Showing 21001 words to 24000 words out of 44948 words
Chapter 8 - UNGOZOMA Book Complete Original by Maman AFRAH F.txt
ina abin ma yake wai maye ya ci ɗan jinjiri, duk abin nan da kika gani ina sane wai karuwa ta taka matar aure, ai kowa ya yi nagari kansa, ki bari mu ga iya gudun ruwan UNGOZOMA tukunna ta faɗa tana kallon Gwaggo da take ta faman sharɓar gumi yankar ita ce take naƙudar, tun da a haifi ɗa da samu ya fi a mutu a bar masa gado"
"Ki taimaka baiwar Allah, duk wanda ya taimaki wani Allah zai taimake shi kuma ai faɗan da ya fi ƙarfinka wasa kake mayar da shi... Maganar Gwaggo ce ta yanke ganin Talatuwar tana wani irin mimmiƙewa, cikin tashin hankali kamar ta kama ta ta rirriƙe ta tana jijjiga ta.
"Ashshahadu an la'ilaha illlallahu wa ashshadu anna muhammadur rasulullahi" Cewar Gwaggo cikin ɗaga murya tana sakin wani kuka jin Talatuwar tana kalmar shahada.
"Dole ne ni ma in yi salatin nan, kar ki cika da kalmar shahada ki bar ni, in cika da hayagagar wofi dan na san ni da ke mutuwar kasko za mu yi tun da ga shi hannuna yana maƙale a jikin ki, to kuwa kina mutuwa na san tare za a haɗa mu a kabari ɗaya" Gwaggo ta faɗa tana sakin wani marayan kuka da ya sanya gaba ɗaya mutanen gidan suka jiyo ta.
Kakar ma kuka ta fasa mai wani irin ƙara, ganin jikin Talatuwar ya saki gaba ɗaya alamar ta daina numfashi.
"Shikenan ta faru ta ƙare an yi wa mai dami ɗaya sata, ni ma mutuwar zan yi yanzu, ni ma wallahi ba zan tafi ni kaɗai ba " Gwaggo ta faɗa tana kai hannun nata ɗaya ta danne Nasiru da yake bayanta ita ala dole ba za ta sauke shi ba tare za su mutu kamar yadda ita ma Talatuwar za ta tafi da ita.
Malam Mammani a sukwane ya shigo, yana zabgar nasa salatin dan yana jin kuka ya ji ya yi kama da na mutuwa, dan haka yana zuwa ya yi sufa har neman faɗuwa yake, sai ga shi a gaban Talatuwa ya yi zaman ƴan bori, haka ya wangame baki yana kuka yana faɗin
"Annabi ya san da zuwanki Talatuwa, Allah sa har a aljanna ke matata ce" Ya faɗa yana kauda kai gefe ya wani face majina ya goge da hannun rigarsa yana cigaba da kuka tamkar wani ƙaramin yaro haka suka kwatsu suna kukan tamkar dai an ce idan suna kukan za ta dawo.
Yana cikin kukan nan Gwaggo ta dakata da nata kukan ta sauke hannun nan nata daga baya inda ta danne Nasiru, ta ɗauki wani murfin silbar da aka kawo wa Talatuwar ruwa ta ɗaga ta sauke wa Malam Mammani a fuska dan a daidai inda hancinsa yake ta ƙwala masa zafin da ya ziyarce shi ne ya sanya ya yi ɗif daga kukan da ya dage yana zabgawa.
"Kai Mammani rufe ido ba makanta bane, kuma duk girman dutse bai kai ƙaramin goro ba, kuma wallahi bar ganin ka tara ka kiyayi mai nema, in banda dai son a sani gaida uwar miji a kasuwa, ka je har gidan mijina ka rabo ni da makawancina kana ganin na saka hannu zan duba yaro, yaron ya totsa hannuna ya riƙe maƙatau ƙofar da zan janyo hannun ma ta rufe ruf sai lanƙwasa mini yatsu ake, yanzu kuma matarka ta cika (Ta mutu) Ni kuma tun da, da sauran kwanana maimakon ka san yadda za a yi in kuɓuta, sai kawai ka zo kana addu'ar ta zama matarka a aljanna" Ta faɗa cikin muryar kuka.
Galala Malam Mammani ya saki baki yana kallon Gwaggo dan shi yadda ya ji zafin dukan murfin silbar ma sai ya rasa bakin magana dan sai a lokacin ma ya lura da cewa hannun Gwaggon yana maƙale a ciki mamaki al'ajabi su ne suka ziyarce shi kafin daga bisani wani bala'in tsoro ya masa dirar mikiya a zuciyarsa, a take ya haɗiye ɗan sauran kukan da yake son ya cigaba da rerawa dan ya fara tunanin ma ya tashi ya gudu.
Bai yi magana ba, ɗakin kuwa baka jin komai sai gunjin kukan Kaka, bai yi ƙasa a gwiwa ba ya fara lallaɓawa yana ƙoƙarin tashi, dan shi ya fara tunanin idan ya fita daga ɗakin babu abin da zai ƙara dawowa ya yi.
"Taɓ! Tabbas ana marin matacce ne dan mai rai ya ji tsoro, wallahi yau sai dai a yi wacce za a yi ɓera ya zubda garin mage, wallahi babu abin da zan tsaya yi dan yau na ga abin al'ajabi budurwa da ciki gwauro da yaye" Ya faɗa a ransa yana haɗiye wani yawu muduk. Yana daf da tashi Gwaggo ta saka hannunta ɗaya ta danna shi ya koma ya zauna cikin hargagi ta ce
"Mammani bari ka ji in faɗa maka wallahi abin ba zai iyu ba auren ɓera da mage, in banda abin ba'a ne an ce da kare mai sunan maza, ta yaya kai da muka taru a nan sabo da kai amma kake neman ka cikawa rigarka iska, ni ka bar ni da hannu lunƙume a jikin matacciyar matarka to ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa" Gwaggo Ramma ta faɗa tana aika masa saƙon harara.
"Keeee! Ke ɗin ma ki rufewa mutane baki, wallahi ku san yadda za ku yi ku fitar mini da hannuna daga jikin gawar nan, in ba haka ba daga ke har shi sai na mayar da ku ƙananun kiyashi, yadda babu wanda zai samu damar ganinku ma bare har ku bada labarin abin da ya faru" Gwaggo Ramma ta faɗa tana kallon Kaka da ta daddage tana rafka kuka, da Malam Mammani da ya koma ya yi zaman raƙumi sanadin durƙusar da shi da Gwaggon ta yi. Daga Kaka har Malam Mammani suka shiga mummunan tashin hankali jin furucin da Ramma ta yi, domin kuwa sun san sabo da bokancin marigayin ubanta kowa yana tsoron sharrinta. Haƙuri suka shiga bata amma fafur ta ƙi haƙura ta ce sai sun san yadda suka yi suka fito mata da hannu nata, kafin a sanar da kowa mutuwar, hatta matan gidan ma suna jin kukan amma basu san abin da yake faruwa ba. Kakar tashi ta yi daga kusa da Talatuwar ta dawo bayan Gwaggo ta ce
"Mammani, tashi ka kama Talatuwar ni in kama Ramma, sai mu ringa fisgarta ko Allah zai sa hannun ya fita...
"Sannu sara mai baƙin takashi, ga ki bulu ga ki jaja-jaja, wato ku ke fisgata sai ka ce wata akori kura, son a je ni ba a fitar mini da hannu ba a je hannun ya guntule gaba ɗaya in tashi daga Ramma UNGOZOMA in koma Ramma mai dungulumi" Gwaggo ta katse mata maganar. Malam Mammani kuwa shi gaba ɗaya an dagula masa lissafi jin an ce shi ne zai kama gawar, yana ganin ta yaya zai kama matar da ɗan jinjirin cikinta ya maƙale hannun UNGOZOMA, har da lanƙwasa mata yatsu lamarin da yake ƙara dulmiyar da shi kogin tsoro.
"Ka kama ta cikin dibara ku fitar mini da hannuna dan idan dai kuka bari muka yi mutuwar kasko da ita, aka binne mu, to kuwa ku ma ku sani naku kwanakin sun ƙare" Gwaggo Ramma ta faɗa cikin halin ko in kula.
"Ko dai in samo bushashshiyar kuɓewa, sai a dama da ruwa a shafa a hannun ko sulɓin zai sa hannun ya fito" Ya faɗa a ransa yana jin ya samo mafita, ba sai ya taɓa gawar ba dan yanzu a halin da ake ciki taɓa gawar shi ne babban tashin hankalinsa.
"Bari in samo wani magani zai taimaka sosai" Ya faɗa cikin rawar muryar dan yana tunanin ko ba lallai bane Rammar ta amince.
Shiru ta ɗan yi tana tunni da nazari a kan maganar, kafin cikin bada umarni ta ce
"Na yarda in dai magani ne, amma ka sani idan ka gudu ka ƙi dawowa, wallahi ni kaɗai na san hukuncin da zan maka"
"Wallahi babu inda zan je maganin kawai zan samo" Ya faɗa yana jin daɗi a ransa dan ya hango yadda zai yi ba tare da ya taɓa gawar ba. Buguzum-buguzum ya tashi ya fita, jim kaɗan sai ga shi ya dawo ɗauke da wani kwano, da ya ɗakko kuɓewar da ya jiƙa, yana shigowa ɗakin sai ya tarar da Gwaggo Ramma tana karkarwa, ita kuma Kaka ta raɓe a jikin bango ita ɗin ma karkarwar jikinta yake kamar mazari, a tsorace yake kallon su yana son gane asalin abin da ya firgita su lokaci guda daga fitarsa. Da hannu Kaka ta shiga nuna masa gawar, da rashin fahimta yake kallon gawar dan duk tunaninsa ma ko ba mutuwa ta yi ba, amma abin da ya ƙara dagula masa lissafi ganin tana nan a yadda take tun farko, yanzun ma a haka take, wato tana kwance a reran kanta ya karkata gefe.
"Ci, ci, cikin Talatuwa Kaka ta faɗa cikin ciccira maganar sabo da tsabar ruɗun da take ciki.
A hankali ya ɗaga idanun nasa ya sauke a kan cikin nata, abin da ya gani ne ya haifar masa da wata iriyar zabura sabo da tsoro, ƙafafunsa suka sage suka fara karkarwa tamkar wanda yake rawa a gaban makaɗi, har hakan ya haifar da faɗuwar kwanon da ya shigo da shi mai ɗauke da kwaɓaɓɓiyar kuɓewa.
*GIDAN MAI GARI*
"Ni wallahi ban taɓa ganin baƙar jaraba irin wannan ba, haka kawai babu gaira babu dalili ka saka mu a cikin masifar da fitowar ta sai wanda ya gani" Salele ya faɗa cikin raɗa shi ma yana sakin na shi marayan kukan marar sauti.
"Aikin banza roƙon a gidan kurma, wannan abin ai sai ido bebiya ta auri makaɗi" Mai Gari ya faɗa hawayen tausayin kansa suna gangaro masa, da sauri ya kai hannunsa wajen kansa jin inda ya ɗora kansa yana masa zafi domin kuwa a kan ƙurunƙusan tsakuwar ɗakin ya ɗora kan.
*LAILA*
Tun da suka fita suka bar ta a ɗakin, ta yi kwanciyarta a kan gadon ƙarfen Gwaggo wanda dakyar ya ɗauke ta, duk da haka sai ƙiƙar-ƙiƙar yake tamkar zai ruguje. Kwanciyarta ke da wuya bacci ya ɗan fara ɗaukanta, sai kawai ta ji alamun tusa tana neman hanyar fitowa, a kiɗime ta tashi zaune ta shiga ƙwalawa Taju kira dan ya zo ko da a kansa ne ko kuma wani mai rabon ta saki tusar, sabo da ta san tabbas idan ta saki tusar ba tare da ta zauna akan kowa ba to akwai matsala, domin kuwa tsagar mazaunan nata ce take ƙaruwa, sai wurin ya tsage amma matuƙar ta zauna a kan wani to babu abin da zai faru da ita, hakan ne ma ya sanya ba ta yarda ta yi tusa sai ta zauna a kan mutum, dan wani lokacin har kuɗi take biyan mutane ta zauna a kan su ta yi rusar. Tun da ta fara kiransa ta ji bai amsa ba sai hankalin ta ya tashi, jin tusar tana neman fitowa sai ta fara ƙoƙarin sama wa kanta mafita ta hanyar tasowa ta buɗe ƙofar ta fito domin zuwa ɗakin da su Tajun suke ko ta samu ta kai farmakin yin tusar tata a kan mai rabo, dan duk wanda ta fara samu to kakarta ta yanke saƙa, haka ta fito riƙe da fitila.
Su Mai Gari kuwa tun da suka ji motsin ƙofa suka ƙara shiga halin ƙaƙanika yi.
"Shikenan kuma mu yau sai yadda hali ya yi karuwa ta ga ɗan sanda, nin banda tashin hankali faɗa da mai gari ranar sallah, ya za a yi a ce sai an zauna a kan mutum za a saki tusa sabo da Allah kamar wanda aka samu kujera" Cewar Mai Gari a ransa yana jin kamar ya yi tsuntsuwa ya gudu dan kar Laila ta ritsa da shi. Jin ta turo ƙofar ɗakin sai kowa ya yi lif tamkar masu bacci har da masu sakin munshari a kai - a kai. a firgice ta shigo tana neman ɗauki sanadin jin tusar tana dab da fitowa. Tana shigowa sai ta haska fitila ai kuwa ta gan su kwance sun yi murhu da kawunansu.
"Shikenan tusa ta za ta fito cikin salama, tun da ga shi a kawunan mutane har uku zan sake ta" Ta faɗa a ranta tana nufar su cikin sassarfa, tana zuwa ta daddage ta ɗora mazaunanta a kawunansu inda suka yi murhun tana ɗorawa kusa tusar kamar jira take a fito da wani irin ƙara da ya bada sautin booottttt. Fitar sautin tusar ne ya sanya kunnuwansu yin dimmm tare da ɗaukewar jin su na sakkanni.
Sai kuma lokaci guda wani uban wari mai kamar mushen akuya ya mamaye gaba ɗaya ɗakin. Laila kuwa sake ɗan karkata mazaunan nata ta sake yi domin wata tusar ta samu damar fitowa.
"Kin kashe mu" Mai Gari ya faɗa jin wari da nauyin danne su ɗin da ta yi yana bazaranar sumar da shi.
"Wayyo an saka hancina a tekun maliyar kashi" Salele ya faɗa yana ta ƙoƙari ya samu inda hancinsa zai shaƙo masa wata iskar ba wacce yake shaƙa ba mai wari da ɗoyin tsiya...
Maman Afrah Wtsapp 09013181851
*META FORCE ARZIƘI DAGA ALLAH*
ƳAR UWA SHIN BAKI DA LABARIN META FORCE? DA IRIN ƊINBIM ARZIƘIN DA AKE KWASHEWA A CIKINSA, YA AKA YI BAKI YI REGISTER BA? KO BAKI DA BUƘATAR KUƊAƊEN DA ZA KI YI HIDIMAR YAU DA KULLUM?
TO KI ZO NI MAMAN AFRAH NA ZO MIKI DA HANYAR SAMUN KUƊI TA WAYAR HANNUNKI KUƊIN YIN REGISTER KAWAI ZA KI TANADA 9K DUBU TARA DOMIN ANA YIN REGISTER DA DALA 5 NE SAI DAI ALLAH KAƊAI YA SAN IRIN RIBAR DA ZA KI SAMU DA KUMA ALKAIRAN DA YAKE CIKIN KASUWANCIN. IDAN KINA SO SHIGA KUMA DA GASKE KIKE KI MINI MAGANA A WANNAN NUMBER 09013181851 IDAN BA YI ZA KI YI BA KAR KI MINI MAGANA DAN BANA SON ƁATA LOKACI!
[8/19, 17:57] Mom mashkur & Afrah: UNGOZOMA
(Mai karɓar haihuwa)
NA
MAMAN AFRAH
FCW
GARGAƊI⚠️
Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ta kowace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowace kafa ba sai da izinina a kiyaye.
Ina mata ƴan ƙwalisa, babbar mace alkyabbar mata, macen mai gyara ita wacce ta isa da miji su o'o sai dai su ga ƙeyar mijinta idan ya wuce amma basu ishe shi kallo ba domin babu abin da za su nuna mata. Gyaran gashi babbar martaba ce da take ɗaga darajar mace, musamman kayan gyaran gashin MAMAN ZEE da ya yi fice a ko ina ake labarinsa. Gani ya kori ji sai an gwada akan san na ƙwarai siyan na gari mayar da kuɗi gida💃💃💃💃💃💃💃💃
Hadaddu Kuma ingantattun kayan gyaran gashin mamanzee(chebe hair set)
Wadanda suke dawowa da martabar gashin Kai komai lalacewarsa biiznillahi Rabbi
Ga kyau ga inganci ga saukin kudi muddin kika fara amfani da kayammu sekindawo Mana da kyakkyawan labari
Kanki zeyi kyau ya rika sheki yayi tsayi yayi laushi duk matsalar da ke cikin kanki zata kau in sha Allah
Munada set complete
Kuma Muna Bada pieces
Haka Kuma Muna Bada Sari
Muna turawa akowanne gari kike Kuma Ako wacce kasa kike
Phone number *08079130166*
Page 1️⃣5️⃣➡️1️⃣6️⃣
*MALAM MAMMANI*
Ƙurawa inda yake kallon ido ya yi, ganin dai tabbas ba gizo idanun nasa suke masa ba sai ya ƙara shiga mummunan tashin hankali, lokaci guda ya ji maƙoshinsa ya bushe.
"Jama'a kuna ganin abin da nake gani kuwa? Yadda nake ganin cikin Talatuwa yana rausaya ubangiji ya nuna mini annabi haka" Gwaggo Ramma ta faɗa cikin sumbatu.
"Lahaula wala quwwata illah billahi aliyal azim, rabbi lima anzalta ilayya min kairin faƙiir" Malam Mammani ya faɗa yana jin jikinsa har wani zafi yake ɗauka kamar wanda zazzafi ya rufe.
"Wallahi ƙur'ani muna gani Ramma ba ke kaɗai kike gani ba" Kakar Talatuwa da abin ya so zautarwa ta faɗa a tsorace. Suna cikin hakan sai kawai suka ga bulll, jaririn ya bullukuto kan nasa ta tsakiyar cikin Talatuwa sai dai iya kansa ne kaɗai ya fito, gabaɗaya sun ma manta da maganar mutuwar Talatua bare su ce ita ce take motsi, tun da dai sun san ta mutu, musamman Gwaggo Ramma da hannunta yaƙe ƙunshe a jikin Talatuwa.
Tun da ya fito da kan yake ta rausaya kan alamar rawa, gaba ɗaya kasaƙe suka yi dan sun yi mutuwar tsaye suna ganin ikon Allah, musamman Gwaggo Ramma da ta ga saitin ta yake kallo, kafin su gama tantancewa sai gani suka yi ya yi tsalle ya fito daga cikin Shamsiyya yana rarraba ido. Hannunsa ɗaya riƙe da cibiyarsa da uwa wacce take faɗowa idan an haifi jarirai. Babu zato ba tsammani ya buɗe baki ya tsanyara kuka irin na jarirai.
"Gwara dai in yi kukan da kowane jariri yake idan ya diro duniya" Ya faɗa yana ƙara rausaya kan nasa tamkar wani ƙadangare. Kukan sa ya yi shi ya sanya matan gidan da suka jiyo kukan suka tabbatar Talatuwa ta haihu. A daidai gaban Malam Mammani ya dira, ƙafafunsa suka sauka a kan kuɓewar da ta zube, jin santsin ledar tsakar ɗakin zai kayar da shi sai ya yi saurin miƙa hannunsa wanda babu komai ya kamo rigar Malam Mammani, Malam Mammani kuwa mutuwar tsaye ya yi, a take ya ji numfashinsa ya tsaya cak jikinsa ya cigaba da rawar tamkar dai wanda aka saka a firiza.
"Baba wallahi na kusa shan ƙasa, Allah ya sa kana kusa Babana da tuni santsin kuɓewar nan ya daɗe da tiƙa jaririn da ya dira duniya yanzu-yanzu da ƙasa" Cewar jaririn cikin muryar yara ƙanana masu koyan magana. Malam kuwa idanunsa ya sauke ƙasa suka sauka a kan jaririn da ya kira shi da suna Babansa.
Gwaggo kuwa tun da ta ga jaririn ya nufi wajen Babansa sai ta bada himma wajen karanta addu'a a hankali