Showing 18001 words to 21000 words out of 32103 words

Chapter 7 - Sanadin Boko Book 1 Complete Document by Halima I Mashi .txt

dube ni,
Hafsatu kin ganni nan da kama aikina yau shekara goma
sha biyu kenan,amma babu miji. Har Malamai na shiga
don kawai in samu miji. Daga wanda zai ce Aljani ya
aure ni, sai wanda zai ce asiri aka mini,suka yi ta cin
kudina suna min karya, daga karshe naga babu wani ci
gaba na watsar da su. Yanzu na rumgumi kaddarar da
nawa kaina, mahaifina ya rasu shekaru hudu da suka
wuce abin da yasa nabar gida katsina na dawo nayi
asibitin kaina shine, kannena yaran amaryar babanmu
duk sun raina ni gashi ba mu cika shiri da hajiyata ba.
Shiyasa da aka raba muna gado na yo nan na gina asibiti
da gidana, sai dai ina zuwa gida kan lokaci in duba su
hajiya ta. Share hawayenta nima sharar kwalla na ke
tayi, dan murmushi me kika fahimta ko nace wane darasi
kika samu cikin labari na? Nace na farko ba kyau
wulakanci, sannan mu daina sanya boko ya zama gaba
da aure kamar yanda nima nayi. Tace hafsatu naki mai
saukine dan ke kin kama saurayi shi ne dai wanda kika
kaman ya cuce ki. Amma ni abinda nayi saboda boko! Ta
jin jina kai sanna tace ko rabi ban fada maki ba kuma
halin da nake ciki yanzun nima na kirashi SANADIN BOKI,
nace auty haryanzu baki wuce aure ba. Tace to in ban
wuce ba hafsat ina mijin? Kwata kwata na daina burge
maza, sam ba sa jin sha‘awa ta sai yan yara wanda da
nayi aure kan ka ida na rantse miki hafsa da yanzu inada
kamarki koma wanda yafiki don haka sha warata dake ki
daure ki haifa dan cikinki baki saniba ko shi kenan
kwanki a duniya. Sannan kiyi aure tun da kuruciya, aure
ba zai hanaki boko ba kamar yanda mahaifinki yace.
Magana daya zan fada maki, kada ki sake yarda saurayi
ya taimaka miki game da komai na kudi, zai iya anfani
da hakan ya cutar da ke, duk da nasan akwai masuyi don
Allah. Asabe da ke gefe cikin tagumi sai yanzu ta tsoma
baki, anty wallahi ban taba zaton kina da matsala ba, duk
kalon da nake maki mijinki da yaranki suna kasar waje.
Maganarta sai ta dan bamu dariya. Har likitar ta barmu
ta koma dakin ta ban daina mamakin lbr ta ba, duk
kyanta duk kudinsu duk bokonta ta kasa samun miji lalle
kuwa boko yaja mata. Wata zuciyar ta ce min ba boko
bane wulakancinta ne ya jamata, koma mene yanzu na
fiskanci aure yana sama da komai. Washe gari gida na
shirya wucewa kaduna, sai dai kudin mota bani dashi
amma ba zan iya fada mata ba. Dan haka nayi shuru dari
biyar ta bani wai nasha ruwa a hanya. Makaranta na
koma na canja kaya na dauki kwalin wayata na nufi
kasuwar masu waya ni dai ban tsaya ciniki ba, dan ba a
cikin nutsuwa nake ba, yace dubu 6 inji mai siyan
wayanr, bani kudin kawai nace don na kosa insami munir
inji yadda zamuyi. Kai tsaye gidansu na dosa ko
unguwarmu ban sauka ba, koda mai gadinsu yace min
sun fita da maman shi sai nasami can gefen gidan na
zauna. Ko shekara zasuyi sun dawo su same ni, na fada
cikin raina. Kusan awa 3 sanan motarsu ta dawo tayi
hon, mai gadinsu ya bude ban bata lokaci ba na mike na
rufa musu baya. Daga inda nake tsaye ina hango
kannanshi mata suna sanye da gajerun wanduna, kai ba
dan kwali suna ta shiga da kaya. Dayarce ta hangoni sai
naji tace mom ga wata can ko mai aiki ce? Matar ta
waiwayo, kamanninta sak da munir haka ma kannanshi.
Ta nufoni lafiya? Warin munir yayana ya aikoni, tace wai
me? Nace abokinsa ne zan amsar masa sako ne, sunyi
magana da munir din. Tace ok ta nufi ciki tana kwala
mashi kira. Yafito daga cikin gida yana cewa yes mom....
ganina yasa shi yin wani turus! Tace gawata can wai
yayanta ya aiko ta." Da sauri ya ce, "Oh na gane sako
zan bata." Ya iso gurina fuska daure, "Lafiya Hafsatu
kika biyo ni gidanmu?" Na ce, "To ciki fa bai fita ba." Da
sauri ya dora yatsanshi a lebe tare da cewa, shishsh. Ya
nufi gefensu gami da cew Zo. Muna shiga ya ce, "Kina
nufin cikin bai fita ba?" Na ce, "Wallahi." Ya ce, "To ki
koma gida zan zo anjima da dare in kaiki wani asibitin a
fitar da shi, wannan bata san aikinta ba." Na ce, "A
gaskiya ba zanje a kasheni ba, don Likitar tayi duk wani
kokari don ganin ya fita amma abin ya ci tura. Ta kuma
fada min in na matsa cewa sai an cire to zan iya rasa
raina. In je in cema Ubangiji na me?" Ya ja tsaki, "To me
kike nufi?" Na ce, "Shine na zo mu san abin yi." Ya ce,
"To me kike ganin za'a yi?" Sanyi na ji cikin raina, Allah
ya sa ya yarda na ce, "Ina ga mu hakura in zauna can
gidan Likitar, ko Inna ba zan fadawa ba in na haihu sai
muyi aure." Ga mamakina sai na ga yana dariya, a zato
na zancen ya masa dadi, kuma shawara ta ta shige shi.
Amma sai naji ya katse tunani na da cewa, "Amma ban
taba sanin baki da hankali ba sai yau. Kina zaton ko aure
na yi yanzun nan da shekara goma zan haihu?" Ya girgiza
kai, "Ba zan haihu ba, saboda haka dole ne a cire
wannan cikin, in kuma kin dage to kije can ki nemi Uban
danki." Da sauri na dube shi, "Munnir ka san me kake
fada?" Ya ce, "Eh, ina da ja kan wannan cikin, cewa nawa
ne. Daga sau 1 shima ba cikin kwanciyar hankali ba
amma shine ciki zai shiga?" Bakin ciki ya hana ni
magana, idanu kawai na tsura mishi, shima ni yake kallo
cikin harara gami da daure fuska. Na ce, "Allah ya sani
ni ba mazinaciya ba ce,,,,,,,,," Kuka ya kwace min, "Kai ne
ka soma keta min mutuncina, ka raba ni da 'yan matanci
na, yanzun kuma ka bini da sharri. Allah ya isa tsakani
na da kai." Ya matso kusa da ni, "Zan mare ki in kika
zage ni, banza butulu. Duk taimakon da nayi miki da
kokarin da nayi miki amma kin kasa gode min,
shashasha, Kin zata zan kashe miki kudi a banza ne
tsawon shekaru? Ki sani in kin ga kare yana shinshina
takalmi to dauka zai yi, ni ba ajinki bane don ki sani."
Kuka mai karfi ya kwace min, "Allah ya isa Munnir, dama
yaudarata kake yi kace zaka aureni?" Ya yi 'yar dariyar
mugunta, "Kin dai yaudari kanki, to ai ni ne ma zanyi
Allah ya isa tsawon shekara 3 zuwa 4 ina miki bauta ke
da me kika taba saka min?" Ban san lokacin da nayi
kukan kura na shako wuyanshi ba ina kuka ina cewa,
"Allah ya isa." Shi kanshi yayi mamakin yadda ya so
kwacewa daga jikinshi ya kasa.Muryar Mom dinsu muka
ji tana cewa, "Lafiya? Ke, ke sake shi mana me ya faru?"
Na kasa magana sai wani irin kuka nake yi ina fadin, "Ya
cuce ni." Ta dubi Munnir, "Me kayi mata?" Ya ce, "Ban fa
ko sanya ba daga aiko ta gurina ta shakeni wai na mata
ciki." Wani kallo Mahaifiyarsa ta watso min sannan ta
nuna ni da yatsa gami da cewa, "Ke! Shiga taitayinki, tafi
can ki nemi wanda ya miki ciki." Cikin tsananin kuka na
ce, "Wallahi shine ya min fyade. Kuma da shi muka je
asibiti Likita ya ce ina da ciki." "Ke!" Ta kara daka min
tsawa, "Fita a nan." Na ce, "Nifa ba inda zani sai dai ya
san yanda zayayi da ni......." Saukar mari na ji, sannan ta
ce, "Fita ko in kirama Iyayenki 'yan sanda." Ta fita da
sauri tana kiran Baba megadi, ya iso ta nuna mishi ni,
"Baba fita da wannan bana son in kuma jin ko labarin an
ganta a layin nan, in haka ta faru har da kai zan
hukunta." Ya dubeni ya cem "Mu je." Na tsaya ya ce,
"Shige mu je mana ina magana kina kallona." Na dago
jajayen idanuna na kalli Munnir, wani murmushi ya saki
na mugunta sannan na ce, "Akwai Allah." Na fita
megadin yana biye da ni sai da muka fito ya ce, "Yarinya
kin yi kuskure, koda ban san abinda ya faru ba, amma na
san yana da nasaba da abinda yayi ta faruwa da wasu
'yan mata a gidan nan." Na dube shi, "Baba me ya faru
da wasu 'yan matan?" Ya ce, "Samarin gidan nan da
abokansu suna kawo 'yan mata ta hanyar yaudararsu da
kudi, su yi lalata da su." Na dube shi bayan mun fito
wajen gidan, "Baba ni nawa salon yaudarar ya bambanta
da na saura


Zaharaddeen Shomar
whatsapp. 08168575100




Sanadin Boko 1-6
Posted by ANaM Dorayi on 12:26 PM, 12-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
." Kuka ya sake sarkeni, na ci gaba da cewa, "Shekara 3
da doriya yana min dawainiya da sunan zai aureni, kuma
Wallahi Baba fyade ya min." Megadi ya ce, "Kuskurenki
shine zuwan da kika yi gidan nan, ki kiyaye zuwa gidan
samari ko dakin samari. Yanzun kije ki yi hakuri, in ba
haka ba zaki jawa Iyayenki matsala. Kin san masu kudin
nan ba duka bane suke da tsoron Allah, 'ya'yansu su ne
'ya'ya na wasu tamkar dabba suka dauke su. Shi Munnir
sau nawa yana samuna yana rokona shi da abokansa wai
in kai musu kudin gaisuwa gidajen 'yan matansu a
matsayin nine Ubansu." Na ce, "Baba ka je?" Ya ce, "A'a
ni nasiha na musu dan nima inada yara da jikoki. Tunda
haka samarin yanzu suke yi, su kai kudin gaisuwa don su
bata yarinya. In ta'ki su ce aurenta zasu yi. Na san koda
ban kai musu ba sun je sun samu wani, kuma ya kai
musu, kila ma sun cimma burinsu, don haka ki je kiyi
hakuri ki kuma kiyaye gaba." Na ce, "Na gode." Ko da
wasa ba zan ce maigadin nan ina da ciki ba.
Tahowa na yi ina mamakin kalaman Munnir, wai ya
taimakeni ne don bukatarshi, dama haka halin maza ya
ke? Dama Munnir mayaudarin 'yan mata ne? Tafiya nake
amma sam ban dauki hanyar gida ba ko cikin mafarki ai
ba zanje gida ba. Zuciyata ta bushe na share hawaye na
na nufi Babban titi. Kwatsam! Sai ga Yayana Umar ya
sauke wani a mashin, cak na tsaya don mun riga mun
hada ido. Cikin mamaki ya ce, "Hafsa daga ina haka?"
Gabana ya fadi matuka, amma sai na kanne banda wata
damuwa na ce, "Na zo ne yau ko gidama ban karasa ba,
gidan su wata na zo." Ya ce, "Wacce watan?" Na 'kirkiro
'yar dariya, "Yar ajinmu ce ta yo mana gaba da kaya to
na zo kuma bata karaso ba." A take karyar tazo min, ya
ce, "Hau na kaiki gida." Muna cikin tafiya ina tunanin ban
so na hadu da Yaya Umar ba, sai ya jeho min tambaya,
"Hafsa sai na ganki duk a hargitse, fuska a kumbure
kamar kin sha kuka." Gabana ya yi mummunar faduwa
amma don kada ya ganoni na ce, "Kukan lafiya? Ka sam
zaman mota, kuma baccina na sha har na gaji." Ya ce,
"Irinku ne ake sace wa, nan da Kano kin hangame baki
kina bacci,." Na ce, "Cikin kwanakin nan ne bamu samu
bacci ba saboda karatu."
Ko Inna abinda ta soma tambaya ta shine lafiya? Cikin
dariyar da bata kai zuci ba na ce, "Lafiya Innarmu." Na
shige daki na kwanta kan gado.Jim kadan Ummi kanwata
ta shigo da kwanon alala ta ce, "Anty gashi." Na amsa
na aje. Ummi ta tsaya tana kallona, ina zaton dan wasan
da na saba yi mata ne taga ban mata ba. Inna ta shigo,
"Wai Hafsa lafiya na ganki kwatsam! Kuma kina zuwa kin
zube a gado?" Ban san yadda aka yi maganar ta zo min
ba, sai dai kawai naji ina bata amsa, "Innarmu gajiyar
mota ce, kuma dama bani da lafiya ne. Can ma muna ta
sintirin asibiti shine aka ce in zo gida in nemi na hausa."
Cikin fargaba da Tausayi ta ce, "Ashsha, me ke
damunki?" Sai kurum na ji bakina ya ce, "Shawara da
Basiri." Ta jinjina kai, "Sannu, Allah ya sauwake, jiki da
jini haka ne. Ta ce ci alalar." Ta daga murya, "Ummi!
Ummi!!" Yarinyar ta shigo da gudu. Inna ta ce, "Kira min
Baban gida in aike sh dattawa ya hadowa Hafsa
maganin basir da shawara." Ta kwance habar zaninta ta
ciro kudi naira dari 3 da ashirin ta ce, "Ungo ka hau
mota ka je layin dattawa gurin masu magungunan
gargajiya ka siyo mata maganin shawara da na basir."
Ya ce, "To." Ya amsa ya fita.
Bani da damar in ki sha domin Inna tsareni take, a
cewarta tun ina karama bana son magani. Duk lokacin da
zan sha ina sha da niyyar cewar Allah ya sa cikin nan ya
fita amma shiru, sai ma tsananin amai da ya karu gareni
da kuma kasala. Tausayin Inna yana sani kuka, in naga
irin fadi-tashin da take yi gurin neman min magani.Wata
rana ina kwance dakin Baabah amai ya sarkeni na tashi
da sauri kafin na bude kofa na soma sheka shi. Baabah
ita ce ta taimaka min na gyara jikina ta kuma kwashe
aman. Har na kwanta ta ce, "Hafsa!" Na ce, "Na'am." Na
tashi zaune, ta ce, "Zo nan." Na mike na bita can kuryar
daki ta ce, "Hafsa ki fada min tsakaninki da Allah me ke
damunku?" Gabana ya yi mummunar faduwa, zufa ta
keto min na ce, "Me,,,,,me kika gani?" Ta ce, "Hafsa na
ga wasu alamu da suke nuna kina da ciki, menene
gaskiyar hasashena?" "A'a bani da komai." Tayi-tayi da ni
in fada mata gaskiya amma na dage kan cewa bani da
komai, don haka ta kyaleni tare da cewa, "Shike nan.
Dama ke nake tunanin zaki bani hadin kai domin Innarku
ba zata fahimce ni ba na sani shi yasa na miki magana."
Na ce, "Ni fa kalau na nake." Don haka sai ta rabu da ni.
Kafin sati 2 duk 'yan gidanmu sun gane halin da ake ciki,
amma banda Innarmu sam bata lura ba bata zata ba, ba
kuma ta tsammanin haka zata faru ba, 'yan tsegumi har
cewa suke mata, "Yaya 'yar boko da jiki?" Haka ta ce,
"Da sauki." Tana washe baki ita a dole an gaishe ni.
Sannu a hankali zance ya soma fita makota sai gashi ana
shigowa dubani, niko ko yaushe ina cikin Hijabi. Baabah
Maimuna ita ce ta shigo dubani yau kawar Innarmu ce
kut da kut ta kalli Innarmu, "Kin san zancen da yake
yawo unguwar nan?" Ta ce, "A'a." "To 'yan gidanku sun
fita suna yada cewa Hafsa ciki ta yo." Inna ta mike cikin
tsananin tashin hankali, "Wane dan sharrin ne? Wallahi
zan iya maka mutum a kotu." Maimuna ta ce, "Saurara
kiji, kafin ki fita kiyi wata magana soma tuhumar ta
tukunna." Innarmu ta ce, "Haba Maimuna, sanin kanki ne
Hafsa bata da rawar kai irin na 'yan iska, sharrine kawai
za'a mata. Kin san bani da hakuril dole sai ba ni ba'asni
wanda ya mata wannan sharrin." Maimuna ta ce, "Don
Allah ki bar zancen nan." Amma Inna bata saurareta ba
ta fita tana fada, wai yaya za'a yi ta bar wannan zancen
ana kallon 'yarta a matsayin 'yar iska!
Kai tsaye sashen su Asabe ta nufa tana fadin, "To
munafukai magulmata masu zuwa lahira da kokon
dambu! Za kuce 'yata cikine da ita, to aniyarku ta biku.
Kuma Insha Allahu 'ya'yanku ne zasu yi ba tawa ba.
Kanta aka fara ciwo da za'a mata sharri?"Kuma in sha
Allahu yayanku ne zasuyi ba tawa ba kanta aka fara ciwo
za a mata shairi? Asabe tace aina kika ji? Mu nan dai ba
wanda ya san haka inna tace rufe min baki munafukai, to
nazone in muku gar gadi zan maka mutun a kotu, sai ta
fito mun da wanda ya fada mata. Ade tace maganar
gaskiya ki bin ciki yarki dan muma a makota mukaji. Inna
tace ahaf na san duk inda aka zaga aka zago kune zaku
fadi wanan maganar, kuma zaku amsa kiran alkali,gida
ya hautsine baba ya shugo yana tambayan ba asi, babah
tace a a yar rigimar yara ce ba sai kaji ba. Nufinta kada
yaji don tasan in yaji sai yabi duddugi amma jin zantukan
sun cika gidan har makota sun soma zagayowa, ya fito
dan jin ba‘asin tun bai karasaba ya soma jin muryarsu
Ade na cewa an dai fada maki kije ki tuhimi yarki, ba kizo
ki tasamu kina zagi ba. Ki dau mataki tun kafin lokaci ya
kure miki, in shairi a ka mata sai kiji dadin kaiwa kotun.
Asabe ta kara da cewa, inko kin tafi yanzun kya iya zuwa
kiji kunya. Ya iso gurin yace zo, babah ta malam na
kiranki don Allah kiyi hakuri ki bar zancen nan, wanda ya
fada ba don kansa ba. Ta nufo daki inda baba ke kiranta,
ina kuryar gado tare da fatan Allah ya dauki raina
yanzunnan. Baba ya dubeta, to in kin gama fadan kira
min yar bokon yar taki inna tace saboda Allah malam
daga ciwo sai ayi mata sharri? Ca wa fa sukayi tana da
ciki yace ai ba abin mamaki bane kira min ita. Hafsa
zonan, na fito kishirya mutafi asibiti inna tace malam
asibiti suna bada maganin basir ne? Acan makarantarsu
fa sunyi na asibitin sun gaji shinefa sukace ta taho gida
ayi na hausa. Yace to ai ba matsala bace wanan,
matsalata in tabatar da zargin da ake yi mata inna tace
ai! Malam kaima ka yarda za ta iya? Yace kwarai kuwa,
yace ita ba mutum bace? Ya ba kanshi amsa yacemutum
ce kuma baliga mai lafiya, don haka yanzu da bayanin
likita zan yarda da duk abinda zakuce. Nan take tsoro ya
kamani hankalina yafi da tashi. Inna tace je kushirya
kutafi asibitin inma har har danine sai muje. Yafita tare
da cewa ina jiranku waje. Nace inna kice masa don Allah
mu bar zuwa asibitin nan kinji? Tace a a ki shirya kindai
san halin babanki, in ba‘aje likita ya wankekiba bamu da
zaman lafiya, nace inna mudai mu hakura ba sai mu
barsu da Allah ba, masu cewa inada cikin? Tace shin
hafsat kodai kina da cikin ne?nazaro ido nace a a ni bani
da komai tace to shirya muje, garuwa ki daureye jiki
nace to a ban daki tamkar in haure yar gajeruwar
katangar mu in gudu, domin na san yau idan mukaje
asibiti asiri na yagama tonuwa. Yau auren iyayena zai
rabu na shiga 3! Nan wata zuciyar ta fada mun ba laifina
bane, in bisu inje asibitin inyaso duk yanda Allah yaga
daman zai faru dani shikenan, sai in rungimi kaddara.
Afili nace Allah ya isa munnir asibitin dutse muka je,
baba shine ya yankar min kati suka tura mu gurin da
zamu ga likitan mata. Duk da halin da nake ceki sai da
nayi Allah wadai da shugabannin da muke dasu. Asibiti
ka mar wannan ace likitoci mata basufi uku ba, ga mata
nan sun kusa 100, wata mata dake kusa dani tace min
tun asubahi suka zo nan tayi sallah. Amma har yanzu
ba‘a zo kanta ba. Ina ganin rashin kula da ba ayi da
likitocin shine dalili da yasa basu zuwa aiki. Haka muka
yini a gurin, amma baba ya dage sai munga likita. Muna
shiga ya bashi kati likita ya tambayi meke damuna?Kafin
nayi magana baba yace yata ce, munzo ne ayi mata
gwaji kotana da juna biyu. Likita yace bari yaji ta bakina,
ya tambayeni meke damuna? Nace basir da shawara,
yace yaya kikeji a jikinki? Nace amai da zazzabi. Kama
hannuna yayi ya duba, nan take ya bamu wata takarda
wai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login