Showing 18001 words to 21000 words out of 44948 words

Chapter 7 - UNGOZOMA Book Complete Original by Maman AFRAH F.txt

19 Oct 2024

5935

Ranki shi daɗe bari a yi yadda kika ce" Ya faɗa a ladabce yana tashi shi ma Salele tashin ya yi, Mai Gari ya juya Salele ya take masa baya, Taju ma bin bayan nasu ya yi ɗauke da akwatin ita kuma ta kame a wajen ba tare da ta motsa ba.


Suna shiga ɗaki Salele cikin raɗa har yana doɓara bakinsa a kunnen Mai Gari ya ce


"Wannan mata an yi shegiya wallahi yanzu Mai Gari kana ji da gani za ka bari mu kwatsu ɗaki ɗaya ina matsayin naka na Mai Gari? Za a mayar da kai sahun gwaurayen samari"


"Kai dalla rufe mini baki sakaran wofi, wannan matar mai halitta jiki duk a murɗe kamar ƴar dambe haka kawai in mata musu in baƙunci lahira ko in kwanta jinya a banza to wallahi gwara ko a turken dabobi ta mini matsugunni in ke kwanciya daga duniyar sai ina?" Mai Gari ya faɗa cikin raɗar shi ma yana aika wa Salele harara, ɗif Salelen ya yi haka suka kwashe tarkacen ɗakin hatta kayan Gwaggo babu abin da suka bari suka share ɗakin tatas. Sun gama sai Taju ya shigo ɗakin da akwatin a hannunsa dan dama a baranda ya tsaya yana ajiyewa ya juya da sauri zai fita ai kuwa Mai Gari ya saka hannu ya damƙo shi ya dawo da shi cikin ɗakin cikin ƙasa da murya ya ce


"Kai ɗan nema a gidan uban wa ka samo wannan matar mai kamar an laulaya tayota abu unguwa guda ko kyan gani babu haka kawai ka kwaso jaraba ka shigo mana da ita gida ana zaune ƙalaw kuma ma, sabo da kun mayar da mu sha ka tafi a ce wai matar shugaban ƙasar sojoji, sai ka ce wanda ba mu da hankali? in ce dai shugaban ƙasa ɗaya ake yi a ƙasa amma sabo da rainin hankali a ce mana wai shugaban ƙasar ma har da na sojoji" Tun da ya fara maganar Taju yake masa nuni da ya yi shiru duk da cikin raɗa yake maganar amma dai ya fi so ya bar maganar dan shi ya san halin Laila kunnuwanta kamar na miciji suke.


"Kai dallah ragwan maza rufe mini baki sai wani mismis kake da baki kamar sabon baƙon munafuki, ga kayan sojoji a jikin ka amma ka kasa kataɓus ka tsaya mace tana juya ka kamar waina a tanda ka ɗakko annoba ka...


"Taju" Kiran da Laila ta yi wa Taju wanda hakan yake nuni da ta matso ƙofar ɗakin dan a dab da ɗakin suka tsinkayi muryarta, hakan ya sanya Taju ya fisge riƙon da Mai Gari ya masa cikin sauri, Mai Gari kuwa wani irin faɗuwa gabansa ya yi, juyawa ya yi ya kalli gabas yana faman rattabo addu'a a zuciyarsa a kan Allah masa tsari da sharrin Laila dan shi tunaninsa Laila ta ji abin da yake faɗa. Bayan ya gama addu'ar a ransa sai kuma ya ɗaga hannunsa ya sauke wa fuskarsa tagwayen maruka guda biyu, a kan idanun Laila ya mari kansa lokacin ta leƙo ɗakin dan ganin wainar da suka toya. Idanu ta sauke a kan Mai Gari da ya koma jikin bango ya raɓe yana murza fuskarsa dan ya maru sosai dan da ƙarfi ya mari kan nasa, dan ma kar ya yi a hankali ta ce za ta sake masa wani shi kuma da a ce ta mare shi da wannan hannun nata gwara ya mari kansa ko da sau goma ne kuwa.


"Na yi wa kaina hisabi ma ba sai kin mini ba" Ya faɗa yana karkarwar baki.


"Taɓ rikicin duniya da mai rai ake, wai yau Mai Gari ne haka ya faɗo ƙasa warwas, mutumin da babu wanda ya isa ya taka shi sai baƙin mulkin tsiya da cin zali amma yau ga shi Allah ya kawo mai yin maganinsa har gida kuma cikin ruwan sanyi" Salele ya faɗa a zuciyarsa.




"To ai ni babu abin da ka mini hisabin mai kuma?" Ta faɗa tana nishi tamkar wacce ta yi tseran gudu sabo da tafiyar da ta yi daga tsakar gida zuwa ɗakin Gwaggo.




"Oh duniya makaranta wallahi da na san baki ji maganar da nake faɗa wa Taju ba da babu abin da zai sa in mari kaina maruka ƙwarara guda biyu ashe dai gudun gara na yi na tarar da zago, ni da na mari kaina sabo da kar ki mini irin marin da kika yi wa Salele mari mai kama da an mari mutum da faskare" Cewar Mai Gari a zuciyarsa a fili kuma cikin ɗacin zuciya ya shiga faɗin.


"Ah dama fa na ɗauka ko gyaran ɗakin ne bai yi ba"
Banza ta masa kamar ma ba ta ji abin da ya ce ba.


"Ku fita ku bani waje" Ta faɗa tamkar wadda ta ke korar dabobi.


"Oh da'ira cuta bayan rai, kai da gidanka amma ake maka korar kare ana maka iko, duk da ba mallakina bane gidan amma dai ai ni ne a ciki, amma sai a ke mini hawan ƙawara" Mai Gari ya faɗa a zuciyarsa har suna rige-rigen fita shi da Salele ban da Taju da yake gefe a tsaye yana jiran abin da za ta ce.


"Fita ka bani waje kai ɗin ma zan yi bacci"


"An gama" Ya faɗa a ransa yana juyawa ya fita har da ja mata ƙofar dan ƙarfin hali. Yana fitowa ya saki wata ajiyar zuciya tamkar wanda ya kuɓuto daga bakin kura. Ɗakin da su Mai Gari suka shiga ya kutsa kai ciki ya same su sun haɗa kai suna magana ƙusƙus. Yana shigowa Salele ya tashi ya fita sai da ya ƙarewa ƙofar ɗakin da Laila take kallo ya tabbatar ba ta wajen ya dawo ya kara ƙofar ɗakin yana shirin saka sakata Taju ya ce


"Kar ka saka sakata ka bar ƙofar a haka dan wannan komai dare kira take kuma daga ta yi kiran dole mutum ya amsa kiran nata, kamar dai kiran mutuwa"


"Sai ka ce gidan mahaukata, to ai ko a gidan kaso ma ana bacci domin shi dare mahutar bawa ne" Mai Gari ya faɗa yana hayayyaƙowa Taju dan yana ganin duk shi ya saka su a cikin wannan masifar da suke ciki. Salele dai bai saka sakatar ba ya bar ƙofar a kare dan ba ya so a ce shi ne da laifin rufe ƙofa dan ba ya so ko a mafarki Laila ta ƙara marinsa bare a zahiri. Dan ya lura al'amuranta hajaran majaran ne shiga aljannar alƙali.


Bayan sun yi tsit tamkar ruwa ya ci su, Mai Gari ya yi gyaran murya ya fara magana cikin raɗa -raɗa dan su duka ukun suna waje ɗaya sun haɗa kai kamar masu neman gafara dan ko ƙwaƙƙwaran motsi ba sa yi sabo da tsananin taka tsan-tsan.


"Wai ni kai Taju ban da rashin hankali kamar renon gwauro, haka kawai ka ɗakko matar nan mai ƙirar samudawa ka kawo mana jaraba gida, kana ganina fuskata kamar ta tsulan biri, ita kuma Kakar ka Ramma kana ganinta caca kurukuci cikon benci, haka kawai ka kawo mana abin da zai kashe mu murus kamar wutar da aka zubawa ruwa"


"Mai Gari ka manta baka ce masa ni jikina akwai ya babu ba ne kakar wajen uba" Salele ya faɗa shi ma cikin raɗar dan su duka sun haɗa fuskoki a waje ɗaya kuma yanzu a duhu suke dan sun kashe haske sai na farin wata fitilar Laila kuwa Taju ya bar mata.


"Na ce a ina ka samo matar nan baƙar fura ana gama ki mai gida yana mutuwa?" Mai Gari ya tambaye sa cikin raɗar dai.


"Ana tsoronka ɗan mayya, ya ce daga ni har uwata" Cewar Taju a zuciyarsa yana jin tamkar ya fashe da dariya dan yana hango yadda bakin Mai Gari yake raɗa ta hasken farin watan da ya shigo kuma yadda yake yi ɗin muryarsa har wani shaƙe ta yake shi ala dole kar Laila ta jiyo abin da yake faɗa duk da ba a ɗaki ɗaya suke ba sai dai hanyar lafiya ce ake bin ta da shekara. A fili kuma sai ya ce


"Mai Gari na faɗa maka matar shugaban ƙasar sojoji ce"


"Gwafar ubanka, na ce gwafar ubanka kai da ƙasar lanjeriyar (Nigeri'a) Da shugan ƙasar sojojin...


"A'a Mai Gari da alheri uwar kishiya ta hau kura,ka san dai kwarankwatsa dubu matar nan ta ji wannan maganar sai ta maka yadda ta yi wa Malam Mammani da ta ɗaga shi sama kamar jemage, kasan farilla tusa a masallaci sai ta maka abin da ya fi hakan" Salele ma ya katse Mai Gari cikin ta shi raɗar. Shiru Mai Gari ya yi tare da haɗiye wani yawu mudukkk dan bai manta irin yadda ta ɗaga Malam Mammani ba kamar wanda ta ɗaga jaririn kyankyaso.


"Haka ne kuma kaima da gaskiyarka Salele tabbas a lokacin da mage take wuri ɓera ba ya sata amma kuma an dake ni a hana ni kuka, duk da dai gwara ya ba ni amsar tambayata tun da a gama yau ya fi a ƙarasa gobe, amma dai da na ɗauka da zafi dan cewa zan yi a yi abin da za a yi mahaukaci ya ɗauki rigar kurma"


"Mai Gari ni fa gaskiya nake faɗa maka" Taju ya faɗa a fili a zuciyarsa kuma ya ce


"Sai dai ku yi haƙuri domin kuwa ni ma ba da son raina ba, babu wata matar shugaban ƙasar sojoji wallahi dadirona ce, ta gidan karuwai haka kawai tun da na haɗu da ita take tatsa ta kamar ta samu nonon saniya, duk wani kuɗi da zan samu ita take ƙwacewa, duk inda na je sai ta bi ni, kuma ni babu aikin sojan da na samu wannan kayan ma a wajen ƴan wanki da guga na sato su a kan igiyar shanya, shi ne na ɓoye dan idan na dawo nan garin in ke yankar mutane da su, ina ƙaryar ni soja ne amma tun da na tafi neman kuɗi nake irin su dako da dai sauran aikin neman kuɗi, yau da na shirya zan taho gida har hula na saka na rufe fuskata dan kar wani ya faɗa wa Laila zan gudu amma abin mamaki, da na shiga motar haya sai da muka yi nisa na gane ashe tana ma cikin motar, har da ɗanta ɗan gaba da fatiha (Wanda aka haifa babu aure) Ana sauke ni ta sauka, shi ne ta saka na saka kayan nan na sojoji muka shigo garin nan tun a hanya ta shinfiɗa mini dokoki ni kaina ban san ranar da za ta bar garin nan ba, kuma kona can ba na mata musu dan ina yin musu sai ta gana mini azaba da ƙibar jikinta, a shegen son manyan matana wanda ake yi wa laƙabi da matan manya, wani abokina ya ce in je wani ɗaki ya tanadar mini irin matar da nake so ina zuwa na yi arba da ita ta yi gandaƙaiƙai, a kiɗime na juya zan gudu ta janyo ni ta dawo da ni ɗakin, tun daga wannan ranar ban sake samun kwanciyar hankali ba duk ta bi ta tatiƙe ni, ko kaina ba na yi wa amfanin da nake mata " Ya faɗa yana jin ƙwallar tausayin kansa tana ciko masa idanu yana jin da na sani a kan neman matan banza tun da ga shi ta dalilin hakan ya gamu da gamonsa.


"To ni dai wallahi ban yarda ba, mene ne haɗina da soja dama kai ne ka tafi aikin kuma shekara guda baka dawo ba, bare ko albarkacin aikin naka mu ci, sai yanzu za ka dawo da wacce za ta kassara ni, ta nakasta mu, yo ciyar da wannan matar ai ba ƙaramin aiki bane" Cewar Mai Gari cikin ɓacin rai har maganar ta shi tana fitowa ya manta cewar raɗa suke, da sauri Salele ya saka hannu ya rufewa Mai Gari baki dan shi ba ya son abin da zai sa ya sake samun mari daga Laila da wannan hannun nata mai kamar na kantoma.


"Kai ni barni in faɗa in banda hankalinsa a kan hanci yake ba a ƙwaƙwalwarsa ba, ta yaya zai kawo mana wannan abin gida wannan ai abin banza ne hanci ba ƙafa" Cewar Mai Gari da ya janye hannun Salele daga kan bakinsa rai a ɓace yake magana.


"Wallahi Mai Gari abin daga Allah yake matar mai takaba ta yi ciki, kuma gani ma na yi abin duniya mene ne dan kaza ta jawo muzuru kwanan gida...


"Taju!!!" Ƙaran kiran da Laila ta ƙwala masa shi ne ya dakatar da shi daga maganar da yake yi. A kiɗime su duka ukun suka kwanta a wajen da suke zaune sai ya zamana gabaɗaya kawunansu a haɗe a waje ɗaya ma'ana sun yi murhu.


"Kai dan matar ubanka da bai aura ba, ka tashi ka tafi kiran wannan" Mai Gari ya faɗa daga kwancen da yake.


"Ai wallahi ka tafi kar ka janyo mana" Salele ya faɗa yana zungurin ƙafar Taju.


"Ku baku san kiran da take yi bane, wallahi na san ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba, tusa ce ta matso ta, kuma kun san ita idan za ta yi tusa dole sai ta zauna a kan mutum, dan in har za ta yi tusa ba tare da ta zauna a kf mutum ba to mazaunanta tsagewa suke saboda yadda tusar ta take fitowa a guje da mugun ƙarfi shi ya sa sai ta zauna a kan mutum ta murtsuka mazaunanta sai ta saki tusar hakan shi ne zaman lafiyar ta" Taju ya faɗa a hankali yana sakin wani marayan kuka dan ya san akwai babbar matsala.


Maman Afrah Whatsapp 09013181851








*META FORCE ARZIƘI DAGA ALLAH*


ƳAR UWA SHIN BAKI DA LABARIN META FORCE? DA IRIN ƊINBIM ARZIƘIN DA AKE KWASHEWA A CIKINSA, YA AKA YI BAKI YI REGISTER BA? KO BAKI DA BUƘATAR KUƊAƊEN DA ZA KI YI HIDIMAR YAU DA KULLUM?


TO KI ZO NI MAMAN AFRAH NA ZO MIKI DA HANYAR SAMUN KUƊI TA WAYAR HANNUNKI KUƊIN YIN REGISTER KAWAI ZA KI TANADA 9K DUBU TARA DOMIN ANA YIN REGISTER DA DALA 5 NE SAI DAI ALLAH KAƊAI YA SAN IRIN RIBAR DA ZA KI SAMU DA KUMA ALKAIRAN DA YAKE CIKIN KASUWANCIN. IDAN KINA SO SHIGA KUMA DA GASKE KIKE KI MINI MAGANA A WANNAN NUMBER 09013181851 IDAN BA YI ZA KI YI BA KAR KI MINI MAGANA DAN BANA SON ƁATA LOKACI!




AKWAI CIKON 2K GA WANDA ZAI YI REGISTER META FORCE ZAI KAWO 7K MAIMAKON 9K KAR KU BARI DAMA TA WUCE KU KI MINI MAGANA A 09013181851 DOMIN A DAMA HARKAR ARZIƘI DA KE, KINA ZAUNE BABU SANA,A GA DAMA TA SAMU DA WAYARKI TA HANNU ZA KI MALLAKI KUƊAƊE😍
[8/19, 17:57] Mom mashkur & Afrah: UNGOZOMA
(Mai karɓar haihuwa)






NA






MAMAN AFRAH


FCW


GARGAƊI⚠️


Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ta kowace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowace kafa ba sai da izinina a kiyaye.






Ina mata ƴan ƙwalisa, babbar mace alkyabbar mata, macen mai gyara ita wacce ta isa da miji su o'o sai dai su ga ƙeyar mijinta idan ya wuce amma basu ishe shi kallo ba domin babu abin da za su nuna mata. Gyaran gashi babbar martaba ce da take ɗaga darajar mace, musamman kayan gyaran gashin MAMAN ZEE da ya yi fice a ko ina ake labarinsa. Gani ya kori ji sai an gwada akan san na ƙwarai siyan na gari mayar da kuɗi gida💃💃💃💃💃💃💃💃
Hadaddu Kuma ingantattun kayan gyaran gashin mamanzee(chebe hair set)
Wadanda suke dawowa da martabar gashin Kai komai lalacewarsa biiznillahi Rabbi


Ga kyau ga inganci ga saukin kudi muddin kika fara amfani da kayammu sekindawo Mana da kyakkyawan labari
Kanki zeyi kyau ya rika sheki yayi tsayi yayi laushi duk matsalar da ke cikin kanki zata kau in sha Allah
Munada set complete
Kuma Muna Bada pieces
Haka Kuma Muna Bada Sari
Muna turawa akowanne gari kike Kuma Ako wacce kasa kike


Phone number *08079130166*







Page 1️⃣3️⃣➡️1️⃣4️⃣


*GWAGGO RAMMA*


Jin ana lallanƙwasa mata yatsunta daga ciki ya sa ta fara karanto addu'ar da duk ta samu nasarar wartowa a bakinta, domin kuwa tun da ta fara sana'ar nan ta UNGOZOMANCI ba ta taɓa tsintar kanta a wannan yanayi ba haƙiƙa wannan baƙon abu ne a gare ta.


"Ni Ramma yau na ga dalili mai sa a leƙa gaban sirika, lallai na yankowa kaina kazar wahalar da ban san ma ta inda zan fara fige ta ba" Ta faɗa a zuciyarta a fili kuma sai ta ce


"Baiwar Allah taimake ni mana kina ganin mafitar ɗa (HQ) Ya rufe da hannuna a ciki, kar fa a je hannun nawa ya shige cikin mahaifar in shiga uku, kuma wallahi ɗan nan ba jariri bane dan ina jin daga ciki sai lanƙwasa mini yatsu yake tamkar ya samu machine ɗin matsa ruga" Ta faɗa cikin sanyin murya tana wani nishi nauyin goyon Nasiru da ta ji gaba ɗaya ya sanya bayanta ya yi sagewar da take jin lallai sai ta nemi maganin ciwon jiki ko ta samu salama. Duk da Kakar Shamsiyya tana cikin tashin hankalin ganin jariri ya koma ƙofar kuma ta rufe ruf da hannun UNGOZOMA a ciki amma kuma ba ta manta da abin da Gwaggo Rammar ta mata ba dan haka sai ta kawar da kanta gefe.


"Kaka dan Allah ki taimaka kar ɗan nan ya sha ruwan naƙuda " Talatuwa ta faɗa cikin sanyin muryar dan gaba ɗaya ta sare da lamarin dan ita ma tana jin tamkar wanda ake yaƙin badar a ƙasan nata, wani lokacin ma sai ta ji tamkar wanda jaririn yake rawa ko tsalle a ciki wannan ne al'amarin da ya ƙara ɗaga mata hankali da ta fara tunanin kar dai ba ɗan mutum bane a cikin nata kamar yadda ta ji Gwaggo Ramma ta faɗa.


"Kaka magana nake fa" Ta ƙara faɗa ganin kakar tata ba ta furta komai ba.


"Haba Shamsiyya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login