Showing 39001 words to 42000 words out of 44948 words

Chapter 14 - UNGOZOMA Book Complete Original by Maman AFRAH F.txt

19 Oct 2024

5943

a ranta tana ganin yadda gaba ɗaya mazaunan Laila suka mata rumfa ba ta ganin komai sai Lailar a samanta. Tun da Laila ta zaune Gwaggo take sakin iska kamar an cakawa tayar mota ƙarfe sai sacewa take babu birki Gwaggo sai addu'a take saki a zuciyarta ga wari ga kuma nauyin Laila. Can Gwaggo da ta ga abin ba na ƙare bane Laila ta ƙi ɗaga ta sai kawai ta fara zubar hawaye a take tunnin su Mai Gari ya faɗo mata, na jiya da suke ba ta labarin yadda Lailar ta zaune su ta rinƙa sakin tusar a kan su tamkar wanda aka aiko ta, har ma Mai Gari yana cewa ko dai kansa ya logaɓe tana ganin jiya da goho ta kwanta saboda ciwon da fuskarsa da kansa suke masa amma lokacin da suke labarta mata, amma ta mayar da abin labarin ƙanzon kurege wato ba komai ba dan tana tunanin raki ne kawai irin nasu da rashin juriya, sai ga shi ita cikin mintuna ƙalilan tana neman ɗauki bata ma san su Mai Gari su iya mintunan da Lailar ta kwashe jibge a kan su ba. Cikin dibara ta ɗago bakinta duk da tana jin warin amma a haka ta jure dan idan ka ji ana ba zan iya ba to bai kama ka bane. Bakinta ta hangame ta saiti ɓari ɗaya na mazaunan Laila ta ɗora mata haƙoranta talatin da biyu.


Laila da hankalinta kwance take sakin tusa babu ko ƙaƙƙautawa sai wani rausaya kai take kamar ƙadangaruwa ɗ, har wani lumshe idanu take kamar ɗan mayen da ya sha ya bugu dan ita a wurinta yin tusa ba ƙaramar samun lafiya bane a gare ta. Tana cikin wannan yanayi na jin daɗin fitar da iskar sai kawai ta ji saukar cizo a mazaunan ta, yadda Gwaggo ta saka tsokar mazaunan Laila a tsakanin haƙoranta na sama da ƙasa ta dantse tamkar kaca a jikin keke ko sakawa ba ta yi ba. A kiɗime Laila ta yi hanzarin tashi dan sai ta ji tamkar an caka mata tsinin mashi sai dai tana tashi sai ta ji gefen mazaunan nata in da Gwaggon ta damƙa da haƙori gaba ɗaya a riƙe yake, tamkar an saka mayen ƙarfe a jikin ƙarfe, ja take amma ina Gwaggo ta riƙe wurin gamgam dan har idanu ta rintse ta dage ƙarfinta dan so take sai Laila ta gane shayi ruwa ne, dan ta lura a zaman nan da ta fara daga jiya zuwa yau idan har ba sa yunƙurin ƙwatawa kansu ƴanci to tabbas bayan dara akwai wata caca. Dan ta fahimci duk abin da suke yi ihu ne bayan hari.




Laila tsabar azaba da sauri ta sake komawa ta zaune kan Gwaggo da bakinta yake a sama, ƙara kaimi Gwaggon ta yi wajen datsa haƙoran Laila ta sake tashi tana faɗin.


"Ramma ki yi wa Allah da ma'aiki kar ki tsunguye mini tsokar ɓarin mazaunai"


"In dai da hankalinki nan gaba ko an ce zaune Ramma ba za ki fara ba ma" Gwaggo ta faɗa a ranta cike da mugunta duk da a wani ɓari na zuciyarta tana shakkar abin da zai je ya zo na hukunci da Lailar za ta mata sai dai ta san ko ma mene ne sai dai ta mata horo da wani abun amma ba wannan ba dan ta riga da ta san hukunci da zaunewa dole ya zama tarihi, dan ta tabbatar mazaunan Lailar sun cizu. Laila jin abin ba na ƙare bane wai tsoho ya samu amarya budurwa sai kawai ta shiga tafiya domin ko ta samu Gwaggo ta saka mata mazaunan haka ta fara tafiya ƙafafu a tattale kamar sabuwar ƴar maye ga shi ta ɗan ranƙafa kamar wata tsohuwa. Ƙiiii take jan Gwaggo da take kwance reran a ƙasa haka suka shiga zagaye ɗakin amma Gwaggo dan ƙarfin hali ɓarawo da sallama ba ta saki Laila ba, wani marayan kuka ne ya ƙwacewa Laila dan dafin haƙorin Gwaggo ya wuce tunaninta. Gwaggo jin Laila ta fara kuka sai haka ya nuna mata cewa haƙarta ta cimma ruwa dan haka sai ta saka cizon da ta yi wa Lailar, cikin tafiya ƙafa a gwale tana sakin numfashin wahala ga hawaye yana kwaranya sai ta lallaɓa ta je jikin gadon ɗakin ta daddafe da hanayenta ta saki wani nishi da ƙarfinta tamkar mai naƙudar da ɗa yake shirin fitowa daga jikinta, a take wata tusa mai ƙata booooot ta fito a jere har guda huɗu, karkata kai Laila ta yi gefe ta ɗora kan nata a kan kafaɗarta tana sauke numfashin wahala.


"Wa ya faɗa miki barno gabas take, dama ai ni na san salon munafurci ne wai auren mijin ƙawa, har za ki ce bakya yin tusa sai kin zauna a kan mutane, yanzu kuma da kika ji uwar bari a kan uban wa kika saki tusar? Duk da na san ramako zai biyo baya wai auren uban ƙawa, amma dai ai yanzu na san na yi wai makaho ta taka kashi ko ma mai za ki mini na san sagegeduwa ne bin diddigin budurwar miji" Gwaggo da take yashe reran a tsakar ɗakin ta faɗa a zuciyarta tana kallon Laila da take tsaye har lokacin tana yadda take.






"Ramma ni kika yi wa wannan ɗiban albarkar? To ki kwana da sanin bashi kika ci kuma sai na rama wai miji ya yi wa matarsa kishiya ta auri ubansa bayan ta bar gidan" Laila ta faɗa a zuciyarta tana jin haushin abin da Gwaggon ta mata dan ta san yanzu tusar nan da ta saki ba a kan kowa ba to tabbas sai jikin mazaunanta sun tsage.


"Sannu Ranki ya daɗe, sannu da dole ke dai kam kin haɗu da jarabawar rayuwa mai wahala tusa a ce mutum ya yi ta sakin tusa kamar bodari" Cewar Gwaggo da ta yi wani firgigit ta tashi zaune tana murza idanu ita ala dole yanzu ta farfaɗo. Banza Laila ta mata tana juyowa ta shiga aika mata da harara har lokacin Gwaggon tana murza idanu har wani gwale su take.


"Ai mun samu lafiya tun da na samo maganinki" Gwaggo ta faɗa a ranta tana danne dariyarta dan ita jin daɗi ji take tamkar ta tashi ta shiga taka rawa.


"Ni kaina ban san halin da nake ba, tun da kika zaune ni sai na rasa suma na yi ne ko kuwa tsofaffin aljannun kaina ne da suka daɗe basu tashi ba suka tashi, dan har wani abu na ji an hangame bakina ana saka mini kamar wasu ƙarafa Allah dai ya sa basu cake ki ba" Gwaggo ta faɗa cikin sanyin murya har da wani rausaya kai ita ala dole tana so ta nunawa Laila cewar duk abin da ya faru ba ta san ya faru ba dan ba ma a cikin hayyacinta take ba. Wani kallo kawai Laila ta mata na kin ma ranawa kan ki hankali ta ɗauke kai kamar ma ba da ita Gwaggon take ba.


"Taɓ ba dai baki yarda da ƙaryar da na shirgo miki ba lallai akwai badaƙala wai dambe da sirika a titi" Gwaggo ta faɗa a ranta tana haɗiye wani yawu muƙut dan ta san tabbas dai bayan dara akwai wata caca.


"Za ki san ni kika yi wa haka dan sai kin gwammace kiɗa da karatu, domin tsakanina da ke akwai ƙura wai mai kaya ya kama ɓarawo da kayansa, dan sai in da mai ya ƙare shiga motar mahaukaci" Laila ta faɗa a ranta tana ɗan jijjiga kai a fili kuma sai ta ce.


"Ayya! Ai ni ma na lura da haka babu komai ai dama mutane masu shafar aljannu sun saba yin haka"


"Tabbas kin yi kuskure da kika yarda da maganata dan na samo lagwanki mu zuba ni da ke, dan yarda da maganata da kika yi haƙiƙa kin yi ƙundunbala wai naushin mashayin giya" Gwaggo ta faɗa a zuciyarta a fili kuma sai ta ce.


"Yawwa godiya nake Ranki ya daɗe"


"Za ki iya tafiya" Cewar Laila cikin murtuke fuska dan ta san yanzu sai ta yi jinyar mazaunanta, saboda tsagewar da suka yi dan ta san duk lokacin da ta yi tusa ba a kan mutum ba to tabbas sai ta samu wannan matsalar. Dakyar Gwaggo ta muskuta ta tashi tsaye tana jin jikinta tamkar wanda ƙattan maza suka yi wa dukan kawo wuƙa saboda ciwon da jikinta yake musamman da Lailar ta tashi daga kanta ta sake komawa ta jaɓe kamar kayan wanki duk a kan nata ga bakinta har wani zafi yake saboda ciwon da ta daddage ta yi, amma dai da dama-dama wai kibiya a ido tun da ga shi yanzu kwalliya ta biya kuɗin sabulu.


Haka ta taso ta fito daga ɗakin ranta fari ƙal, tana shiga ɗakin nasu ta zauna tana ta tiƙar dariyar ƙetar da ta yi wa Laila, shi kuwa Mai Gari sai taya ta dariyar yake yana faɗin ta masa dai dai duk abin da suke yi basu san Laila tana tsaye a laɓe tana jin duk abin da suke cewa.




Haka dai aka yi wunin ranar kowa ya sha jinin jikinsa Laila kuma zaman kirki ma ba ta iyawa saboda yadda mazaunanta suke mata raɗaɗi. Gwaggo kuwa abincin ranar da ta dafa jikinta sai ciwo yake dan ba laifi ta aikatu.


*DARE*


Zaune suke a ɗakin su duka kowa da abin da yake tunani, Mai Gari ya rasa mai yake masa daɗi dan ya saba ya ci ya ƙoshi amma wunin ranar yau duk sai sam barka domin abincin da ya ci a yau akwai ya babu ne kakar wajen uba, dan haka yanzu cikinsa sai kiran ciroma yake kawai baccin ma ya gagare shi shi ne ya tashi zaune ya jingina da bango yake faman ambaton Allah ko ya samu sassaucin yunwar da yake.


"Bunnu ta ƙi binnuwa" Salele ya faɗa cike da sheƙiyanci.


"Inuwa" Taju ya ba shi amsa yana danne dariyarsa dan ya san Mai Gari Salele zai yi wa sheƙiyanci shi ya sa ya fara haka.


"Na waiga -na waiga ban ganta ba"


"Ƙeya" Taju ya ƙara ba Salele amsa.


"Shanun gidanmu dubu-dubu amma a turke ɗaya ake ɗaure su"


"Tsintsiya"


"Faɗe yaro faɗe babba" Salele ya faɗa lokacin gaba ɗaya dariyar da yake dannewa ta fara bayyana a cikin maganarsa.


"Yunwa" Taju ya faɗa yana tuntsurewa da dariya, dan dama ya san kwanan zancen dan Salele ya san Mai Gari yana jin yunwa shi ya sa ya tarki zayyanowa dan ya zo in da zai ce faɗe yaro faɗe babba. Salele ma dariyar yake yi har da ƙyaƙyatawa dan kana kallon idanun Mai Gari za ka san ya haɗu da gamonsa wato yunwa.


"Allah dai ya tsinewa yunwar, sakarkarun banza sakarkarun wofi, ban da iya shege taɗe ƙafar makaho ni za ku zauna kuna yi wa sheƙiyanci wancan ba Kakar ku bace ko ita yunwar ba ta faɗe ta ba sai ni marenin wayon ku" Mai Gari da dama kaar jira yake ya fara surfa faɗa yana kumfar baki tamkar dai su ne suka hana shi abinci ya ci ya ƙoshi.


"Ran Mai Gari ya daɗe Allah dai ya taimaki Mai Garin Gumurzu wa ya isa ya ja da kai" Salele ya faɗa.


"Sai yunwa" Taju ya faɗa har lokacin yana dariyar, dan ya kasa riƙe dariyar musamman yadda Mai Gari yake nuna su da yatsa tamkar wanda suka yi masa sata.






"Wallahi Taju ka kiyaye ni, mutumin banza da wofi ni nan da kake gani labule ne ni rufin asirin ɗaki, kuma kowa ya ci tuwo da ni miya ya sha, hatsabibin banza in banda kai sha ka tafi ne kana soja amma ka kawo mana jaraba gida ai ni gwara da ka cire kayan sojojin ka ajiye ni ban ga amfaninsu ba aikin banza harara a duhu" Ya faɗa yana jan tsaki tare da komawa ya jingina da bango jin idanunsa suna ganin duhu-duhu saboda yunwar da yake ji.




"To Mai Gari ya kake so na mata ne ka dai ga yadda take ƙatuwa"


"Yo ƙatuwar me, girman banza ne fa yanzu wannan soson katifa sai ya fi ta nauyi abu shirgaga kamar bijimin sa...


"Ramma, Ramma" Muryar Laila da ta turo ƙofar ɗakin da take kira Gwaggo ta katse wa Mai Gari maganar. Gwaggo da take ringishe abin duniya ya haɗe mata goma da ashirin tana tsoron bacci ya ɗauke ta dare ya tsala jaririn jiya ya zo mata sannan a gefe ɗaya tana fargabar zuwa kiranta UNGOZOMANCI dan ita gaba ɗaya yanzu abin ya fice mata a rai.


"Laila, Laila, Laila, sarauniyar kyau Laila, mai halin dattako, tausayi da kyautatawa riƙon amana Laila" Mai Gari da ya fara waƙar da babu shiri tamkar sabon maroƙi, shi kansa jin baitocin ya yi suna masa dirar mikiya bai ma san asalin waƙar ta ya aka yi ta zo a kansa ba. Burinsa bai wuce a ce Laila ba ta ji abin da ya faɗa ba dan ya san in har ta ji to kashinsa ya bushe.
Ko kallonsa Laila ba ta yi ba duk irin yaƙi da ƙugin da cikinsa yake masa da ya yi, ya hangame baki yana rattabo baitikan.


Gwaggo kuwa gabanta ne ya bada rasss, dan babu abin da ta ƙi jini irin a zo kiranta karɓar haihuwa dan yanzu har ta fi ƙin jin tsoron kiran Laila ta tsani kiran karɓar haihuwar tun da ta samu tangarɗar nan.


"Na'am Ranki ya daɗe" Ta faɗa lokacin da ta tashi zaune tana gyara ɗaurin ɗankwalinta da ya sunce


"Duk kun cikawa mutane kunne da hayaniya, ana ta buga gida bakwa ji"


"Bugun gida kuma Ranki ya daɗe?" Gwaggo ta yi saurin tambaya gabanta yana faɗuwa tana fatan Allah ya sa ba ita aka zo kira ba.


"Wasu ne suka zo kiranki, tun da ke kin san sana'arki kamar fashi da makami take, wato har da dare ma ana zuwa kiranki ai ba kwa kw surutu ba yanzu sai ni na je na tambayo da bugun ƙofar ya dame ni"


"Allah ƙadiran wa maridan wa aliman wa hayyan" Gwaggo ta faɗa a ranta tana jin kamar dai ta suma saboda tsoro da tashin hankalin da ta shiga, dan ita ba dan mutanen gari za su ce ta gaza ba da ta daina karɓar haihuwar sai dai ta riga da ta san cewa kasawa ce yin hakan kuma ma alƙawarin Kakanta da ya bar mata sana'ar nan ya mata hanyar samunta.


"Wallahi ka bar mini gadon wahala" Ta faɗa a ranta tana jin ƙwalla tana ciko mata.








"Wai ya ana miki magana kin tsaya wani abu" Laila ta faɗa a zafafe wanda hakan ya sanya Mai Gari babu shiri ya tashi tsaye dan shi kansa bai san ya aka yi ya tashi ba ya dai gan shi a tsaye yana dawurwurin nema in da zai bi, saboda a tsorace yake matuƙa ya san matsawar dai Lailar ta ji abin da yake faɗa a kan ta na wulaƙanci to tabbas za a kwashi ƴan kallo. Gwaggo kuwa cikin sanyin jiki ta tashi ta ɗakko aska da zaren ta fara tafiya tamkar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki dan ko jiya da ta fita aikin INGOZOMANCIN nan gidan Malam Mammani haka ta je ta sha baƙar wahala ta dawo babu ko sisi yo wa yake ta kuɗi ma yana ta ceton rai da ta samu ta kuɓuto dakyar. Juyawa Laila ta yi ta fita Gwaggo ta take mata baya, Mai Gari kuwa da sauri ya koma ya zauna yana maida numfashi ganin Laila ba ta ji abin da yake cewa ba dan ya san da a ce ta ji to tabbas da ta yi magana. Salele da Taju kuwa dariyar da suke dannewa ce ta fito fili dan tun shigowar Laila suka yi wa idanunsu masauki a kan Mai Gari yadda ya yi wani wurjanjan kamar kwarton da mai gida ya kama.


"Ansitu lilƙaniyatukum" Mai Gari ya faɗa.


"To fa Mai Gari ya fara koyo larabci wato mu yi shiru dan ƙaniyar mu" Taju ya faɗa yana ƙara dariya har da riƙe ciki. Salele ma dariyar yake yana rufe bakinsa da tafin hannunsa.


"Ku ungo ku raba" Mai Gari ya faɗa yana watsa musu yatsun sa biyar alamar daƙuwa.




*KAFIN A GAMA FREE PAGES MAI BUƘATA ZAI BIYA KUƊIN KARATU 400 IDAN NA KAMMALA FREE PAGES ZAI KOMA 500 ZA A BIYA TA ASUSUN FAIZA ABUBAKAR 9030283375 OPAY SHAIDAR BIYA TA 09013181851* .
[8/19, 17:57] Mom mashkur & Afrah: UNGOZOMA
(Mai karɓar haihuwa)


NA








MAMAN AFRAH




F.C.W




GARGAƊI⚠️


Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ta kowace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowace kafa ba sai da izinina a kiyaye.






*PAID ADVERT 1* 💃


Ina mata ƴan ƙwalisa, babbar mace alkyabbar mata, macen mai gyara ita wacce ta isa da miji su o'o sai dai su ga ƙeyar mijinta idan ya wuce amma basu ishe shi kallo ba domin babu abin da za su nuna mata. Gyaran gashi babbar martaba ce da take ɗaga darajar mace, musamman kayan gyaran gashin MAMAN ZEE da ya yi fice a ko ina ake labarinsa. Gani ya kori ji sai an gwada akan san na ƙwarai siyan na gari mayar da kuɗi gida💃💃💃💃💃💃💃💃
Hadaddu Kuma ingantattun kayan gyaran gashin mamanzee(chebe hair set)
Wadanda suke dawowa da martabar gashin Kai komai lalacewarsa biiznillahi Rabbi


Ga kyau ga inganci ga saukin kudi muddin kika fara amfani da kayammu sekindawo Mana da kyakkyawan labari
Kanki zeyi kyau ya rika sheki yayi tsayi yayi laushi duk matsalar da ke cikin kanki zata kau in sha Allah
Munada set complete
Kuma Muna Bada pieces
Haka Kuma Muna Bada Sari
Muna turawa akowanne gari kike Kuma Ako wacce kasa kike


Phone number *08079130166*




*PAID ADVERT 2* 💃

*BOJUWA HERBAL'S & SCENTS*
*Suna kawo Saiwowin sanyi da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.*
*Haka nan akwai dafaffen maganin ga wanda tafi son ready made.*
*Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah*
*Saiwowin tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru*
*Saiwowin matsi gangariya*
*Original gadalin mata*
*Ƴaƴan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login