bayin nan wallahi idan ka shige ka shiga haƙƙina kai hatta da alhakina wallahi ka ɗauka dan ko ƙafar takalmi ɗaya ban samu zarafin tsayawa saka wa ba duk dan in je in sauke nauyin cikin nan nawa...


Kafin ta kai ƙarshen maganar Salele da ko kallo bata ishe shi ba, burinsa ya je ya tsugunna, haka ya shige ya barta a bakin ƙofar, dan duk saurinta ya riga ta ƙarasawa.


A hankali ta ɗago ƙafafunta ta baro bakin ƙofar sabo da wani wari da ya far wa hancinta, ga ƙaran gudawar Salele hakan ya tabbatar mata kashin ta yana dab da zubowa. Jin hakan sai ta haɗe ƙafafunta ta matse su ta ɗan sunkuya duk dan yaƙi da gudawar kar ta fito. Mai Gari da shi tsabar ruɗewarsa bai hangi Salele ba ma yana ƙarasowa ganin Gwaggo a sunkuye sai ya ji ransa fari ƙal dan haka ya nufi ƙofar bayin gadan-gadan. Yana shirin afkawa sai ya jiyo nishi da ƙaran kashin Salele tamkar mace mai nakuda.


"Oh ni Mai Gari Garba ma ga larura auren namiji da ƴaƴa, yanzu a ce wai kashi ma in za ka yi sai kana jiran layi sai ka ce wanda kake zaune a gidan haya" Ya faɗa a zuciyarsa yana jin babu daɗi a ransa da ya baro gidansa ya dawo wannan gidan sabo da aljannu da suke tsorata shi ashe dai ya yi gudun gara ne ya tarar da zago.
Gwaggo kuwa waige-waige ta fara ai kuwa ta sauke idanunta a kan wani tsohon kwanon silba rafkeke tana daga sunkuyen ta fara takawa a duƙe har ta kai wajen kwanon ta ɗauka dan ita da ta yi gudawar nan a zanenta gwara ta yi a kwanon dan ta san Salele ko kusa ba zai fito yanzu ba. Tana ɗaukan kwanon sai ta nufi wajen wani tsohon langa-langa za ta laɓe a wajen ta juye abin da yake cikinta, Mai Gari ma ganin ta ɗauki kwanon ta cikin hasken farin wata idanunsa suka sauka a kan wata tsohuwar samira (Kwano) Yashe a wajen dan haka shi ma bai yi bori da sanyin jiki ba ya ɗauke hannayensa daga jikin mazaunansa dan yana ganin nesa ta zo kusa, da sauri ya ɗauki kwanon ya shiga wani ɗan lungu da yake kusa da bayin.


Gwaggo Ramma da Mai Gari kusan a tare suka yi masauki a kan kwanukan da za su juyi abin da ke nuƙurƙusar su, amma kuma mai? Ƙaran wani uban bugu da aka yi wa ƙofar gidan nasu ne ya saka Gwaggo miƙe wa tsaye babu shiri, a ɓangaren Mai Gari ma hakan ce ta kasance dan shi bai san lokacin da ya faɗi ba daga shi har kwanon da ko ɗigon kashi bai yi a ciki ba, da sauri ya daure ya tashi dan ya san babu mai ɗaga shi ko taimaka masa ya tashi. Salele kuwa da shi ma bai kai ga gama nashi kashin ba hannunsa yana karkarwa ya ɗauki butar da take cikin bayin ya wanke ya miƙe daga tsugunnon, ko ta kan wayarsa raka ni kashi da ta faɗi a bayin bai bi ba, haka ya fito da gudu daga bayin.

Yana fitowa Mai Gari ma ya shawo kwanar lungun da ya shiga ai kuwa suka ci karo goshin su ya bugu da na juna, Gwaggo Ramma da take saurin ɗaura zanenta amma ya ƙi ɗauruwa sai kawai ta riƙe zanen a hannu fitilarta kuwa a baki ta saka a take ta ranta a na kare dan babu batun yin gudawa tun da ga abin da ya fi gudawa ya tunkaro su. Mai Gari kuwa ko ta kan goshinsa bai bi ba da suka yi karo da jikan nasa a haka ya fara gudun ceton ransa yana riƙe da tazuge da hannu ɗaya, ɗaya hannun kuwa yana hantsar wandonsa dan kar wandon ya faɗi.


"Ya Rahmanu, ya Rahimu" Su ne kalmomin da suke safa da marwa a zuciyar Mai Gari, dan ya san yau sai ta Allah ɓarawo a hannun mata tun da dai fatallun da ake labari a garin GUMURZU ta kawo musu farmaki sai yadda hali ya yi dan ya san shikenan kuma za ta musu ɗauki ɗai-ɗai shi da matarsa da kuma jikansa.


Salele da yake rike da tsantsar wandonsa da hannu biyu dan shi ma bai sami zarafin ɗaure tazugen na shi ba, a haka ya durfafi ɗakinsa yana fatan ya shige ya kulle ba tare da fatallun ta buɗe ƙofar gidan ta shigo ta fara ta kansa ba dan yanzu bugu bibbiyu ake yi wa ƙofar langa-langan gidan tamkar za a ɓalle, har ma da jikin langa-langan wanda aka kewaye gidan da shiw. Yana shiga ɗakin na shi ya banka ƙofar tare da garƙama sakata, jingina ya yi a jikin ƙofar yana mayar da lumfashi. Jin bugun ya yi yawa ya yanke shawarar ya lallaɓa wa ya koma makwancinsa ya kwanta sai ya rufa in ya so sai yake karanta fatiha da salatin annabi S.A.W ne ko da a ce fatallun ta zo in za ta ɗauke shi sai ya mutu da ɓurɓushin imani tun da yana karatu ba wai waƙa yake yi ba. Yana ɗaga ƙafarsa ya sauke ta a kan kwalbar lemon kwalbar coca colan da ya sha kafin ya kwanta ai kwa ta tafi suuuuuu tare da shi tamkar wanda yake a kan sirnane sufar da ya yi sai ya je a kife bakinsa ya bugu da simintin ɗakin da ko ledar tsakar ɗaki bai samu ba.
A hankali cikin zafin ciwo na goshinsa da suka yi gware da Mai Gari da kuma zafin buguwar da bakinsa ya yi amma a haka ya lallaɓa ya hau kan kalalliyar katifarsa ya kwanta lifet tare da rufa gabaɗaya har kansa sai ya ji ya gagara karanto komai ma sai faɗuwar da gabansa yake yi dan ƙirjinsa sai dakan lugude yake yi tamkar Bafulatana ta samu surfen hatsi(Gero).


Gwaggo Ramma kuwa riƙe da zanenta ta shiga ɗaki, tana zazzare ido dan ta daina jin kashin ma kwata -kwata tana shiga ta saka sakatar sama da ta ƙasa. Daɓas ta zauna tana mayar da numfashi, a cikin duhun ɗakin dan fitilar tata ma ta faɗi a hanya.


"Kai wallahi kam ni dai ina ganin takaici, haka kurum an ɗakko mu an kawo mu ƙarshen gari kusa da maƙabarta sunan ina matar Mai Gari gashi yanzu jafa'i zai same mu da rana tsaka fatallun da aka ce tana kashe mutane mus har lahira ga shi ta zo za ta yi wa gidan da muke ciki kutse da tsakar daren nan...


Ƙaran bugun ƙofar ɗakin nata ne ya sanya ta haɗiye wani yawu muƙut. A take ta shiga kokawa da lumfashin ta zuciyarta ta shiga raya mata cewa fatallun ba guda ɗaya bace wata ce take buga ƙofa wata kuma tuni ta shigo ta saman iska...


Maman Afrah Whatsapp 09013181851






*META FORCE ARZIƘI DAGA ALLAH*


ƳAR UWA SHIN BAKI DA LABARIN META FORCE? DA IRIN ƊINBIM ARZIƘIN DA AKE KWASHEWA A CIKINSA, YA AKA YI BAKI YI REGISTER BA? KO BAKI DA BUƘATAR KUƊAƊEN DA ZA KI YI HIDIMAR YAU DA KULLUM?


TO KI ZO NI MAMAN AFRAH NA ZO MIKI DA HANYAR SAMUN KUƊI TA WAYAR HANNUNKI KUƊIN YIN REGISTER KAWAI ZA KI TANADA 9K DUBU TARA DOMIN ANA YIN REGISTER DA DALA 5 NE SAI DAI ALLAH KAƊAI YA SAN IRIN RIBAR DA ZA KI SAMU DA KUMA ALKAIRAN DA YAKE CIKIN KASUWANCIN. IDAN KINA SO SHIGA KUMA DA GASKE KIKE KI MINI MAGANA A WANNAN NUMBER 09013181851 IDAN BA YI ZA KI YI BA KAR KI MINI MAGANA DAN BANA SON ƁATA LOKACI!
[8/19, 17:57] Mom mashkur & Afrah: *UNGOZOMA*
(Mai karɓar haihuwa)








NA



MAMAN AFRAH




F.C.W




GARGAƊI⚠️


Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ta kowace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowace kafa ba sai da izinina a kiyaye.




Page 3️⃣➡️4️⃣






Gwaggo Ramma sosai jikinta ya shiga karkarwa jin ana ta buga ɗakin nata, a take ta fara da na sanin rufe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login