Showing 3001 words to 6000 words out of 44948 words

Chapter 2 - UNGOZOMA Book Complete Original by Maman AFRAH F.txt

19 Oct 2024

5929

ɗakin ita kaɗai da ta san haka za ta faru ai da ta jira zuwan Mai Gari mijinta in ya so ko ma mene ne zai same ta sai ya same su tare, musamman ma da ya kasance Mai Garin ba shi da ɗakin kansa a gidan tun da jiya ne suka tare a gidan kuma ɗakuna biyu ne kaɗai a gidan suka ɗauki ɗaya Salele ya ɗauki ɗaya.


"Ni Ramma na shigenge yanzu haka Mai Gari ɗakin Salele suka shige ni ina nan ni kaɗai kamar mayya, an bar ni a gefe kamar yajin ƙosai, haka fatallun nan za ta zo ta yi awon gaba da ni, ba tabbas abin da yawa mutuwa ta shiga kasuwa" Ta faɗa tana sharar ƙwallar tausayin kanta. Mai Gari kuwa da yake faman buga mata ƙofar yana jira ta buɗe masa ya shiga, sai dai tsoro ne fal ransa dan haka ma ya ƙi yin magana sabo da gudun kar fatallun ta jiyo maganarsa ta ji daɗin tsallakowa ta sama dan haka himma kawai ya bada wajen bugawa dan ya samu ta buɗe masa shi ma ya afka ɗakin.


"Yau kam na ƙara yarda da kirarin, ƊAKI KO KANA ZUBA KA FI WAJE" Mai Gari ya faɗa a ransa yana cije leɓe ganin ya ɗaki amma yana waje sanyi yana ƙarewa a kansa ga tsoron fatallu.


Jin har lokacin ba a buɗe masa ba kuma dai fatallun da alama ba fasa buga ƙofar za ta yi ba dan zuwa yanzu tamkar za a ɓalle ƙofar kai har ma da langa-langan da aka yi wa gidan ƙawanya da shi wannan ne babban abin da yake ƙara kaɗa hantar gabaɗayan waɗan da suke cikin gidan, hakan ne ya sanya Mai Gari hasaso cewa dab yake da kai wa barzahu ziyara matsawar dai fatallun ta ɓalle ta shigo gidan domin shi kaɗai ne a tsakar gida kowa ya shige ɗaki ya banke a hankali ya fara bin bango tamkar wani ƙadangare, har sai da ya dangana da saitin inda windown ɗakin yake, cikin karkarwa jiki da bugun zuciya ya fara dafa bangon a hankali dan ba ya fatan ko motsinsa a jiyo bare a kawo masa farmaki, hatta da numfashi ɗai-ɗai yake yi idan ya shaƙi ɗaya sai ya ɗan jima zai huro sai ya sake shaƙa duk dan sabo da tsaro ba wai dan tsoro. Bayansa ya waiwaya sai kawai idanunsa suka masa gizo da ganin wata mata da farin kaya a take cikinsa ya ɗuri ruwa maƙoshinsa ya bushe ƙamas cikin hanzari ya kama katangar ya ɗare windown ƙofa uku ce a windown amma ƙanana Mai Gari cikin ruɗani ya dage ya tura kansa cikin ƙofa ɗaya, ta cikin hasken da ya ratsa ɗakin ta windown ya hangi Gwaggo da ta yi zaman ƴan bori a ƙasa sai wani abu take kamar zararriya


"Taɓ! Lallai duniya gidan kashe ahu, yanzu Ramma ce a cikin wannan halin lallai abin al'ajabi ango ya kwana da ƙunzugu" Cewar Mai Gari a zuciyarsa amma halin da yake ciki ya hana shi yin ko da murmushi ne bare a kai ga dariya. Ƙoƙarin yaƙi da harshensa yake kafin a kai ga laɓɓa domin ya ba shi damar furta wata kalma da za ta ankarar da Ramma cewar yana window yana jiran ta kawo masa ɗauki amma ganin fitowar furuci daga bakinsa zai ƙara kabbama halin tsoron da yake ciki sai ya ƙara jan bakinsa ya tamke shi gam. Cikin rashin kuzari ya ɗaga hannunsa guda ɗaya ya ɗan daki jikin bangon ɗakin daga ciki amma kuma Gwaggo tana jin sautin taɓa bangon sai hakan ya ƙara rura wutar tsoro da fargabar da take ciki a nan take cikin ta ya karta sai sautin tusar ta kawai kake ji ƙuiittt-ƙuiit tamkar sabuwar bodara.
"La sharikalahu Allahu, la sharika lahu Allah, manzallazi yashfa'u indahu illah bi'izinihi" Gwaggo ta faɗa a ranta tana jin tamkar ƙasa ta tsage ta shige ciki ko ta samu sukuni.
"Mai Gari ne mijinki daure ki lallaɓo ki buɗe mini in samu ni ma in shigo daga...
Ƙaran buɗewar ƙofar gidan ne da ya ziyarci majiyar sautin Mai Gari ya dakatar da shi daga ƴar maganar da ya samu kuɓutowar ta daga bakinsa da ya bushe wanda ya yi ta a cikin salon raɗa-raɗa tamkar wanda mura ta yi wa kamun kazar kuku. Dan ita Gwaggo a halin da take ciki ma bata tsinkayi muryar mijin nata ba ma bare har ta san abin da ya ce hasali ma bata san ana yi ba wai kunu a maƙota ita abu ɗaya kaɗai ta san tana iya jin sa a kunnuwanta shi ne sautin fitar tusar ta sai kuma bugun ƙofar gida da kuma langa-langan gidan, hana rantsuwa ta ji bugun jikin bango wanda ta yi amanna da cewa fatallun ce ta tsaga bango za ta shigo ɗakin hakan kuwa shi ne ya ƙara kaɗa mata hantar cikinta bare kuma a yanzu da ƙaran buɗuwar ƙofar gidan ya sanya ta ƙara saka wa a ranta cewar suna daf da zama gawarwakin da za a kai maƙabartar da take kusa da su a wayewar garin gobe. Cikin sanɗar rarrafe ta fara rarrafawa domin ganin ta sama wa kanta mafaka a cikin ɗakin ko Allah zai sa ta tsira da ranta, haka ta fara rarrafe riƙe da zanenta a hannun ta wanda har yanzu bata samu zarafin ɗaura shi a ƙugunta ba, tana fara rarrafen ta ji gabaɗaya gwiwoyinta sun sage hakan ya tabbtar mata da gwiwar ba za ta iya ɗaukanta ba, babu shiri sai ta mayar da akalar rarrafen nata ga jan mazaunanta, amma kuma tana ja sau biyu sai ta ji tamkar tana janyo gudawar da ta samu komawar ta ne dan haka ta yi rufda ciki ta fara jan cikin ta a haka ta kai wa wani duro irin gajeran duro ɗin nan marar tsayi cikin ƙarfin hali ta lallaɓa ta yi dabara ta ɗaura zanen nata sai ta shige cikin duron da aka zuba dawa wacce ko casawa ba a yi ba sai kuma cikin sanɗa ta ɗauki wata fantekar kukar kaɗi ta kifa a kan nata ba tare da damuwa da yadda gabaɗaya ta sheƙawa jikinta kukar ba amma a haka ta duƙunƙuna a cikin duron tana danne atishawar da take son fitowa sabo da kukar da ta shaƙa, amma bata damu ba fatan ta wurin ya zama maɓoyarta da fatallun ba za ta ganta ba.


Mai Gari kuwa tun da ƙofar nan ya ji ƙaran buɗewar ta sai da ya ƙara ƙanƙame ƙarfen windown sabo da gudun faɗowa dan ya lura karkarwar da jikinsa ya ɗauka kamar mazari ko kuma mai masassara dan ya san ko da a ce fatallun za ta kashe kowa to ya yi imani ta kansa za ta fara tun da shi ne a tantagayyar tsakar gidan bai samu damar afkawa ɗaki ba. Ganin Gwaggo ta fara ƙoƙarin sama wa kanta mafaka sai ya shiga gyaɗa kai kamar wani ƙadangare wai hakan alamu ne yake yi wa Gwaggo da bata san da wanzuwarsa a wajen ba, dan ta taimaka masa amma ina! Gwaggo ta samu nasarar shigewa cikin duro mai dawa ta ƙara da sheƙawa kanta kukar kaɗi da kifa wa kan nata fanteka dan tana ganin ta samu maɓoya. Abin duniya ne ya haɗe wa Mai Gari goma da ashirin jin ƙaran tahowar mutum da alama dai fatallun ta samu nasarar shigowa cikin gidan, Mai Gari cikin ficewar hayyaci ya fara ƙara kutsa kansa cikin ƙofar dan ya samu gangan jikinsa ya shige ko ya dira cikin ɗakin amma ina! Sai ya ji hatta da kafaɗarsa ba za ta shige ba bare a yi zancen shigewar gangan jiki. Wani fitsari da ya taru ya samu mafaka mararsa ne ya samu nasarar fitowar shaaaa kamar an buɗe famfo sabo da tsabar duniyar tsoron da ya tsinci kansa a ciki cikin sauri ya saki inda ya kama sai ya zamana ya riƙe da hannu ɗaya, hannun ɗaya ya miƙa ya shafo mazaunansa ai kuwa zaton da yake ya zama gaskiya domin kuwa jin hannunsa ya sauka a kan asalin fatar jikinsa ba wai wando ba hakan ya sanya ya tuna ashe dai tun lokacin da ya taho bai ɗaure mazugin wandon ba, da ya tashi hawa windown ya ma manta da cewa wandonsa ba a ɗaure yake ba.


"Kai ni na ga abin da ya ture wa buzu ɗani, yau mazaunan Mai Gari ne a buɗe muraran babu rufa sai ka ce mazaunan ɗan akuya" Mai Gari ya faɗa a ransa yana fashewa da wani irin kuka marar sautin sai hangame baki yake yana jin ina ma yana da layar zana da ya ɓace ɓat ya huta da wannan tashin hankalin da yake ciki.

A ɓangaren Salele ma tun da ya ji ƙaran buɗewar ƙofar sai lumfashinsa ya tsaya cak, dan shi babu abin da ya ƙi jini sama da fatallun nan da yake ta ji ana labarin ta a gari amma sai ga shi yau ta shigo musu gida tabbas ya san suna cikin jalala. Jin yana neman mutuwa sabo da rashin numfashi da ƙarfi ya huro numfashin tare da buɗe rufar da ya yi domin ya shaƙi iska da kyau.


Malam Mammani wanda shi ne ya yake ta bugun ƙofar gidan har dai ya samu ƙofar ta buɗe da kanta shi ne ya shigo cikin gidan na Mai Gari a rikice dan shi ma a tsorace yake sabo da gamo da ya yi a hanyar zuwansa gidan na Mai Gari domin shi ma matarsa ce take naƙuda wannan ne dalilin da ya sanya ya fito domin zuwa ya kira INGOZOMA Gwaggo Ramma dan ta ƙarɓi haihuwar sabo da duk garin Gumurzu ita kaɗai ce take karɓar haihuwa. Da yake a tsorace yake wannan dalilin ne ya sanya yake yi wa gidan bugun ta ko ina sannan yanzu ma da ta shigo gidan ko sukunin yin sallama bai samu ba burinsa kawai ya samu mafaka, tun da ya san masu gidan suna can suna bacci tun da ba su suka buɗe masa ba tamkar zararre haka ya shiga baza idanu cikin wani irin faɗuwar gaba ya zaro idanunsa domin tabbatar da abin da idanun nasa suka yi arba da shi wato mutum ya hanga a maƙale a jikin bango daga wajen window yana sukur-sukurtu ji ya yi tamkar ya juya ya koma inda ya fito sai dai ba zai iya ba sabo da tsoron fita yake. Cikin wulga ido kamar tsohon munafuki ya fara neman mafakar fakewa. Ta cikin farin watan idanunsa suka sauka a kan dabbobi, inda runfar su take suna ɗaɗɗaure sai dai dukan su a kwance suke babu wani dogon tunani Malam Mammani ya nufi turken dabobin nan. Amma jin ƙaran ƙofar da ya biyo ta can sai ƙafafunsa suka sage masa ƙafafun nasa suka gagari ɗaukan gangar jikinsa dan yanzu ya gane fatallun ma ashe sun cika gari ne tun da ya baro wata da ta biyo shi a can baya sannan yanzu shigowarsa ya hangi wata maƙale a window dan haka sai ya zube a ƙasa cikin ƙarfin hali ya shiga rarrafawa ya nufi turken dabobin yana zuwa dabobin ganin an tunkaro su sai suka fara tashi tsaye kowanne ya wage baki yana meeeyyyyy.


"Ku yi haƙuri dabbobi kun samu baƙon bil adama a cikin talatainin daren nan, ku yi shiru in samu in yi ɓadda kama a cikin jinsinku sabo da kar fatallu ta yi arba da ni in shiga tara ba ma uku ba" Cewar Malam Mammani a hankali cikin raɗa-raɗa kamar wanda yake magana da mutum mai hankali yana kutsawa cikin ayarin dabbobin wanda suka cigaba da raira kukan su tamkar dai an zuga su ne an ce su yi ta yin kukan babu ƙaƙƙautawa. Sai da ya shige tsakiyar su duk da warin kashi da zarnin fitsarinsu amma ta haka ya shiga har sai da ya je kusa da wani jigo wanda ba a ɗaure dabba a yana zuwa bai jira komai ba ya kama igiyar jiki ya sarƙafa hannunsa na dama alamar shi ma ya shiga sahun dabbobin dan yana ganin babu yadda za a yi fatallun ta gano shi.


Sai da ya ga ya samu waje sannan ya shiga tunano matarsa kuma amaryarsa Talatuwa wacce take can cikin halin naƙuda domin wannan dalilin ne ya sanya ya taho. Hannunsa na hagun ya kai kan kansa tare da fuskarsa zuwa wuyansa ai kuwa ya yi nasarar shafo garin tuwo wanda Talatuwar ta ɗaga ƙwaryar ta juye masa garin a kansa tare da kifa masa ƙwaryar a kansa, duk a cikin halin naƙuda
"Kai Talatuwa haka kika mayar da ni kamar an fito da ni daga injin fulawa fari fat babu kyan...


Ganin wannan fatallun ta jikin bango tana zamowa ta sakko ƙasa shi ne abin da ya hana Malam Mammani ƙarasa maganar zucin da yake yi. Mai Gari kuwa dama tun lokacin da ya waiwaya ya hangi Malam Mammani ya shigo a tunaninsa fatallunce dan yadda ya gan shi busu-busu da farin abu tun daga kai har fuskarsa wannan ne abin da ya ƙara tsorata shi, sai dai juyawar da ya yi kafin ya juyo sai ya nemi inda fatallun ta yi ya rasa hakan ne ya sanya ya yanke shawarar sakkowa daga saman windown domin ya sama wa kansa maɓoya dan ya ga Gwaggo Ramma bata da niyyar buɗe masa.


Yana sakkowa ya tsaya cikin rawar jiki ya ɗaura tazugen wandonsa sabo da ruɗewa sai da ya yi ɗauri bakwai maimakon ya yi ɗaya da azargagiya ɗaya. Wani marayan kukan tausayin kansa ne ya kama shi ganin babu inda zai ɓuya dan ya san ko wajen Salele ya je ba zai saurare shi ya buɗe masa ƙofar ba dan ya ga ko lokacin da suka fara gudun ceton rai har gware suka yi da shi amma ko ya tausaya masa sai ma ya hau gudu ya shige ɗaki ya banko wannan ne ya sanya Mai Gari ya gane cewa yau nafsi-nafsi ake kamar a filin ƙiyama. Durƙusawa ya yi dan ba ya so ya fara tafiya a kan ƙafafunsa fatallu ta ji ƙaran tafiyarsa ta bayyana dn haka rarrafe ya fara duk da yana jin yadda gwiwoyinsa suke gurziwa da ƙurunƙusan tsakuwa amma haka ya daure ya nufi turken dabobi dan ya ga kamar a can ne kaɗai zai samu mafaka tun da yana ganin babu wata fatallu da za ta yi tunanin akwai ɗan adam a wajen dabbobi bare har ta kai masa farmaki.


"Kai jama'a! Zawo mai saka manya sauri, wai ni Mai Gari ni ne da rarrafe zan je turken awaki neman mafakar fakewa" Ya faɗa a ransa yana jin tausayin kansa da kansa ganin ba shi da ƴancin shiga ɗaki a ciki gidan.


Malam Mammani da yake durƙushe a wajen dabobin yana saƙale da igiyar jigon da ya yi wa kansa a rumfar dabobin tamkar dama nan ne mazauninsa, ganin Mai Gari ya nufo inda yake dan a tunaninsa fatallun ce dan haka sai ya ƙara shan ruwan jikinsa a take jikin nasa ya shiga karkarwa kamar mazari dan bashi da wata nutsuwa da zai gane cewa Mai Gari ne ya nufo wajensa ba fatallun ba. Fitsarin da ya matse shi ne ya kufce masa a take ya fara jin ya ƙara shiga mugun tashin hankali.


"Wayyo! Yanzu nan ɗin ma an gudu ba a tsira bane kenan" Ya jefa wa kansa tambayar da ko kusa ba shi da amsar ta.




Maman Afrah Whatsapp 09013181851






*META FORCE ARZIƘI DAGA ALLAH*


ƳAR UWA SHIN BAKI DA LABARIN META FORCE? DA IRIN ƊINBIM ARZIƘIN DA AKE KWASHEWA A CIKINSA, YA AKA YI BAKI YI REGISTER BA? KO BAKI DA BUƘATAR KUƊAƊEN DA ZA KI YI HIDIMAR YAU DA KULLUM?


TO KI ZO NI MAMAN AFRAH NA ZO MIKI DA HANYAR SAMUN KUƊI TA WAYAR HANNUNKI KUƊIN YIN REGISTER KAWAI ZA KI TANADA 9K DUBU TARA DOMIN ANA YIN REGISTER DA DALA 5 NE SAI DAI ALLAH KAƊAI YA SAN IRIN RIBAR DA ZA KI SAMU DA KUMA ALKAIRAN DA YAKE CIKIN KASUWANCIN. IDAN KINA SO SHIGA KUMA DA GASKE KIKE KI MINI MAGANA A WANNAN NUMBER 09013181851 IDAN BA YI ZA KI YI BA KAR KI MINI MAGANA DAN BANA SON ƁATA LOKACI!
[8/19, 17:57] Mom mashkur & Afrah: UNGOZOMA
(Mai karɓar haihuwa)






NA






MAMAN AFRAH






F. C.W




GARGAƊI⚠️


Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ta kowace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowace kafa ba sai da izinina a kiyaye.




Page5️⃣➡️6️⃣


Ganin hakan sai Malam Mammani wata dabara ta zo masa a take ya hangame baki ya shiga ƙuga kukan tinkiya sai kukan nasa ya kwatse da na sauran dabbobin wai shi duk a tunaninsa fatallun da ta tunkaro shi ta gane duka dabbobi ne a rumfar babu mutun ko ɗaya. Tun ƙarfi Malam Mammani cewa yake imbeeeee amma Mai Gari ma da yake a ruɗe ba zai ma iya tantance cewar kukan nan ba fa na dabobi bane kaɗai har da na bil adama, dan shi ma ta kansa yake. Malam Mammani da yake ta kukan tunkiya ko saurarawa ba ya yi bai ankara ba sai ji ya yi wani ƙaton rago ya ɗane bayansa, wannan ne ya dakatar da shi daga kukan da ya daddage ƙarfinsa yana yi.Kafin ya gama tantanewa sai jin ragon ya yi ya fara masa barbara. Bai gama dawowa daga mamakin da ya tafi ba sai ya ƙara ganin wani ɗan akuya shi ma ya zo yana sansanar bakinsa. Wani jaririn ɗan tinkiya shi kuma sai ya shiga tura baki jikin rigar Malam Mammani, da alama nono yake nema ya mamula, dibara Malam ɗin ya yi ya tura shi gefe a ransa yana cewa.




"Abu ya haɗe mini goma da ashirin in banda lalacewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login