Showing 36001 words to 39000 words out of 44948 words
Chapter 13 - UNGOZOMA Book Complete Original by Maman AFRAH F.txt
nan sabo da neman sababi dambe da uwar kishiya? Ni ba ma wannan bane abin da ya ɓata mini rai yadda kika saka zuciyata bugun lugude da faɗuwar gaban da na rinƙa yi, da za a yanka jikina ko ɗigon jini ba za a samu ba, sabo da yadda na razana duk tunanina matar nan ce ta ƙara kawo farmaki domin ta saki tusar ta a kan ƙafafuna. Da in banda son a sani gaishe da uwar miji a kasuwa a ce wai tusa wannan idan za a yi ba za a yi ta a sirri ba sai an taho yawon bankaɗa a zaune mutane kamar wasu kiyashi za a sake ta" Mai gari ya shiga faɗa yana surfa masifa amma har lokacin a tsorace yake dan bai gama wartsakewa daga tsoratar da ya yi ba, sai dai duk da haka a hankali yake faɗan dan kar Laila ta jiyo, yo ana tsoronka ɗan mayya, ya ce daga ni har uwata. Gwaggo ko kallon Mai Gari ba ta yi ba hasali ma idanu take wurwurgawa domin ganin in da jaririn yake sai sakin numfarfashi take tamkar wacce ta yi tseran gudu. Dan ko maganar da Mai Garin yake ma ba ta fahimtar komai ita kaɗai ta san abin da take ji.
"Wai ba magana ba nake ba kin bar ni sai zuba nake kamar bishiyar kanya to wallahi kar ki ƙara zuwar mini shimfiɗa, tun da dai yanzu kin san ba mu kaɗai bane a ɗakin an kwamustsa mu a ɗaki ɗaya da ƙartan samari"
Har lokacin ba ta furta komai ba, zaune ta tashi dakyar tana jin tamkar an an bubbuga mata taɓarya a jikin. Tana tashi ta cigaba da ƙarewa ɗakin kallo amma abin mamaki wai kwalli a ido babu alamar jariri babu dalilinsa. Wasu nannauyin ajiyar zuciya Gwaggo ta sauke ƙwarara a jere guda uku, sannan ta shiga haɗiye yawu muƙut.
"Wai haka kawai kin tashe ni daga bacci, kin mayar da ni sauna kira mana shashasha in ka ga sakarai ku taho tare sai wani ciccira idanu kike kamar an kama kwarto a ɗakin sabuwar amaryar data cika sati da tarewa ba, to wallahi idan matar nan ta jiyo hayaniya ta tashi ta zo yin tusa sai dai ta murƙushe ki ke kaɗai" Ya faɗa yana aika mata harara.
"Haba kai baka san dalili ne yake sa a leƙa gaban surika ba, in ba akwai abin da ya kawo ni ba mai zai sa in zo wajenka a sulusun daren nan amma ka balbale ni da masifa"
"To dama in ba dalili mai sa a leƙa tsiraicin sirika ba, mai zai sa ni faɗuwar gaba ma"
"Wannan kuwa amma dai in ba wajenka ba ina zan je tun da kai ne mijina"
"Yanzu dai da kika zo a gigicen nan kamar an biyo ki sai wata fisfisga kike kina kalle-kalle kamar a ce kule ki ce cas, mene ne ya tsorata ki"
"Mafarki na yi" Ta samu kanta da shirga ƙaryar da ba ta shirya ba.
"Mafarki kuma? Yanzu a kan mafarkin ne kika zo kika ɗaga mini hankali kamar dai an aiko ki"
"Kai dai bari Mai Gari ai kawai wata tattabara ce na ga tana bina a guje" Gwaggo ta samu kanta da faɗa.
"Aikin banza a tattabara mene ne abin tsoro ni na ɗauka ma zaki ne lo kura suka biyo ki, ko baƙin aljani ko dai fatalwa, to sai ki koma ki kwanta dan ni ba zan zauna zaman asara ba in je ban runtsa ba garin Allah ya waye wancan basamudiyar ta hana ni wali" Ya faɗa yana lallaɓawa ya koma ya yi gohonsa tare da rufa da abin rufarsa.
"Yo mene ne marabar dambe da faɗa, jaririn da ya fito ta cikin uwarsa ya ƙara komawa yanzu na dawo gida ya zo ya tashe ni tsakiyar dare in masa yankan cibiya in binne uwa, ina lafiya ai sai dai a taya ni da addu'a" Gwaggo ta faɗa a ranta a fili kuma sai ta ce.
"Allah sarki ni ma komawar zan yi in kwanta tun da na ga mafarki ne ba a gaske ba" Ta faɗa tana lallaɓawa ta koma ta kwanta a katalalliyar katifar cike da tsoro, baccin da bai ta ƙara komawa ba a kan kunnanta aka kira assalatu sai dai sa'ar ta ɗaya ba ta ƙara ganin jaririn ba.
Su Salele kuwa babu wanda ya motsa duk bidirin nan da a ke sai shaƙar baccin su suke.
*WASHE GARI*
Kowa a tsorace yake da Laila ita kuwa sai ta yi kamar ma ba ta san abin da suke yi ba. Haka ta saka Salele da Taju suka kama manyan ragunan Mai Gari tirkakku har guda biyu aka kai kasuwa aka sayar, buhun shinkafa aka sayo da komai na buƙata da babu a gidan. Gasarar koko ta Gwaggo da take ajiye ta kwano biyu Laila ta saka aka dame kokon a ƙatuwar tukunya na kwano guda aka dama aka karɓi kuɗin suga a gun Mai Gari da yake ƙunshe a ɗaki yana ɗan mammatse hawayen takaicin ragunan da ya ci buri a kan su sai ga shi rana ɗaya wacce ta fi shi ta sayar ta sayi shinkafa, shinkafar ma ƴar gwabnati. Shi ma dama a wajen wasu daga cikin mutanen gari ya yi fin ƙarfi a matsayinsa na Mai Gari ya karɓe, dan shi ko makiyayi ne zai wuce kiwo da dabobin mutane sai ya tsayar da shi ya zaɓi na zaɓa sai dai a faɗawa mai kayan cewar Mai Gari ya ƙwace kuma babu yadda ya iya sai dai ya yi Allah ya isa ba tare da kowa ya ji ba.
Biredi manyan sinƙi aka siyo guda goma, lokacin Gwaggo tana ɗana ƙosan kwano ɗaya da rabi. Haka ta gama ta kawo ɗakin da ya zama mallakin Laila ta ajiye a ƙatuwar roba, kokon kuwa a bokitin fanti babba yake, bayan an jere komai Gwaggo ta durƙusa ta ce.
"Ranki ya daɗe an kammala" Kallon Gwaggon ta yi a yatsine, ta muskuta dakyar ta tashi ta sakko daga gadon ƙarfen da zuwa yanzu ya lanƙwashe ya wani mogaɗe saboda nauyin da ta masa ga nauyin Nasiru. Tun da ta zauna ta saka kofin silba babba a cikin bokitin kokon ta ciko, ta ajiye ta buɗe birredin ta cira shi a uku duk girmansa ya yi mutum uku su raba su ci su ƙoshi amma ta raba shi gida uku ta kwaso ƙosai ta haɗa da biredin ta ɗauki biredi curi ɗayan da ta raba a uku ta saka ƙosan ta tura shi duka a baki tauna ɗaya biyu sai kawai Gwaggo ta ga ta ɗaga kofin ta kafa kai ta shanye.
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" Gwaggo ta faɗa a ranta ganin yadda Laila take cin abincin kamar wanda take zubarwa a ƙasa. Sai da ta ci ta ƙoshi dan kokon ta shanye saura kaɗan ta ɗauki plate ta tsakuri ƙosan ta ɗora biredin guda ɗaya, ta kwalfi koko cikin kofin silba ta miƙa wa Gwaggo ta ce
"Ɗauki ga shi nan ki ɓace mini a gani ku je ku raba ku karya"
"To, to, to" Ta faɗa tana rawar murya ta ɗauka ta fita a ɗakin.
"Haba Ramma ya za ki ɗakko wannan ɗan abincin kamar wanda za a ba wa ɗan kwikuyo (Jaririn kare) Haka kawai kina ganin basamudiyar matar nan tana neman karya mini tattali arziƙi za ta talauta ni, ta nakasta mini dukiya, amma maimakon ki ɗakko abincin a daro yadda za mu ci mu ƙoshi in ɗan hucin takaici shi ne za ki ɗakko abu kamar wanda kika roƙo, ita kuma da babu biyar ɗinta a ciki kika tura mata duka" Mai Gari ya faɗa lokacin da Gwaggo ta shigo ta ajiye abincin da Laila ta basu.
"Ni fa ba ni na ɗakko ba ita ta bani kuma wallahi gabaɗaga komai ya zama saura dan ta cinye kuma ina ga ɗanta da yake ta faman bacci ta ajiye wa, kai dai ka ga yadda take haɗiyar abu kamar walƙiya, amma in za ka je ka faɗa mata ta ƙaro mana ga hanya shawara ta ragewa mai rijiya"
"In kin ganni a lahira kai ni aka yi" Ya faɗa wasu hawaye suka sirnano masa ya sanya hannu ya goge yana tuna cewa zaluncin da yake yi ne abin ya dawo kansa wato ƙaiƙayi ne ya koma kan masheƙiya.
"Haba tsoho ai kawai ka bada kai bori ya hau, dan hausawa sun ce faɗan da ya fi ƙarfinka ka mayar da shi wasa" Salele ya faɗa cikin muryar gagara.
"Gaskiya ne Salele ai dama faɗa da mahaukacin kare sai wawa, amma dai na san duniya rawar ƴan mata ce kuma ta fi bagaruwa iya jima" Cewar Mai Gari yana jan hanci.
Haka Gwaggo ta kasa kowa ya ɗauka, su duka suna aikawa Taju harara, dan sun san shi ne silar jefa su a masifar da suka tsinci kansu a ciki. Mai Gari lamushewa ya yi ba tare da ya ƙoshi ba sai muzurai yake yana aikawa Gwaggo harara.
"Ba ni na kai zomon ba rataya aka bani" Ta faɗa tana taɓe baki.
"Oh ni kam sai dai in ce Allah ya mini sakayya, ni da na saba samun malmalar tuwon hatsi in ci in ƙoshi, amma a haɗa ni da ƙwayar ƙosai guda biyar da gutsiren biredi sai wani koko a ƙaramin kofi kamar wanda za a ba ɗan yaye" Ya faɗa yana miƙa ƙafa ya dunguren kofin kokon da ya shanye tsabar haushi.
"Ba ni kofina nan kar ka fasa mini ta taƙaice ni ka tashe ni tsaye, ai ni ta mini dai dai wallahi, abin da yau wajen kwanan mu huɗu rabon da a tuƙa tuwon ma a gidan, ga hatsin nan amma ba za a ɗauka ba jiya ma sai wake ka bayar aka yi alala muka ci rana da dare kowa ya kwanta yana sakin iska a ƙarshe ta saka mana ciki muka rinƙa tseran zuwa bayi" Gwaggo ta faɗa tana tashi ta ɗauki kayan ta fita.
"Wai Mai Gari ƙoshi ne baka yi ba" Taju ya faɗa yana ƙunshe dariyarsa.
"Ubanka ne ban yi ba, na ce ubanka ne ban yi ba" Mai Gari da ya harzuƙa ganin Taju ne ya jaza musu komai ya faɗa kamar ya hau Taju da duka.
Shi dai Salele bai ƙara magana ba, dan shi gaba ɗaya bayan rashin ƙoshi ma har da takurar takunkumin da Laila ta saka musu na rashin fita ko nan da can.
Tana fitowa ta samu Nasiru ya cinye sauran abincin da Laila ta rage masa sai bokitin kokon hatta ƙosan ko ɗaya babu biredin ma sai ledojin kawai. Mamaki duk ya cika Gwaggo ita dama a tunaninta idan ta zo kwashe kayan ta samu ragowa sai ga shi duk sun cinye.
"Kashi zan yi" Gwaggo ta tsinkayi muryar Nasiru yana faɗa wa Laila.
"Ramma" Laila ta ƙwala mata kira.
"Ni Ramma na gamu da gamona, dama an ce gba da gabanta aljani ya taka wuta" Ta faɗa a zuciyarta ta taho da sauri har tana neman tuntuɓe.
"Zai yi kashi ki ɗora shi a fo"
"Fo fa Ranki ya daɗe?" Gwaggo ta faɗa tana jimanta al'amarin da ta san dai babu wani fo da zai yi dai dai da mazaunan Nasiru.
"Kar ki kai shi ya yi ki zauna neman magana idan ya saki kashin nan a wando kafin ki wanke sai kin yi amai bakwai d...
Ai kafin Laila ta ƙarasa Gwaggo ta saɓi Nasiru dakyar ma ta ɗauke shi saboda yadda ya ƙara nauyin caccakar abincin da ya yi, haka suka fito, ta nufi hanyar bayi da shi, ɗaya daga cikin robar wankan su ta ɗakko ta kalli bahon wankan ta kalli mazaunan Nasiru ta jijjiga kai.
"Wallahi wannan mazaunan naka masu kama da an hura balan-balan babu inda zai ɗauke su sai dai robar wanka, sai dai a mayar maka da ita fo ɗin kake kashin a ciki tun da duk girman nan da ka yi girman biredi ne ko shadda ba za ka iya hawa ka yi kashi ba" Ta faɗa a ranta tana ɗora shi amma abin takaici da mamaki sai da robar ta tsage daga bakin, saboda bakin robar ma ya masa kaɗan haka ya jibga kashin Gwaggo sai jefar da bahon wankan ta yi dan ba zai amfanu ba.
"Haba ni wallahi na gaji ina dalili ina ɗan mafari haka kawai mata ta zo za ta ɓalɓalta mini dukiya, ta karya mini tattalin arziƙi" Mai Gari ya faɗa yana kumfar baki sai wani muzurai yake yana faɗa, a kan Laila ta saka dillalai sun zo sun sayi ɗaga daga cikin gonakansa wanda shi ma asali ba tashi ba ce ƙwata ya yi a matsayinsa na Mai Gari.
'Wannan kuma ai sai ka je ɗakinta ka mata faɗan amma ba wai ka zo kana mini faɗa ba wato ga Ramma kuka mai daɗin hawa" Gwaggo ta faɗa har da gatsinan gefen baki, dan ita cike take da gajiyar girkin jalof ɗin shinkafa da ta ɗora a tukunyar da ake girki da ita a gidan biki.
'Yo ba dole na faɗa ba, tsabar matar nan ta mayar da ni sha ka tafi tirajalin ajansi, a siyar da gonar amma a bani jaka biyu(400) Sai ka ce wanda iyayensa suka ce jeka ka gani"
"Kan ka ake ji mahaukaci ya faɗa rijiya, ka je can ka faɗa mata ina laifi dan mai kaza ya tashi da ƙafa, kana gani dai ƙarfi sa yaji rainon yaron nan ya dawo kaina ko ɗazu da ya yi kashi sai jefar da robar na yi, ni ma duk tattalin arziƙin robobina sunan su matattu, haka kawai ba dangin iya ba, ba na baba ba, babu haɗin danga da garahunu ta zo ta addabi mutane"
"Ramma" Laila ta ƙwalawa Gwaggo kira.
"Allazina iza asabatkum musibatun ƙ...Allazina kafaru wa saddu an sabilillahi..." Gwaggo da ta ringisa har ta fara jin daɗin kwanciyar Laila ta kira ta.
Ɗakin ta dosa a tsorace dan gudun abin da zai je ya zo.
KAFIN A GAMA FREE PAGES MAI BUƘATA ZAI BIYA KUƊIN KARATU 400 IDAN NA KAMMALA FREE PAGES ZAI KOMA 500 ZA A BIYA TA ASUSUN FAIZA ABUBAKAR 9030283375 OPAY SHAIDAR BIYA TA 09013181851.
[8/19, 17:57] Mom mashkur & Afrah: UNGOZOMA
(Mai karɓar haihuwa)
NA
MAMAN AFRAH
F.C.W
GARGAƊI⚠️
Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ta kowace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowace kafa ba sai da izinina a kiyaye.
*PAID ADVERT 1* 💃
Ina mata ƴan ƙwalisa, babbar mace alkyabbar mata, macen mai gyara ita wacce ta isa da miji su o'o sai dai su ga ƙeyar mijinta idan ya wuce amma basu ishe shi kallo ba domin babu abin da za su nuna mata. Gyaran gashi babbar martaba ce da take ɗaga darajar mace, musamman kayan gyaran gashin MAMAN ZEE da ya yi fice a ko ina ake labarinsa. Gani ya kori ji sai an gwada akan san na ƙwarai siyan na gari mayar da kuɗi gida💃💃💃💃💃💃💃💃
Hadaddu Kuma ingantattun kayan gyaran gashin mamanzee(chebe hair set)
Wadanda suke dawowa da martabar gashin Kai komai lalacewarsa biiznillahi Rabbi
Ga kyau ga inganci ga saukin kudi muddin kika fara amfani da kayammu sekindawo Mana da kyakkyawan labari
Kanki zeyi kyau ya rika sheki yayi tsayi yayi laushi duk matsalar da ke cikin kanki zata kau in sha Allah
Munada set complete
Kuma Muna Bada pieces
Haka Kuma Muna Bada Sari
Muna turawa akowanne gari kike Kuma Ako wacce kasa kike
Phone number *08079130166*
*PAID ADVERT 2* 💃
*BOJUWA HERBAL'S & SCENTS*
*Suna kawo Saiwowin sanyi da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.*
*Haka nan akwai dafaffen maganin ga wanda tafi son ready made.*
*Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah*
*Saiwowin tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru*
*Saiwowin matsi gangariya*
*Original gadalin mata*
*Ƴaƴan gadali na asali*
*Original gumba*
*Tsumin Saiwowi*
*Tsumin kwakwa da Dabino*
*Igiyar alkairi*
*Zumar goran tula*
*Hakkin daka na musamman na asali*
*Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*.
*Akwai bridal package*
*Mai jego package*
*Ƴar gata package*.
*Dukkan kayan kuma available ne for pickup or immediate delivery.*
*A Kano nake amma kuma nationwide delivery ne*
*Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi*
*08032773332*
*Iyah Basiru na gaisuwa*😅
Page2️⃣3️⃣➡️2️⃣4️⃣
A ɗarare ta shigo ɗakin in da ta samu Laila durƙushe a tsakar ɗaki tana murƙususu tamkar mai naƙuda.
"Allah sa ciwon cikin nan ya zama ajalinki kowa ma ya huta yo ina dalili" Cewar Gwaggo a zuciyarta a fili kuma sai ta ƙarasa gaban Laila tana ta faman ambatar mata sannu duk da ba ta san takamaimai abin da yake damunta ba. A take tunnin Nasiru ya ɗarsu a ranta.
"Yaro dab kake da zama maraya dan wannan uwar taka tana mutuwa sai dai a nemi gidan marayu a kai ka, dan wallahi riƙon mahaukaci sai sarki, kuma dai ciyar da kai sai ƙaramar hukuma amma mu sai dai ku nakasta mana tattalin arziƙinmu ku haɗa mu ƙaƙƙarfan zumunci da talauci...
"Ramma, matso da sauri taki ta same ki wai an haɗa namiji da wankan jego" Maganar Laila ta katse mata zancan zucin da take.
"Tawa ta same ni ko taki ta same ki?, ke da za ki mutu ai ke za a faɗawa haka" Gwaggo ta faɗa a ranta tana taɓe baki ta ƙarasa ta tsugunna domin taimakawa Laila, ai durƙuson da Ramma ta yi sai ta ji Laila ta fisgi hannunfa tamkar wacce wutar nepa ta ja, haka Ramma ta ji fisgar da Lailar ta mata kafin ka ce me ye wannan Laila ta ja ƙafar Gwaggo ƙiii sai ga Gwaggo a reran cikin hanzari Laila ta juyo mazaunanta ta zaune Gwaggo. Gwaggo sai ta shiga salati tana ihun neman ɗauki dan tamkar an loda mata buhun siminta goma haka ta ji nauyi jiƙit Lailar ta mata.
"Wayyo Allah na, abin na ba a ne an ce da kare mai sunan mata" Gwaggo ta faɗa