Showing 6001 words to 9000 words out of 32103 words
Chapter 3 - Sanadin Boko Book 1 Complete Document by Halima I Mashi .txt
kalle ta, "To
yanzu doctor ya za'a yi tunda gaskiya ni da ita karatu
muke yi, bamu shirya taron Baby yanzun ba." Na dube
shi yana magana hankalinshi kwance kamar wanda ya
aikata abin arziki. Ta ce, "Baka shirya tarban Baby ba
mai ya kaiku aikata haka?" Ya ce, "Tsautsayi ne." Ta
ce, "A'a ku ji tsoron Allah, aure shine ya fi dacewa da
ku, karatun boko ba zai hanaku aure ba. Amma sai
kaga ana wasa da Sunnag kun zabi boko sama da raya
sunnar Manzo (S.A.W), to ku sani Manzon Tsira
(S.A.W) ya ce aure Sunnar shi ne, duk wanda ya ki
sunnarshi baya tare da shi. Kun fi yadda kuyi ZINA fiye
da aure." Ta nuna shi da biron hannunta, "Musamman
irinku 'ya'yan 'yan boko, Iyayenku sun rike wuta sai
kunyi karatu mai zurfi basu damu da halin da zaku
shiga ba kasancewarku balagaggu, burin su ku iya
turanci tare da kawo musu kyawawan sakamako
lokutan jarabawar ku. Ba su damu ku san addininku ba
bare kusan illar ZINA."munir yace to doctor, yanzu
menene mafita? Don matsala ne cikin nan don Allah a
cire shi tayi suru tana tunani. Bello yace in bazaki
iyaba muje wani asibiti doctor hindu tayi shuru tana
nazari, tace to zan tai makeku sai a lokacin naji sanyi
ya ratsa zuciya ta. Ta bani wasu kwayoyi wai kafin nan
da sati daya zai fita, suka ce nawa? Tace dubu goma
nan take suka biya. Sun saukeni makaranta sanan suka
wuce, da alkawarin zaya rinka kira yaji abinda ke tafiya.
Yau kwana tara shuru sai laulayin da nasoma gadan-
gadan, ga sheka amai nan ga zazzabi na kwasa na
koma wajen doctor hindu ana kai mata kati na tace a
turo ni duk da yarinyar da naga ta shiga bata fito ba,
itama yarinyar duk a firgice take, taci kuka ta gode
Allah nace sannu doctor. Tace yauwa ya jiki? Cikin
saurin baki nace da sauki amma fa har yanzu bai fita
ba. Ta mikye tare da diban wayoyin ta ce ku biyo ni.
Muka biyo ta cikin harabar asibitin muka nufi wani gida
kirar zamani dan madaidai ci. Ta umurce mu mu zauna
kan kujerum da ke kayatacen falon,ta shiga wani daki
daga cikin dakunan biyu dake cikin falon. Jim kadan ta
fito ta canja shigarta zuwa doguwar riga ta atanfa. Ta
shiga kicin yafito da doguwar gorar ruwa (swan) da
kofuna guda biyu. Ina takure cikin hijabi na, zazzabi ne
ya rufe ni ta tsiyaya ruwan ta miko min, sha ruwa nace
a a sanyi nake ji ta koma takawo min paracetamol na
sha. Ta zauna ta zuba mana ido, ta dubi dayar tace
asabe ko? Yarinyar tace eh, menene labarinki?
Yarinyar ta ce, Sunana Zainabu,amma an fi kirana da
Asabe.Mu 'yan asalin nan kano ne, a karamar hukumar
kunci can wani kauye ana ce masa kurje. Wata mata
mai suna Gambo tana zuwa kayaunkan garinmu tana
diban yara 'yan aiki, wata rana taxo gidanmu ta ce da
Babata su bada ni ana samun kudi sosai, wai can zan
samu kudin kayan daki. Sai na ce ni ba zani ba, nafi
son nan don ina talla kuma ina zuwa karatun allo. Sai
Babata ta ce to abar shi, don Babanmu in ya ji ba zai
yarda ba, ta ce can ma ana karatun Muhammadiyya,
kuma za su saki ga cima mai kyau za ki canza. Haka
dai ta zuga Babata hr ta yarda, sai da suka yi rigima da
Babana sannan ya yarda. Gidn Hjy Mairo aka kai ni, ba
wani aiki sosai kuma bata da tukara. Ba ta da Matsala
in kaga damuwarta to ran danta ya 6aci, don shi ne
dan ta kwallin tal. Yawancin aikin nawa duk nashi ne
don tana zuwa aiki shi ma yana zuwa makaranta,
amma ya fi ta zama gida.Ba mu cika shiri da Yasir ba,
don shi yana da fada. Watana 3,ranar wata Litinin ina
kicin, ya shigo wai in dafa masa Idomie, nan na bar
komi na shiga dafa masa, don Hjy ta ce kome nake yi
in yazo da nasa in bari in masa don a zauna lfy. Ba ta
so ta ga yana zagina, na ce to. Da na gama na nufi
dakinsa, na aje zan fita ya ce in dawo, cikin sauri na
dawo don ina matukar tsoronsa, kawai sai ya ce in cire
kayana. Na soma zare ido, ya ciro wuka da sauri na
cire ya kwantar dani ya aikata alfasha da ni, sannan ya
hana ni kuka. Ya kuma ce idan wani ya ji sai ya kashe
ni. Naja baki nayi shiru, duk uwar wuyar da na sha tun
daga nan muka daina fada, Yasir ya maida ni tamkar
matarsa. In Hjy bata nan sai ya kira ni dakinsa, akwai
lkcn ma da Hjyn taje Umra ta barmu tare da wata 'yar
uwarta don ta lura da mu, da kuma gidan,amma Yasir
cikin dare zai zo ya buga in kofa, dakinshi nake kwana.
Nan da nan nayi wani girma, kirjina ya cika. Daku abn
da ya gani zai sai min,wata rana na tashi ba lafiya,sai
amai nake shekawa,Hjy ta kira Likitansu tun kafin ya
gwada Ni ya ce yana zaton ina da ciki,ya ce amma bari
dai ya gwada. Gwajin Farko ya nuna ina da ciki, nan ta
shiga salati da sallallami, ta tsare ni wai in fada mata
wanda ya min, na ce Yasir ne.
Nan ta hau ni da duka wai na masa sharri, dan shekara
ashirin da biyar dinne yaya iya yi min ciki? Da ya dawo
ta tambaye shi da har ya musa sai yaga ta watso min
kayana, wai na tafi zan yi ma danta sharri, sai ya ce
mata shi ne,amma tsautsayi ne. Ga mamakina, bata yi
masa wani fada ba, sai dai ce masa tayi kada ya kara,
kuma Babanshi zai dawo. Ta kai ni wani asibitu aka
cire min shi ta dinga min fada wai ko ya kira ni kada
naje. A cewarta, wai bashi da laifi ni ce mai laifi. Sati
biyu ina jinya, Sannan na gyagije, ganin ta sa mana ido,
sai ya ce in dinga barin dakina a bude zai ringa zuwa.
Na ce Hjy ta ce mu daina. Ya sake zare min ido, dole
na bi yanda yake so, wai baya so Hjynshi ta sani, don
ta ce mishi in ya sake sai ta aura masa ni, shi yasa duk
ya tashi hankalinsa yanzun. Doctor ta ce, To shi baya
son ya aure ki ne? Asabe ta ce, tab ita ma nasan tana
tsorata shi ne, domin ba ta da burin yayi aure yanzun.
Burinta shi ne ya yi karatun boko mai zurfi,kuma ya
zama wani abu a kasar nan SANADIN BOKO." Na jinjina
kai, tuni zazza6ina ya sauka. Labarin Asabe ya ta6a ni,
kallo na dinga bn ta da shi, Yarinya ce ba zata wuce
Shekara sha uku zuwa sha hudu ba. Wanna ma ai child
abuse ne, ya kamata a hukunta su shi da Hajiyar shi.
Doctor ta katse min tunani da cewa Hafsat me ya faru
da ke kuma, menene labarinki?? Na zuba mata ido,
hawaye suna zubowa, ta ce fada min ina so ne in
taimake ku, na ce zaki cire min cikin? Ta ce Eh, zan
cire miki in har naji labarinka, kin cancanta a cire
miki.Ina nufin in ban da son ranki hakan ta faru ba. Na
share hawaye,sannan na ce da ita. "Sunana Hafsatu,
Mahaifina dan asalin jihar Borno ne, ya fito daga gida
tun zamanin yana saurayi, a kano ya yada zango, nan
yake 'yar sana"arshi.Sun hadu da Mahaifiyata a can
lkcn tazo gidn yarta a Na'ibawa. Babana Shi ne ta
tambaya ya yi mata kwantancan gidan Malam Ma'aru
me Almajirai mijin yarta kenan.Daga lkcn ya nuna yana
sonta, ta amince hr yaje Maliunfashi jihar Katsina,
unguwar Fayamasa. Ya samu kar6uwa cikin dangi, don
yana da nutsuwa da ilimin addini aka ce ya turo
magabatansa.Mahaifanshi sun rasu sai babban wansu
Babagana, shi ne ya zo suka hadu da wani uban
dakinsa. A nan kano suka zo, sune suka amsar masa
auran Innarmu.Ba su jima a kano ba ya soma zuwa
kaduna, ya fara sana'ar saida lemo da Ayaba,daga
bisani ya nemi gida a hayin rigasa ya dawo da
Innarmu,lkcn tayi haihuwar farko wato Yayana Ummar.
Gidanmu gidan haya ne, Mai girma gaske a layinmu kaf
ba gidan da ya kai namu yawa don gidan yawa ake ce
mana. Mata goma sha ne, kowace da 'ya'yanta wasu
hudu wasu shida,wasu goma sha. Babana ya sake auro
wata matar daga kano, itama nan gidan ya samu daki
kusa da na Innarmu., Babah tana da kirki da nutsuwa,
shi yasa duk yanda Innarmu taso suyi rigima bata
biyewa, dole itama ta saki suka zauna lfy. Yanzun
Babah 'ya'yanta 6, Innarmu 8. Ni ce 'ya ta 2, masu bina
3 duk maza ne, sannan mata. Innarmu gidan su 'yan
boko ne, ko na ce kowa yasan Katsinawa da boko. Don
haka tana da burin mu 'ya'yanta muyi boko, shi ko
Baba ba ya da burin mace ta wuce primary. A nashi
ra'ayin nayi saukar Alkur'ani mai girma ya min aure.
Tun muna kanana Innarmu ta kwadaita mana boko, don
haka ni da yayana mun taso muna son karatun
boko,Primary 5 Umar yake lkcn da ni ma aka sani.
Babanmu bai cika biya mana kudi Makarnta ba, don bai
cika samu ba.Amma in yana da shi yana ba mu,ganin
haka ne yasa Innarmu ta kama sana'a. Gyada take
soya mana ni da Yayana in lkcn dafaffiya ne kuma ta
dafa mana da wannan muke samun rufin asiri. Cikin
haka Yayana ya gama Primary aka kukata ya shiga
Junior. Kwanci tashi nima na gama primary, sai dai
lkcn ne Baba ya ce Bokona ya isa haka, izifina ishirin a
Islamiya ya ce da na sauke za a min aure. Innarmu ta
ce ina, yanzun kai ya waye ko ita tayi makarantar gaba
da primary balle 'yarta. Sun yi hatsaniya hr abokinsa
makocinmu Baba Garba, ya saka baki kan cewa Baba
yayi hakur ko aji 3 in yi wato karamar Sakandire. Baba
ya ce, shi kenan,amma fa ba ruwan shi, ko yana taka
kudi ba zaya ba ni ko na fensir ba. Abubuwa suka kara
yi wa Innarmu yawa, ga Yayana Umar kudin jarabawa
yasa makarantar tsaya. Sai dai karen mota ya koma
yana yi wa wani mu2m a layinmu,kasuwa-kasuwa.Inna
ta zaunar da ni ta ce Hafsatu,kin san yanda zamu yi?
Na ce A'a na me? Ta ce, na karatunki, kina so ko? Na
ce "Tab so kai ba ki ga su Saliman ajinmu na su suna
ta zuwa, ta ce to dagewa za ki yi zan dinga alala da
safe ki dan zaga. Sai kuma ki zo ki dauki gyada, na ce
Innarmu ni wlh Na gaji da talla,wata rana mu2m ya yi
ta yawo a ki sayar ta ce sakarya kin zaga tas za a
saye. Asusu zan yi riba ko nawa aka ci sai mu zuba
kafin gama zangon farko mun tara kudin da za ki shiga,
na ceto,gwangwanayen gyada muka fafe wasu tayi
alala.Nan da nan ya kare, Ta dafa min gyada na dauka
ta ce maza Hafsatu, Allah ya bada sa'a kin ji, kan lkcn
Ismaiyya ki saida. Na ce to, Ta ce bn da wasa fa, don
na san ki, na ce to.Wasa kam inadashi,kowa ya sani
har na gama primary duk report card dina ba wanda ba
a rubuta min na cika wasa ba, a haka kuma nake
karatuna.
a haka kuma nake karatuna haka kuma na dage da talla
na wata ranar litinin ina tafiya nice har baban titi na
tsallaka, sai ga wata yarinya tana tallan kwakumeti,
tace ke ina kike zuwa? Na ba ko ina yawon talla nake.
Tace zomuje (governmeet college) ana cinikin gyada in
yan makaranta suka tashi nace, to muje tafiya ce sosai
har gidan gwamna ta nuna min. Muna isa agajiye muka
zauna gin din bishiyoyi ga yan talla nan kala-kala har
da masu gyada babu abin da yafi mun dadi irin yanda
naga yara nata wasa saboda yan makaranta basu tashi
ba. Masu carafke masu yar gala gala nayi, wasu na
tayin ziro-ziro duwatsu na tsinta nima nashiga yin yar
carafke, batare da na huta ba koda dalibai suka taso
nan kowa yasaki wasa suka shiga saida kayansu, ni ko
ban damu ba na cigaba da wasa na sai da takowa ta
kare sanan aka shiga siyan nawa. Washe gari nacewa
innarmu a kara mai makon mudu hudu a dafa biyar.
Yau ma wasa na dora haka nan sai da ta kowa ta kare
don su suna zaune, a gaban kayan su niko ina can ina
wasa na. Zuwa yanzu na saba da dabar hanya zuwa
(government college) wata rana ina zaune kan duntsen
da na dasa a matsayin abin zama na, gaban tirena
hannuna zarene ina ta wasa dashi na hada injin nikan
barira inata yar waka ta. Sai naji magana kusa dani
ance ke gyadarki ba ta saida wa bace? Ba tare da na
dubeshi ba nace ta saidawa ce mana,ya ce, "Sa min
daya a leda sarkin wasa." Na ce, "Zaba." Ya ce, "Zabar
min." Sai lokacin na kalle shi na dan kara zare ido
saboda kyawun shi. Haka nan ba Uniform a jikin shi,
kenan ba dan Makaranta ba ne. Na mika mishi ya ciro
wani farin kyalle ya shinfida akan jijiyar bishiya ya
zauna ya soma cin gyadar. Ni kam kallonshi nike a
raina ina cewa, "Dama 'yan gayu suna cin gyada?" Ya
dube ni, "Ki yi wasanki mana kada ki sa na kware." Na
dauke idona daga bisani na tashi, na soma 'yar gala-
gala ta. Yana lura da yadda kowa ke tsaye kan kayansa
banda ni, da ya mi'ke zaya tafi ya ce, "To sarkin wasa
ga kudinki." Sabuwar naira biyar ya bani a mike, a
rayuwa ta babu abinda ke burgeni irin sabon kudi, na
ce, "Amma na gode, kalleta kar-kar bazan kashe ta ba."
Ya ce, "Mai zaki yi da ita?" Na ce, "Ajiyewa zanyi ba
zan sashi cikin asusu ba bare har na lankwasa ta."
Murmushi yayi sannan ya ce na bashi daya. Ba bashi
ya ci rabi ya bar saura, na ce, "Ji fa baka cinye ba." Ya
ce, "Na koshi." Da zai tafi ya kuma bani sabuwar naira
goma wai in bashi canji na ce, "Wai don Allah kai kuwa
a ina kake samun sababbin kudi?" Bai amsa ba yana ta
kallona. Na ciro tsohuwar biyar na mika mishi. Ya
girgiza kai, "Ba na amfani da Tsohon kudi." Na ce,
"Saboda mene?" Bai amsa ba ya ce, "Gobe zan amshi
gyada." Na ce, "Toh"Ku san kwana 2 ban ga mu2min
ba, sai ranar 3. Yau ma shigar shi ta 'yan gayu kamar
kullum. Ya amshi gyada zai tafi ya kuma bani sabuwar
10. Na ce a, ka manta ne kana bi na canji? Ya ce haka
ne, to rike wannan don ni in na ciro kudi bana maida
su. Na ce ko? Tab, amma dai sun maka yawa ne ko?
Ya dube ni ba alamar wasa, ya ce "Mu ne ai muke kera
su. Na zaro ido ina kallon shi, cikin matukar mmk
"Kana nufin ku ke buga kudi? Ya sake dubana, kwarai
kuwa, na Maida hankalina duk a gare shi. Ka ce kana
da su lodi? Ya saka hannu cikin aljihu shi ya ciro
sabababn dal 'yan naira ashirin da goma-goma na zaro
idanu. Tabbas yanzun na yarda na ce kai ko kaji
dadinka, ina ma ni ce. Ya ce da me za ki siya? Na ce
na farko zan biya kudin makarantana, kuma na dinga
sai mana kayan dadi da su nama da mota, su
mashin.Kai komai sai na sai mana. Ban lura ba, ashe
shi kam dariya na ba shi, ya ce to ai ni kin ga duk na
siya abubuwan da ki ka ce, na yarda kam, shi yasa
gaka nan dan gayu da kai, ka ta6a zuwa kasar waje?
Ya sake darawa, sannan ya ce eh, da yawa ma. Ya tafi
ina ta kallon shi. Sa'a da Zaituna wadanda muke tafiya
tare dasu, da na basu labarin dan gayun nan na ce
ashe sune suka buga kudi kin yarda suka yi. Suka ce to
in shi ne me zai kawo shi nan yana karyawa? Na ce shi
ne ya fadamuku karyawa yake yi? Suka ce min tun
yaushe suka san shi a nan Makarantar. Na ce ko dai
yana koyarwa ni na yarda su ke buga kudi, Ga sabbin
kudi nan dami a gunsa, Lura da su Sa'a suka yu cewa
ba zan yarda da su ba sai suka bar ni. Sau dai suka ce
min ni wawiya ce, sai ka ce bn yi zaman aji ba, sunan
na gama aji 6 bn san komai ba, na ce naji din. Su
Innarmu a da Baba na kuke ina ba su labarin dan gayu
mai buga kudi, amma wai sai suka ce zolayata yake yi,
nayi duk wani kokari na wai don su yarda da ni cewa
gaske ne,amma sun ki. Sai dai na dauki alwashin zan
masa tambayoyin da zai gamsar da su.
washegari jumma‘a ba mu cika jimawa ba, saboda ana
sallah juma‘a a masallacin da ke kallon makarantar
amma kin bin su Sa‘a nayi na fake da cewa sai gyada
ta ta kare. In tashi yan makaranta tuni sun watse ina
ina zaune gaban gyada yar ragowa ce ma, sai kalke
kakle nake. Can na hangoshi zai shiga makarantar, ya
sanye da wani ubansun yadi fari kar hatta takalminshi
da hular kanshi. Duk da yau ce na soma ganin shi da
manyan kaya ban kasa ganeshi ba. Da gudu na bishi
ina cewa tsaya tsaya ban san sunan shi ba bare na
kira. Shiko bai san dashi nake ba a haka mukayi nisa
cikin makaran tar sai dai wani ya lura shi nake bi sai
ya tai maka ya tsai da mun shi. Na lura yaji mama kin
ganina yace, sarkin wasa ina zaki haka? Na tsaya ina
haki saboda gudun da nasha yace sannu na ce yauwa,
dama kai nake ta jira zan tam bayeka ne. Yace na me?
Nace wai dan Allah da takarda kuke yin kudi? Yayi
dariya har hakoranshi farare suka fito yace eh, da
takarda ne to in na baka zaka iya yi min saboda
mutane sun kiyarda ne dani in nace naga masu buga
kudi sai ace karya ne zolayata kake yi. Yace zanyi
maki in kina so nace innaso kai, to da wace irin takarda
kuke yi? Yace ta rubutu nace gobe zan duba jaka ta da
in dauko. Yace ba ayi fa da tsohon littafi ko kina son
tsohon kudi ne? Nace a a taf na fison sabo yace to
shike nan ki kawo sabo nawa za abuga maki yawan
kudin? Nace zaka iya min dubu malala gashin tunkiya?
Ga mamaki na sai naga yana dariya har da rike ciki
nima na soma dariyar ya numfasa ya ce,in ban da abin
ki sarkin wasa wane ne ya san yawan malala gashin
tinkiya, Na ce to ko dai nawa ne ina so yanda dai ishe
ni na gama karatuna. Ya ce,wai dama nan kin yi
karatu? Na dube shi, ba na fada maka ba cewa na
gama primary? ya ce ban ji ba lokacin da ki ka
fada,yanzun JS1 za ki shiga? "Eh tallar da nake ai kudin
rijista muke nema, kaga in ka bugo min kudin na daina
talla, ina gama secondry har ta gaba in je in fara aiki.
Ya ce "Wane aiki ki ke son yi,? Ina nufin me ki ke son
ki zama? na daga kaina sama ina nazarin ya ma ake ce
musu? Ya ce ba ki san me ki ke so ki zama ba? Na ce,
"Ya ma mutanen da ke yin labarai a Talabijin ko
Rediyo? Ya ce, " Media ki ke so? na ce yawwa, haka
zan zama 'yar