Showing 1 words to 3000 words out of 32103 words
Chapter 1 - Sanadin Boko Book 1 Complete Document by Halima I Mashi .txt
Sanadin Boko 1 01
Posted by Mukhtar Ismail Muhammad
On
www.arewarulers.com.ng
Under: SANADIN BOKO
Na
Maryam Abdullah K.Mashi
Ina sauraren duk hirar da kowaccen su ke yi, motar ta
kacame da surutu. Wasu na murnar ganin Iyayensu, wasu
kuma suna zancen auren su. Mafi yawa daga ciki kuma
suna fadin makarantun da za su ci gaba, wasu su ce
poly wasu Jami'a, wasu Nursing school.
Sa'adatu da ke kusa da ni ta ce, "Hafsy don Allah kema
ki shigo (A.B.U Zariya) mu hadu mana." Nayi dan
murmushin takaici.
"Samun (A.B.U) fa ba kamar shiga Bakori ba ne, saboda
in ma zan samun bani da wani tabbas akan za a barni."
Ta zaro ido. "Kada kice min kina cikin wadanda za'a
dakile a kai gidan miji?
Na sake ajiyar zuciya.
"Ke dai Sa'a taya ni da addu'a, Allah Yasa ina da rabo,
dan kuwa ina son in ga karshen boko." Jamila ta dube ni,
"Hafsy ko yaushe kina bani mamaki in kina cewa za ki
ga karshen boko. To bari kiji, sai dai boko yaga karshen
ki. Ance miki wannan lokacin yana jira ne?
Na ce, "To Malama, ban saka bakin ki ba, ina ruwanki. Ke
ba kince aure ba?" Jamila ta ce, "Aure kuwa insha Allahu
ba ya hana karatu, zan yi aurena na ci gaba da karatuna.
Sa'a ta ce, "Wahala ai daya za ki zaba, don da kin yi ciki
za ki watsar da batun karatu. Na ce, "Dubu nawa akayi?
Ai ni boko yanzu muka sa dan ba."
Ta ce, "Shikenan, Allah Ya taimaki kowa kan niyyarshi ta
aikhairi". Na ce, "Ga magana da za ki yi kawai, Amin".
Da tafiya tayi tafiya, sai ka ji kowa shiru. Ni kam
fargabar Babana nake yi, nasan inba wani ikon Allah ba,
da wuya naje wata Makarantar.
An sauke *yan zariya, sannan mu *yan Kaduna muka
nausa hanya, motar makaranta da ke Bakori Katsina, ita
ce ta debo mu zuwa gidajenmu, bayan mun yi bankwana
da makarantar wato mun kammala.
Gidanmu ya kaure da sowa, yara na ta murna "Ga Hafsat
ga Hafsat". Innarmu ta fito da gudu ta rungume ni, ina ta
dariya. Almajiran da suka dauko min kaya suka sauke, na
ce, "Innarmu ba su hamsin". Ta kwance habar zani ta
mika musu.
Yaran gida suka taya ni da kaya zuwa cikin daki, matan
gidanmu kowa sai sannu da zuwa suke min ina amsawa.
Inna ta aje min kwano tare da cewa, "Alalar har ta
huce". Ta dire min kofin ruwa na ce, "Har yanzu bata
kare ba ne?" Ta ce, "Ta kare mana, ai tun kwanaki da
Kawunku Bako yazo ya ce min cikin kwanakin nan za ku
kammala, kullum sai na aje alalar sai dai in naga
magariba tayi ne sannan in ba yara.
Nayi dariya tare da cewa, "Innarmu kenan! Ina Yaya
Ummar?" Ta ce, "Tun safe bai dawo ba, kin san nasai
mashin da aka yi mana rabon gadon nan, Kawun ku Bako
na kawo min kudin na ce a sai mishi mashin wannan
yaran, tunda zaman banza yake, aikin gyaran wutar nan
ba ko yaushe ake samu ba. Ina fama da kannan shi ina
fama da shi.
Na ce, "Kinyi dabara Innarmu, in yayi Achabar sai a rufa
asiri". Ta ce "Kwarai kuwa. Ummi ta zo ta zauna kusa da
ni, na ce "Ummi da ba ina ta kiranki kin ki zuwa ba? Inna
ta ce, "Kullum sai ta ce Innarmu ina Auntyna?"
Na rungumota a jikina ina cewa, "Gani na dawo". Ta rufe
fuskarta, ita dole taji kunya.
Cin alalata nake ina jin dadi ga ni ga Innata, ta ce "Kin
zo a daidai bikin su Hajara da Sakina ya kusa". Na rike
baki, "Inna har da Sakina?"
Ta ce, "Eh! Na ce, "Uhm! Ni da so samu ne in ci gaba da
karatuna ma". Innarmu ta ce, "Malam ne matsala, amma
ko Nas din nan da 'ya'yan Kawunki suke yi ai zan so
kiyi." Na ce, "Wane Nurse? Ni fa Jami'a nake so, burina
in zama 'yar Media".
Ta ce, "Me kenan? Na kafa kofin ruwa na daddaka,
sannan na ajiye tare da cewa, " 'yar jarida mana! Sai dai
matsalar kudi ne". Kai lomar alala da nayi baki, ta zo
daidai da sallamar Baba, nan take naji wani daci tamkar
na tauna madaci. Innarmu ta mishi sannu da shigowa,
tare da shimfida mishi tabarma.
Cikin fargaba na soma gaida shi, ga mamakina yau
fuskar shi sake ya amsa, har da ce min "An dawo lafiya?"
Na ce, "Lafiya lau". Innarmu ta ce, "Allah cikin ikonSa
Malam yau dai su Hafsat karatun Sakandire ya
kammala."
Ya ce, "To dama tunda da mai sonta sai ta yi masa
magana ya fito in hada su da Sakina in huta". Inna ta ce,
"Anya kuwa? Ina ga daurewa da zaka sake yi ta tafi
makarantar gaba da..."
Wani kallo da ya mata shi ne ya dakatar da ita. Ya mike
tsaye ransa a bace.
"Na gaji da wasa da hankalina da ku ke yi, ba zan iya
ganin Hafsa gandandan cikin gidan nan ba, duk wanda ya
shigo ba zai bambance ta da matan gida ba, duk wata
tana zubar da jini, ta zama Uwar mata. Wannan karon
zamu yi tsiya da ku yanda bakwa zato. Wai menene cikin
wannan bokon da ku ka nace mawa? Ina ce karatun
gidan duniya ne?"
Inna ta kufulo itama, ta ce, "To dama ka saba ka min
tijara cikin gida gaban kowa akan Hafsa, tun da babu
sisinka kasa ido, kuma karatu ba fashi. Ya ce, "To zan ga
wanda ke auren wani, tsakanin ni da ke". Ya fita.
Na dago ido da hawaye, takaicina ace kullum Iyayena
basa rigima sai a kaina, bari Munnir yazo anjima, zan ce
masa kawai ya turo manyansa ayi magana, ko ina dakin
nasa zanyi karatuna. Ban dai fadi ma Innarmu kudurina
ba.
Na mike ina tattara kwanukan gabana, Inna kuma sai
mita take, na ce "Innarmu ki bar batun haka, kinsan
gidan nan da gulma, yanzu kowa ya baza kunnuwa yana
sauraro". Ta ce, "Suyi ta sauraro din, ina ruwana. Iyaka
dai mace tayi da ni naji mu kwashi 'yan kallo ni da ita".
Na idar da sallar isha'i, ina zaune a gurin ina istigfari,
wani yaron gidanmu yayi sallama, bai jira amsa ba ya ce
"Innarsu Ummi wai ana kiran Hafsa a waje". Ta ce, "To".
Na mike, nasan Munnir ne, don na aika masa da letter
cewa na dawo.
Na bude jakata na ciro turarena forever na fesa, sannan
na sabi gyalena na fita. Tun kafin na karaso na jiyo
kamshin turarensa.
Yana zaune saman motarsa kirar (Toyota camry), baka
wuluk, sanye yake da wando jean baki, rigarsa fara. Cikin
farin ciki na isa gabansa, nayi masa sallama ya dago da
kanshi daga wayar da ke hannunsa yana latsawa.
"Babyna". Sunan da yake kirana kenan. Na ce, Na'am".
Ya diro "Zo muje cikin mota." Na ce, "A'a mu zauna
can". Na nuna mishi dakalin kofar gidanmu.
Ya dan gyara tsaiwa, "Kin ce fa baki son Baba ya dinga
ganina da kananan kaya, kin san dai in muna can zai
ganni dole ko?"
Na dan yi jim ina nazari. Hakika Baba na fada cewa
Munnir ba dan mutunci ba ne, ya gane haka ne tun daga
suturar da yake sakawa.
Amma bana son shiga motarsa saboda ya cika son taba
jikina.. Ya katsemin tunani da cewa.
"Zo muje, na zo da muhimmiyar magana". Na ce masa,
"Nima ina da nawa muhimmin zancen". Baya ya bude ya
shiga, nima na shiga dayan gefen, sai dai ban rufe ba. Ya
ce "Rufo kofar mana". Na ce, "Ka barshi haka ma ya yi.
Ya kunna wutar motar, haske ya bayyana, ni da shi muka
kalli juna cikin ido. Nayi saurin janye nawa idanun, domin
wani abu da na ji yana bin jijiyoyin jikina.
Ya ce, "Ina sonki Hafsy, ban san irin son da nake miki
ba." Ya kama hannuna na kwace, tare da mai da su baya
na ce, "Don Allah Munnir ka daina son taba jikina,
haramunne fa". Ya ce, "Zamu fara ko? Haba Hafsy, ni ne
fa zan aure ki. Ko yaushe ina son in gwada miki so sai ki
yi ta ki, yaya ki ke yi tamkar wacce bata je makaranta
ba? Sai ka ce ba *yar boko ba? Ni fa kullum ina fada miki
ba zan auri mata muje kina min wani kunshe-kunshen jiki
ba.
Na bata rai, ya shafi kumatuna.
"Small beby, dan yi murmushi. Ba kya yin kyau in kin
daure fuska". Shikenan, ban san lokacin da murmushin
ya subuce min ba, matsalar ina mutuwar son Munnir. Ya
ce, "To fada min maganar kafin kiji tawa, don tawa in
kinji saikin bani goron albishir.
Na ce, "To ni dai dama ina son ne in ce maka ya dace
yanzun muyi aure, don wallahi da kyar Baba ya bari na
gama karatun nan. Sam shi ba ruwan shi da da boko, ka
dai sani". Ya ce, "Haba Baby, aure fa ki ka ce? Kin
manta alkawarin da muka yi ni da ke?"
Na ce, "Ban manta ba". Ya ce, "To ki kyale fadan Baba
kawai, ba nine ke biyan komai na karatunki ba? Come on
aje wannan topic din. Na shirya miki gagarumin party ne
saboda murnar gama karatunki, don haka yaushe zamu je
kasuwa musai kayan sawa?
Takaici ya cika ni, don haka ban tanka ba. Ya sake
matsowa in banyi magana ba nasan zai iya cewa zai
rungume ni. Da sauri na ce, "Duk lokacin da ka shirya".
Ya ce, "Gobe yayi? Dan ranar sati ne party din."
Na ce, "Um". Ya ce, "Wai ba ki murna ne angel dina?
Kada ki damu, kwanan nan za ki zana (JAMB), sai kin
zama *yar media insha Allah.
Na dube shi, "Yanzu sai zuwa yaushe zamu yi aure?" Ya
ce, "Mun kusa, ai shekara hudu ya rage min na hada
master dina, before time din kin zama *yar media ko?
Nayi shiru. Ya sake matsowa har muna jin numfashin
juna, bakinshi daidai kunnena ya ce, "Kin san ina son
aure nima tuntuni damuwa daya Dad dinmu shi ne yaki.
Yayyena guda uku suna nan harda mace, kin sani dai ya
ce duk sai sunyi master sun fara aiki balle ni.
Na ce, "To sai yanda Innarmu ta ce". Ya ce, "Bana jin
Inna, zata yarda". Ya sake yin kasa da murya "In dan yi
kissing din kunnenki?" Naja baya tare da cwa, "A'a". Ya
ce, "To bari na tafi". Yana magana yana kallon agogon
hannunshi, "Zan kalli wasan Arsenal yau." Na ce, "Kai
kam har yanzu kana nan da kallon kwallon nan."
Ya ce, "Kema za ki koya in kinzo gidanmu". Nayi dan
murmushi. Ina son Munnir, shi yasa zan jure na jira shi,
amma Allah Ya sani ina son aure, don ina zaton ina cikin
mata masu bukata.... Ya katse tunanina da cewa, "Ko
kada in tafi ne?" na ce, "A'a kaje sai gobe". Ya ce,
"Shikenan." Ya miko min wata farar leda.
""Gashi kisha, ice cream ne da fresh milk." Na ce na
gode, amma don Allah ka daina yimin irin wannan
dawainiyar.
Innarmu ta dubi ledar bayan na ciro kayan ciki, ashe har
da kayan tea. Ta ce, "Kai yaron nan baya gajiya da
dawainiya. Ni da zai fito ayi auren nan tunda yana zon
karatun kyayi can a dakin shi.
"Inna nayi mishi wannan zancen ya ce min in kara
hakuri." Kamar na fadawa Inna zancen party din gobe,
sai na fasa don nayi imani ba zata barni ba, duk da tana
son abinda nike so.
Yau Baba dakinmu yake, don haka dakin Babah kishiyar
Innarmu zamu kwana. Ina kwance kan yaloluwar katifata
mu da Sakina, can kasa sauran kannena da aka musu
shimfida. Ko wannan cakudin na daga cikin abin da yasa
nake son in ganni a dakin kaina.
Washe gari tun safe muka soma aikin alalar siyarwa da
Innarmu ke yi. Misalin uku saura Nazifi ya shigo yana
cewa, "Hafsa ga saurayinki a waje. Ko da bai ce na kira
ki ba, nasan gurin ki ya zo.
Dama tuni nayi wankana, ina sanye da riga da siket na
atamfar (Java), gyale na sura na ce "Inna Munnir na
kirana."
Ta ce, "To." Na nufi waje kai tsaye.
Yana sanye da kananan kaya kamar ko yaushe, ina isa
ya budemin gaban motar na shiga, sannan shima ya
shigo. Na gaida shi ya amsa tare da yiwa motar key, na
ce, "Muyi sauri ban ce zamu fita ba." Ya ce, "To".
Wani (Boutique) muka je, duk tsinannun kaya ne a
gurin, shi dai ya zabi nashi, amma ni nace ban ga
wanda ya yi min ba. Nan ya shiga jidar min, na bata rai
tare da nuna mishi sunyi yawa. Ya ce, "To zabi wanda
ki ke so."
Na daga duka babu na arziki, siraran wanduna ne da
*yan riguna, sai doguwar riga wadda in nasa da kyar
zata wuce gwiwata. Na aje su gefe, na dube shi.
"Duk ba su yi min ba". Ya bata rai sosai, "Tashi muje".
Na kafa mishi ido. Ya ce, "Tashi mana". Cikin daga
sauti na ce, "To, to naji zan amsa, amma ni na gane
kamar zasu yimin kadan." Ya dan sassauto "Muje
gidanmu ki gwada." Da sauri nace, "A'a zasu yi min."
Yayi murmushi, sannan muka je ya biya muka shiga
motarshi. Ya ce, "Muje mu dan sha Ice cream". Na ce,
"A'a kai ni gida, Innarmu bata san na fita ba, kuma
nasan zata sa a leka ni, fada kuma zata yi min". Ya ce,
"To naji sarkin tsoro, ke dai kawai kina tsoro ne kada
na cinye ki."
Gabana yayi muguwar faduwa ganin Baba zaune a
dakalin kofar gidanmu, na ce na shiga uku, ga Babana,
ya ce "To menene? Ina jin mamakin ki wallahi. Shi
yasa Dad din mu yake matukar burge ni, baya takura
mana, shi dai in dai zamuyi karatun boko to duk abin da
muka ga dama muyi. Kuma zai kashe mana the last
kudin shi don muyi karatu.
Na ce, "Uhm, don Allah ka tafi da kayan, na karba,
amma ka fito ku gaisa.
Tare muka fito daga motar, jikina har bari yake. Na nufi
cikin gida, Munnir yayi gurinshi. Ina isa Inna ta ce,
"Daga ina ki ke Malam ya shigo yana ta fada yaga
lokacin da ki ka shiga mota? Na ce, "Um asibiti muka je
dubo kanwarshi". Ta ce, "Shi ne ba za ki fada ba? Kin
san fadan Malam, don Allah ki rufamin asiri kada ki ja
min surutu sanadin bokon nan."
Na ce, "Kiyi hakuri Inna." Ina rufe baki Babanmu yana
shigowa, tun kafin ya karaso na jiyo muryarshi yana
cewa.
"Na fada maka kenan, in da gaske ka ke yi ka turo min
manyanka. Shekara nawa ina ganinka a kofar gidan nan
wai ku *yan boko, zaku ce min sai kun gama boko, to
ban laminci wannan ba."
Hanyar uwar daka nayi, don nasan yanzun ya make ni,
ya ce "Ke *yar boko kinbi saurayi kasuwa ko? Inna ta
ce, "A'a Malam asibiti fa suka je." Ya zaburo tamkar
zai kai ma Inna duka, ya ce, "In ji wa? Wa ya fada
miki?"
Inna ta ce, "Ga ta nan." Ya ce, "Makaryaciya, to shi
abokin yawon nata ya ce min daga kasuwa suke, duk
ya rasa wanda zai ce ya raka shi kasuwa sai ke?" Inna
ta tsare ni da ido, "Kasuwa Hafsa?" Nace, "Kuyi hakuri,
ba zan kara zuwa ba." Tayi kwafa tare da ci gaba da
yin aikinta. Baba ya ce "To wallahi ba zan yarda da
gantali ba, wai ku *yan boko."
Inna ta dube ni, "Ai gara ki saka min da haka. Tunda ni
na jajirce ki samu karatun boko." Na ce, "Don Allah
Innarmu kiyi hakuri, wallahi ba zan sake ba". Ta ce, "To
me yasa ki ka min karya? Kin san dai na tsani a min
karya, duk abin da ya faru nafi son gaskiya ko?" Na ce,
"Na sani.
Haka nayi ta bata hakuri, kun san Uwa, nan da nan ta
sauka. Ta min fadan cewa kada na sake yarda na bi
saurayi wani guri.
Kwana daya, biyu ban ji daga Munnir ba, lallai Babane
ya kore shi letter na rubuta na ba Nasirun gidanmu na
ce ya kai masa. Tambayarshi nayi ko lafiya? Na jishi
shiru. A bayan takardar ya rubuto cewa Babana ya kore
shi, don haka shi ya hakura da ni. Na girgiza da jin
wannan zancen, don ina son shi kullum burina na aure
shi. Shi kadai nake jin sha'awa. Na rasa yanda zan yi
ko satar jiki zan yi na je gidan su? Innarmu ta gane ina
cikin damuwa, ta ce "Hafsat ba ki jin dadi ne? Na ce,
"Ciwon kai ne yake damuna." Ta bayar da Naira goma
a amsomin panadol."
Da dare nace Innarmu zan je gidansu wata yarinya *yar
makarantar mu, in amso wasu takarduna, ta ce, "Kar ki
zauna, maimakon kije tun ido na ganin ido?" Na ce, "Ai
dazun ciwon kai ke damuna." Ban yi wata kwalliya ba,
kada ta gane, sai kawai na dan fesa turare. Na zari
mayafi, gidan su Munnir da dan tafiya tsakanin mu
saboda mu muna Rigasa ne Abuja Road ta kasa, su
kuma suna Makarfi Road.
Tun daga nesa na hango shi su da wani tsaye, ga
motarshi gefe, ina zaton fita zasu yi. Sai na kara sauri.
Daidai ya bude motar zai shiga na ce, "Munnir" Ya juyo
da sauri, ya mai da motar ya rufe. Abokin nasa yana
ciki, ya ce, "Beby lafiya?" Na jingina da motar, sannan
na sauke ajiyar zuciya, domin na gaji. Sai dai kuma
lokacin ne naga rashin hankalina.
Yanzun ince mishi me? Na zo in bashi hakuri ko nazo
biko? Ya sake cewa, "Me ya faru Baby? Na ce, "Ai ba
ka ma sani ba?" Dabara tazo min, na ce "Dama nazo ne
na maka godiya akan dawainiyar da kayi da ni, don ko
zamu rabu bai dace mu rabu ba zumunci ba."
Ya ce, "Baby kenan, don na fada kina ganin zan iya
rabuwa daKe? Ni ina sonki, Babanku ne ya tozarta ni"
Kafin nayi magana ya ce, "Ina zuwa." Ya leka motar
yayi magana, sannan ya ce, "Zo muje ciki kiji." Na ce,
"A'a. Ya bata rai, "Bana son yawan gaddamar nan, ki
daina kada muyi aure mu zo muna samun matsala.
Na ce, "Ina jin kunya ne, saboda Mamanku, Ya ce, "Ba
za ta san kin shigo ba, zo muje. Na bishi, ya tura Gate
din gidan, muka shiga.
Yau ne na soma shiga gidansu, ginin zamani ne ga
haske tamkar rana, me gadinsu ya ce, "A'a, ka fasa fita
dinne? Ya ce, "A'a Baba, yanzun zan fita.
Na gaida maigadin muka tafi ginin farko daga cikin
gine-gine ukun da ke harabar gidan, ya ce, "Yau kin zo
gidan mu, ba don kunya ba da na kira miki kannena su
Nana.
Na ce, "Barsu yanzun zan tafi, kuma bai dace su ganni
cikin wannan yanayi ba, ina nufin shigar da nayi. Ya ce,
"Shikenan.
Katon falo ne, yana dauke da kayan more rayuwa, sai
kofofi guda uku, yace in zauna kan kujera, na zauna.
Ina kallon ko ina, ya nufi kofa daya daga cikin kofofin,
jim kadan ya fito dauke da gwangwanin maltina da kofi
ya zauna hannun kujerar da nike
Mukhtar Ismail Muhammad
WhatsApp: 08161892123
Sanadin Boko 1 02
Posted by Mukhtar Ismail Muhammad
On
www.arewarulers.com.ng
Under: SANADIN BOKO
Na
Maryam Abdullahi K/Mashi
Katon falo ne, yana dauke da kayan more rayuwa, sai
kofofi guda uku, yace in zauna kan kujera, na zauna. Ina
kallon ko ina, ya nufi kofa daya daga cikin kofofin, jim
kadan ya fito dauke da gwangwanin maltina da kofi ya
zauna hannun kujerar da nike.
Ya balle hancin gwangwanin ya cika dan kofin ya mika
min, na girgiza kai tare da cewa, "Na gode. Ya ce, "Wasa
ki ke yarinya, rike nan ko na dura miki.
Da sauri na amsa saboda nasan halin shi sarai, zai iya.
Kurbata biyu na aje, ya kama hannuna na kwace tare da
mikewa.
"Tunda ka huce ni zan tafi. Ya ce, "Dama ni banyi fushi
ba. Na kalli fuskarshi muka hada ido, ya kashemin
idonshi daya, nayi saurin