Showing 3001 words to 6000 words out of 32103 words
Chapter 2 - Sanadin Boko Book 1 Complete Document by Halima I Mashi .txt
kauda idona saboda yarr din da
tsigar jikina tayi.
Na ce, "Yaushe zaka zo? Ya ce, "Zauna to mu tsara in da
zamu dinga haduwa, don Babanku ya ce in manyana ba
su zo ba kada ya sake ganina.
Na ce, "Fada min daidai ina ne zamu dinga tsayawa? Ya
dan yi shiru, "To ni bansan yaya zamu yi ba, na ce zan
hada miki phone kin ce a gida ba za a barki ba, wai ke
ba ki da irin 'yar dabarar ku ta mata ne? Ki saka ta a
silent.
Na ce, "Barta kawai. Ya dube ni, fatin kuma fa? Na
marairaice murya ina kallon shi da idanuna, da na lura
yana son su. Mu bar maganar party din nan, wallahi ba
Babana ba har Innarmu in ta sani zan bani, ka ji.
Ya tsare ni da manyan idanunsa.
"Yanzun nayi asara kenan? Ya ci gaba "Ban san me yasa
gidanku ake yin haka ba, ni kinga kannena su Nana da
Suhaila Mom din mu da Dad din mu sune suka shirya
musu party din su last week. Amma ku sai ana hana ku.
Wannan duhun kai ne, yanzu fa an waye.
Na ce "Ba wani duhun kai, kowa da irin tarbiyar da yake
son ya yi ma 'ya'yanshi. Ya ce "Shikenan dai, mu bar
maganar, naji nayi asarar kudina, kuma ba wani gida ke
ce dai ba ki ga dama ba.
Wani friend dina yarinyarshi itama 'yar Geto ce, amma ta
jirga Iyayenta da cewa suna biki ne tazo muka yi shagali,
amma ke kin kasa.
Na ce, "Ni dai kayi hakuri kawai. Ya zuba min ido, sai kin
yi min kiss zan hakura. Da sauri na dauki hanyar fita, sai
kawai naji ya rungume ni ta baya, jikina ya dauki rawa.
Cikin rawar murya na ce, "Munnir la..la....lafiyarka? Don
Allah sake ni. Da kyar na kwace, kamanninshi sun canza,
da sassarfa na fito na dau hanya. Ya biyo ni da mota shi
da abokinshi, wai na shiga su kaini gida, na ce, "A'a don
na tsorata, dole suka bar ni.
Da na zo barci na jima ina tuno abin da Munir ya min,
dama an ce mace da namiji in suka kebe na ukun
shaidan ne. Ba don son da nake yiwa Munir ba, da tuni
na bar shi.
Mun canza gurin hira, bayan layinmu yake tsayawa. Na
fada ma Innarmu ta ce saboda me? Na ce, Baba ya hana
shi zuwa nan.
Inna ta ce, "Mallam ho! Shikenan, ki dinga zuwa da
Ummi kin san mutane da sa ido, yanzun sai ace wani
abin ne yasa ku ke zuwa can. Fatana ki kama kanki.
Na ce, "To, nima zuwa da Ummi zai fi min, duk da Munir
ganin Ummi bai hana shi son taba jikina ba.
Cikin haka muka soma shirin zana (JAMB), Baba bai sani
ba, Munir ne ya sai min form, sai dai tsorona daya randa
Baba zai sani.
Na zama cikin sa'a kamar ko yaushe, Munir ya tsaya
tsayin daka har na samu gurbin karatu a (B.U.K) Kano,
sai dai ya zamuyi da Baba? Haka na ce ma Innarmu, ta
ce yau na yanke shawarar sanar da shi komai, tunda
gobe za ku je yin rijista.
Kusan goman dare, lokacin ina kwance muryar Innarmu
nake ji tar daga dakin Baba, domin bangonsu daya. Tana
sanar da Babanmu komai.
Bai katse ta ba har ta kai karshe, ya ce, "To bokon nan
ba da yawuna ba, bayan shekara shidan da na hakura
tayi yanzu kuma wata zata? Wai lahira take so ko
duniya?
Inna ta ce, "Duka. Ya ce, "Karya ne, duniya ku ke nema,
kuma ga ku gata nan. Jami'ar da aka ce 'ya'ya suna
lalacewa? Yarinyar ta fada a gabanki sama da shekaru
amma baki damu ba. To magana ta ni uku ce, bata kai
hudu ba.
Na farko duk abin da ya faru da ita SANADIN BOKO ba
ruwana, zai shafe ki ne da ita.
Na biyu ba zan yafe hakkina da ku ka tauye ba,
matsayina na Ubanta, kuka hana ni in sauke nauyin da
Allah Ya dora min.
Na uku kuma ta nemi Ubanta ke kuma ki nemi mijinki,
duk ranar da wata ashsha ta samu SANADIN BOKO.
Ba innarmu ba, ni kaina zancen ya girgiza ni. Baba
kishiyar Innarmu ta fito daga uwar dakinta, ta zo kusa
dani ta zauna.
Tasa hannu ta dan dake ni, "Tashi Hafsatu.
Na tashi zaune jikina sharkaf da zufa, ta ce "Nasan kin ji
duk zancen da Malam yake yi ko?
Na ce, "Eh. Muryar Innarmu ta katse ni, ta ce, "Insha
Allahu Malam karatun Hafsa zai zama alkhairi garemu da
kai gaba daya.
Ya ce "Ruwanku. Cikinsu ba wanda ya sake magana.
Babah ta ce, " Hafsatu ki bar Babanki yayi iko da ke, ki
ce ma Innarku kin fasa karatu. Kalamanshi ba baki yayi
miki ba, amma ina ji miki tsoron alhakinshi kada ya kama
ki.
Na ce, "Babah wanda zan aura karatu yake yi, ba yanzu
zai yi aure ba, kuma Iyayenshi ba za su yarda ya auri
mara ilimi ba.
Babah ta ce, "Sai shi? Akwai masu sonki da yawa, kuma
sun ma Babanki magana. Nayi shiru ina nazari, nasan
Babah gaskiya ta fada min, amma ya zan yi da son
Munnir?
Na dube ta, "Babah ki duba irin hidimar da Munnir yake
yi da ni, ba zan mishi adalci ba in na ce ba zan jirashi ba.
Ta ce, "To yanda ki ka gani, amma karatun nan tunda ba
na Muhammadiyya ba ne, banga dalilin naci ba.
Kuma ni sai in ga yaron nan tamkar yaudararki yake yi.
Anya auranki zai yi? Na ce, "Allah Babah aurena zai yi, ki
dubi dadewar mu da hidimar da yake min.
Ta ce, "Ba ta a nan, amma fa shawara ce." Na koma na
kwanta, ita kuma ta mike ta nufi cikin dakinta.
Zancen Babah ya taba zuciyata, illah magana daya da
ban kama ba, wai tana ga Munnir ba zai aure ni ba. Nayi
guntun murmushi, me zai sa shi ya yi ta dawainiya da ni
ba zai aure ni ba?
Yanda na raba dare ban yi bacci ba, na tabbata
Mahaifana biyu ma haka ne, duk SANADIN BOKO. Da
safe ina zaune da kofin koko sai juya shi nake yi na kasa
sha, Innarmu ma sukuku take.
Lokacin da ta zauna tana shafa ma gwangwanayan
alalarta manja, na ce "Inna ko dai zamu hakura da batun
bokon nan ne?
Ta dube ni, "Saboda me? Na sunkuyar da kai na ce, "Naji
duk yadda ku ka yi da Baba jiya. Tayi shiru, can ta ce,
"Abu daya zuwa biyu nike so ki min.
Na zuba mata ido, na farko ki tsaremin kanki da
mutuncinki, kada ki banzantar da kanki, na biyu kiyi abin
da ya kai ki makaranta, wato karatunki wanda nike fata
ya zama sanadin alkhairi.
Ta haka ne za ki wanke wa Mahaifinki tsanar da ya yi
wa boko, har kannanki suma su samu dama suyi cikin
kwanciyar hankali. Yayanki da bai samu damar ci gaba
ba yana jin haushi.
Ke tunda kin samu dama kada ki bani kunya. Na hada ki
da Allah, ki rufamin asiri. Tausayin Innarmu ya cika ni,
na ce, "Insha Allahu zan kula sosai, kuma zan fidda ki
kunya, SANADIN
BOKOn nan kowa zai huta, Baba zai yi alfahari da ni.
Munnir yayi tsayin daka har na zama daliba a jami'ar
Bayero da ke Kano, har lokacin da zan tafi Innarmu bata
daina rokona in rufa mata asiri in lura da kaina ba.
Nan na tafi na barta da surutun 'yan gidanmu, da 'yan
unguwarmu. Wasu suce tana so ne ta auri mai kudi, shi
yasa muka nace boko, wasu su ce dan kyan nawa bai fi
cikin cokali ba, amma mun kuke sai nayi boko.
Wasu su ce dan-dan masu hali ke sona, duk dai ta toshe
kunne watan kwaram daya ne. Baba har fushi yayi da ita,
sun jima kafin ya soma amsa gaisuwarta.
Karin haushi yakai kararta ga danginta, maimakon su
bata rashin gaskiya suyi mata fada, sai suka ba shi
hakuri suka ce wai karatun yana da amfani.
Ya ce, shi ba ya ce babu amfani ba ne, a'a tayi shi can
gidan mijinta. Aure shi ne sama da karatun ta, sai suka
ce ya yi hakuri 'yan kwanaki ne zata gama, don haka sai
ya dawo ya zura mana ido
******* ********** ********** *********** *********
Jami'a wata rayuwa ce da ta sha bamban da
secondary, banga laifin Baba ba yanzun don ya
kyamaci boko, sai dai na sha alwashin kula da kaina,
don haka na tsare gida bani da kawa ko aboki. Duk da
Munnir na shirin tafiya Dubai karatu don kammala
Masters dinshi, haka bai hana shi zuwa duk bayan sati
biyu ba. Tafiyar tashi bata yuwu ba har muka samu
hutun first semester, sati biyu dai za mu yi amma naji
dadi, sai dai wannan hutun ne hutun da ba zan taba
mantawa dashi ba a rayuwata. (Kuma shi ne dalilin
rubuta labari na "SANADIN BOKO" .
Sauran kwana biyar na koma Makaranta duk da inata
dokin zuwa gida amma zaman gidan bai mun dadi ba,
ko gaisuwata Baba baya amsawa har ta kai da naji
muryarshi zan boye.
Bello Abokin Munnir shi yayi sallama da ni, na sha
mamaki don bai taba zuwa shi daya ba. Ya ce, Munnir
ya aiko shi muje tare bashi da lafiya. A rude na je na
fadawa Inna, ta ce, "Yana asibiti ne?" Duk da ban sani
ba sai na ce mata, "Eh." A zatona yana asibiti ne, sai
da yaja mota sannan nace, "Wane asibiti ne." Sai ya
ce, "Ai yana gida." Har gefen su Munnir Bello ya raka
ni, ina shiga sai yace mun, "Toh yana ciki ni na wuce ki
fada masa don ya dameni in kawo ki har ciki. Na ce,
"Toh!" Na nufi ciki da tafiya cikin dari-dari. Tsakiyar
falon na tsaya na zabga Sallama, ga mamakina sai ga
Munnir ya fito daga kitchen sanye da gajeren wando da
vest duka farare tas, hannunshi dauke da ruwa (C way)
yana sha. Na ce, "Ah! Ka samu sauki ne?" Ya ce, "Eh,
A'a." Ya nuna min kujera, "Zauna." Na zauna ina kallon
shi tare da son jin karin bayani, "Ban gane eh, a'a ba?"
Ya tsugunna a gabana, "Ciwon ya dade yana ci na, ga
shi zan iya tafiya Makaranta cikin kowane lokaci ba
tare da na samu maganin ba." Na ce, "Wane irin ciwo
ne?" Ba tare da shakka ki tunani ba ya ce, "Ciwon
sha'awarki....."
Gabana ya fadi, na mike tsaye da sauri. Shima ya mike,
"Hafsat kin san ina son ki, wallahi na gaji da
sha'awarki. Ki so ni kamar yanda nike son ki." Na ce,
"Munnir ka san ina son ka." Ya ce, "To ki nuna min."
Na ce, "Ban gane ba? Sau nawa nake cwa ina son ka?
Ka sani." Ya ja tsaki, "Kin dai gane nufi na, ina son yau
daya ki taimaka ki nuna kaunarki gare ni." Na ce, "A'a
ba zan iya ba, domin haramun ne." Ya ce, "Ni fa zan
aure ki!" Na soma tafiya don fita ina cewa, "Sai ka jira
sai ka....." Maganata ta tsaya sakamakon murda kofar
da naji nayi ta a rufe gam. Na dube shi yana murmushi
ya ce, "Ki bani hadin kai don yau ta karfin tsiya ma zan
iya biyan bukata ta." Jikina ya soma bari na ce,
"Wallahi Munnir zan maka ihu, ka bude min kofa." Ya
zauna, "Ko kin yi ihu ba wanda za ya ji ki. Mom bata
nan tana gurin aiki, Dad ma haka, su Nana da Suhaila
suna Makaranta." Na zube gwiwoyina biyu a rude ina
cewa, "Ka min rai kada ka sa ni cikin matsala, don
Allah." Na soma kuka. Ya ce, "Nima ki taimake ni na
gaji, wanene za ya gane me muka yi?" Na ce, "Allah ya
sani, na tabbata zai kama mu." Amma da yake Shaidan
ya hura ma Munnir kaho sam ya ki karban uzirina.
Muka yi ta zaga falon har na fada wani daki, sai dai
kafin na rufo tuni ya banko, mun yi damben bala'i dashi
kafin ya samu nasarar aikata mummunan nufinshi a
kaina, bayan ya bi duk wata gaba ta jikina ya bugeta,
fuskata kuwa ta sha mari sai na ga kamar ba Munnir
dina ba.
Kuka iya kuka na yi shi, na mike ina gyara daurin
zanina, da kyar nake tafiya na fito falon, ya ce, "Duk kin
sa mun wahala, a yanzu wa zau sani in ba kin fada
ba?" Na ce, "Bude min kofa kawai ni dai na tafi." Ya
nufo ni, "Come on kiyi wanka sai na kai ki." Ban san
lokacin dana daka mishi tsawa ba, "Budeni mana"
Sabon kuka ya kwace min na ce, "Allah ya isa tsakani
na da kai, Insha Allahu sai Allah ya saka min." Ya tashi
ya bude tare da cewa, "Sai na zo." Ban kulashi ba na
fita, dole na share hawayena saboda Maigadinsu, na
fita ko ina a jikina ciwo ya ke. A haka na kai gida, kallo
daya Inna ta min tace, "Lafiya?" Jikina ya soma bari, ta
ce, "Ba dai jikin nashi ba? Na ga duk kin rude fuska a
kumbure." Na ce, "Umm jikin ne." Ta ce, "To shine na
kuka? ki masa addu'a." Na ce, "To." Na nufi ciki. Ta ce,
"Hafsa zo nan, menene wannan a zaninki?"mummunar
faduwar gaba ta ziyarce ni, zufa kuma ta shiga keto
min, amma sai na yi saurin cewa, "Fashin Sallah ne."
Duk da ban juyo ba kuma ban san mai ta gani jikin
zanin ba. A gani na in muka hada ido zata gane, ta ce,
"Haka kika ratso titi? Ga ruwa da na daura chan kan
wuta na tuwo ki diba ki maida min sai ki dauraye
jikinki."
Cikin bayi ina wanka ina kuka tausayin Innarmu ya cika
zuciyata, na karya alkawarin da na daukar mata, Allah
ya isa Munnir.
Cikin kwanakin da suka biyo baya ko Munnir ya zo
bana fita, ranar da zan koma Makaranta har goman
safe ina kwance a tsakar daki, Innarmu ta ce, "Ke da
naji kina cewa sammako zaki yi? Har yanzun kin kasa
tashi?" Na ja tsaki, yanzun na soma tsanar boko bani da
daman in tona asirina...
Yaron gidanmu ya shigo ya ce, "Hafsa wai in kin shirya
wani mai mota ya ce ki fito yana can saman layi." Na
ja tsaki, "Ka ce masa ya tafi na san hanya." Innarmu ta
ce ma yaron, "Kai zo, je kace tana zuwa." Yana fita ta
fara min fada wai bani da hankali, ta lura kullum zai
kirani in 'ki fita, haka ake yi? In ma sabani kuka samu
ba sai kiyi hakuri ba tunda shi har ya zo? Na kalli
Innarmu a zuciya na ce, "Da kin san abinda ya min sai
kin fini tsanar shi." Ban ce komai ba na ci gaba da
shiri. Inna ta kwance habar zaninta kudine 'yan hamsin
hamsin dubu uku na adashena na kwasa, sannan cikin
robar can tumatir ne na tafasa shi ga sabulu can inji
Baabarki..... Na ce, "Ki bar kudinki." Ta ce, "A'a na dai
baki ne, amma badan zasu ishe ki wani abu ba ne.
Yaron nan dake dawainiya da ke Allah ya gwada min
aurenku." Yana zaune yana latse-latsen waya ya diro,
"Gimbiyata, amaryata har yau fushi kike da ni? Gashi
doguwar tafiya za muyi? Don Kano zan kaiki." Ban
tanka shi ba ya amshi robar hannuna da leda ya daga
but ya sa. Ni dai tamkar na haushi da duka nake ji, ya
bude mun gaba na shiga don bani da yadda zan yi.
Tunda muka dau hanya yake mun magana amma ban
tanka shi ba. Ya ciro waya daga gefen shi ya ce, "Ga
wayarki." Sai lokacin na yi magana, "Bana so." Ya
daurata kan cinyarshi, "Dole ki so ta Hafsat don in na
tafi karatu ta yaya zan dinga jin muryarki? Ki saki ranki,
abun da ya faru ba wata matsala bace saboda ni zan
aureki..." Na zabga mishi harara tare da cewa, "A
ganinka kenan, amma ni addinina bai yadda don zaka
aure ni kayi ZINA dani ba." Ya katseni, "Ki daina cewa
Zina." Na daga murya na ce, "Ka biya sadaki na ne?
Iyayenka sun nemi aurena gun iyayena ne an basu? Ko
jama'a sun shaida." Ya ce, "Ba daya." Na ja tsaki ban
kara tanka shi ba har muka kai.
A dakinmu ba yadda bai yi ba na'ki tankashi, ya aje
mun kudi da waya ya tafi. Na saka kuka nayi ma ishi
na, tunanina in Allah bai yi aurena da Munnir ba fa? Ya
sakani cikin matsala kenan don ban san mai zance ma
mijina ba yayin da yace ina nakai budurcina? Dole in
dauki hakuri in lallaba Munnir ya aureni.
-Yana kiran wayata sosai, tun ina sharewa har na
hakura don ban san yadda zan yi ba, sai dai bashi da
wata daraja ko kima a ido ba, ko na aureshi gani nake
ba zan girmama shi ba, tunda na ga irin nashi rashin
Imani.
Sai mene? Tun jiya sha hudu ga wata ya dace in ga
al'adata amma har yau sha biyar shiru. Wannan ya
tilastamin shiga rudani.
Dora John dakinmu daya har ta gane ina da matsala ta
ce, "Hafsy yaya ne?" Na ce, "Ciwon kai ne." Ta bani
panadol da sauri na sha don kuwa kan nawa na ciwo.
Kwanaki uku suka biyo baya gashi banji daga Munnir ba
cikin 'yan kwanakin, naje na sai kati na kira shi, yana
dagawa na soma kuka, ya ce, "Mai ya faru?" Na ce,
"Banga period dina ba yau kwana uku." Ga mamaki na
sai na ji bai damu ba ya ce, "Zan shigo wannan ba
wani abun damuwa ba ne."
Washegari sai gashi da wani abokin shi, yana shigowa
na soma kuka nan take ya bata rai, "Kukan nan ya
soma isata, zan barki ki karata in dai ba zaki daina mun
kuka ba." Abokin shi Bello ba karamin tsanarshi nayi ba
har da cewa, "Daga sau daya sai ciki?" Munnir ya ce,
"Nima dai nayi mamaki bata fa tsaya ba ma, gaskiya in
anyi bikin mu juya Mahaifarta za'ayi don bana son yara
su wuce biyu tsanani uku." Tsabar bakin ciki ya hana ni
tankasu, ni dai burina ya san yadda zai yi dani. Bello ya
kira wani abokin shi anan Kano wai shi Nasir, ya zo
suka tafi suka yi magana sannan suka ce inzo mu je
asibiti.
Mun shiga office din Likita mace 'yar kimanin shekara
arba'in tana tsaye da farin gilashi, ta tsareni da ido
bayan duk mun zauna ta kalli Nasir, "Me ke tafe da
ku?" Duk muka yi shiru, Munnir ne mara kunya shine ya
ce, "Mun kawota ne bata ga period dinta ba, so muna
so a gwada ta." Ta tsareshi da ido, "Kanwarka ce?" Ya
ce, "Budurwa ta ce." Bakin ciki ya cika ni, na sunkuyar
da kai ina hawaye, "To ku dan bamu wuri." Suka fita.
Ta zabga min harara, "Kin bashi kan ki ko?" Murya ta a
sarke na ce, "Wallahi...
Mukhtar Ismail Muhammad
WhatsApp: 08161892123
Sanadin Boko 1-03
Posted by Mukhtar Ismail Muhammad
On
www.arewarulers.com.ng
Under: SANADIN BOKO
NA
Maryam Abdullahi K/Mashi
To ku dan bamu wuri." Suka fita. Ta zabga min harara,
"Kin bashi kan ki ko?" Murya ta a sarke na ce, "Wallahi
Anty fyade yayi mun." Ta ce, "Tun yaushe?" Na ce,
"Za'a kai wata daya." Ta bani wata 'yar roba ta nuna
min wata kofa, "Shiga toilet ki bani fitsarinki." Ina
fitowa naga wata nurse tsaye ta ce, "Don Allah sister
ina son result yanzun nan." Ba jimawa ta shigo, Likitar
tayi ta juya takardar sannan ta dube ni ta ce, "Kina da
cikin wata daya da kwanaki." Nan da nan na soma
zufa, zuciyata na kwadayin ina ma mafarki ne? Cikin
tsananin kuka da kunan rai na ce, "Ya cuce ni. Mai
zance da Innarmu? Abun da Baba yake tsoro ya faru.
Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un." Kuka na ya shigo da
su, ta mika mishi result ya duba sannan ya