Showing 15001 words to 18000 words out of 44948 words

Chapter 6 - UNGOZOMA Book Complete Original by Maman AFRAH F.txt

19 Oct 2024

5931

ta goya a bayanta sai dai ya ta iya ai faɗan da ya fi ƙarfinka wasa kake mayar da shi.


"Ko da na ji" Ta faɗa tana mayar da kallonta kan Mai Gari, Salele da kuma Malam Mammani.


"Za ku kwanta a jere rubda ciki zan taka bayan ku wato in yi bene da shi zan wuce" Suka tsinkayi muryar Laila da ta musu dirar mikiya. Su duka sai jikinsu ya fara ƙyarma dan sun tabbata matsawar dai ta taka bayansu to sun kaɗe dan haka Mai Gari cikin sanyin murya ya ce.


"Allah ya tamake ki, wallahi wandon nan nawa da kika gani jargaf yake da gudawa, na saki gudawar nan a cikinsa ni kaina ban san adadin kashin da na yi a ciki ba, ko tsayuwar nan ban da wari babu abin da nake yi shi ya sa nake daga baya-baya" Ya faɗa yana fatan Allah sa maganar ta samu shiga. Shiru ta yi kamar ba za ta yi magama ba sai kuma ta ce


"Ka tafi ka cire kayan nan yanzun nan kafin warin ya kumbura mutane" Da mugun gudu Mai Gari ya juya ya nufi hanyar bayi ko fitala babu bare takalmi yana ta godewa Allah da ya kuɓutar da shi.


Malam Mammani ma ƙarfinsa ya daddage ya ƙwaƙulo kashin ya sake shi a wandon dan shi ma ya tsira daga taka bayansa da shirgegiyar matar nan za ta yi.


"Wallahi ni ma hakan take, wandon nan nawa ni ba ma gudawa bane a cikinsa kashi ne mai tauri yana nan musgura-musgura" Ya faɗa a ɗan tsorace dan ba ya so ta ƙara cafkar wuyansa ta ɗaga shi sama irin na ɗazu. Wani mugun kallo ta jefa masa da ya sanya ya sunkuyar da kansa ƙasa.


"Ni kuma jinin haila nake in banda ƙarni babu abin da nake, sabo da ban yi ƙunzugu ba(Sanya pad)"Salele da maganar ta fito tamkar an fisgo ta ya faɗa yana tsiltsilla ido
Leɓanta na ƙasa ta cije tana saƙa irin abubuwan da za ta shuka a cikin gidan sabo da ta ga abin nasu rainin wayo ne. Malam Mammani da Salele kuwa sai suka ji tamkar su taka rawa dan murna musamman Salele da yake ganin tashi ƙaryar ta take ta kowa dan ya san dai a iya saninsa mata basa haila amna kuma ga shi ana yarda da maganarsa


"Ki zunkuɗa shi mana baka ganin goyon kamar bai ji daɗinsa ba"


Da sauri Gwaggo ta shiga zunkuɗa Nasiru duk da tana zunkuɗa wa ne dai kwai dan a zunkuɗuwa yake yi ba sabo da yadda gaba ɗaya ya fi ƙarfinta.


"Na zunkuɗa shi Ranki ya daɗe, kin san ni ba aikina bane raino shi ya sa ma ban ƙware a goyon ba ɗiya ta ɗaya a duniya kuma ta mutu sai waɗan nan ƴaƴan nata da ta tafi ta barmin su, ni aikina INGOZOMANCI wato karɓar haihuwa, shi ya sa ma kika ji Malam Mammani yana cewa ni ya zo ya kira in karɓi haihuwar matarsa" Gwaggo ta faɗa a ɗan tsrorace tana fatan haƙarta ta cim ma ruwa dan burinta bai wuce Laila ta ce a ajiye goyon ba ta tafi karɓar haihuwar. Shiru Lailar ta yi a ranta tana rayar muguntar da za ta yi wa Gwaggon dan ta lura goyon ne bata so shi ya sa har take ikirarin ba ta iya raino ba.


"Ku je da Malam Mammanin ki karɓi haihuwar...
"Na gode, na gode sosai " Cewar Gwaggo tana ƙoƙarin sauke Nasiru dan ta tafi, tana jin za ta jefar da ƙwallon mangwaro ta huta da ƙuda.


"Idan aka goye shi ba a sauke shi sai dai idan shi ya buƙaci hakan dan haka da shi za ki tafi a bayanki kar ki kuskura ki sauke shi" Ta tsinkayi muryar Laila cikin bada umarni. Wani irin uban zare ido Gwaggo ta yi a ɓoye tana jin tamkar ta kurma ihu dan tana ganin a ce ta tafi har gidan Malam Mammani goye da shirgegen yaron nan ai kuwa tana da jan aiki ja jawur ma kuwa.
Gwaggo hatta bakin magana ma rasa wa ta yi Malam Mammani kuwa sai godiya yake zabgawa tamkar ya ari baki dan ya ji hanyar tsora ɗoɗar babu lanƙwasa.


"Za ku iya tafiya"


"Bari in ɗakko kayan aikin nawa " Gwaggo ta faɗa, tana kama hanyar ɗaki tana tafiya dakyar tamkar an mata dabibayi da igiya ta je ta ɗakko kayanta na karɓar haihuwa. Haka ta fito tana takawa dakyar tamkar raƙumin da aka lodawa kaya, Malam Mammani kuwa gaba ya yi ta bi shi a baya shi yana tafiya zugui-zungui ita kuma tana takawa tinƙis-tinƙis sai wani nishi take tamkar mai naƙudar da take gargarar haihuwa.


Malam Mammani sai zabga sauri yake yi dan ya san ya baro matarsa cikin wani hali sannan shi ba dan dole ba, kwata -kwata ba ya so ya kira Gwaggo Ramma karɓar haihuwar matarsa sai dai dan babu yadda zai yi ne, sabo da yadda take bi wajen karɓar haihuwar dan sai an ɗauki mai haihuwa zuwa asibiti ita kuma ba karatun likita ta yi ba amma dan jan magana sai a gado asibiti take karɓar haihuwa bayan suna da masu aikin asibitin nasu wanda suka yi karatu ƴan asalin cikin garin kuma suka samu aiki a asibitin garin amma sabo da mulkin zalunci irin na Mai Gari da Ramma kasa albashin masu aikin asibitin ƙauyen nasu suke a uku su ɗauki kashi ɗai-ɗai, wato idan aka yi albashi dan dole ma'aikatan su kawo albashin su, sai Mai Gari ya raba gida uku shi ɗaya a matsayinsa na Mai Gari sai kuma Gwaggo Ramma a matsayin mai karɓar haihuwa tun da ta hana su, yin aikin su, amma wai sai ana biya ta tun da ita take karɓar haihuwar.


"Alla ka fitar da A'i daga rogo, Allah sa yadda Ramma take a birkice kar ta ce sai an kai Shamsiya asibiti ta yarda ta karɓi haihuwar a gida" Cewar Malam Mammani a zuciyarsa. Yana mai waiwaya wa bayansa amma sai ya hango Gwaggo a can bayan tana tafiya a ɗan sunkuye kamar mai ƙusumbin
Sai da ya dangana da ƙofar gidansa ya samu ya tsaya domin jiran Gwaggon ta ƙara so, yana nan tsaye sai ga ta, ta ƙara so bakinta buɗe tana ta sakin numfashi ta bakin dan zuwa lokacin Nasiru ya yi bacci a bayan nata, ga wani warin kashin Malam Mammani da ya cika mata hanci, duk da kashin nasa ya faɗi a hanya ta ƙafar wandon.


"Wash Allah na, da a ce in yi goyon nan gwara a ce a ɗora mini buhun hatsi a ganina sai na fi jin rashin nauyinsa" Cewar Gwaggo lokacin da ta ƙaraso ta kama jikin bishiya ta riƙe tamkar mai haihuwar da kan ɗa ke ƙoƙarin fitowa.


" A yi haƙuri dai Ramma, mai kika ce gwara buhun hatsi?"


"Abin da wancan ya ce shi na ce kirarin mai tsoro" Gwaggo ta faɗa tana aikawa Malam Mammani harara.


"Allah baki haƙuri ba ni na kai zomon ba rataya aka ba ni" Ya faɗa a zuciyarsa.


"Ramma in samo amalanken shanu a kai Talatuwar asibitin ne?"


"Haba Malam Mammani in banda dai rashin imani cirewa kare hanta da ransa ta yaya zan iya zuwa wani asibiti da wannan goyon to aradu sai dai in tafi da rarrafe dan na yi imani da Allah babu mai machine ɗin da zai iya ɗaukana da goyon ɗan nan, ko amalanken shanun na hau na san sai taya ta sace, ko ma shanun su kasa tafiya amalanken take ƙiƙar-ƙiƙar"


"Alhamdulillah! Ni kamar dan ni tsintuwar haƙorin makka a hasken farin wata" Cewar Malam Mammani a ransa.


A hankali Gwaggo ta juya ta shiga gidan tana ɗaga ƙafa dakyar
Haka ya bi bayanta, matan gidan suna jin sallamar mai gidan suka fara shigewa ɗaki suna rufowa da yake matansa huɗu Shamsiyya ita ce amarya kuma ita ce yarinya ba ta fi ƴar cikinsa ba ko ma jika. Kowacce tana leƙowa daga window sabo da tsegumi dan tun da suka Talatuwar tana naƙuda kowacce ta ƙi kwanta wa a cewar su sai sun ga ƙwal uwar daka. Malam Mammani kuwa turakarsa ya wuce ya tsafta ce jikinsa ya canja kaya ya dawo lokacin Gwaggo tana durƙushe a gaban Talatuwaa da take ta rafka ihu da kakarta da take ta miƙa mata wani ruwan rubutu a kofi.


"Kar ki kuskura ki bata rubutun naƙuda, idan kuwa kika aikata haka ki sani tabbas kin aikata babban kuskuren da ba za taɓa gyaruwa ba" Gwaggo ta faɗa cikin bada umarni tana sakin nishi tamkar ita ce mai naƙudar sabo da goyon da yake bayanta. Karkarwa hannun matar ya shiga yi dan ta san dama ba a neman wani abu da ya shafi haihuwa a wajen kowa sai dai wajen Gwaggo Ramma.


Haka Gwaggon ta saka hannu duk da nauyin goyon bayanta, ta sakarwa Talatuwa duka a baya wai sabo da rakin da take yi, ƙaran dukan sai da ya sanya Kakar Talatuwa zabura ta dafe haɓa ganin an daki wacce take cikin halin naƙuda amma sai dai babu yadda za ta yi dan ta san tana yin magana cibi zai zama ƙari. Dama haka Gwaggo take Ungozomanci kafin ta gama karɓar haihuwa mai naƙuda ta ci uban dukaTalatuwa kuwa sai ta ji tamkar an ƙara mata ciwon ne amma haka ta daure ta danne ta yi shiru take salati a zuciyarta.




Gwagggo ko a jikinta wai an tsikari kakkausa, cikin rashin tausayi ta saka hannu wai za ta gyara kan ɗan da ya ƙi gaba ya ƙi baya. Tana saka hannun sai ta ji hannun jariri ya damƙi hannunta, cikin tsantsar mamaki take ƙoƙarin ciro hannunta amma abin sai ya gagari kwandila, jin hannun yaro ya mata riƙon da ko ƙaton hannun ba za ta iya ba.


"To mai yake faruwa da ni ne?" Gwaggo ta jefawa kanta tambayar a zuciyarta amma tsoro fal ranta dan yanzu tana fuskantar matsaloli a wajen aiwatar da aikinta na UNGOZOMA.


"Kai shegen jariri sakar mini hannu tun da tun kan uwaka ta bayyana a duniya hannun yake a duniyar" Gwaggo ta faɗa a fili tana yaƙi da kuɓuto da hannunta. Kakar Talatuwa sai ta bi Gwaggo da kallon mamaki ganin tana ta janyo hannunta amma kamar ma hannun ƙara yin ciki yake yi, kafin Kakar Talatuwar ta samu zarafin yin magana sai kawai suka ga wuri ya fara komawa yana matsewa tamkar dai ba shi ne ya buɗe ba sabo da fitowar ɗa amma yanzu sai ya koma kamar ba haihuwa Shamsiyyar za ta yi ba, sai wuri ya koma ya rufe ruf amma da hannun Gwaggon a ciki.


"Keeee! Ɗiyar nan tashi maza aljani ne a cikin ki ba ɗan mutum bane ya kama hannuna ya riƙe ku taimakeni ku kawo ɗauki kar na zama mai hannu ɗaya a garin karɓar haihuwa" Cewar Inna da gumi ya gama jiƙa ta jargaf idanu sun raina fata sai zare su take tamar an kama kwarto a ɗakin amarya, ga wannan goyo na Nasiru da bata sauke ba sabo da Laila da ta ce ba a sauke shi. Talatuwa kwa da take kwance ta buɗe ƙafafu a take gabanta ya bada wani dududuuummmmmm!


Masu biyo ni pc a kan a saka su grp ga link nan.




Wanda suke tambayar litattafaina na abin dariya akwai cmplt kowanne doc 500
ƳAR ZAMAN WANKA
ƘARA'IN INNA DELU
JALLI JOGA.




MAMAN AFRAH Whatsapp 09013181851








*META FORCE ARZIƘI DAGA ALLAH*


ƳAR UWA SHIN BAKI DA LABARIN META FORCE? DA IRIN ƊINBIM ARZIƘIN DA AKE KWASHEWA A CIKINSA, YA AKA YI BAKI YI REGISTER BA? KO BAKI DA BUƘATAR KUƊAƊEN DA ZA KI YI HIDIMAR YAU DA KULLUM?


TO KI ZO NI MAMAN AFRAH NA ZO MIKI DA HANYAR SAMUN KUƊI TA WAYAR HANNUNKI KUƊIN YIN REGISTER KAWAI ZA KI TANADA 9K DUBU TARA DOMIN ANA YIN REGISTER DA DALA 5 NE SAI DAI ALLAH KAƊAI YA SAN IRIN RIBAR DA ZA KI SAMU DA KUMA ALKAIRAN DA YAKE CIKIN KASUWANCIN. IDAN KINA SO SHIGA KUMA DA GASKE KIKE KI MINI MAGANA A WANNAN NUMBER 09013181851 IDAN BA YI ZA KI YI BA KAR KI MINI MAGANA DAN BANA SON ƁATA LOKACI!
[8/19, 17:57] Mom mashkur & Afrah: UNGOZOMA
(Mai karɓar haihuwa)










NA







MAMAN AFRAH






F.C.W


GARGAƊI⚠️


Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ta kowace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowace kafa ba sai da izinina a kiyaye.







Ina mata ƴan ƙwalisa, babbar mace alkyabbar mata, macen mai gyara ita wacce ta isa da miji su o'o sai dai su ga ƙeyar mijinta idan ya wuce amma basu ishe shi kallo ba domin babu abin da za su nuna mata. Gyaran gashi babbar martaba ce da take ɗaga darajar mace, musamman kayan gyaran gashin MAMAN ZEE da ya yi fice a ko ina ake labarinsa. Gani ya kori ji sai an gwada akan san na ƙwarai siyan na gari mayar da kuɗi gida💃💃💃💃💃💃💃💃
Hadaddu Kuma ingantattun kayan gyaran gashin mamanzee(chebe hair set)
Wadanda suke dawowa da martabar gashin Kai komai lalacewarsa biiznillahi Rabbi


Ga kyau ga inganci ga saukin kudi muddin kika fara amfani da kayammu sekindawo Mana da kyakkyawan labari
Kanki zeyi kyau ya rika sheki yayi tsayi yayi laushi duk matsalar da ke cikin kanki zata kau in sha Allah
Munada set complete
Kuma Muna Bada pieces
Haka Kuma Muna Bada Sari
Muna turawa akowanne gari kike Kuma Ako wacce kasa kike


Phone number *08079130166*






Page 1️⃣1️⃣➡️1️⃣2️⃣






*GIDAN MAI GARI*


Tun da su Gwaggo suka fita, Laila ba ta matsa daga inda take ba, tana nan a tsaye har Mai Gari ya canja kaya, haka ma Salele, shi kuma Taju umarni ta ba shi ya fita ya ɗakko akwatin kayanta da ta sanya ya ajiye a waje, domin tun da suka je gidan Mai Gari tsohon inda ya taso sai wasu samari da suke tsaye a wajen kamar dai ma ƴan shaye-shaye ne suka iyo dare daga yawonsu suka sanar musu inda ya koma suka musu kwatance hakan ya sanya basu yi ƙasa a gwiwa ba suka ɗunguma zuwa sabon gidan da suka koma ɗin. Mai Gari kai tsaye ya shiga ɗaki yana ƙoƙarin turo ƙofa Laila ta rangaɗa masa kira mai kama da na ƴan farauta wanda sai da hantar cikinsa ta kaɗa. Cikin son cika umarninta ya taho dan ya san dai bahaushe yana cewa in ka ji kira samu ne amma ban da kiran ɗan sanda, to yanzu ma dai ya san wannan kiran matar mai kama da butar shayi kan gajarta kiranta ba zai taɓa zama alkairi ba. Tun da ya zo ba ta ce masa komai ba dan haka da ya tsaya sai ya ja bakinsa ya rufe yana jiran umarni daga gareta a hakan ne ya ɗan kalli Taju da yake daga bayanta yana riƙe da akwati kuma ya ƙame a wuri ɗaya, alama Taju ya masa a kan ya durƙusa aikuwa cikin sauri Mai Gari ya duƙa tamkar mai neman yafiya.


"Kai! Mai jinin haila (Priod) Idan ka yi ƙunzugun ina son ganinka a nan" Ta faɗa daidai lokacin da Salele ya durfafi ɗaki zai shiga bayan ya fito daga bayi wanda can ya je da kayansa ya tsaftace jikinsa daga fitsarin da ya sha shararawa ya sako kayansa ransa fal murna ya tsira daga hannun masifaffiyar matar nan amma kuma kiran da ta masa ya sa ya sha jinin jikinsa. Da har hannu ya kai ya taɓo hantsar wandonsa jin ta ce idan ya gama ƙunzugun. Cikin sanyin jiki ya taho yana zuwa shi ma sai ya je kusa da Kakan nasa ya durƙusa kamar yadda Kakan na shi ya yi sai suka yi layi tamkar wasu almajirai.


"Ina so cikin sauri ku gyara mini ɗakin da zan zauna, dan haka duk wani tarkace ku kwashe daga wancan ɗakin, ku mayar wancan inda za ku kwatsu a ciki ni kuma in zauna a wancan ɗin" Ta faɗa tana musu nuni da ɗakin Gwago, kallon kallo aka fara tsakanin Salele da Mai Gari, Taju kwa da dama ya san a rina wai an saci zanen mahaukaciya babu abin da ya furta sai ma danne dariyarsa da yake sabo da yadda ya hangi idanun Mai Gari sai micincina su yake bakin nan nashi a hangame kamar ƙofar gari tsabar mamaki sai dai babu damar yin musu, dan da a ce wani ne ya nemi shigarwa Mai Garin hanci da ƙudundune da tuni ya yi maganinsa nan take amma yadda matar nan take jibgaga tabbas ko a hamatar ta, ta saka shi ta matse zai iya garzayawa barzahu ya rasa ma dalilin da ya sa yake jin wani mugun tsoranta.


"Tabbas matar nan na ga alama hatta shugabancin nawa na Mai Gari da nake tattalawa nema take ta saka ƙafa ta yi fatali da shi wallahi ba dan Allah ya yi ta gansamemiyar nan ba da babu abin da ta isa ta yi iko da ni in yi" Mai Gari ya faɗa a zuciyarsa yana sauke idanunsa a kan dantsen hannun Laila da yake ganin kaurin dantsen tamkar jikin ƙatuwar bishiyar ayaba, sai dai gashin kanta da ya zubo har kan kafaɗarta wanda dare bai hana shi yin sheƙi ba kana ganinsa ka san yana samun gyara da kayan gyaran kai a MAMAN ZEE (Chebe hair set)
Wadanda suke dawowa da martabar gashin Kai komai lalacewarsa biiznillahi Rabbi


Ga kyau ga inganci ga saukin kudi muddin kika fara amfani da kayammu sekindawo Mana da kyakkyawan labari
Kanki zeyi kyau ya rika sheki yayi tsayi yayi laushi duk matsalar da ke cikin kanki zata kau in sha Allah
Munada set complete
Kuma Muna Bada pieces
Haka Kuma Muna Bada Sari
Muna turawa akowanne gari kike Kuma Ako wacce kasa kike


Phone number *08079130166*






"To, to, to,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login