Showing 9001 words to 12000 words out of 44948 words

Chapter 4 - UNGOZOMA Book Complete Original by Maman AFRAH F.txt

19 Oct 2024

5932

ai tun da dai ku kaɗai fatallun ta gani sai ku haƙura ku tafi lahirar ku kaɗai" Ya faɗa yana fara lallaɓawa ya je can inda yake ajiye takalman ball ɗinsa yana zuwa ya miƙa hannu ya ja mazugin takalmin ya zugi tamkar zai saka takalmin a ƙafarsa amma abin mamaki sai ya durƙusa ya saka fuskarsa a kan takalmin yana ƙoƙarin saka kansa a cikin takalmi.


"Dan Allah kaina ka mini rai ka shige cikin takalmin nan na ƴan ball, ka cece ni na tsira da mutuncina, in shiga cikin ka in laɓe sai ƙura ta lafa na fito" Ya faɗa har lokacin yana ƙoƙarin ganin kan nasa ya shige cikin takalmi dan sai dannawa yake bayan gabaɗaya ma ko faɗin fuskarsa bai shiga ciki ba.


"Allah ka bani layar zana in ɓace in huta, Allah na tuba ka yafe mini kura-kuraina zan cigaba da yin sallah" Ya faɗa yana ɗaga hannu sama alamar addu'a idanunsa suna zubar hawaye.


"Allah ka sa in koma kamar ɓera ko ma kiyashi yadda zan ɓuya ba tare da an ga mafaka ta ba" Ya faɗa hawaye suna kwaranyo masa tamkar an buɗe famfo.




"Yeeee jama' a ku fito Tajuddin ya dawo sanye da kayan sojoji shikenan mun warke" Cewar Mai Gari da ƙarfi dan ya ga idan ba haka ya yi ba babu wanda zai fito.


Ɗif Gwaggo ta yi fuska a cikin dawa.


"Ikon Allah na zaune ya faɗi, Taju kuma? Allah sarki Mai Gari kin dai ji yana mini albishir mai daɗi, ya ɗauka ban san na rufe masa ƙofa ba ni kuwa ina sane wai karuwa ta taka matar aure" Ta faɗa a zuciyarta, a take ta yi jifa da fantekar kanta bizigir ta fito daga cikin duron har zaninta yana neman faɗuwa ta kama ta ɗaura.


"Kai dai zanin nan nawa kana son a ke ganin tsiraicina, in ba haka ba da yaushe ma na ɗauraka"


"Allah sarki ashe dai rai kan ga rai, lallai in da rai da rabo yo ni yanzu ina na ga ta zama wai an ɗaurawa karya zane" Ta faɗa tana fitowa ta buɗe ƙofar ta fito dan sai da ma ta leƙo ta windown ta tabbatar ganin wata dalleliyar fitila.


Salele ma bai san ma ya sauke hannuwansa ba, daga ɗaga wa da ya yi yana addu'ar, jin an ce Taju ya dawo. A sukwane ya buɗe ƙofar ya bazamo yana tahowa da sauri har yana tuntuɓehaka ya fito yana haɗa wa da gudu, Kusan a tare suka fito shi da Gwaggo, Malam Mammani ma da ya hango Gwaggo sai ya ji matsalarsa ta zo ƙarshe tun da ga Gwaggo sai su tafi ta karɓi haihuwar amaryarsa Shamsiya. Dan haka shi ma cikin zafin nama ya taho daga turken dabobin da wani jargaggaɓin wandonsa da ya sha fitsari sama da cikin kwando. Fara gudunsa kenan wani ƙaton rago mai manyan ƙaho ya tunguje Malam Mammani sai ga Malam Mammani tamkar iska ta ɗaga leda ya faɗi yashe a wurin ya ji faɗuwar sosai amma sabo da ganin INGOZOMA sai ya yi ta maza ya tashi tsaye ya taho da gudu.


Mai Gari ma ganin sun yi ayari kowa ya nufi wajen Taju sai shi ma gudun kar a yi babu shi, amma shi gogan da yake riƙe da fitilar nan ko motsi bai yi ba kamar ma bai san ana yi ba wai kunu a maƙota.


"Kai!!!" Matar nan da take tsaye daga gefen Taju ta faɗa da mugun ƙarfi wanda hakan ya sanya su duka suka dakata. Cikin tsananin mamaki Gwaggo ta saki baki dan ita har ga Allah bata lura da matar ba ma, da yake hasken duk ya dalle mata idanu. Su duka huɗun sai yanzu suka yi wa matar kallon nutsuwa, mace ce gabjejiya dan ko za a jaɗe su, su duka huɗun kar in ma za a haɗa har Taju to ba za su kai girman rabin jikinta ba ma. Dan faɗin jikinta tamkar ka haɗa buhun gero biyu ne, girmanta ma ya wuce misali
Sai shegen gajarta kamar wata wada.


"Taju ka cigaba da aikin ka" Ta faɗa da kakkausar murya, hakan ya sanya su Mai Gari sakin baki kamar layar mai tafiya suna kallonta. Taju kuwa a take ya fara buga ƙafafu yadda sojoji suke yi, ya sara mata kafin daga bisani kuma ya fara fareti yana ta yi yana faɗin "Left right" Tamkar zai ari baki.


"Ku in banda ku sakarkaru ne, kuma ma banda sakarci waƙa a tasha haka kuka fito kuna wani gudu tamkar wasu shanaye, shin baku ganni bane? Ko an ce muku bakin rijiya wajan wasan makaho ne? To ku buɗe kunnuwanku ku ji ni, hatta Taju da kuke gani a ƙarƙashin ikona yake dan haka kowa ya iya bakinsa domin bahaushe ya ce iya ruwa fidda kai" Cewar tiƙeƙiyar matar nan cikin wata irin murya mai kama da ta ƴan bariki.


"Haba ke kuwa baiwar Allah, yanzu a talatainin daren nan duk da an ce dare mahutar bawa ne amma za ki zo ki nemi ki ɗaga mana hankali, muna cikin tsoron zuwan fatallun ashe dai bonono ne muka yi wai rufin ƙofa da ɓarawo" Gwaggo Ramma ta faɗa tana tafa hannuwa duk da irin dukan luguden da ƙirjinta yake na tsabar tsananin tsoron ƙatuwar matar da tun da uwarta ta haifeta bata taɓa ganin halitta mai girman wannan ba, dan idan akwai wani abu da za a kwatanta da matar to kuwa sai dai a kwatanta ta da giwa, dan tsawo kawai giwa za ta faɗa wa matar. Kuma abin da ya ƙara sanyaya musu jiki irin yadda take ba Taju umarni duk da kayan sojojin da yake jikinsa hakan ne ya sanya suka kasa banbance aya da tsakuwa.


"Au Allah har kina da bakin magana to ki sanya a ranki daga yau kun yi ban kwana da zaman lafiya ke hatta dare da rana zai zama ɗaya a wajenku" Matar ta faɗa tana kallonsu.


"Haba gingimemiya wai ya haka ne, za ki zo ki yi wani tiƙiƙi da ke kina mana wasu maganganu mararsa kai da ƙaf... Wani mari da ƙatuwar matar nan ta ɗauke Salele da shi, shi ne ya dakatar da shi daga maganar da bai ƙarasa ba.
Ƙaran marin ne ya sanya Gwaggo da Mai Gari, juyawa a kiɗime za su koma ɗaki har zanin Gwaggo yana neman faɗuwa ta taro shi.


"Duk wanda ya ƙara ɗaga ƙafarsa daga nan sai ya gwammace kiɗa da karatu" Tun kan matar ta ida maganar Gwaggo da Mai Gari suka ja wani uban birki tamkar motar da ta kusa hantsilawa rami ta yi birki. Taju kuwa ganin hukunci da aka yi wa ƙaninsa na mari sai ya bada himma wajen cibaga da faretin da yake yi har ƙara ƙuga "Left right ɗin yake.

Salele kuwa marin da aka masa sai da ya ga gilawar taurari masu mugun haske, sannan sai idanun nasa suka yi wani dilim ya daina ganin komai, sai kuma ganinsa ya dawo zafin marin kuwa sai da ya saka shi sakin fitsari a wando. Malam Mammani kuwa a take ya shiga janyo salatin annabi bakinsa banda mismis babu abin da yake dan shi ya tabbatar da shi aka ɗauke da marin to da kuwa idan suma ne ma da ya yi dan yana jin ko zai falka daga suman wataƙila sai ya yi wata bakwai ko sama da haka dan ya ga yanayin jikin matar nan akwai matsala a ce ko lakucin mutum ta yi bare kuma mari.




Ɗif gidan ya yi tamkar babu wata halitta a ciki, baka jin komai sai ƙaran faretin Taju da left right da yake faɗa.


"Ko akwai mai magana ? Idan akwai ina sauraro dan ni wandon roba nake daidai da ƙugun kowa, duk abin wani zai yi to abin zai zo min a daidai wai mai ido ɗaya ya leƙa kwalba" Ta faɗa tana ƙoƙarin ɗaga ƙafafunta kowa kallonta kawai yake yana mamakin irin ƙibarta, ita kuwa ko a jikinta wai an tsikari kakkausa dan ta san ƙibar nan tata ita ce take ceton ta.


Malam Mammani hawaye ya fara na tausayin matarsa ya san ana can ana jiran zuwansa da INGOZOMA amma kuma ga shi daga shi har INGOZOMAR a cikin wani hali.


"Taju dakata da aikin nan" Kafin ta rufe bakinta ƙafafun Taju sun tsaya daga faretin, nakinsa ma ya yi ɗif kamar an yi ruwa an ƙafe lunfashinsa ne kaɗai yake aiki a jikinsa dan ya ƙame a waje ɗaya sai hannunsa da ke gefen kunnensa wanda ya sara mata irin yadda sojoji suke sarawa na sama da su.


Taju ina so ka faɗa musu wacece ni"


"Su ,su, su"


"Ka nutsu dalla! Bana son wata in'inna" Ta faɗa tamkar za ta kai masa duka, da sauri ya saita nutsuwarsa ya fara bayani.


"Sunan ta yallaɓiya Laila, matar shugaban ƙasar sojojin duniya, tana da ɗa mai suna Nasiru" Ya faɗa yana ƙara daidata nutsuwarsa dan ba ya so ko kaɗan ya yi katoɓara daga bayanin da ta masa abin da zai samu hukunci daga wajenta dan da a ce ta hukunta shi gwara a bashi aikin ƙarfi na sati guda.


"Zan zauna da ku na tsawon lukuta ni kaina ban san lokacin tafiyata ba...


Dididim diiimmm Gaban Mai Gari Salele, da kuma Gwaggo ya buga jin wai zama za ta yi a gidan bata san ranar tafiyarta ba lallai akwai gwarama.


"Taɓɗi! Sha biyun dare marecan kura, ai ni da zuwa gidan nan sai ranar da kika bar gidan nan" Cewar Malam Mammani a ransa yana fatan Allah ya kuɓutar da shi daga gidan.


"Ba na son a ke barina da yunwa ko ni ko ɗana, sannan a kowace rana ina cin shinkafa kwano biyar da rana, kai a taƙaice ma a rana ban san iyakacin abin da nake ci ba dan haka a kiyaye, sannan idan lokaci tusa ta ya yi ba na iya yin tusa sai na zauna a kan mutum, sannan tusar take samun damar fitowa, dan haka a duk lokacin da zan yi tusa zan ƙwalawa ɗaya daga cikin ku kira sai ya zo na zauna a kansa na saki tusa ta"


Ƙulululuuuuuu, cikin Mai Gari da Gwaggo ya bada, cikin Salele kuwa ya fi na kowa murɗawa saboda ya san yanzun nan matar iya hannu kaɗai ta sa ta mare shi sai da ya gwammace kiɗa da karatu bare kuma a ce ta danne mutum ai sai mutuwa kuma. Malam Mammani kuwa dariyar ƙeta ya fara a zuciyarsa jin wai sai an danne su Mai Gari za a ke yin tusa tabbas ya san za a sha dirama ba ƴar kaɗan ba a gidan.


"Allah ya kawo wa jama'ar garin Gumurzu wacce za ta rama musu cuta da cin zalin da Ramma da Mai Gari suke yi" Ya faɗa a ransa yana godewa Allah dan ya san tabbas matar nan sai ta gyara musu zama musamman Mai Gari da ba shi da aiki sai karɓe gonaki da abincin mutane da suka noma kai babu wani abu da Mai Gari ba ya karɓa a hannun mutanensa.


MMn Afrah Wtsapp 09013181851






*META FORCE ARZIƘI DAGA ALLAH*


ƳAR UWA SHIN BAKI DA LABARIN META FORCE? DA IRIN ƊINBIM ARZIƘIN DA AKE KWASHEWA A CIKINSA, YA AKA YI BAKI YI REGISTER BA? KO BAKI DA BUƘATAR KUƊAƊEN DA ZA KI YI HIDIMAR YAU DA KULLUM?


TO KI ZO NI MAMAN AFRAH NA ZO MIKI DA HANYAR SAMUN KUƊI TA WAYAR HANNUNKI KUƊIN YIN REGISTER KAWAI ZA KI TANADA 9K DUBU TARA DOMIN ANA YIN REGISTER DA DALA 5 NE SAI DAI ALLAH KAƊAI YA SAN IRIN RIBAR DA ZA KI SAMU DA KUMA ALKAIRAN DA YAKE CIKIN KASUWANCIN. IDAN KINA SO SHIGA KUMA DA GASKE KIKE KI MINI MAGANA A WANNAN NUMBER 09013181851 IDAN BA YI ZA KI YI BA KAR KI MINI MAGANA DAN BANA SON ƁATA LOKACI!




MASU MINI MAGANA KAN HARKAR META FORCE SUNA YIN REGISTER, INA MUKU FATAN ALKAIRI INA TAYA KU MURNA DA SHIGOWA GIDAN ARZIƘI ALLAH SA AN FARA A SA'A🥰
[8/19, 17:57] Mom mashkur & Afrah: UNGOZOMA
(Mai karɓar haihuwa)


NA

MAMAN AFRAH




F.C.W






GARGAƊI⚠️


Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ta kowace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowace kafa ba sai da
izinina a kiyaye.




Wannan tallar hajar mata masu aji ce💃


Ina mata ƴan ƙwalisa, babbar mace alkyabbar mata, macen mai gyara ita wacce ta isa da miji su o'o sai dai su ga ƙeyar mijinta idan ya wuce amma basu ishe shi kallo ba domin babu abin da za su nuna mata. Gyaran gashi babbar martaba ce da take ɗaga darajar mace, musamman kayan gyaran gashin MAMAN ZEE da ya yi fice a ko ina ake labarinsa. Gani ya kori ji sai an gwada akan san na ƙwarai siyan na gari mayar da kuɗi gida💃💃💃💃💃💃💃💃
Hadaddu Kuma ingantattun kayan gyaran gashin mamanzee(chebe hair set)
Wadanda suke dawowa da martabar gashin Kai komai lalacewarsa biiznillahi Rabbi


Ga kyau ga inganci ga saukin kudi muddin kika fara amfani da kayammu sekindawo Mana da kyakkyawan labari
Kanki zeyi kyau ya rika sheki yayi tsayi yayi laushi duk matsalar da ke cikin kanki zata kau in sha Allah
Munada set complete
Kuma Muna Bada pieces
Haka Kuma Muna Bada Sari
Muna turawa akowanne gari kike Kuma Ako wacce kasa kike


Phone number *08079130166*



Page 7️⃣➡️8️⃣






*Dawo wa daga labari.*


Tsoron da su Malam Mammani suke ji ne ya ragu ganin Taju da kayan sojoji sun san kuwa dole fatallu ta ji tsoron bindiga. Wata ajiyar zuciya mai ƙarfi suka saki a tare dan suna ganin ai kakarsu ta yanke saƙa.
"Mamaki kwalli a kunne, yau kuma Taju ne ya dawo" Mai Gari ya faɗa a ransa cikin murna dan babu wani abu da ya daɗaɗa masa rai sama da ganin Taju da kayan sojoji kuma a lokacin da yake cikin halin buƙatar taimako.


Cikin sauri Malam Mammani da Mai Gari suka shiga ƙoƙarin tashi sai dai Malam Mammani gabaɗaya ya sha'afa da hannunsa na dama da ke ƙulle a jigon dabobi dan haka zai tashi tsaye sai ya ji hannun a maƙale a take ya shiga fitar da hannun dan yanzu tun da halin da suke ciki ya zo ƙarshe to kuwa burinsa bai wuce ya gan shi a gaban matarsa da ya baro ta a cikin halin naƙuda ba.


Mai Gari ko ta kan Malam Mammani bai bi ba ya nufi wajen su Taju har yana neman yin tuntuɓe, dan shi yana ganin shikenan waraka ta zo masa wai mazaunan matar mai bayar da maganin wuta ya ƙone.


"Taju, taɓ lallai abu rabo ne tsintar ƙwan jaki, kai ne wannan" Ya faɗa yana dab da ƙarasowa wajen su Taju har ya kusa ƙarasa wa kamar wanda aka ce ya tsaya ai kuwa ya ja tunga ya shiga rafkawa Gwaggo Ramma kira.


"Ramma! Ramma! Ramma, Salele, Salele Salelee" Mai Gari da ya wawake dogon maƙogwaronsa ya shiga faɗa ko jan numfashi ba ya yi.


"Kai jama'a, a yi a gama ai ya fi a ƙarasa gobe, in banda dai lokacin da mage take wuri ɓera ba ya wasa ta yaya kai da kake hannun fatallu za ka shiga kiran sunana son a gano maɓoyata a zo a tafi da ni to wallahi ta Allah ba taka ba, dan wallahi sai dai a yi abin da za a yi wai mahaukaci ya ɗau rigar kura dan wallahi wanda za shi sama ya taka leda haƙiƙa ya ci ƙarfin tafiya kuma nan gani nan bari farar tumfafiya" Cewar Gwaggo Ramma tana ciko hannunta taf da dawar cikin duron da take ciki ta tura a bakinta, ta ƙara cunkusowa ta ƙara cusawa a bakin wai duk dan gudun kar ma ta yi suɓutar baki ta yi magana a jiyo ta. Ko kuma Mai Gari ya yi abin da za ta tausaya masa kar ta yi magana.


"Ramma" Ta ƙara tsinkayar muryarsa tamkar dai ba a tsakiyar dare yake kiran ba.


"Ka yi haƙuri Mai Gari tun da dai sa'i ya yi to sai dai mu ce Allah rahama maka, ya kai haske kabarinka, kuma mundahanar da ka sha yi da kayan jama'a talakawanka sai dai in ce Allah yafe maka" Ta faɗa a ranta lokacin da ta ji dawar bakinta wata har tana wuce mata maƙogwaro amma dan ƙarfin hali haka ta cigaba da daurewa dan a kan ta fito fatallu ta yi watanda da namanta ko ta kashe ta ma lokaci guda gwara ta cigaba da zama a cikin dawar. Dan da ta ji ma kiran Mai Garin yana ƙara kaɗa mata hanjin cikinta sai ta cusa fuskarta a cikin dawar ya zamana numfashi ma dakyar take shaƙa.




Mai Gari kuwa jin Gwaggo bata amsa ba sai ya ƙara mayar da akalar kiran kwacakwam ga Salele.


Salele da yake ta faman yin sujada a kan katifarsa har lokacin bai dakata ba, dan yanzu ko shi kansa bai san iya adadin sujadar da ya yi ba, jin muryar kankansa Mai Gari yana kiran sunnansa a take ya kasa dungura goshin nasa.


"Wallahi kai dai mutumin nan an yi ɗan nema wallahi, haka kawai dan son ka ɓallo mini ruwa za kake kirana kuna can cikin halin ƙaƙanika yi, ai tun da dai ku kaɗai fatallun ta gani sai ku haƙura ku tafi lahirar ku kaɗai" Ya faɗa yana fara lallaɓawa ya je can inda yake ajiye takalman ball ɗinsa yana zuwa ya miƙa hannu ya ja mazugin takalmin ya zugi tamkar zai saka takalmin a ƙafarsa amma abin mamaki sai ya durƙusa ya saka fuskarsa a kan takalmin yana ƙoƙarin saka kansa a cikin takalmi.


"Dan Allah kaina ka mini rai ka shige

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login