Showing 1 words to 3000 words out of 18680 words

Chapter 1 - UWAR GAFALALLU book 1 By Oum Yasmeen .txt

07 Jan 2025

2093

WAR GAFALALLU


oumyasmeen


Da sunan Allah mai rahama mai jin kai duk kan yabo da godiya sun tabbata ga ubangiji ayau Allah ya ƙara haɗa mu a wannan sabon littafin nawa Allah ya bani ikon gamawa lafiya..


GARGADI!!!


Ban yadda wani ko wata suyi min amfani da wannan labari ta kuwanne siga idan kunne yaji jiki ya tsira


Wannan labarin kirkirarre ne banyi da nufin tuzarta wani ko wata ba duk wanda ya ga yayi dai-dai da rayuwar sa ya dauka arashi ne...






بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ














Allah ya tsare Allah ya kare ban da ɗaukan na mara hakuri amma ban hana ku ɗaukan na wanda yayi wasa rare da kayansa ba ,ku kiyaye bana son Ku dauko min magana daman makota sun sakamin ido idan ban daku ai saidai mu yini ba mu ci ba


Sumy tace ''....Momcy kar ki damu yau aljihunki zai cika da ya'yan banki ,


wata uwar buɗa ta saki tana cewa na gode ta gidana shi yasa ka nake ƙara son ku bakwa son damuwata


dafa ta naja tayi tace '' momcy inhar kina doran duniya bamu da damuwa...,


wallahi kuwa kudai Allah yayi muku abarka


amin ya Allah suka faɗa suna ƙoƙarin fita ko wacce akwai me jiranta a waje


tashi nayi dana gama sauraron duk zancen su na fita zama nayi a kan kujera kee mufeeda wai har yau ba me dan danshi da yake zuwa gurin ki


ajiyar zuciya na sauke nayi shiru


garbati da yake zaune yana nan naɗa tabar wiwi yace


''uwar gafalallu sai kin bada kuɗi an mata roƙon Allah duk wannan kyawun nata ba wani me dan mai ko da yake zowa gurin ta...,


a hassale mufeeda tace "...da hallacan yiwa mutane shiru ina neman tsari da wannan rayuwar suma da suka saka kan su a ciki Allah ya shirye su..,


Asabe reza tace ...tab lallai yarinyar nan baki da hankali


tashi nayi na shiga daki na koma na kwanta abuna idan dai rayuwar gidan mu ce hmm sai dai addu'a


zama tayi a dokin kofa tana fito da wiwi da sauri suka taso rufe kayar ta tayi tace


'' ku dakata bana son rashin hankali kowa ya bi layi ga ta nan da yawa kuma wallahi..,


wai ke me isaka kin fiye yawa da yawa ne..


Gaddafi ya faɗa yana cije baki hadi da zaro huƙa


Asabe reza tace '' gaddafi wallahi zakai ka gama baza ku durani da ka ba wallahi ƙarshe mutan unguwar nan su fara nuna ni da baki ana ga asabe reza ta ƙare mata..,


cikin cije baki gaddafi yace '' amma dai...,


kai yi min shiru ko yanzu billahillazi nayi ƙasa ƙasa dakai tsohon tsumi ya tashi ta faɗa tana zare ido haɗi da nannade hannun rigarta


a'a asabe reza duk bata kai haka ba mai kuɗi ya baki, ki bashi fakat wanda bashi da shi ya raka ki da na jiyamu ( ido)


kar ma ku kawo ni nasan yadda zanyi da ku yan hau yanzu ina zuwa bakin titi karfe biyun dare wallahi rubibinta za ayi tas zata ƙare


haladune ya shigo ya caka huƙa a ƙasa yace
'' ...shege naki dan iska naki duk irin laifin da kayi kazo gidan uwar marayu tana da masauki har me tsinuwar iyaye kina mara ba dashi ana gudin dan iska amma ke shi kike so kaga uwar da take kara saka ya'yan ta akan hanya dodar..,


dukkan su, suka haɗa baki gurin faɗar doɗar


wata iriyar dariya tayi tace '' haladu na gode da wannan kirarin...,


kuttumar ubancen lallai yau za a yi ta da mai da yaji ....ni za ta tozar ta


tashi tayi tana cewa jalila lafiya yau she kika dawo ban sani ba baki baki balance


dauke kai jalila tayi tana cewa momcy yau akwai tashin hankali a gidan nan


dan ubanki ni tashin hankali damata yayi bani dai labari me ya faru kike tada jijiyoyin wuya


nuna mata wayar'ta tayi tana cewa momcy yan zunan aka turo min picture din naja da honourable suna can hotel


wata dariya ta sheƙe da ita har da bugun cinya tace '' wallahi tarairayar customer tafi ki shi ya saka kika ga ya dawo gunta kema sai ki dage idan abin yayi miki ciwo a dinga gyara headquarter sosai ta inda ba ta yadda za a yi yaje gurin wata ko matar sa bata isa ba..amma munafikin da ya turo mik wannan rashin mutuncin shi ya kamata kije kici ubansa..,


yanzu dai a takaice kin goyi bayan ta


zama asabe reza tayi tana gyara zanin'ta tace '' naja zancen kike so kai ta nawa za'a baka..?,
miƙa mata riɗa ɗaya yayi (dari) juya ta ta fara sannan ta soke a ƙafa wani almajiri ya shigo yana cewa sallamu'alaikum wai mufeeda tazo


naɗe ledar wiwi tayi ta kulle tana cewa masha Allah inji wa


inji malam rufa'i


je ka kace bata nan haka kurum mutum yawa maye nace ya barmin ya'ta yaƙi kullum ya zo hannu na bugun cinya , ya wani taje gemunsa yayi tsaibebe a tsaye wallahi baza ta saɓu ba ya'ta kallar gaban mota ce ni bance lallai sai tayi aure ba ya barmin kayata


da sauri mufeeda ta fito tana ni wallahi momcy ki dena abin da kike


da sauri ta jayo ta aguje ta fita bin ta tayi ganin taje soro ta dawo ƙarasawa tayi tana dariya kallon ta yayi yace


"Mufeeda...,


Na'am ina wuni yau saukar rana


zama yayi akan dan kututturen bishiya yace


''eh wallahi kin ganni nan barka da rana..,


yauwa ta faɗa tana wasa da mayafinta


Tufafi yace '' ...a maman tamu ,


kaje can ka nemi uwar ka ni ba uwar ka bace
da sauri ta juyo shi kuma ya tashi durƙusawa yayi har ƙasa yace


''barka da rana ....,


barka da ubanka ka fitar min daga sabgar ya'ta wallahi ,me nasama ya ci balle ya bawa na ƙasa


haba momcy me yasa ka kike haka kowa kina kyale sa amma ni


rufe min baki ko na zubar miki da haƙora kece ƙarama amma ki na nema ki gagare ni wallahi bazai yiwu ba


hawaye ne suka fara sintiri a fuskarta wannan tozarci da me yayi kama kallon rufa'i tayi tace


''kai hakuri katafi gida mayi magana ta waya...,


tashi yayi daga durƙusan da yake ya gyaɗa mata kai kawai ba tare da yayi magana ba juyowa kan momcy tayi tace


''yanzu abin da kikai ya dace kenan...,


zo ki wuce ko saina ballaki


wucewa tayi ba yadda ta iya tana shiga ta samu guri ta zauna ta ci gaba da kukan ta jalila ce ta fito tace




''mufeeda me ya faru kike kuka...?,


momcy ce ta kori rufa'i


kallon maman tasu tayi da take ta siyar da wiwi ba abin da ya dame ta juyowa tayi tana ƙasa da murya tace


''kice mai idan har zai dinga zuwa ya tawo da leda idan kuwa ba haka ba wallahi hulakanci yanzu ya fara gani..,


ni dai gaskiya bazan iya faɗa mai haka ba


tsaki ta ja ta shiga daki itama tashi tayi ta mara mata baya kwanciya tayi tana kallon rufin kwanon dakin nasu tana da burin yin karatu amma halin babu ya hanata yi juyawa tayi ta kalli jalila tace




'' aunty jalila dan Allah bani kuɗi na ci abinci yunwa nake ji...,


yau baba be bayar da kuɗi bane


ajiyar zuciya ta sauke tace


''tun safe da ya futa be dawo ba...,


tab aikuwa yau balallai aci abinci a gidan nan ni kuma gaskiya bani da kuɗin da zan baki tun da kin ƙi sakin jiki ayi harkar arziki


insha Allahu wannan mutuncin nawa har gidan mijina


dariya jalila tayi tana saka waka a wayar ta tana bi


jin wata uwar sallama da sauri ta fito tasan me amsar kuɗin huta ne kallon momcy tayi tace




'' momcy ya dace ba fa ko baki ji sallamar sa ba...,


mufeeda na ji wallahi duk wata karya da zan mai ta ƙare


momcy yaufa da uban gidan sa yace zai zo kar ya saka a rufe mu


kuma fa haka ne saka mayafin ki ki fita duk wata karrairaya da kika iya da wacce kika ga yan uwanki suna yi kiyi musu ko za a dace


Mufeeda tace ''gaskiya ni bazan iya ba haba momcy ki dena abin da kike ..,


Gaddafi kuna jin abin da take faɗa ko wake amfanuwa da wutar gidan nan idan ba ita ba , bata da aiki sai kayana ya yamutsai bazan iya saka shi a haka ba to wallahi zan ci uwar baban ki idan baki je ba


ni kuma zan ci kuttumar uban ki asabe ashe daman rashin mutuncin ki har ya kai haka da sauri ta juyo jin muryar lami mahaifiyar mijinta rufe baki tayi domin idan dai tujara ce sai dai ta take mata baya lami yar tijara ce har yanzu da tsofanta shan taba sigari take


dariya mazan gidan suka saka har da masu tafi Allah ya dawo da lami yar gumama


kai mufeeda ta girgiza wannan rayuwa da me tayi kama ke dan uwar ki kin tsaya kina kallo na ga kayan nan kin tsaya kina kallo na da idanuwanki yawa na mujiya


tafiya ta fara tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki


ke barshi kawata jalila ko bakya gidan ne


jalila ce ta fito tana miƙa tace


'' baba lami saukar yaushe...?,


Baba lami tace...wallahi yanzu na sauka kai munsha Niger duk wani kaya da na tafi da shi tas ya ƙare


kai masha Allah haka ake so ni wallahi ban taɓa zaton zaki dawo da wuri haka ba


baba lami yar gumama tace '' na siyar da kaya zaman me zanyi yar albarka ga kayana nan zoki tayani ɗauka ..,


karasa fitowa tayi da yake da a dokin kofa data tsaya ɗaukan mata kaya tayi takai mata dakin ta jiki a sanyaye mufeeda ta fita gaban tane ya waɗi ganin yau a mota suka zo daga ganin motar an saka makudan kudade kafin a siye ta gaban tane ya waɗi ganin har wani ya hau yana nema ya tsinke wutar su da sauri ta ƙarasa ta soma..,


girgiza tsanin tana cewa wallahi idan baka sauko ba wallahi Allah sai na karya ka ɗan uwar ka ba magana nake maka ba kai wanne irin matsiyaci......ne


cire glass dinsa yayi da sauri ta ja baya gaban ta ya yanke ya waɗi ƙarasa cire wayar yayi ya fara saukowa a hankali cikin nutsuwa da izza lokaci ɗaya tsanar yarinyar ta durar mai a zuciya yarinya ƙarama amma tana wannan tujarar


tun da suka haɗa ido da shi gaban ta ya yanke ya waɗi tamkar an kafa mata turke a gurin ta kasa barin wajen zagi ba halinta bane tana cikin wannan hali Anai ya zo wucewa cikin muryar rukakkun yan daba yace


'' mufeeda...yane..,


da sauri ta ɗago tare da sakin ajiyar zuciya idan har Anai yana kusa tofa ba wanda ya isa ya taba ta shi ya saka ma take tare dashi ko su kansu yan uwanta idan har tace zata haɗasi dashi basa iya yi mata wani abu da zai cutar da ita kallon inda yake tsaye tayi ya murtuƙe fuska yawa hadari ya gangamo ba wani annuri a fuskarsa dukan mace ba dabi'arsa bace amma yau da yarinyar nan sai dai a ɗauke ta har shi zata zagar mai


Uwa tasan irin so da kaunar da yake wa mahaifiyar sa duk abin da ya zama sularta ce cije lips dinsa yayi ya fara tafiya da sauri yaran nasa suka karaso ɗaya daga cikin su yana cewa


oga wallahi Sai hakuri ba mutunci ne da su ba wai a haka ma gwara ita da sauran kaf gidan ta fisu kirki mahaifinsu shi ne fa tsohon dan daban nan idirisa kyalli


zuciyar ta ce tayi mata wani uban baki ko ace babu halin yayyunta to wallahi abin kunyar da iyayensu sukai ba zai taɓa barin su , su zauna lafiya ba kallon ANAI tayi ta zauna akan inda rufa'i ya tashi tace


'' kwana dubu ina ka shiga...,


gyara hular kaurayen sa yayi yace


'' wallahi naje umarane yau ɗin nan aka sallamoni..,


me ka ɗauka


shiru yayi ɗagowa tayi ta kallesa idanuwanta tab da hawaye tana kaunar rufa'i amma ba yadda zata yi mahaifansa idan har suna numfashi a doran duniyan nan ba zasu bari ya aure ta ba ANAI kuma ɗan daba ne ta baso ta zaɓowa ya'yanta uba na gari cikin rawar murya da take bayyana rauninta tace


'' dan girman Allah ANAI Ka nutsu kaga ɗaukan hakkin wani babbar illace gidan yari ya zamar maka tamkar ibada yau kana can gobe ka fito..,


harki damu insha Allahu na kusan ajiye komai muyi aure


Anai bazan iya auren ka ba inhar kana wannan abun wannan shi ne gaskiya


to ba matsala duk sanda na shiryu mayi auren nima ba yanzu nake nufi ba


sai yau she kenan...?,


ba rana ya fada yana gyara zaman hukarsa a jikin sa


tashi tayi tana cewa....okay kar ka sake ka ƙarayi min magana ta faɗa tana shige wa cikin gidan su


yauwa ya kikai da su sun hakura


cewar momcy


dafa kejin kaji tayi tana cewa momcy yaufa da Uban gidan su suka zo wallahi ya yanke


amma wannan anyi ƙwallon shege muna talakawa yaushe zamu iya biyan kuɗin wuta muji ma da na abinci


wallahi kuwa baba ai wannan shugaban gidan wutar da aka saka bashi da kirki wallahi dakan sa yake yawon karɓar kuɗin wuta dan gidan Alhaji mansur Gwarzo ne...




UWAR GAFALALLU


OUMYASMEEN


Wannan littafin na kudine ku hanzarta payment din Ku free page ba yawa


8141785374


Amina alhasan Muhammad opay ku turo da she da ta wannan hanyar


09061890481


EPISODE 2


Wannan dai babban dan kasuwar


shifa baba lami ta faɗa tana gyara goron da ta siyo


Baba lami yar gumama tace ''..kwanaki na taɓa zuwa gidan su karɓar sadaka ubansa mutumin kirki ne dana san shi ne yazo da wallahi sai na fita ya bani sadaka


wallahi duk irin wannan abin ne yake zubar mana da mutunci gaskiya baki kyauta ba


da sauri bana ta dauki roba ta wullo mata kaucewa tayi


baba lami yar gumama tace ''kaji yar butar uwar nan sabe ce bata kyauta ba koni..,


shiga daki tayi tana cewa aunty jalila wallahi duk abin da akai mana a unguwar nan su baba suna da sa hannu wannan wanne irin son kuɗi ne har ki dinga tafiya bara bayan Allah ya wore miki lafiyar da zaki nema...


banza tayi mata taci gaba da shirinta daga ko ina na jikinta take yi tana zuba turare tare da murya ko ina kai ta girgiza sallamar naja taji da sauri ta saka zani ta fito tana cewa yau wallahi me rabamu sai Allah ki rasa wacce zaki ci amana sai ni


dariya naja tayi tana daga ledojin da ta shigo dashi tace


'' yarinya kwantar da hankalin ki ba wani abu mukai ba kawai sau ɗaya yayi ashe ma ba wani jarumi bane..dan haka na barmi ki shi kawai dandana shi nayi kullum baki da zance sai honourable ashe muna maza ne ba namiji bane...,


kut ni kike faɗawa haka tab lallai yau me rabani dake sai Allah momcy kina ji ko


jalila bana son neman fitina dame zanji da wannan masifar ta yaran nan kina ga an kama sunusi dan kuɗin da suke tarawa a guri na saboda bacin rana nawa yake dole naje nayi belinsa su kan su yayensu sun barmin su komai ni kenan raina ɗaya ku ga kunan kuna mata ban wuta ba jalila fitinar ki ta isheni


Nuna kanta ta shiga yi tana cewa momcy yau ni kika juyawa baya dan ta shigo da abin duniya duk irin abin da nake kawo miki


a'a jalila yanzu ba wannan maganar ake ba ku duka haifar ku nayi to ba wanda zan ware nace bana so i dan fadar gaskiya ta tashi zan faɗa muku ato


naja ce tayi dariya tare da juya duwawu tace '' momcy manta da ita ga wannan yace na kawo miki..,


da sauri ta saka hannu zata amsa jalila ta warce buge hannunta tayi ta amsa tana cewa wallahi ki, kiyayeni jalila ni sa'ar wasan ki ce


batare da tace komai ba ta shiga daki dariya naja tayi tana cire mayafinta akan igiya ta rataye ta shiga bayi


Sumy ce ta shigo ba ko sallama da alama a buge take zama tayi a kasa yawa yar bori ta miƙe ƙafafuwan ta jakarta ta jefar kanta na mata wani irin juyawa da kyar ta kawo kanta gida wayar tace tayi ringing bude jakarta tayi ta dauko ba tare da ta daga ba ta kara a kunne tace


'' hello ka-na-ji-na ta fada a rarrabe ajiye wayar tayi Gaddafi ne yace


''tab yau kinsha wacc tafi ƙarfin kanki...,


wara hannu wanta tayi ta yi a lamar uku da yatsun hannunta dakyar ta iya cewa


kwalba uku nasha nayi tatul


naja ce ta fito tace


'' badai kamru uwar laifi kika sha ba...?,


ita na sha wani abu ne


tab tsoho ya haifi wacce tafi ƙarfin sa dan Allah lokacin ku momcy tsoho yasha giya...?,


tab ai besha ba iya kacin sa taba daga baya ma tun kafin muyi aure ya dena


to yau gashi ya haifi wacce ta fi karfinsa wai dan Allah momcy a haka kika yadda kika aure tsoho


dariya tayi tana gyara zaman rigarta tace


'' ke nima gagara nayi mahaifina ya bashi ni na san kuma ɗan dabane mene abin gudu a dan daba wallahi ina sane na aure shi...kuma ina son kayana


wani ihu su Gaddafi suka saki suna mata kirarin da suka saba yi mata cau cau cau uwar gafalallu dan iska naki ban da dan banza dan kirki me tsinuwar iyaye shi ne babban shedani na hannun daman ki an buga dake an barki maƙiyan ki fadawanki dubu jiran dubu bilahillazi ba me taddo ki cau cau ki yi taki kinyi ta wasu bata kare miki ba


Sai ma gaba da kikai ke ce uwar da zamu ɗauko magana ki shige mana gaba a fito damu


ya isa haka yanzu haka sumy salon ki saka a dinga zagina a unguwar nan shi ne kika tawo a haka haba sumayya so kuke baƙin mutane ya durarmin


dakyar ta iya tashi tana haɗa hanya komai da ta shigo dashi anan ta bar shi tana zuwa daki ta kwanta a ƙasa matsawa mufeeda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login